IMAANI

Chapter Seventeen

by @suttie0

Safiyar Saturday Imaani ta tashi with a nervous feeling, lafiya ƙalau ta kwanta bayan sunsha soyayya da Nurain ɗinta daren jiya, wanda ke Lagos har yanzu. 

Throughout that morning she couldn't shake the feeling, haka ta gabatar da al'amuranta tayi tidying ɗakinta ta gyara closet. 

Da weekends dama Abbu privately yake breakfast shida Ammi a sama, sometimes suyi joining ɗinsu suci abinci tare. 

Imaani ta nufi section ɗinshi da kayan baccinta off-white cotton top and long bottoms, a dining ta sameshi yana bama ƴar lelenshi Shukrah abinci. Gaisheshi ta ƙarayi bayan wanda sukeyi da asuba, Abbu ya amsa yasa ta ɗebi abinci ta zauna taci.

Black Assam tea ne with golden yam, plantain and scrambled eggs aka kawo daga kitchen ɗin ƙasa. Ta zauna ta ɗiba daidai cikinta ta fara ci, nan Asma'u ta samesu tayi joining ɗinsu har suka kammala.

Bayan sun gama sukayi clearing wurin, Abbu ya shiga home office ɗinshi Shukrah na biye dashi. Imaani kuma tashiga ɗakin Abbu da niyyar gyarawa tasamu har ya gyara ɗakin, ko ina yayi neat. Dama Ammi ke kula da part ɗinshi, idan bata nan kuma su sukeyi.

Bayinshi ta shiga ta wanke ta fito. Ta kunna mishi turarenwutan Kajiji na Gidan Ƙamshi by Suttie tasa a closet for some minutes sai ta fito dashi. 

Ta ɗan jira ya kama ɗakin kafin ta ƙara turaren ta fito da kaskon parlour dan ya kore ƙarnin ƙwai da suka ci. Ta ajiye kaskon a dining table sai ta shiga Kitchen, nan taga Asma'u ta gyara ta killace leftovers a kwanukan da aka kawo abincin, tasa utensils a dishwasher yana cikin wankewa bai gama ba saboda akwai yawa kwanukan.

Asma'un ta shigo tace, “Abbu yana kiranki.” Imaani ta amsata ta barta a Kitchen ɗin. 

A cikin office ta sameshi shi kaɗai ba Shukrah yana desk ɗinshi yana duba computer, tace, “Abbu gani.”

Abbu ya ɗaga kai ya kalleta tana jingine da babban desk ɗin, yayi mata wani wistful smile da ta mayar mishi confusedly. A ranshi yace shikenan fa girma yazo, nan bada jimawa ba ƴaƴanshi zasu fara barin gidan.

Yayi clearing throat ɗinshi to clear the emotions that suddenly got stuck there, “Zanyi baƙi anjima, a faɗa ma Baaba ta shirya musu abinci.”

Curiously ta kalleshi cikin neman ƙarin bayani amma bai ce mata komai ba. Tace, “Okay zan faɗa mata. Abbu I think I'll be going out after Zuhr to get some personal supplies.”

Abbu ya girgiza kai yace, “Not today ki bari sai gobe.”

Bata kawo komai ba illa ko saboda Ammi bata nan shiyasa yace tazauna tunda zaiyi baƙi, kuma ƙila Asma'u ta rigata tambayan izinin fita. It does make sense for one of them to be at home. Tace, “Okay bari na faɗa mata.”

Imaani ta sauka ƙasa ta isar da saƙon Abbu zuwa Baaba Salame, wacce ke kitchen tanata hidimar ɗora abincin rana. 

Baaba tace, “Dama tuwon garin shinkafa zan ɗaura da miyar kuɓewa sai farfesun kazar hausa, ko kina ganin a ɗaura wani abu daban?”

Imaani tace, “A'a tuwon yayi, zan ƙara da farfesun kayan ciki sai ayi zoɓo idan babu.”

“Akwai zoɓon ma jiya nasa yarinyar nan Ƙarama tayi da yawa wanda zai isa zuwa litinin idan Allah Ya kaimu. Saidai ko idan abokin mai gidana yazo, shi yake sha sosai shiyasa yanzu nake sa a ɗora wani da zaran ya ƙare.”

Imaani ta kalli Baaba Salame, “Wani aboki kuma?” Sanin Rafeeq take kira da mai gidanta.

Baaba tace, “Wannan ɗan fulanin mai cikar gashi mana dayazo yayi hijira kwanakin baya ya tafi. Kinsan yakan shigo ran Jumma'a da daddare ko Asabar da rana, sai mai gidan yasa akawo mishi zoɓo mai sanyi sashenshi, harma na ƙara mishi da wanda zai tafi dashi idan zai koma gida.”

Imaani ta ɗaga kafaɗarta tace, “Indai akwai kuma zai isa ai shikenan.” Ta buɗe babban industrial fridge dake kitchen ɗin ta fara ciro ziplock bags da ake storing kayan ciki bayan an gyarasu. 

A ranta kuwa tace akwai wani abokin Rafeeq da Baaba tayi describing wanda daya wuce Sameer ne, tayi addu'ar Allah Yasa bazasu taɓa haɗuwa ba har yazo ya tafi kafin yayi mata wani sharrin. 

Dama ta kwana biyu bata ganshi ba tun sanda suka haɗu a bikin gidansu. Wani kinibibi zaisa ya taso tun daga gidansu yazo har nan wai shan zoɓo in banda san banza, toh gashinan abincin ma akwai, idan yaso yayita zuwa yana ci.

Tayi wondering ko Sameer ɗin ya koyi zubama kanshi abinci yanzu koh abokinshi ke zuba mishi kafin yaci. Ɗan tsaki tayi ta fara gabatar da aikin gabanta.

Bayan Zuhr ta kusa kammala komai, sai alla alla takeyi tagama kafin baƙin suzo. Da Abbu ya faɗa mata da wuri da ta gama tuntuni. 

Baaba Salame ta kori Imaani taje tayi wanka, tai ta mata tsiya wai rana tayi har anyi azahar da kayan baccin jiya a jikinta. Bata bari Imaani tayi dishing pepper soup ɗin ba ta korata, Baabar tace dakanta zata sa a casserole dishes ta ajiye inda aka jera sauran abincin.

Around 2:00 PM wani sleek Mercedes-Benz ya shigo gidan, dama Rafeeq ya tura mishi address ɗinsu dukda yayi tunanin yasani because how else did he know where to send those flowers he sent if he didn't know.

Rafeeq dakanshi yayi recieving ɗinsu a parking lot, su biyu sukazo. Ya shigo dasu guest parlour a ƙasa. 

Sanye yake da light ash shadda da hular ƙube akai fuskarshi ɗauke da murmushi. Rafeeq ya ɗan zauna dasu suka gaisa sukayi conversing lightly kafin ya tashi yaje ya kira Abbu.

Bayan tafiyar Rafeeq, abokinshi yace, “Guy kar fa ace za'a ɗaura aure yau ɗinnan, kazo da sadakinka koh before you shame us both.” 

Zunnurain yayi mishi ƙaramin tsaki, “Bafa neman aure zamuyi ba, izinin zuwa zance zamu tambaya kafin mudawo mu tambayi mai gaba ɗayan.” Ya saki wani lallausan murmushi yana hango ranan a idanunshi.

Dariya abokin yayi mishi suka cigaba da magana, ba jimawa aka buɗe sliding doors dake leading zuwa cikin gidan. Su biyu suka shigo dukkansu masu haske sosai da kamanni irin na Fulani, ɗaya older version ɗin wanda ya shigo dasu ciki. 

Miƙewa Zunnurain yayi shi da abokinshi har Abbu ya ƙaraso ya basu hannu kafin su zazzauna.

Abbu ya zauna yace, “Da fatan kun iso lafiya? Ya mahaifin naka mun kwana biyu bamu haɗu ba.”

Humbly Zunnurain yace “Alhamdulillah, yana nan lafiya Abbu.”

Abbu ya ɗaga girarshi ɗaya jin sunan da ya kirashi kai tsaye. Ya juya gun abokin, da raha yace, “Kaima kazo taya shi tambaya ne ko dan ku cikamin ido ne?”

Abokin yayi murmushi yace, “A’a ba haka bane Abbu.”

Abbu ma yayi murmushi yace, “I too was once a young man, yaya sunanka?”

Abokin yace, “Sunana Uthman Maifata.”

Abbu yace, “Ɗan gidan Auwal Maifatan da na sani dai.”

Uthman yayi nodding yace, “Eh shi ɗinne.”

Collectively Abbu yace musu, “Sannunku da zuwa, me ke tafe daku?”

Shuru sukayi suka kasa magana, Zunnurain ya ɗan taɓa Uthman jin bakinshi yau yayi nauyi duk surutunshi kuwa.

Abbu na kallonsu yana dariya aciki, shi da aka kira yazo yanzu kuma an kasa magana. Yace, “Ina jinku, kai aboki gafa inda zaka yi aiki.”

Ɗan dariya Uthman yayi yace, “Dama munaso mu fara zuwa zance ne shine mukace zamu fara zuwa muganku, kuma asan da mu.”

Abbu yayi inclining kanshi, “Kunyi daidai abinda ya kamata kenan. Toh wurin wa zaku zo zancen?”

Sai sannan Zunnurain yace, “Wurin Imaani ne.”

Abbu ya kalleshi sai ya juya yacema Rafeeq, “Sai yanzu mutuminka ya magantu.”

Sukayi mishi dariya, nan Abbu ya tambayeshi yanda suka haɗu da juna.

Masu aiki suka shigo da refreshments da Rafeeq yace akawo ɗazu kafin ya kira Abbu. 

Zunnurain ya fara ma Abbu bayani, tun daga ranar da ya fara ganinta a Dadan-Garba Chambers, co-incidental haɗuwarsu a makarantarsu sai kuma a restaurant ɗinta kafin ya tafi Tanzania, zuwa yanzu da ya dawo yazo gidan. 

Mamaki ya kama Abbu jin ashe sun haɗu ranar da mahaifin Zunnurain ya aiko shi office da wasu documents. Abbu ya cigaba da yi mishi tambayoyi yana auna amsoshin against wanda yake dashi already. 

Ya tambayi Uthman idan shi yanada aure, Uthman ya duƙar da kai kafin yace bai dashi. Abbu yayi murmushi, duk tarin tuzurai ne ashe.

Daga bisanni Abbu ya gyara zama yace, “Naji me kazo dashi ni kuma yanzu zan bada nawa sharuɗɗan.” Yayi shuru for some moments kafin ya cigaba, “Boɗɗo dai bani na haifeta ba amma nine ubanta wanda shari'a ya bata halak malak. Bata da bambanci a wurina da Rafeeq dake zaune a nan. Bana ɗaukan al'amuranta da sauƙi ko kaɗan, ita kaɗai ce cikin ƴaƴana ta tashi babu ɗumin uba kusa da ita kafin Allah Ya ƙaddara saduwanmu da mahaifiyarta.”

Duk suka natsu suna sauraron Abbu.

“Yanda kazo min cikin girmamawa ina fatan haka zaka nema amincewar ta, nima kuma zan dubeka da wannan girman. Idan Allah Yayi Imaani rabonka ce falillaHil hamd, idan ba rabonka bace ina fatan zaku rabu cikin aminci kamar yanza ka shigo rayuwarta cikin aminci.”

A tare abokan sukace “In Sha Allah za'a kiyaye Abbu.”

Abbu yace, “To yayi,” ya cema Rafeeq, “Je ka kiramin ita.”

Rafeeq ya tashi ya nufi ƙofar fita Abbu ya jasu wani hirar daban. A hanya Rafeeq yaga Shukrah da Halita mai kula da ita ta sata a gaba tana cin abinci. 

Yayi knocking ƙofar ɗakin Imaani bayan ya haura sama. Imaani ta amsashi daga ciki kafin ya buɗe ya shiga.

Tana zaune a armchair tana karanta wani paperback novel, she was deeply invested in the fantasy novel kafin shigowan Hammanta ya katseta. Tunda tayi wanka ta shirya cikin atamfar Vlisco riga da skirt ɗinkin maiduguri style, tayi simple kwalliyar da takeyi a gida da casual ɗaurin ɗankwali. 

Rafeeq yace, “Wannan kwalliyar fa Boɗɗo duk shi akai mawa?”

Imaani taɗan bude ido, “Kwalliya kuma Hamma? Wa zanyi ma kwalliya, atamfa ce fa kawai nace zansa yau saboda na daɗe bansa ba.”

Rafeeq ya jijjiga kanshi bata san wasu baƙi akayi ba kenan. “Sa mayafinki kizo Abbu na kira a ƙasa.”

Da mamaki tace, “Toh.” Kafin ta shiga closet da ɗauko gyale ta yafa a kanta, sai tabi bayan Rafeeq daya fita.

Yana gabanta suka sauko ƙasa, Ƙarama ta fito daga guest parlour.n bayan sun gama kai musu abinci apart from the snacks they brought in earlier. 

Suna shiga Zunnurain ya ɗaga kanshi suka haɗa ido da Imaani.

Cak ta tsaya tana kallonshi in shock, anya kuwa tagani da kyau?

Murmushi yayi mata kafin ya duƙar da kanshi ƙasa.

Abbu yayi dariya, da fillanci yace mata, “A rufe bakin mana.”

Sai sannan ta dawo hayyacinta. Rufe fuskarta tayi da veil ɗinta cike da kunya taje ta zauna bakin ƙafan Abbu. 

Yana dariya teasingly yace, “Boɗɗo dama haka kike?”

Ta girgiza kanta while laughing at herself. 

Yace, “Na kiraki ne na tambayeki idan kinsanshi, yanzu na samu ansana. Yazo ya nemi izinin fara zuwa wurinki kuma na bashi dama. Zanja hankalinku da ku kiyaye kanku kada ku taka iyakoki da addini ya shimfiɗa, idan kun fahimci juna don't waste any more time and move your relationship further unto the next step. Allah Ya bada sa'a.”

Suka amsa da ameen kafin Abbu yace su tabbata sunci abinci kafin su wuce, sai ya tashi ya basu wuri Rafeeq ma yabi bayanshi.

***

Halal love is sweet 😇