茒AURIN ZUCI

Chapter 47

by @maryamstar248

***

***


***

饾樋饾樇饾檺饾檷饾檮饾檳 饾檿饾檺饾樉饾檮馃攼
Chapter 47.
    *
Sakin baki da hanci Zunaina ta yi, tana kallon Junaid a mamakance domin kuwa maganar cikin da ya yi ta dake ta da 茩arfi. 
     Sau bakwai tana bu蓷e bakinta da zummar yin magana, amma kuma maganar bata fitowa, tana tsayawa ne a cikin kanta.
     Rintse idanuwanta ta yi tana sauraren adadin dokawar da zuciyarta ke yi a 茩irjinta, cikin rawar baki ta fara da ambatar sunan shi murya a raunane.
    "Ju, Ju, JUNAID ina cikin ya ke, waye ke 蓷auke da cikin, cikin Muhammad 蓷ina?." Ta 茩arashe maganar tana saka duka hannayenta ta dafe cikinta, wani 蓷umi na saukar mata lokaci 蓷aya.
    Rintse rinannun idanuwansa Junaid ya yi, yana jin yanda kanshi ke sarawa da tunanin Masoyi, 蓷an uwa, aboki kuma aminin shi Muhammad ko wane hali ya ke ciki.
     "Na tabbar, ba ni dakaina na tabbatar ba, Doctor ne ya tabbatar min kina 蓷auke da ciki na haihuwa a jikin ki, lokacin dana ka蓷e ki da mota."
   
"Miyasa sai yanzu?". Ta yi tambayar murya a bushe.

  "A'a ba sai yanzu ba, tun lokacin ne". Ya tabbatar mata.

"Muhammad fa! koya sani?." Ta yi tanbayar wani abu me nauyi na taushe zuciyarta.
   
 "Bansani ba ko ya sani, bazan iya tabbatarwa." Ya amsata yanajin 蓷aci a bakinsa.

   "To ka sanar da shi please, zai yi murna, zai yi farinciki wata茩ila har kukan da蓷i zai yi, idan ya ji ina 蓷auke da cikinsa." Ta fa蓷a tana hasaso yanayin da Muhammad 蓷inta zai iya kasancewa idan ya yi tozali da labarin tana 蓷auke da cikinsa na haihuwa.

  "A ina zangan shi?." Tambayar ta kubto daga bakin shi.

  Bu蓷e baki Zunaina ta yi da zummar yin magana, amma sai mi zai faru? wani dun茩ulallen jini ne ya soma fa蓷owa daga bakinta guda-guda.
   
Wannan shine ga samu ga rashi, zuciyar Junaid ta fa蓷i.
 A razane ya matsa kusa da ita, zai yi magana sai ya soma lura da numfashinta na sauyawa, bai daina fita baki 蓷aya ba, amma yana iya gane yanda ya ke mata wahalar sha茩a. Cak ya 蓷auketa  cikin hannunwan shi ya nufi 茩ofar fita.

   "Innalillahi, mi yake faruwa haka miya sameta wai?." Uncle da fitowar shi kenan ya watsowa Junaid tambayar yana 茩arasowa inda yake sa蓳e da ita.

   A kuma daidai lokacin ne Tambari ya soma bayyana, ba a wani waje na daban ba a jikinta akan fuskarta wajen goshinta, a nan tambarin ya bayyana, kamar yanda ya saba bayyana a mabanbanta wajaje, yana nan kamar yanda ya ke tambari ne me kalar 蓷igon ruwa ko wani abu me kauri da za'a iya 蓷igawa, amma kuma shi jah ne launin ja ne dake danganta tambari da jini kai tsaye 馃挧.
    A mugun razane Uncle ya ja da baya, yana sharce gumin da ya soma tsatsafo ma shi nan take, a 蓷imauce ya fa蓷a 蓷akin Saminaka shi kanshi bazai iya cewa ga abin da yake yi ba, kawai de ya san ya 蓷auko abu guda biyu a hannunsa, bai san kuma yanda aka yi ba sai ya tsinci kan shi da bu蓷e gora 蓷aya ya matsa inda suke hannun shi na kakkarwa ya bu蓷e bakinta da 茩yar na soma bulbula mata shi.

Minti 蓷aya, minti biyu, uku, hu蓷u.
    茦wararan mintuna goma suka shu蓷e shiru, babu hayaniya, babu kuma sauti me 茩arfi, haka kuma fitar numfashin Zunaina bai daidaita ba saide sannu ahankali tambarin ya soma 蓳acewa yana bajewa, haya茩i na fita daga goshinta, sannan wani tsinkakken jini ya sake 蓳alle mata hanci da baki.

   "Junaid, Innalillahi ya zamuyi da ita?."
Uncle ya tambaya yana du茩ewa kamar yanda shima Junaid 蓷in ya du茩e tare da kwantar da ita a saman lallausan carpet.
  "Mu jira."
"Ka蓷an."

Ya fa蓷a yana sake nitsar da ganin shi a kanta, zuciyar shi naharbawa fiye da 茩ima.

A can cikin kwanyar shi kuma soma tarawa yana warwarewa ya yi, tare da tattaro bakunan zarurran da suka har蓷e yana son daidaita komi.
    
"Jini."
Ya fa蓷a a fili kamar me son tabbatarwa, can 茩asan zuciyar shi na 茩ullewa da wani abu, wani abu me kama da son 蓷aukar mataki, matakin da zai datse 蓷aurin zaluncin da azzalumai ke yi don cimma wata manufa da ku蓷iri nasu, yayinda yakai matu茩a wajen hasala shi.

"Ta ina zan soma?."
Ya yi maganar a gajiye.

Kallon tuhuma Uncle yabi shi da shi, kafin ya girgiza ma shi kai cikin son kyautata ma shi zato ya ce.

   "Ban sani ba."
"Amma kuma..." Sai ya yi shiru bai 茩arasa ba ya raba hankalin shi biyu, rabi ga Zunaina rabi ga Junaid.

   "Uncle!." Junaid ya kira sunan shi kamar me son ro茩on wani abu.

"Ina so ka kauda kanka matsawar kasan ba zaka taimaka min ba a wannan karon.

Bazan iya jure ganin wannan abin na faruwa ba ana cutar da bayin Allah basu jiba basu gani ba, ina da ikon dakatarwa amma ka hana ni aikata hakan."

    A razane Uncle ya mi茩e tsaye yana nuna Jay da yatsa, bakin shi na rawa, sai kuma ya kasa cewa komi, ya juya ya fice yana ha蓷e hanya.


"A wannan karon bazan takata ba dole ne inkawo 茩arshen du wannan, kobadan abin da suka yiwa Abeey ba, zan 蓷auki fansar Muhammad da sauran rayukan da basu ji ba basu gani ba."
    Wani abin mamaki daya sake 茩arfafa shi ne ya faru a lokacin.

Zunaina, a cikin yahayin ciwo da azaba take amma hakan bai hana ta ri茩e wani sashe na Jay ba tana kokowa da fita da shigar numfashinta ta furta.
   "Zan..zan.zankasance a.a.a.a.tare da kai, ina bayanka  zamuyi ya茩i a tare na yi al茩awari da rayuwa da jinina wannan yaron da ke cikina bazai fito duniya ba face komi ya daidaita zamu kawo 茩arshen komi, zamu sauya komi, ni da kai da kuma abin da zan haifawa Muhammad."
   Ta fa蓷a numfashinta na tsayawa cak.

Wani irin lumashe ido Junaid ya yi yana sha茩ar iska da 茩arfi yana janta har cikin huhun shi.

 *

A daidai wannan lokacin a 蓳angaren Maryam wani al茩awari da yayi daidai da cikar wata 茩addara ya afku.

Ta kama hannun Rimsha ta rintse a cikin nata hannun, sannan a hankali cikin sanyi wanda ke cike da sassarfa ta lumshe ido da sassanyan sauti me fitowa caku蓷e da bacin rai ta soma fa蓷in.
    "Hafsa da du wani me hannu cikin aikata zalunci da son zuciya na yi al茩awarin kawo 茩arshen su."
Sai taja numfashin sannan taci gaba
"Ni ka蓷ai bazan iya ba amma kuma ina da tabbacin iyayena da suka raineni ba zasu barni haka nan ba, zasu agazamin har sai na cimma burina, Makafa, 茦waro, Hafsa da sauran mu茩arrabansu su jirayi bayyanata a gare su."
   Ta fa蓷a jikinta na kakkarwa har kokacin idonta na a rintse.

To masu karatu da Junaid da Zunaina da Maryam sun yi 茩uduri iri 蓷aya.

Mi kuke tunanin zai faru, shin zasu cimma burukansu, ko kuma wani abun na daban zai faru?.

Ina labarin 茦waro ubangidan Makafa da tun da ya 蓷anawa Makafa tarko ya kama gabanshi.

Kuci gaba da bina sannu a hankali dan jin yanda zata kaya.


Ina baku ha茩uri akan rashin zuwan labari jiya, yauma kuma bai samu da yawa ba in sha Allah zanyi 茩o茩ari zuwa goben idan rayuwarmu ta kai inyi muku me 蓷an yawa.

MARYAM STAR.