Love beyond time

CHAPTER 8️⃣

by @sauwama

Tashi tayi ta jawo jakarta tana duba takardun ta tsintar kanta tayi da tuna abinda ya faru dayake kokarin amsar jakar sai a lokacin ta fahimci ashe lokacin dayakai hannu jakar zai amsa dafe kanata tayi tana tuno yadda ruwa ke digowa daga gashin kanshi “ kai zaima dauka kallon shi nikeyi da gang an” ta fada tareda yin tsaki cigaba tayi da ciro abubuwan ta dake jakar tana gogewa da dan towel knocking taji a kofa hakan yasa ta kalli kofan tareda fadin “ come in” tasan yaya ne da taji muryar shi Kuma tasan duk sanda zasu shigo dakinta sai sunyi knocking sbd karsuyi unveiling privacy dinta 
Shigowa dakin yayi yana murmushi yace “ last card kin bani bani tsoro yau 
Ammi tace Azad ne ya kawoki gida koh so sorry wlh wani meeting ne ya tsayar dani Kuma dayake Ina cikin building bansan ruwa ake sosai ba” murmushi tayi tana fadin yaya “am fine” “ okay my little sissy but nayi mamakin yadda Azad din dabai san gari ba ya iya gane school dinki harya daukoki ya akayi ne” yaya ya fada yana kallon ta daga Mai kafada tayi itama tace” I don't know Nima kawaii saina ganshi maybe wani gurin zaije sai ya biyo ta hanyar kawaii ya gan ni” shuru yaya yayi sannan yasa “ okay’ but yayi mamakin abun Kuma Ina Azad zaije  
Tashi yayi ya fita daga dakin yana mata sallama “ Good night last card” ya fada tareda daga mata hannu murmushi tayi itama tana dagamai hannu tace “ good night yaya” 

Tunda Azad ya sauketa ya koma gida shigar shi dakin shi keda wuya saiga Mom tana mishi knocking “ Azad son ka dawo” Mom ta fada tana kara knocking din “ yes Mom come in” ya bata amsa lokacin ya gama cire jallabiyyan jikin Shi yasa wani Dan da sauri ya cire shi tareda boxer dinshi ya sa wasu saboda knocking din Mom da yaji shigowa dakin tayi tana karemai kallo ganin yana tsane kanshi da towel “ where did you go” Mom ta tambaye shi tana zama a sofa din dake dakin shuru yayi Bai ce mata komai ba ta kara magana “ kasan bawai gurare dayawa kasani ba but ka fita da dare Kuma baka tafi tareda Mu'azam ba” ajiye towel din hannun shi yayi yana matsowa kusa da ita “ Mom am not a kid hmm naje nadan ga gari ne shine ruwa ya sauko” ya fada yana dafa cinyar Mom “ But why are you wet” Mom ta kara jefo mishi tambaya Hadi da kallon kanshi da haryanzu kana iya ganin a jike yake “ I helped someone that's why” ya bata amsa Hadi da komawa ya dauki wayar shi “ okay hakan ma yayi kyau Allah yayi maka Albarkah” Mom ta fada tana yi wajen kofar “ good night son” Mom tace hadi da fita “ good night mom” ya maida mata lokacin tana janyo mishi kofa tashi yayi ya dauko laptop dinshi domin yin wani aiki akan company din shi ya jima yana aiki sau wajen 1 na dare sannan ya rufe laptop din ya dauro alwala yazo ya kabbara sallah saida ya idan yayi addu'a sosai sannan ya tashi ya hau gado da niyar bacci kwanciya yayi yana kallon saman “ you can't even say thanks” yafada hadi da jan tsaki “ mtswwww” 

DAWA GOGAN NAMU YAKE MAGANA NE THIS IS GETTING SPICY 🥵 🔥 🤭