Chapter 5
1:30
ta gama hada komai na bukata ta ajihe su a tsakar gida, ta shirya cikin wani tsohon material da hijab dinta fari a goge tsaf da ita.
babu wata makusa inde tsafta ce kasami Azima ka gama, bata kamshi bata wari dan bata da kudin siyan turare,
yau made Anisa da inna ba sannan tun da hantsi suka futa tarasa ina suke zuwa amma ta fu jin daɗin gidan haka babu ita babu borin inna da Anisa, tanannan tsahe Usman ya daho daga makaranta kalon sa Tayi ta ce,
"hi sauri Usman yau baka daho da huri ba"
da gudu ya karasa dakin inna yana " bari nasa kaya yaya Azima wlh yau test mukayi a Makaranta shi yasa,
cikin kana nun mituna ya futo cikin bakin yadi na yau de yadanfi najiya kyan gani saide shima tsohone sosai,
"to inna mu mun huce a mana addu'ar ciniki da kariyar uban giji kinsan titinnan babu tsaro"
cewar Azima futowa inna Tayi sanhe da yaluwar atanfa tana daura dan kwali gashin kanta na fulani kwance a bayanta kamar wata budurwa,
"Allah ya kiyahe Azima ku kula baruwanku da kowa kin fishi hankali, ki kula dashi kar ya hau titi,
"insha Allahu inna suka fada suna daukar kayan ita ta dauki bokitin awara shi ya dauki botikan lemo dole sai yadaho ya dauki murhu da kasko.
da sauransu suka futa hanyar titi suka nufa hankalin su nakan hanya ba ruwansu da kowa, har suka isa titi yauma kamar kullum da wannan gosulan ga masu sihe da siyarwa duk sun futo.
yan mata sai sayar da kaya suke masu abinci da masu awara da sauransu, ajihe kayan sukai Usman ya juya be dau lokaci ba yadaho da sauran kayan inna ma ta hura mata huta
ta fara aikin siyar da awarar ta kamar yadda ta saba babu ruwanta da kowa, daga ashahon samari gurin wanda dama ba harkarta suke shiga ba,
zuwa ga marasa kamun kan yan matan (kunsan de halin wasu masu tallan babu kamun kai sai gantali kamar ba mata ba Allah kashirya zuruyar mu)
tana nan me kayan miya ya kaho mata dari biyu da hamsin dinta, shima de Usman sai cinikin sa yake ya rugata sayarwa sabida lemon inna ba baya ba wajan dadi haka zalika awarar da yajin tafarnuwa
5:55
ta kammala suyar suka hada kayansu suka nufi gida, kamar jiyama Usman be shuga gida ba ya ce yatafi gareji amma saide yau ya bata cinikin lemon sannan yatafi
gidan ta shiga tasamu inna a dakinsu zaune sannu da gida ta mata ta zauna tare da mika mata kudin ta ce,
"inna baba fa?"
"babanku dazu ya shugo amma be dade ba sun tafi Kaduna wani aiki sati 1 zehi ya daho, baki ta tabe ta ce
"Allah ya kiyahe hanya nawa ya bada kudin cefannan abinci, dariya inna Tayi tana dungure mata kai ta ce
"babu ruwanki ina shi Usman din yake?" "uhm inna yatafi gareji kinsan Usman da san kudi, kai ta girgiza cike da son ƴaƴanta tana musu addu'a a zuciyarta.......
chapter 3
.........haka rayuwa ta cigaba da gudana acikin wannan a halin masu cike da kaunar junnansu kullum cikin kokarin rufawa kansu asiri suke,
ita kuma inna kullum cikin kokarin hiwa yayanta tarbiyya take ana cikin haka akai musu waya ta nokiar inna biki ya tashi sokoto gashi har lokacin baba be daho ba
haka suka fara shirhe shirhen tafiya biki dan saura kwana 4 tafiyar yau ta kama juma a kuma saura kwana 2 suhi tafiyar batahe suyar awara ba.
tana zaune a daki ita kade tana jigida inna batannan ta je kasuwa siyayya Usman na gareji suko su innar Anisa sun futa kamar yadda suka tsira a tsukukin dan ko neman rugimar da suke dasu sun kwana 2 basu hi ba,
sallamar safeeya ce tashugo gidan tana kokarin tashi tana amsawa safeeyar tashugo cikin dakin sanhe da green din atanfa ta mata kyau da yake ita fara ce jajir gashi takara da mai sai hasken nata yahi bau kuma ba lefi kyakyawa ce kin kowa kin wanda yarasa,
"Aa yau kuma jigida kika tuna" tafada tana zama a kusa da ita, kalonta Tayi da murmushi a fuskarta ta ce,
"su safeeya manyan gari wannan baza capacity haka ina zaki?"
"kede bari ai ke kinki challawa zan tafi kinsan yau juma'a sai ansako daga masalaci ke kinki kin nace sai awara ko?
to bakiga kudin da nake samu ba ga masu aikin a Companyn akwai sakin kudin, baki ta tabe tana kokarin kulle jigidarta da tagama tana kokarin kama wata taji safeeya ta ce,
"woow Allah kayi mana arziki ko kasa mu auri masu arziki mu runka zuba capacity"
"wai ke safeeya lafiyar ki kuwa sai wani surutai kike hala de kin fara zarewa kinzo sai wani woow kike, woow din kaniya mwss"
"to sarkin balaki wlh ke gabadayanki local ce, kinsan de inda zakihi masifar ki dede nake dake wlh aikin sani, sai zafin zuciyar masifa,
Allah kawata rashin kudi ke damunki ki dage da neman kudi zaki dena zafi zuciyar nan,
kinsan wani abu kuwa? banza ta mata tana cigaba da abin da take, cigaba da maganar ta Tayi hankalinta kwance
"ke kinga kuwa girman Companyn nan da haduwar shi al jannar duniya, ke ni wallahi gani nake ko a chaina al barka karewar haduwar gini da tsahi kinsan an ce in kaje chaina ki gama.
to wallahi karya ne in kaje challawa ka gama" dagowa Tayi ta watsa mata kalon bakida hankali kafin ta mike Tayi hanyar waje tana cewa,
"gaskiya kin fara zau cewa lafiyar ki kuwa kawai ki auri me Companyn kinga daman burinki shine auran me kudi,
tafada tana fucewa, daga murya safeeya Tayi tana cewa,
"kai i love You masohiya wannan kyakyawar adu' a Allah ya amsa na auri me Companyn nan ba karamin morewa nahi ba,
kai wayyo dadi gobe ina saudi jibi ina italy, gata ina turky, citta ina dubai haka saide kujini a America,
shugowa Azima Tayi dauke da kofin ruwa da jarkar kunnun aya ta ajihe a gaban safeeya ta koma ta zauna tana ciga ba da shirin ta kafin ta ce,
"safeeya tafiya fa za muyi"
da sauri safeeya ta dago tana kalonta kafin ta ce, tafiya kuma Azima ina to za kuje?"
murmushi Azima Tayi dan bakaramin jin daɗin tafiyar da za suhi take ba,
"Sokoto za muje bikin yar yayar inna"
"ohh kice dogon zango zakuhi sati nawa za kuhi? "ban sani ba amma ina ga muyi sati 2 zuwa 4 ke har sati 6 zaki iya gani munhi,
wai sharaban mu da zuwa Sokoto kinga kwa ya kamata mu zagaya dangi"
kai safeeya ta girgiza tana jinjina dadewar da zasuhi "kuma harda Usman zaku?"
murmushi Azima ta kumahi jerarun fararan hakoranta masu kamar kankara na bayyana ta ce, "kwarai kuwa safeeya"
"to Allah ya tsare inaga ranar da zaku tafi inshugo gidannan bari ni natafi kinga har 3 bantafi ba ga nisa ta tashi tana yafa gyalenta itama Azima mikewa Tayi suka futo tace
"to sai kin daho safeeya sai a runka kula banda san kudi dan kudi sai yakaika ya baro ka, kai kawai safeeya ta girgiza ta futa ita kuma ta koma ciki ta ciga ba da abinda take,
bata dade da zama ba ta juyo sallmar inna ta shugo tashi Tayi da sauri ta futo
"sannu da zuwa inna har kin daho na dauka sai kinkai dare ma"
ta fada tana karasawa ta karbi kayan hannu innna,
"yauwa Azima ai da yake ba wata siyaya na hi ba shi yasa nadaho da huri, amma da sai nakai dare biyoni dasu daki,
kayan ta kinkima ta bita daki ta ajihe ta zauna kusa da inna, "inna wai dame dame kika siyone naga ledar cike da kaya da yawa