Chapter 11
╔══════════════════════╗
🌹 *WASAN ƘADDARA* 🌹
╚══════════════════════╝
_A Story of Love, Pain and Destiny. That Even Fate Cannot Escape_
> ✍️ BY ASMEETAH WRITER
━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━
🏆 JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION
🌟 Under:
THE SHIDORIA WRITERS TEAM
━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━
📞 ***
📚 BOOK 1
📖 CHAPTER ___21 and 22
━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━
Wasu soyayyar ƙaddara ce ke haɗata...
Wasu kuma ƙaddara ce ke raba su...
Amma me zai faru idan zuciya ta ƙi amincewa da hukuncin ƙaddara?
━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━
Washegari da safe, Zaitun ta fito sanye da doguwar riga marar nauyi, fuskarta a murtuƙe. Ta sami Chief a teburin cin abinci, ta gyara tsayuwarta bayan ta gaishe shi ta ce,
"Dad, zan je unguwar su yarinyar nan na ba su haƙuri, domin inaso komawa ɗakin mijina."
Chief ya ɗago ya kalleta, fuskar nan tasa ta bayyana tsananin gamsuwa da farin ciki.. Ya ajiye kofin shayin hannunsa,
"Yauwa Zaitun Baba, haka nake son ji... Hakan shi ne mutunci. Amma kiyi hattara, kada ki kuskura ki ɗauki waɗancan ƙawayen naki marasa ji ku tafi tare, domin su ba abokan arziki ba ne, tura ki rami kawai suke yi. Ki tafi ke kaɗai cikin kwanciyar hankali."
Zaitun ba tare da ta ce uffan ba, ta juya ta fice. Cikin motarta ta zauna ta ɗauki tsayin lokaci tana bincike a intanet, ta dinga bin labaran da aka ta yaɗawa a shafukan sada zumunta ranar da abun ya faru, har ta dace ta gano asalin sunan unguwar da Amira take, wato kuryar Rigasa..
Da ƙyar da tambaya, cikin layuka matsatsu masu cike da datti da kwata, Zaitun ta karkata motarta har ta gano daidai ƙofar gidan su Amira.. Ta danna wa motar birki ta faka..
Tsayuwar katuwar motar alfarma a wannan matsiyacin layin ya sa nan da nan mutanen unguwa, musamman mata da matasa masu wucewa, suka tsaya suna tsegumi da jifanta da kallo, kowa na son ganin wace ce ta zo gidan Malam shehu. Zaitun ganin ana kallonta ya sa ta turo kofofin motar ta fito da sauri, ta gilce ta shige cikin gidan domin ba ta son kowa ya gane fuskarta a wannan gurin na ƙasƙanci...
Tana shiga tsakar gidan da sauri, ta yi sallama, sannan ta tsaya tana bin gidan da kallo. Ta dinga kallon tsofaffin katanga, rariya dake wari, da kofofin langa-langa, gidan gaba ɗaya babu wani tsari...
Khadijah ce ta fito daga ɗaki tana amsa sallamar, ta tsaya tana kallon Zaitun ta ce,
"Sannu da zuwa."
Zaitun ta yi fari da ido, ta yatsina fuska ta ce, "Yauwa... Ina kajin gidan?"
Khadijah ta ɗaure fuska, ta soma waige-waige a tsakar gidan, "Mu bamu da kaji a gidan nan."
Zaitun ta taɓe baki, "Ina nufin mutanen gidan"
Khadijah ta zurfafa kallonta sannan ta gyara tsayuwarta cikin tsiwa ta ce,
"Aww... sai yanzu kika dawo kan hanya? Domin ba yadda za'a yi mutum mai hankali ya haɗa dabba da mutane a magana."
Zaitun, ta daka mata tsawa da faɗin,
"Ke dallah kiyi min shiru. Kina nan kwaila dake zaki tsaya kina faɗa min maganar banza?"
A daidai lokacin, Amira ta fito daga ɗaki tana riƙe da ƙaramin littafin addu'o'in nan da dattijon ya ba ta, tana dubawa...
Jin tsawar da aka daka wa ƙanwarta ya sa ta fito da sauri tana kallon abin da ke faruwa.
Ganin Amira bai sa Khadijah ta yi shiru ba, ta sake duban Zaitun,
"Baiwar Allah, duk da dai ban san ki ba, ban taɓa ganin ki ba, ban kuma san me ya kawo ki gidanmu ba, amma da dukkan alamu ba ƙalau kika zo nema ba. To bari kiji, ina daidai dake wallahi"
Zaitun ta kauda idonta daga kan Khadijah, ta kafa wa Amira kallo, ta ce,
"Ba dake nake yi ba kwaila....Da wancan nazo yin magana... kuma wannan shi ne gargaɗi na ƙarshe."
Khadijah ta tare gaban Amira, "To pah... Kin manta ne baiwar Allah? Ai idan kika yi da ita, tamkar kinyi da ni ne..."
A lokacin a gidan babu kowa, Uma ta fita tun asuba gidan mutuwa, Malam ya fita, Kaka ma ba ta nan, sauran yaran kuma duk sun tafi ɗibar ruwan fanfo. Sai Amira da Khadijah kawai ke gidan..
Zaitun ta nuna Amira da yatsa, ta ce,
"Ke kuma... ance nazo na baki haƙuri, kuma na yarda na zo ɗin...Amma ki sani a cikin zuciyata, na fi ƙarfin na buɗe baki na baki haƙuri keee... Ni Zaitun, ina mai ƙara gargaɗinki da cewa zan yi maganinki muddin zuwa nan da sati guda ban koma gidan mijina ba, duk kece silar komai, kika wargaza min lissafin rayuwata, kika tarwatsa min farin cikin gidan miji.. Kika haɗa ni da mijina, to wallahi zan yi maganin ki.."
Khadijah ta kalli Amira, ta jinjina kai,
"Ohhh... sai yanzu na fahimta. Kenan wannan matar ce wacce ta ci mutuncinki a makaranta a kan miji?" Ta dawo da kallonta kan Zaitun, "Na ji sai cewa kike zaki yi maganinta. Shin baki da ta cewa ne sai wannan kalmar? Ki fara maganin kanki tukunna domin ke kike buƙatar hakan.."
Zaitun ta watsa wa Khadijah harara, ta sake kallon Amira,
"Na yi bincike, na gano cewa ke da mijina ba ku da wata alaƙa, bai ma san ki ba... Haba, ni kaina na yi mamaki, domin mata irinku a matsayin almajirai yake ɗaukan ku, wayayyu ma bai tsaya ya kalla ba bare ku kucakai, ƴaƴan matsiyata"
Wannan kalmar ta ƙona wa Khadijah rai, ta fusata ta ce,
"Ke baiwar Allah, me kike faɗi ne?! Wa ya gaya miki mijinki da ita ba su da alaƙa? To bari kiji kije ki sake bincike da kyau, domin shekaranjiya ma ya zo har ƙofar gidan nan gurin Amira, har ya bamu kyautar miliyan goma..."
Zaitun ta ja dogon tsaki tana musu kallon ƙasƙanci ta ce,
"To don ya baku miliyan goma sai me? Ya ɗauke ku ne a matsayin kaji a gidan gona ya zuba maku abinci saboda tausayi, ya dubi matsiyacin halin da kuke ciki (ta kalli gidan ta harare shi). Sannan ba a kanku kaɗai ya fara ba, dama shi can ya saba waɗannan kananan taimakon. Miliyan goma kuwa ni ban ɗauke shi a matsayin kuɗi ba, shi nake bayarwa a yanke min farce..."
Khadijah ta tintsire da dariya tare da faɗin,
"Aww... na ɗauka kuɗin yankan farcen naki zai iya kaiwa irin miliyan ɗari, ashe a goma kika tsaya ƴar gidan Ƙaruna, jinin Fir'auna..."
Zaitun ta cika ta yi fam, ta nuna Khadijah, "Keee...!"
Khadijah ta tare ta da faɗin,
"Laaa... shiru kar kiyi fushi... Ɗan jira ni maza."
Cikin zafin nama Khadijah ta juya ta ruga cikin ɗakinsu da gudu. Ta tafi daidai gurin da Amira ta ɓoye takardar Doctor Arman jiya, domin dama tana kallo sanda Amira ke ɓoyewa. Ta ɗauko takardar ta fito da gudu, ta ƙaraso gaban Zaitun ta liƙa takardar daidai saitin hancinta...
Zaitun ta buge hannun Khadijah cikin fushi, amma a daidai lokacin da takardar ta gito ta hancinta, wani daddaɗan ƙamshi ya dake ta...
Khadijah ta ce, "Na san dai kin san wannan ƙamshin ko?" Ta buɗe wasiƙar ta nuna mata rubutun,
"Kuma na san kin san wannan rubutun ko... Ba sai na tsaya karanta miki abin da ke ciki ba, domin abin da ya rubuto sirri ne na masoya, bai kamata ke kiji ba..."
Nan take jikin Zaitun ya soma ɓari. Hawaye masu zafi suka fara gangarowa a fuskarta, ta fizge takardar daga hannun Khadijah ta matsa ta kusa da hancinta tana kuka,
"Wannan... wannan ƙamshin turarensa ne...!"
Khadijah ta ƙara zuga ta da faɗin,
"Ƙamshin turare na musamman ko?"
Zaitun cikin muryar kuka ta ce, "Ba ko wani namiji ne yake amfani da wannan turaren ba..."
Khadijah ta ce, "To kin gani kuwa... Abun ya tabbata, alaƙa mai ƙarfi da soyayya ta shiga tsakanin mijinki da ƴar uwata.."
Zaitun tana ƙoƙarin buɗe takardar cikin kuka, "Zan karanta... zan ga me ya rubuto maki"
Khadijah ta yi saurin fizge takardar daga hannunta, ta ce,
"Ba za ki karanta ba...Domin wanda ya rubuta shi ya san dalilin da ya sa ya rubuta don Amira kawai."
Zaitun ta fashe da wani marayan kuka mai sauti, ta dafe kanta,
"Ni... me na rasa a jikina da zai nemi wata mace daban?"
Khadijah ta ce, "Babu abin da kika rasa ƴar uwa... Kina da kyau, kina da ilimi, kina da kuɗi, kuma kina tare da miji na musamman. Amma sai dai abu ɗaya kacal kika rasa a rayuwarki."
Zaitun ta ɗago da jajayen idanuwanta cikin rashin fahimta, "Me kenan?"
Khadijah ta dube ta sannan ta ce,
"Hankali, Kin rasa hankali... tabbas ƙwaƙwalwarki ta samu matsala gaba ɗaya.."
Jin waɗannan kalaman a daidai lokacin da take cikin tsananin fushi da tashin hankali ya sa idanuwan Zaitun suka ƙara kaɗawa suka yi jawur. Zuciyarta ta soma yin wani irin bugun. Cikin matsanancin zafi, ta dafe saitin zuciyarta, numfashinta ya ɗauke cak na wasu daƙiƙu, nan take wani ɗan jini ya tsiyayo ta fatar bakinta saboda asalin matsalar lafiyar zuciya dake damunta tun fil azal.
Jiri mai ƙarfi ya kwashe ta, ta soma karkata zata faɗi, Amira dake tsaye tana kallon ikon Allah ta rugo da gudu ta riƙe ta, ta rungume ta a jikinta tana kuka cikin firgici,
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'unnn...!"
Zaitun tana gani dishi-dishi, idanuwanta na shirin rufewa, da ƙyar ta tattaro sauran ƙarfin dake jikinta ta janye jikinta daga na Amira, ta dafe bango ta soma takawa a hankali tana dingishi tana neman hanyar fita waje.
Amira ta juyo kan Khadijah cikin fushi, "Muje mu taimaka mata mana"
Khadijah ta ce, "Wallahi ba zan je ko'ina ba. Ita da ta zo tana ƙiran mu da kaji a gidanmu?"
Amira ba ta jira ba, ta bi bayan Zaitun da gudu. A zauren gidan ta tarar da ita ta mannu da jikin bango, ta ɗaga kanta tana kallon sama, numfashinta na fita da kyar, hannunta ɗaya yana kan ƙirjinta...
Amira ta kama hannunta tare da faɗin,
"Aunty, anya zaki iya tafiya kuwa a haka?"
Zaitun ba ta da ikon hanawa, Amira ta riƙe ta ta soma fito da ita waje.
Da ƙyar Zaitun ta buɗe ƙofar motarta ta faɗa kan kujerar direba.
Amira ta tsaya a jikin ƙofar tana faɗin, "Ki tsaya Aunty, azo a kaiki asibiti ko gida, ba za ki iya tuƙi a wannan yanayin ba."
Zaitun ta juyo da jajayen idanuwanta dake fitar da hawaye, ta watsa wa Amira wani irin kallo mai ban tsoro, ga ɗan jinin nan yana jikin leɓen bakinta. Da ƙyar ta buɗe baki muryarta na rawa ta ce,
"Har... har kin fara ƙirana da Aunty... tun kafin ma ya ce zai aure ki?"
Amira ta buga ƙafarta a ƙasa ta yarfe hannunta cikin tsananin takaici da gajiyar jin wannan maganar da ba ta san tushenta ba, kuma tana tsoron kar mutanen unguwa su taru...
Zaitun ta ci gaba da cewa, "Kar ki damu... zan iya control kaina. Zan kai kaina gida."
Tana maganar tana lumshe idanuwanta alamar jiri na neman kwashe ta..
Amira ta ce, "A'a! Ba zan bar ki ki tafi ke kaɗai ba.." Ba tare da ɓata lokaci ba, ta zagaya ta buɗe ɗayan ɓangaren kujerar gaba ta shige ta zauna..
Zaitun dake cikin raunin jiki ta tada motar ta danna ribas ta fito, ba ta da wani ƙarfin da zai ba ta damar yin magana balle ta kora Amira daga motar...
Khadijah ta fito da gudu kofar gida tana ɗaga hannu,
"Ina kuma zaki bita ku tafi Aunty Amee?!"
Mota ta bar layin. Tafiyar ba ta da wani tabbas, domin duk lokacin da motar ta zo karkata sai Amira ta sa hannu biyu ta fige sitiyarin ta saita ta, duk da cewa ita kanta Amira ba ta iya tuƙi ba...
Haka suka dinga faɗi-tashi har suka fito babban titin kwalta. Amira duk hankalinta yana kan Zaitun dake faman lumshe idanuwanta, tana tuƙi tana tangal-tangal...
Amira tana zaune tana kallon abubuwan dake faruwa, zuciyarta ta cika da tambayoyi, ta soma magana a ranta,
"Me yasa kowa yake haɗa ni da mutumin nan? Ni fa ban taɓa ganinsa ba a zahiri, ban san dalilin wannan rikicin da ya addabi rayuwata ba"
A daidai wannan daƙiƙar, bugun zuciyar Zaitun ya tsananta sosai ta yadda ba ta iya jurewa. Lokaci guda ta saki sitiyarin ta suma..
Motar ta sauƙa daga kan titi ta ɗauki wani layi da gudu. Wani irin ihu Amira ta fasa mai ban tsoro, ta ɗora hannayenta guda biyu a kan sitiyarin. Motar tana gudu, Amira ba ta san yadda ake taka birki ba ko yadda ake control na mota.. Ta dinga fige sitiyarin hagu da dama tana ƙoƙarin kauce wa bishiyoyi, da haka tayi mugun ƙoƙari wurin dawo da motar kan kwaltar...
Duk wata mota dake tafe a gaba da suka zo wucewa, sai dai direban ya kauce musu da sauri..
Aka zo daidai wani kwana Amira ba ta san yadda ake juyawa ba, sai ihu take yi tana kuka tana jero duk addu'ar da ta zo bakinta...Motar ta sake sauƙa daga kan titi ta nufi sashen shagunan dake gefen titi, mutanen gurin suka dinga gudu suna kauce wa motar cikin firgici...
Wani irin uban ƙugi aka ji sanda motar ta bugi jikin wani babban shago da ƙarfi. Gaban motar ya lalace, gilasan gaba suka fashe da ƙarfi.
Sakamakon karfin dukan, Amira ta tafi da gudu ta buga goshinta a kan sitiyarin motar. Ita kuma Zaitun, saboda ba ta saka banti ba, ta zame ta faɗo ƙasan dashbodi ta matse ta tsakanin kafafun kujerun gaba, ba ta numfashi ko kaɗan..
Cikin hanzari da gaggawa mutane suka taru a gurin da hatsarin ya faru. Ganinsu jina-jina ya sa hankalin kowa ya tashi. Cikin sa'a, da yawa daga cikin masu wucewa sun gane motar da kuma fuskar Zaitun a matsayin matar shahararren likitan nan Doctor Arman. Hakan ya sa aka fito da su da sauri, aka shigar da Amira da Zaitun a wani motar aka nufi asibiti da su...
Kafin ma su ƙarasa isa, Amira ta farfaɗo a cikin motar da suke. Duk da cewa goshinta ya fashe jini na ta tsiyaya a fuskarta, sam ba ta damu da kanta ba, hankalinta gaba ɗaya yana kan Zaitun. Tana ta faman jero addu'o'i a ranta cikin tsananin fargaba...
Suka isa babban Asibitin AYZ.
A lokacin, Doctor Arman yana zaune a ofishinsa yana duba wasu rahotanni. Ba zato ba tsammani, wani ma'aikacin asibitin ya shigo da gudu riƙe da takarda, yana haki,
"Sir! An kawo Hajiya yanzu-yanzu tayi mummunan hatsari a hanya"
Arman ya haɗe gira, bai gane wace Hajiya ba, ya ce, "Mahaifiyata?"
Yaron ya girgiza kai, "A'a sir, matarka Hajiya Zaitun ce. Kuma gaba ɗaya ba ta cikin hayyacinta."
Arman fuskarsa ba ta nuna wata girgiza ba, ya ce cikin daƙiya,
"Shin ni kaɗai ne likita a asibitin nan? Meye amfanin aikinku da ba za ku duba ta ba sai ni?"
Yaron ya dafe goshi, "Sorry sir, amma abin ya fi ƙarfin mu. Mun ga tana aman jini, matsalar ba iya hatsarin ba ne kadai, har da ciwon zuciya... Muna tunanin shi ne ya yi sanadin hatsarin."
Arman ya yi shiru, ya kalli gefen titi ta gilashin ofis ɗinsa. Ya san sarai cewa Zaitun tana da matsalar zuciya, kuma dama shi ne asalin likitan dake duba ta a gida...
Yaron ya ƙara da cewa, "Kuma sir... kasan kai ne kaɗai ƙwararren likitan zuciya a asibitin nan a halin yanzu."
Arman bai sake cewa uffan ba, ya miƙe da sauri ya fita.
Kai tsaye ɗakin gaggawa da aka kwantar da ita ya nufa. A daidai ƙofar ɗakin, Amira tana zaune a kan kujera ta dafe goshinta dake ta zubar da jini...
Ma'aikatan jinya sun zo zasu duba ta, amma fur ta ƙeƙashe ƙasa ta ƙi yarda, sai cewa take,
"Dan Allah ku ƙyaleni, a fara kula da ita tukunna, Shi ne mafi mahimmanci. Ni lafiyata ƙalau ba na jin wani ciwo."
Arman ya taho da sauri, bai ko kalli inda Amira take ba ya gilce ta ya shige cikin ɗakin. Ya saka safar hannu da face mask sannan ya shiga duba Zaitun.
Itama Amira tana zaune a waje, ta sunkuyar da kanta ta haɗe hannayenta biyu, hankalinta ya kai ƙarshe wajen tashi. Zaitun kuwa tana nan shame a kan gado ta sume, ba ta san inda kanta yake ba..
Arman ya duba ta sosai, ya binciki raunukan da ta ji na hatsarin da kuma bugun zuciyarta dake faman sarkewa...
Bayan ya kammala, ya fito daga ɗakin yana rage tsayin safar hannunsa. Amira na ganinsa ta zabura ta miƙe tsaye da sauri, ta nufi gareshi tana kallon fuskarsa dake sanye da mask, ta ce cikin hanzari,
"Likita... likita dan Allah ya jikin natan? Ina dai ba ta mutu ba ko? Don Allah kada kace ta mutu. Zamu iya shiga babban matsala idan wani abu ya same ta, domin daga gidanmu ta fito da wannan matsalar."
Arman ya tsaya cak, ya zuba wa Amira idanu ta cikin mask ɗinsa, yana ƙare mata kallo. Nan take ƙwakwalwarsa ta hango masa fuskar Amira a jikin glass ɗin motarsa sanda take maganganu tana imagining rayuwarta ta gaba da mijinta. Ya gane yarinyar...
Amira ganin ya yi shiru yana kallonta ya sa ta ce, "Likita ka yi min magana mana. Ya ita ɗin take?"
Arman bai amsa tambayarta ba, idonsa ya sauƙa a kan goshinta dake ta faman ambaliyar jini tun ɗazu amma sam ita ba ta ma sani ba saboda tsabar tashin hankali. Ba tare da ya ce komai ba, ya kama damtsen hannunta da ƙarfi, ya juyo da ita ya soma jan ta zuwa wani sashe na daban..
Amira ta shiga mutsu-mutsu tana ƙoƙarin ƙwace hannunta,
"Likita ina zaka kai ni ne? Ka sake ni. Anya kuwa kai ɗin cikakken likita ne? Ina tambayarka jikin marar lafiyar da aka kawo amma kana ƙoƙarin kaini wani guri na daban?"
Arman bai saurara mata ba, ya tura ƙofar wani ɗaki na musamman na duba raunuka, ya shigar da ita sannan ya zaunar da ita a kan gadon jinya.
Ya juya ya jawo treatment box.
Ya matso kusa da ita, ya shiga goge jinin goshinta yana duba zurfin raunin cikin natsuwa, ba tare da ya furta ko kalma ɗaya ba.
Amira ta buɗe baki zata sake yin magana, Arman ya ɗago idanuwansa ya kalle ta ta cikin mask, ya ce, "Please..." Alamar ta yi shiru ta ba shi haɗin kai. Ganin kwarjininsa da yanayin muryarsa ya sa ta tsuke bakinta ta yi shirun dole...
Cikin ƙwarewa ya wanke mata goshin, ya saka mata magani sannan ya manne shi da bandeji. Ya duba sauran hannayenta da ƙafafunta inda ta ɗan gurje ya shafa mata magani. Daga nan ya ɗauki sirinji da allura ta musamman ta kashe kwayoyin cuta na hatsari...
Amira na ganin allura ta zaro idanu cikin firgici, ta ja da baya,
"Ni fa lafiyata ƙalau... Dan Allah kada ka yi min allura... tsoronta nake yi sosai"
Arman ya matso da allurar yana ƙoƙarin yi mata, amma Amira ta dinga mutsu-mutsu taƙi tsayawa guri guda. Ya amfani da ƙarfin hannunsa ya riƙe ta sosai, amma sam ta ƙi daidaita jikinta...
Arman ya haɗe rai, ya dube ta da kyau,
"Ke, what's wrong with you?"
Muryarsa ta fito a dake, ta tsaya na ɗan lokaci. A hankali, yana riƙe da hannunta cikin dabara, ya danna mata allurar.
Amira ta ƙanƙame idanuwanta, bata san lokacin da ta cakumi gaban rigarsa ba da ƙarfi saboda zafi... Har ya gama ya cire allurar, ba ta buɗe idon ba, sai da ya kai hannu ya zamar da hannunta daga riƙon da tayi masa sannan ya ce,
"It's okay."
Tana buɗe idon ta sauƙe numfashi, ta ce, "Dan Allah doctor, ina son naje na duba marar lafiyar can, sannan na wuce gida domin na san Umana tana can hankalinta a tashe."
Arman ya zura hannayensa a aljihun rigarsa, ya ce, "Shin kin san matar da aka kwantar ne?"
Amira ta jinjina kai, "Ban san ta ba gaskiya. Kawai dai ta zo gidanmu ne yau da safe." Nan take ta tuna maganganun da suka yi da Khadijah, ta yi shiru ta faɗa dogon tunani...
Arman ya sake tambayarta, "Ta je gidanku yin meye kuma bayan kin ce ba ki san ta ba?"
Amira ta ɗago kai ta kalle shi ta cikin mask ɗinsa, ta taɓe baki cikin tsiwa saboda har yanzu tana jin haushin allurar da ya yi mata, ta ce,
"To kai likita ina ruwanka? Wannan ai abin da ya shafe ni ne na sirri...Kai ceto rai ne babban aikinka, ba jin gulma ba" Ta ƙarasa maganar tana kauda kanta gefe guda, tana gatsine da gunguni ƙasa-ƙasa yadda ba zai ji ba...
Arman ya tsaya ya ƙare mata kallo na wasu daƙiƙu, ya gano cewa yarinyar tana da tsiwa da kafiya... Ya gyara tsayuwarsa ya ce,
"Ok, zaki iya tafiya."
Amira ba ta jira a sake yi mata magana ba, ta zabura ta fice daga ɗakin da gudu.
Ta koma daidai ɗakin da Zaitun take, ta tura ta shiga. Har yanzu Zaitun ba ta farfaɗo ba, tana nan da na'urori. Amira ta ƙaraso ta zauna a bakin gadon, ta kalli fuskar Zaitun ta ce ƙasa-ƙasa,
"Abin da kike tunani sam ba haka yake ba... Ni ba ni da wata alaƙa ko kaɗan da mijinki."
Ba ta gama rufe bakinta ba, sai ga Chief ya tura ƙofar ɗakin ya shigo da hanzarinsa, fuskarsa cike da tashin hankali, tare da Doctor Arman dake biye da shi a baya. Ganin manyan mutane ya sa Amira ta miƙe tsaye da sauri jikinta na rawa...
Chief ya ƙaraso gaban gadon, ya kalli Zaitun sannan ya juyo kan Arman, "Ciwon zuciyar nata ne ya motsa ko? Dama na sani, domin yadda ta sa damuwa da hauka a ranta ba ci ba sha ba isasshen bacci..."
Arman dake tsaye ya ce, "An duba ta yanzu sir, babu wata matsala, an shawo kan komai."
A daidai lokacin, Chief ya juya idonsa ya kalli Amira dake tsaye a gefe. Kallo ɗaya ya yi mata, sai da ya ji wani irin bugu a tsakar zuciyarsa wanda shi kansa bai san dalilinsa ba. Ya kurawa fuskarta ido na tsayin lokaci, sannan cikin rawar murya ya ce,
"Ke... wacece ke?"
Amira ta tsaya tana in-in-da saboda tsoron kwarjininsa, "Daman... daman daga gidanmu take..."
Chief ya zaro ido cikin fahimta,
"Ohhh... kece yarinyar nan da ake ta magana a kanki? Ta je gidanku ne domin ta baku haƙuri akan abinda ta aikata miki... Amma fatan dai babu wata matsala da ta faru ko?"
Amira ta jinjina kai da sauri alamar babu.
Chief ya juyo ya kalli Arman, ya ce,
"Ni ne ma na tura ta da kaina taje ta ba su haƙuri..." Sannan ya sake dawo da kallonsa kan Amira,
"Meye silar da yasa kuka yi hatsari tare? Domin an sanar da ni cewa kuna tare da ita a cikin motar."
Amira tana murza hannunta cikin tsoro da fargaba, ta ce,
"Daman ta je ta bamu haƙuri ne... tana shirin fita sai muka ga ta fara aman jini, jiri na neman kwashe ta. Shi ne na shiga motarta akan na rako ta asibiti ko gida. Amma muna kan hanya sai ta suma..."
Chief ya gyara tsayuwarsa ya ce,
"To ke daman kin iya tuƙa motar ne?"
Amira ta sunkuyar da kai, "Ban iya ba gaskiya... hakan yasa motar ta sauƙa mukayi hatsari."
Chief cikin ɓacin rai da faɗa ya soma cewa,
"Ban da rashin hankali irin naku, zaku je ku kashe kanku a banza? Shin kun san zaku iya fita a motar nan da rai ko akasin haka? Ba kwa jin ana mutuwa a hatsarin mota ne a gari? Ita Zaitun saboda rashin hankali da ta ga ciwonta zai tashi meyasa ba ta tsaya ta ƙira waya a zo a ɗauke ta ba... Ke kuma yarinta da rashin duba ya sa ki ka shige wai zaki taya ta tuƙi alhalin baki iya ba..."
Ya ƙarasa maganar cikin takaici yana kallon Arman, "Kaji min rashin hankali da hauka irin na yaran nan ko?"
Doctor Arman bai motsa ba daga inda yake tsaye, takunkumin fuskar nan yana nan like a fuskarsa, ya zuba wa Amira idanu ta cikinsa ba tare da ya ce uffan ba....
★★★
Bayan awanni,
Chief yana zaune a kan ɗayan kujerun dake kusa da gadon da Zaitun ke kwance.. Amira kuma tana zaune a gefe, kanta a sunkuye cikin natsuwa...
Chief ya gyara zaman gilashinsa, ya kalli Amira da kyau sannan ya ce, "Ya kamata ki koma gida ƴata, tunda dare ya riga ya yi... Bari na ƙira ɗaya daga cikin ma'aikatana ya ɗauke ki a mota ya kai ki har ƙofar gida."
Amira ta ɗan kalli gadon Zaitun, sannan cikin in-ina ta ce,
"Kawu... na ga tun da muka zo asibitin nan, babu wasu ƴan uwa ko danginta da suka zo duba ta sai kai kaɗai. Ko ba su ji labari ba ne?"
Chief ya sauƙe wani numfashi, ya jinjina kansa cikin sanyin jiki tare da faɗin,
"Ita ɗin marainiya ce... Mahaifiyarta ta rasu tun tana ƙarama sosai, ba ta da kowa a duniyar nan yanzu sai ni kaɗai."
Amira ta ɗan matso kusa, "Amma... ba ta da wasu ƴan uwan ko ta ɓangaren mahaifiyarta ne, ko kuma na ɓangaren mahaifinta?"
Chief ya girgiza kai cikin nuna damuwa,
"Mummunan labari kenan yarinya... Kiyi shiru kawai shi ne alkhairi... amma dai Zaitun ba ta da kowa sai ni. Yan uwan mahaifiya ko na mahaifi duka babu su, sai dai ba za'a rasa dangin nesa can ba waɗanda basu san mu ba bamu san su ba."
Jin waɗannan kalaman ya sa idanun Amira suka cika da hawaye. Maganar Chief ta sosa mata zuciya, domin nan take ta tuna da kanta, itama tun da take a rayuwarta ba ta taɓa ganin dangin mahaifinta ba, ko jin labarinsu, haka kuma dangin mahaifiyarta duka ba ta san su ba. Sai dai kawai wani tsoho da ya kula da mahaifiyarta a baya wanda suke ƙira da Baffa, shima kuma ba wai ɗan uwansu na jini ba ne...
Nan ta ji wata irin alaƙa ta tausayi ta shiga tsakaninta da Zaitun lokaci guda...
Chief ya lura da yanayinta, ya ce,
"Ya dai yarinya? Na san kina da tausayi sosai, kuma kina da tarbiyya da hankali. Ganinki na ɗan takaitaccen lokaci ya sa kin shiga raina sosai. Ina son mutum mai matuƙar haƙuri da juriya irinki. Duk da irin mummunan abin da ƴata ta miki a baya, amma hakan bai hana ki ceto rayuwarta ba a yau."
Amira ta goge ɗan hawayen daya zubo mata, ta ce,
"Musulmi ɗan uwan musulmi ne Kawu... Ba komai don na kula da ita, ai addininmu ya koyar da mu cewa duk wanda ya yi maka sharri, sai ka saka masa da alkhairi."
Da daidai lokacin, Doctor Arman ya turo ƙofar ɗakin zai shigo, sai kalaman Amira suka tsaya masa a kunne. Ya tsaya na ɗan takaitaccen lokaci yana sauraronta bayan ya shigo...
Amira ba ta lura da shigowar kowa ba, ta ƙara tambayar Chief cikin rashin sani,
"Amma Kawu... ina mijinta yake ne? Ya kamata ace shi ne a gaba-gaba a wurin nan yanzu, amma tunda aka kawo ta ban ga alamar wani miji ya zo ba."
Chief ya dube ta, ya kasa cewa uffan, sai kawai ya yi wani ɗan murmushi mai cike da ma'ana wanda ba ta fahimci tushensa ba.
Chief ya juya ya kalli Doctor Arman dake tsaye...
Arman yana nan da mask a fuskarsa da fararen safar hannu dake like a hannunsa daman haka yake, muddin ba a cikin ofishinsa yake ba, baya taɓa cire su a gaban mutane...
Arman ya ƙaraso cikin natsuwa, ya kalli Chief ta cikin gilashin idonsa ya ce,
"Sir, ya kamata ka koma gida ka huta. Akwai kwararrun ma'aikatan jinya da na bari a nan waɗanda zasu kula da ita."
Chief ya duba agogon hannunsa, ya ce, "Eh, gaskiya ne dole zan wuce yanzu, saboda kasan yau muna da wani zama na musamman a Sector 7."
Arman ya jinjina kai, domin shima yana sane da zaman...
Chief ya nuna Amira, "To ga wannan yarinyar ma, a nemo direba ya mayar da ita gida."
Amira ta zabura da sauri ta ce,
"A'a Kawu... Ni zan kwana da ita a nan. Tun da babu wata mace ko ƴan uwa da zasu zauna da ita, ya kamata ni ɗin na tsaya na tayata jinya."
Chief ya ɗan tsaya cikin mamaki, "Amma gidanku ba zasu damu da rashinki ba a wannan daren?"
Amira ta sunkuyar da kanta ƙasa, ta tuna da Uma, ta san sarai idan ba ta dawo ba hankalinta zai tashi... Amma ganin halin da Zaitun ke ciki, sai ta daure ta ce,
"Ba damuwa Kawu, zan zauna... idan na koma gida gobe da safe zan musu bayanin abin da ya faru..."
Chief ya gamsu da karamcin Amira, ya jinjina kai cikin girmamawa...
A daidai lokacin, sai ga Ahan ya turo ƙofar ya shigo ciki. Daman Arman ne ya ƙira wayar gida, ya ce a haɗa abin taɓawa a kawo masa asibiti. Ahan ya zo ne da mota, riƙe da manyan kuloli...
Ya yi sallama, ya ƙaraso ya ajiye katon flask na ruwan tea, da na abinci, plate, kofuna, da kuma manyan ledodi cike da kayan fruits a kan teburin dakin...
Chief ya kalli kayan, ya ce cikin mamaki, "A'a Ahan, yaushe aka kawo waɗannan kuma daga ina?"
Ahan ya shafa kansa cikin rashin sani da surutu irin nasu ya ce,
"Abba, ai bamu san kuna asibiti ba. Sai ɗazu ne Yaya ya ƙira gida ya ce a hanzarta a kawo masa abinci da abin sha asibiti... Mu a zatonmu zai yi aikin dare ko zai kwana anan, ashe ashe Aunty Zaitun ce ba lafiya aka kawo ta..."
Take Arman ya watsa wa Ahan wani irin harara. Ya harare shi ne domin ya cika surutu, gashi ya bayyana sirrin cewa tun sanda aka kawo Zaitun asibitin tun rana, Arman bai sanar da kowa a gidansu ba, kuma yanzu da ya ƙira ma, don kansa ya yi akan a kawo abinci, bai faɗa musu cewa Zaitun ce a kwance ba. Arman ba ya son Chief ya ji ba daɗi a ransa ko ya zargi wani abu...
Ahan ganin hararan Yayan nasa ya tsuke baki da sauri, ya ce,
"To... Abba, ni zan koma gida yanzu."
Chief ya gyaɗa masa kai, "Kayi maza ka koma gida dare ya yi, yanzu har ƙarfe goma na dare..."
Bayan Ahan ya fice, Chief ya juyo ya kalli Amira cikin kulawa, "Ƴata, ya kamata ki ci abinci ko? Tun ɗazu kina ta faman riƙe da yunwa." Ya juyo kan Arman, "Ni zan wuce... sai mun haɗu a S7."
Arman ya jinjina kai cikin girmamawa, Chief ya juya ya fice daga ɗakin..
Bayan ficewar Chief, ɗakin ya yi tsit, sai ƙarar na'urorin dake jikin Zaitun kawai ke tashi. Arman ya matso a hankali zuwa gurin teburin. Ya buɗe kular abincin da Ahan ya kawo, ya zuba shinkafa da miya mai daɗin ƙanshi a cikin plate, ya ɗora cokali a kai, sannan ya juya ya tako daidai inda Amira take zaune...
Ya miƙa mata plate ɗin abincin gabanta. Amira ta ɗago kai ta kalle shi, ta karɓa cikin sanyin jiki ta ce, "Nagode Doctor..."
Arman bai ce uffan ba, ya nuna mata ledar fruits da kofin ruwan dake kan teburin da yatsansa ɗaya, alamar ta tabbatar ta sha idan ta gama cin abincin.
Kafin ya juya ya fita daga ɗakin, ya ƙara matso wa dab da ita. Ya ɗago da hannunsa na dama, ya gyara mata zaman bandejin dake like a kan goshinta wanda ya ɗan zame da ɗazu ta ke kokuwan allura..
A daidai wannan lokacin da jikinsa ya matso kusa da fuskarta, sannan hankalinta gaba ɗaya ya dawo jikinta, sai wani irin daddaɗan ƙamshin turare mai sanyaya rai ya daki hancinta...
Wannan ƙamshin ya kasance mai ƙarfin gaske, mai ratsa jiki da kwakwalwa. Amira ta lumshe idanuwanta biyu lokaci guda, tana shanshanar ƙamshin a cikin ranta. Can kuma, cikin ƙanƙanin daƙiƙa, wani abu ya dake ta a ƙwakwalwa...Ta tuna da wannan ƙamshin... shi ne ƙamshin turaren dake jikin takardar nan...
Da sauri ta buɗe idanuwanta duka biyu, ta zura wa likitan dake gyara mata goshi ido cikin tsananin firgici da mamaki...
★★★
Uma tana zaune a ƙasa a kan wani tsohon tabarma, ta ƙanƙame jikinta, sai kuka take yi babu kaukautawa. Idanuwanta sun yi lufu-lufu sun kumbura sun yi jajir saboda tsananin kuka. Hankalinta ya tashi fiye da yadda tunani zai iya haskawa. Zazzaɓin da yake jikinta ma tuni ya tashi saboda fargaba...
"Ina ƴata take? Wayyo Allahna... Amira! Ina kika tafi kika bar ni a cikin wannan halin?"
Uma ta shiga rera kuka tana buga hannunta a ƙasa. "An sace min ƴata... Na sani, Amira ba zata taɓa barina a wannan lokacin ba tare da ta sanar da ni ba, Dama jikina yana ba ni wani abu zai faru..."
Zuwa ƙarfe sha ɗaya na dare, babu wani labari na Amira...
A tsakar gidan kuwa, tuni Malam da Kaka suka baje nasu kolin na faɗa da tsinuwa... Suka dinga faɗin maganganu na ɓatanci wa Amira..
Kaka ta dafe ƙugunta tana zage-zage idonta na kallon sama, ban da duhu ba abinda take gani sai jaraba...
"Ai tuni na gaya muku yarinyar nan ta lalace... Wanne irin yawon banza ne wannan da za'a fita tun da safe har dare ya yi shiru babu ita? Wannan buɗewar ido har ya kai ta fara kwana a waje? Karuwan ma ai suna dawowa gida kafin sha ɗaya..."
Malam ma ya ƙara zafafa kalaman Kaka, yana faɗin,
"Wlh indai har ta kuskura ta kwana a waje yau, to ta tabbatar ta nemi wani gidan amma ba nan ba... Dama can fitsararriya ce, yau ta bayyana ainihin halinta."
Suka gama kintsa duk wani laifi suka ɗora mata, sannan suka juya kowannensu ya tafi ya kwanta abinsa bayan sun gama tsinewa yarinyar...
Zuwa jumawa Kaka har ta fara sauƙe minshari mai ƙarfi a ɗakinta, tana baccinta hankali kwance tamkar babu abin da ya faru...
Shi kuwa Malam, kafin ya shiga ɗakinsa, ya daɗe yana addabar Uma da surutu da masifa... Ya shigo har ɗakin nata ya tsaye akanta, yana cewa,
"Ke tashi mu je ki kwanta a turakata... Wanne irin hauka ne zaki zauna kina kuka a kan yarinyar da ta zaɓi ta biye wa son zuciyarta? Tashi mu je na ce miki"
Amma Uma, cikin ɓacin rai ta kalli Malam dta ce,
"Ba zan tashi ba Malam... Idan kana son barci ka tafi ka yi baccinka, amma ni ba zan bar ɗakin nan ba, ban san a wani hali ƴata ke ciki ba.."
Ganin ta kafiye ya sa Malam ya buga ƙofa ya tafi turakarsa shi ma ya yi kwanciyarsa cikin fushi..
Duk sauran yaran gidan tuni barci ya yi awon gaba da su. Yanzu gidan ya rage mutum biyu ne kawai a farke, daga Uma sai Khadija...
Khadija tana zaune a gefen gado, ta haɗe gwiwoyinta da kanta, jikinta duk ya yi sanyi.
Ta kalli Uma dake ta faman kuka a ƙasa, ta kasa cewa uffan, sai faɗuwar gaba dake ƙaruwa a cikin ƙirjinta kowane daƙiƙa.
Zuciyar Uma kuwa tana ta faman bugawa, tana matse hannunta tana kallon ƙofa, tana jiran sautin takun ƙafar Amira, a yayin da agogon bango yake ci gaba da tafiya yana nuna 12 saura, dare ya tsala sosai...