BLACK DAGGER❤️🔥 THE SHADOW OF THE BLACK
The Al-Amin Estate
page 3️⃣&4️⃣
Suna shiga ya zaunar dashi akan wata kujera wacce aka ƙerata da itaciya mai inganci kogon ya kasance tamkar wani parlour hatta bed Akwai ga wani grass carpet malale a tsakiyar kogon zama shima yayi a ɗaya daga cikin kujerun yana lumshe blue eyes ɗinsa babu jimawa bacchi ya ɗauke Kian A hankali ya miƙe yana gyara masa kwanciyar sa sannan ya koma ya zauna ya sake lumshe ido.
NEUILLY-SUR-SEINSE
PARIS
A cikin birnin Paris,akwai wani katafaren gida mai cike da tsantsar alfarma da kuma tsaro mai tsoratarwa. Wannan gida na wani hamshaƙin ɗan kasuwa ne kuma Billionaire mai suna Alhaji Ibrahim Al-Amin wanda asalin sa ɗan Najeriya ne Kano, amma ya zuba jari tare da kafa daular kasuwancinsa a faɗin duniya. Gidansa, wanda aka fi sani da sunan "The Al-Amin Estate", ya kasance tamkar wani ƙaramin fada mai cike da sirri da kuma tsaro.
Ginin gidan an kewaye shi da wani katanga mai tsayi da aka ƙawata da fasahar zamani ta tsaro (smart security perimeter). A wajen babban gate ɗin ƙarfe mai sheƙi da alamar zinariya, akwai ƙwararrun jami'an tsaro masu ɗauke da manyan makamai, tare da na'urorin tantance fuskoki (facial recognition cameras) waɗanda ba sa barin ko tsuntsu ya wuce ba tare da an gani ba.
1The Grounds & Gardens
Idan ka shigo ta babban gate ɗin, za a ga wani katafaren titin motoci da aka yi shi da duwatsu masu daraja (paved cobblestone driveway). Gefe da gefe yana cike da kyawawan lambuna masu ɗauke da furanni na musamman, ruwan fanfo (fountains) da aka ƙawata da hasken wuta da kuma motoci masu tsada (irinsu Rolls-Royce Phantom da Bugatti) da ke ajiye a wajen parking.
2.Architecture & Interior Design
Gidan an gina shi ne ta hanyar haɗa salon zane na zamani (modern luxury architecture) da kuma tsohon salon sarauta na Faransa.
4.Main parlour
Yana da manyan glasses da suke kallon Garden da manyan fitilun lu'ulu'u (crystal chandeliers) da suka sauko daga saman rufi mai tsayi. Gidan yana da shimfidu da dardumar da aka yi su da ulu mai laushi, da kuma kujeru na alfarma da aka ƙawata da zinariya.
5.Communication Section
Akwai wani babban ɗakin taro da na'urorin computer's na zamani inda Alhaji Ibrahim yake gudanar da harkokin Company's ɗinsa.
kofar wani ƙayataccen bedroom ta buɗe a hankali. Aaliyah ta fito cikin wani irin taku mai cike da nutsuwa Daga ita sai bumshorts mai laushi da wata 'yar crop top wacce ko cibiyarta ba ta rufe mata ba, hakan ya bayyana flat tummy ɗinta Wanda tamkar bata zuba mashi abincin
Kyakyawace ajin farko tamkar wata aljana ko tauraruwar da ta sauko daga sama. Tana da madaidaicin tsayi da wata irin sura mai ɗaukar hankali ƙugunta a baje yaku yayin da dogon baƙin gashinta wanda ya sha gyara yana ta baza kamshi na musamman ya zubo har yana taɓa ƙugunta da bombom ɗinta a duk lokacin da ta motsa. Idanunta masu kyau da haske suna sheƙi, sai dai fuskarta a ɗan haɗe take, tana tura ɗan ƙaramin bakinta gaba cikin tsantsar shagwaɓar da ta saba yi a matsayinta na 'ɗaya tilo a wajen mahaifinta.
Cikin tafiyarta mai cike da jan hankali da shagwaɓa, ta sauko daga staircase da aka yi da farin marmara, ta nufi Main Parlour, inda mahaifinta Alhaji Ibrahim Al-Amin yake zaune yana duba wasu takardu.
Tun kafin ta ƙarasa inda yake, muryarta mai zaƙi da shagwaɓa ta fara cika falon:
"Papi! Papi, ka ga Aunty Zahid wai ba za ta zo ba!"
Ta ƙarasa maganar tana zama kusa da shi a kan kujera tana ƙara turo baki gaba tamkar za ta fashe da kuka saboda sangarta.
Miss Nasir ✍️