Chapter Eighteen
by @suttie0
Bayan fitarsu Abbu falon yayi shuru, Zunnurain sai kallonta yakeyi yana tasbihi a zuciyarshi. Duk ganin da yayi mata farko farkon haɗuwarsu a video calls da photos ɗinda ta turo mishi, ganinta a zahiri ya shallace su duka.
Tayi kyau abinta ta fito a bahaushiyarta sak. Kwarjininta ya ƙaru, ga kunyarta dake ƙara burgeshi. Yasan ita ɗin ba ƙaramar mace bace, koda kuɗinshi saida rabonshi, kuma ya ɗauki alwashin tunda Allah Ya haɗasu to zai yaƙi duk wani abu dazai shiga tsakaninsu, wanda zai kawo rabuwarsu indai a bakin ikonshi yake. Mutuwa kaɗai zai rabashi da Imaani, saboda wannan ikon Allah ne ba nashi ba.
Uthman yayi breaking silence ɗin da, “Sannu fa madam.”
Zunnurain ya ɗan kalleshi, yama manta basu kaɗai bane, “Wai baka fita ba dama? To me ka tsaya yi anan?”
Uthman ya jijjiga kai, “Dole kace haka ai tunda na gama yimaka anfani.”
Dariya Imaani tayi musu tace, “Ina wuni ya gida?”
Uthman yace, “Lafiya ƙalau alhamdulillah, since my friend here has no more need for me,” yayi ma Zunnurain wani kallo, “bari in barku kusha soyayya.” Ya miƙe daga zaunen da suke a carpet.
Zunnurain ya harareshi har Uthman ɗin ya fita yana dariya.
Imaani ta wani kalleshi da tuhuma a idanunta, by now yasan ma'anar duk wani kallo da zatayi mishi. Ya sauke murya yace, “Surprise surprise.”
Tayi rolling manyan idanunta tace, “Surprise indeed. I never expected this.”
Dariya yayi yace, “That's the aim Baby.”
Tayi murmushi tace, “Kadawo lafiya? Wait yaushe ma kadawo? Jiya kace min you're still in Lagos.”
“I was, yesterday evening naje Abuja. Yau nabiyo morning train zuwa Kaduna. Banyi 2 hours ba a gida Uthman yazo ya ɗaukeni muka taho nan. I told you I wouldn't waste any time before coming to see you.”
Imaani ta sauke kanta ƙasa ganin yana wani tsattsareta da idanunshi.
Nurain ya miƙe ƙafafunshi daga tanƙwashen da suke, yayi folding hannayenshi ya jingina bayanshi da kujera yana kallonta ko ƙiftawa babu.
Tace, “Zaka fara ko?”
Da muryar nan tashi innocently yace , “What? I followed all protocols dutifuly before seeing you.”
Ta ɗan harareshi tana jinta wani iri, duk confidence ɗinda takeji idan suna waya yau ya ɓace ɓat. Ta kauda zancen tace, “Ga abinci nan fa kuci.”
Ya shafa cikinshi kafin yace, “You know, tunda nayi breakfast a Abuja ban ƙara cin komai ba fa.”
Imaani ta ɗaga girarta, “Impatient much?”
Yayi mata lallausan murmushi yace, “You have no idea.”
Suka cigaba da hira which felt like they were getting to know each other all over again saboda basu saba da juna physically ba. Suna cikin magana Shukrah ta shigo tana shagwaɓa, ita bata ga Addarta ba tayita nemanta since after breakfast. Imaani tasa ta tayi gaisuwa, Zunnurain ya amsata yaganta fara sol itama kaman Abbu. Sai ya fara tsokanarta tana nonnoƙe mishi tunda bata sanshi ba.
Imaani tasashi yaci abinci, ya kira Uthman wanda ya koma mota yace yadawo suci bayan ta basu wuri, da Asr suka fito sukaje masallaci.
Bayan sun dawo Zunnurain yashigo guest parlour.n ya ganta zaune tana jiranshi. Yace mata mamanshi na nemanshi a gida, bazai samu yayima Abbu sallama ba saboda ya fita ɗazu tareda Rafeeq.
Tare suka fito waje, Imaani ta rakoshi har car pack. Ya buɗe back seat ya fara ciro wasu packages na paper bags. Da mamaki take kallonshi, zatayi mishi magana bai saurareta ba ya kira ɗaya daga cikin ma'aikatan gidan dasuke shawagi a compound ɗin ya miƙa mishi yace yakai mata cikin gidan.
Kaman bazai tafi ba, yayita janta da hira. Saida Uthman ya tuna mishi ana jiranshi fa sannan yayi mata sallama ya shiga mota suka wuce.
Imaani ta koma ciki ta tarar da packages ɗin a parlour inda yaron ya ajiye, Baaba Salame na wurin tana directing Shamsiyya tayi sama dasu takai ɗakin Imaani. Imaani tace ta ajiye parlour.n Ammi instead anan zata dubasu.
Nan Baaba ta fara tsokanarta tace ai taga saurayinta har sun gaisa daya shigo ɗazu daga masallaci. Wani dogo samɓalele dashi son kowa ƙin wanda ya rasa. Imaani ta fara jin kunya, duk abubuwan nan sabo yake zuwa mata, Baaba tayi mata fatan alkhairi, Imaani ta amsa a kunyace kafin ta hau sama.
Parlour.n Ammi ta nufa taga an ajiye packages ɗin, ta ajiye wayar hannunta ta zauna ta fara buɗesu. Chocolates ne dasu cookies, kayan ciye ciye dai da ake tsaraba dasu idan anyi tafiya, a wani bag ɗin taga turaruka guda uku masu tsada, wasu daga collection ɗinda take amfani irinsu Shumukh by The Spirit of Dubai, Baccarat Les Larmes Sacrées de Thèbes da sauransu.
Tayi mishi dropping text:
Thank you so much, this is a very pleasant gift.
I love the perfumes especially.
Immediately ya amsa:
Don't mention, anything for you my love. I knew you'd love it.
Tayi liking text ɗin bata amsashi ba, tana murmushi tana jinjina self-confidence dinshi. Camera ta shiga ta ɗauki short video.n kayan ta turama Ammi da Naseemah.
Ba ɓata lokaci ƙawarta ta buɗe chat ɗin, Naseemah batayi reply ba sai ganin call ɗinta Imaani tayi.
Rolling idanunta Imaani tayi kafin ta ɗauka, Naseemah tace, “Har yazo kenan? I thought kince bai dawo ba, girrrlllll those perfumes are mad! I made an order for them last week basu iso ba tukunna. Gaskiya I approve.”
Imaani tace, “Ni kaina bansan yadawo ba, I was reading Throne of Glass ɗazu a ɗaki Hamma ya kirani wai Abbu yana kirana, dama yace zaiyi baƙi I never thought Nurain ne zaizo.”
Excitedly Naseemah tace, “Really? I love this for you ƙawata he seems to be really serious about you. I definitely like.”
Cikin farin ciki Imaani ta cigaba da yi mata bayani, suna cikin waya call ɗin Sadiq that at this point ya mayar ibaada ya fara shigowa. Dama idan ya fara kiranta baya tsayawa sai ya ɗauka almost an hour kafin ya haƙura sai kuma gobe ya sake.
Impatiently tacema Naseemah, “Na gaji da kiran da wannan yaron yakemin I'm honestly going to report him.”
Naseemah tace, “Since he refuses to give up ki ɗauka kiji me zaice mana sai kibashi serious warning. Idan bai daina ba you can then go ahead and report him since you've blocked him several times bai gane message ɗinba.”
Imaani tayi tsaki tace, “Ni muryarshi ne banson ji, haushi yake bani wallahi. Kinganshi ne kwata kwata zubinshi baiyi ba kaman wanda baida addini fa.”
Naseemah tace, “Kedai ɗaga kiran ki arta mishi warning idan yaƙi ji sai yagani a aikace.”
Bata rufe baki ba kiranshi ya ƙara shigowa. Imaani tace, “Ina zuwa zan kiraki.”
Naseemah tace, “Okay.” Kafin ta katse wayar daga wurinta.
Saida wannan kiran daya shigo yayi yagama, wani call ɗin ya shigo ta jira ya kusa katsewa tukunna ta ɗaga.
Daga cikin wayan Sadiq yayi murmushi, yace, “Today is my lucky day it seems, bazan gaji da kiranki ba ko bazaki ɗauka ba princess amma kar zuciyata ta fashe dawa kike waya yanzu?”
Bai kamata ace audacity ɗinshi ya bata mamaki ba but she was still caught off guard, da ɗan zafi tace, “Jira kaji, na gaji da damuna da kakeyi I thought you'd get the message already but it seems you can't comprehend so I'm giving you a final warning, get out of my life before you regret ever seeing me.”
Kamar baiji me tace ba yace, “I hope ba da wani ƙato bane ko? Dan ke tawa ce ba ta wani ba, ina nan zuwa gareki nan ba da jimawa ba.”
Ranta a ɓace tace, “Idan ka isa ka hanani yin wayar.” Ta yanke kiran.
Text ɗinshi ya shigo wayarta:
Let me tell you, I win every dare princess.
You're MINE alone, see you soon.
Wani tsaki Imaani tayi, tayi blocking number.n amma batayi deleting text ɗinba ta sa kiran Naseemah. Ta kalli kayan gabanta, sai ta ɗauka chocolate ɗaya ta buɗe ta fara ci ko zataji sanyi a ranta.
Naseemah ta ɗauka kiran tace, “Ya akayi yaji warning ɗin?”
“I think it just gave the opposite effect yadda nayi tunani kwanaki, can you believe this guy was behaving like a self-entitled piece of shit? Tambaya na yayi wai da wa nake waya fa?”
Dariya Naseemah ta fashe dashi Imaani ta ƙara jin haushi, kafin ta fara mata masifa Naseemah tace, “Oh my God, the audacity is applauding! Gaskiya case ɗinshi ba karami bane, ke kuma haka Allah Ya tsara haɗuwarki na farko da guys.”
Cikin takaici Imaani tace, “Harda wani cemun see you soon so I should be preparing for his visit yake nufi?”
“Woah, now that's giving stalker-ish vibes. Although your security is tight you should better be careful Imaani, nasan bazai iya shigowa gidanku ba amma zaku iya haɗuwa idan kinfita.”
Dismissingly Imaani tace, “Rabu dashi dallah, nace mishi idan ya isa ya hanani wayan sai naga me-”
“Ke! Imaani kinsan halin irin guys ɗinnan kuwa? Daga jinshi irin tantirannan ne bazaki so attention ɗinshi yazama focused akanki ba more than it already is." Naseemah tayi shuru, ta tuna da wani labari da yayarta ta taɓa faɗa mata. "Wallahi akwai wata friend ɗin Yaa Samna da take bani labari haka sukaita fama da wani daya biyo friend ɗinta tun daga Harvard da suke school har nan, bahaushe ne kuma ɗan Lagos. Irin marasa jin maganan nan, daƙyar yabar friend ɗin fa. Saida tayi aure ta samu lafiya saboda mijinta a tsaye yake. It was a serious case, he became obsessed with her the more she pushed him away gata dama masha Allah in kin ganta. Ki kiyayi kanki fa ƙawata ki samu ya rabu dake in peace.”
Tsoro yaɗan kama Imaani jin wannan labarin, Sadiq yayi kama da irin waɗannan mutanen, ga irin halayenda take gani tattare dashi already. Sai kuma ta katse tunaninnan, da wuya ma hakan ya faru. Zata ƙara zama careful kuma zata gani idan ya shafa ma kanshi lafiya yayi heeding to warning ɗinta toh, idan baiyi ba she'll take the necessary action against him.
Tace, “Bari mugani idan zaiji, har kin fara bani tsoro wallahi.”
Naseemah tace, “Karki damu just pray about it komai zaizo da sauƙi In Sha Allah. I'll be going to restock my skincare products tomorrow at NNDC Mall, let's go on a date if you're free. Ke wai yaushe zasu mana graduation ne? Daddy sai tambaya na yakeyi because yanaso naje Abuja na amsa aikin dake hotel ɗinshi nacan.”
Imaani ta sauke ajiyar zuciya, “It's been almost a month tunda muka gama exams fa ni kaina na ƙosa ayi awuce wajen. Nima zanje Abuja fa amma sai Ammi tadawo. And yes I'm free tomorrow after Zuhr and I need supplies, I'll come pick you up.”
Suka cigaba da hira da shirye-shiryen graduation ɗinsu har sukayi sallama lokacin sallar Maghrib.
***
Me kuke tunanin Sadiq zaiyi?
Me zai faru idan yayi realising Imaani itace cousin ɗinshi da akeso a haɗasu aure?
Ga sahibinta Nurain yazo gida yaga Abbu.
Hmm, jama'a yanzu muka fara labari😂😂