UQUBA

UQUBA CHAPTER 3

by @115427907984105099906

UQUBA CHAPTER 3
‎BY
‎
‎FATIMA USMAN 
‎SHA LELEN TERAWAN GAMJI.......
‎
‎
‎
‎Haka Rafi 'a taci gaba da rayuwa cikin wahala da qunci,
‎Har ta kai shekara 16 "
‎Maqerin budurci ya fara qera ta '
‎
‎Kyawunta ya qara bayyana sosai duk wanda ya kalleta seya yaba,
‎Samari sun fara yimata sintiri a qofar gida kullum se an aiko nemanta,,
‎
‎Sa'banin Naja 'atu da ko kare be ta'ba zuwa da sunan neman aurenta ba.
‎Wannan ya qara wutar hassada da qiyayyar Amo da Naja 'atu'
‎
‎Duk sanda wani yazo zance gurin Rafi 'a jisukeyi ina wuta su sakata saboda hassada da baqin ciki,
‎Wani lokacin idan saurayi yazo hira gurin Rafi 'a"
‎
‎Haka Amo da Naja 'atu zasu fito suyi tijara suyimasa cin mutuncin da baze qara dawowa ba,
‎Amma hakan baze hana wani zuwa gobe ba '
‎
‎Saboda Allah yayiwa Rafi 'a nitsuwa da kamun kai,,
‎Ga uwa uba kynan halittar ta wanda shine yake janyo wasu zuwa gurin ta.
‎
‎Rafi 'a ta shigo gida se sand'a take tana maqalewa a jikin gini kamar wata marar gaskiya"
‎Domin bata sayar da kunu da qosan ba.
‎
‎Haka taketa ra'be ra'be a jikin bango tana leqen cikin gidan '
‎Domin tasan yau kam babu abunda ze hanata kar'bar na jakuna a hannun Amo,
‎
‎Naja 'atu ce da ta dawo daga yawon ta da sunan makaranta "
‎salati tayi sannan ta danqarawa Rafi 'a wani uban ashar"
‎
‎La ila ha illallahu innalillahi,
‎Rafi 'a dan uwarki ashe idan Amo ta aikeki talle bakya zuwa la'bewa kikezuwa kiyi shiyasa bakya sayarwa koh?
‎
‎Shegiya muguwa wato saboda bana uwarki bane idan Amo tayi asara bakida damuwa koh?
‎
‎Munafuka ustaziyar qarya idan anyi magana kikama qiqqifta wad'annan munafukan idanun naki na aljanu ki nuna zakiyi kuka saboda ace ana cutar ki.
‎
‎Ai kuwa kamar amo jira takeyi tayi saurin fitowa daga d'aki tana salati,,
‎Rafi 'atu Dan ubanki ashe idan na baki talle makya zuwa?
‎
‎Haba biri yayi kama da mutum,
‎Yanzu Rafi 'atu saboda tsabar bakisan mutunci ba ni zakiyiwa mugunta?
‎
‎keda iyayenkima sukayi abun kunya suka haifeki suka kasa riqeki saboda tsoron maganar duniya suka yasar da ke,,
‎Amma ni da na temakeki na riqeki kirasa wanda zaki cutar se ni.
‎
‎Kamar sauqan ruwan dalma Rafi 'a taji sauqan maganganun Amo a cikin kunnunwanta '
‎Wasu siraran hawaye masu d'umi suka gan garo mata ,,
‎
‎Dak'yar ta iya bud'e baki tace '
‎
‎Amo dan Allah kiyi haquri wallahi ba haka bane "
‎
‎Nayi iyakar qoqarina wajen ganin na sayar duka amma wallahi ,
‎
‎Yimin shiru munafuka....
‎
‎Amo ta dakatar da ita cikin tsawa da fad'a sannan taci gaba da cewa"
‎D'an wani busasshen kashi mugun iri tuwon qar,
‎
‎Allah ya d'aga garinki iska ta kwashe makira munafuka "
‎
‎Tsintacciya jefaffiya qaramar karuwa an gama bin maza anzo ana nuna anada hankali a fuska ,
‎
‎Tun kina qarama babu d'akin saurayin da baki haddace ba,,
‎Babu wani saurayi da besan kalar jikin ki ba.
‎
‎Fasiqa karuwa wallahi yau se nayi maganinki a cikin gidan nan.
‎
‎Ta kai qarshen maganar tana kaiwa Rafi 'a wani mugun duka da sandar hannun ta ,
‎
‎Rafi 'a bata motsa ba kuma bataji kamar zata motsa d'in ba domin ko kad'an bataji zafin dukan ba '
‎
‎Koda taji ma tasan bazekai kalaman Amo zafi da suka ba "
‎Wani irin abu takeji ya taru ya cunkushe mata a qasan zuciyar ta,
‎
‎Wani abu me d'aci ya tokare mata maqogoro tanajin wani irin nauyi a cikin qirjinta har numfashin ta na barazanar d'auke wa '
‎
‎Wani irin jiri ne yake d'ibarta wasu hawaye suna ambaliya akan fuskar ta.
‎Durqushewa tayi badan zafin dukan da Amo keyimata ba ,,
‎
‎Se dan jin qafafunta suna qoqarin kasa d'aukar ta.
‎Wani irin duhu take gani a idonta,
‎
‎Sam bata kula da jinin da yake zuba daga cikin hancinta da goshinta ba domin hankalinta ba a nan yake ba.
‎
‎Haba Amo wannan wani irin zalunci ne haka?
‎Me yarinyar nan tayimiki ne haka da ko kad'an bakyason ganin hutu ko farin cikin ta?
‎
‎Ajimal da tun lokacin da Amo ta fara zagin Rafi 'a ya shigo gidan yake kallonta ya furta a hasale '
‎
‎Yaci gaba da fad'in ,
‎Me yarinyar nan tayimiki ne har kike hukuntata da abunda bazata iya d'auka ba?
‎
‎Wad'annan kalaman sunyi muni sosai Amo "
‎Har nawa Rafi 'a take da kike fad'ar irin wannan maganar a kanta?
‎
‎Rafi 'a fa amanace a gurinki wallahi dede da kwayar zarra idan kika cutar da ita Allah baze bari ba seya bimata hakkinta,
‎
‎Yanzu misali ki kwatanta"
‎
‎Wani irin zafi zakiji idan kikaji wani yana jifar Naja 'atu ko ni da irin wad'annan miyagun kalaman?
‎
‎Dan Allah Amo ki dinga jin tsoron Allah '
‎Rafi 'a qaramar yarinya ce wannan cutarwar tayi yawa.
‎
‎Ya qarasa maganar yana durqusawa a gaban Rafi 'a wacce taketa faman kuka kamar dama dan shi aka halicce ta ,,
‎
‎Hannunsa ya saka a cikin tafin hannun ta yana kallon yadda taketa rusa kuka cike da tausayawa '
‎
‎Ita kuwa kamar dama jira take tayi saurin fad'awa jikinsa ta fashe da wani irin kuka me ta'ba zuciya,
‎
‎Hanu Amo ta daura a kayi ta fasa wani uban ihu tayi wani irin fad'uwa a tsakiyar gidan tana fad'in '
‎
‎Shikenan na shiga uku"
‎
‎Malam fito kagani yau Ajimal da Rafi 'atu sun had'emin kai a cikin gidan nan ,
‎
‎Wannan tsintacciyar magen ta shiga tsakani na da d'ana baya ganina da mutunci '
‎
‎Ta riga ta gama da shi bayajin maganar kowa se nata.
‎Baffa da yake d'aki yana hawaye tun da Amo ta fara cin mutuncincin Rafi 'a Yayi saurin fitowa jikinsa har 'bari yake saboda kar ran Amo ya 'baci ,,
‎
‎Kai Ajimal zan ci mutuncinka wallahi,
‎
‎Aminatu ba mahaifiyar ka bace da kake fad'a mata irin maganganun nan ?
‎
‎Waye Rafi 'atu ta fi Ido da kwalli da in tayi lefi baza ayimata fad'a ba?
‎Wallahi akan yiwa Aminatu rashin kunya sena tsinemaka Ajimal"
‎
‎Yaron banza kawai ka zauna kanayiwa mahaifiyarka rashin kunya akan wata can,
‎
‎Wallahi duk randa kasake yiwa Amina magana akan abunda takeyiwa Rafi 'a sekabar gidan nan kuma sena tsinemaka.
‎
‎Baffa ya qarasa maganar cikin fad'a kamar ze daki Ajimal '
‎
‎Wani irin mamaki ne ya kama Ajimal da jin kalaman baffa akan Rafi 'a ,,
‎
‎Duk yadda baffa yake qaunar Rafi 'a wai yau shine da kansa yake fad'ar haka a kanta?
‎
‎Kallon Amo yayi cike da mamaki domin yasan idan ya rantse ko kaffara bazeyiba itace ta shiga tsakanin baffa da Rafi 'a,
‎
‎A hankali ya gir giza kai sannan ya kalli Rafi 'a ya sake kallon Amo"
‎Shikenan Amo kinyi nasara kin shiga tsakanin su amma ki jira kamun Allah '
‎
‎Kiyi haquri Rafi 'a Allah yana kallo ya sani ana zaluntarki babu yadda zakiyi,,
‎
‎Ki qara haquri insha Allah se Allah ya sakamiki tabbas zasuga sakayya suma sun haifa kuma tabbas se Allah ya kar'ba miki hakkin ki '
‎
‎Yana gama fad'ar haka ya miqe ya fice daga cikin gidan da sauri yanajin qirjinsa nayimasa zafi kamar wuta .
‎
‎Qasaitaccen gidan yanada girma sosai,
‎Cike yake da kayan k'ayle k'yale na zamani "
‎
‎Kai da gani kasan gidan wani hamshaqin attajiri ne '
‎Wata babbar mata ce zaune a parlor tana sanye da wasu tsadaddun leshi na alfrma,,
‎
‎tayi ado na kece reni da manyan sarqoqin gold da awarwaro ,
‎A qasaice take danna wayar ta fuskarta d'auke da annuri '
‎
‎Kallo guda zakayimata ka karanto farin ciki akan fuskar ta"
‎Daga 'bangaren ta na dama wata farar matashiya ce kyakkwa ,
‎
‎Itama kana ganinta zakasan tana cikin farin ciki.
‎
‎Wallahi Momi na matsu su yaya Muazzam su iso nayi missing d'in shi sosai gani nake kamar bazasu iso ba '
‎Ma tashiyar tayiwa matar magana cikin zaquwa "
‎
‎Seda ta d'anyi mur mushi Sannan tace,
‎umai ma kin cika gaggawa da yawa wallahi,
‎
‎Nagade kinyi shekaru ma baki gansa ba se jiran y'an awanni su gagareki?
‎umai ma ta gyara zama sosai sannan tace "
‎
‎Momi kinsan fah ance aski in yazo gaban goshi yafi zafi '
‎To nima duk da ya kammala makaranta kuma idan ya dawo yanzu shikenan baze koma ba amma wallahi jinakeyi kamar baze dawoba,,
‎
‎Gaba d'aya lokacin ma baya wani tafiya sosai.
‎Ta qarasa maganar tana duba agogon hannunta '
‎
‎To yanzude idan kikayi haquri Daddyn ku da yayanki sun tafi taroshi daga airport,,
‎Kinga kenana duk inda yake yanzu haka ya kusa qarasowa gida.
‎
‎Nide wallahi Momi.....
‎Bata qarasa ba sallamarsa ta doki dodon kunnen ta"
‎
‎Fari ne tass le'ben bakinsa har wani pink pink yakeyi,
‎Lafiyayyen karan hancinsa yana tsaye ral a kan fuskar sa '
‎
‎Yanada wadataccen gashin gemu da yakeshan gyara da tsadaddun mayuka  ,,
‎Inda yalwataccen sajen sa yayi luf ya had'e da gashin gemun nasa,
‎
‎Fararen suit ne a jikinsa se takalma sau ciki baqaqe '
‎Ya bala in yin kyau sosai kamar wani jarumin film d'in indea.
‎
‎Sumar kansa me cika da laushi tayi luf a saman kansa kamar hula se sheqi take '
‎Fuskarsa d'auke take da wani lallausan mur mushi me kyalli.
‎
‎Nasan zakuce wanene wannan mutumin da aketa zayyano muku bayanai a kansa haka babu qaqqautawa'
‎
‎"Barrister Ibrahim Ibrahim Yuri "
‎
‎Wanda akeyiwa laqani da,
‎Muazzam...
‎
‎Ya kammala karatunsa a qadar Jordan a bangaren shari a '
‎Kuma Alhamdulillah ya fito da aikinsa a matsayin babban lawyer.
‎
‎Wani irin firo umai ma tayi da pillown hannunta ta nufoshi a guje ta rungumeshi tana dariya,,
‎
‎Yaya Muazzam Oyoyo '
‎Ta fad'a tana dariya cike da farin cikin ganinshi sassanyan qamshin turaren sa ya daki hancin ta zuciyar ta ta harba da qarfi hakan ne ya tilasta ta sauqe wata qaqqarfar ajiyar zuciya ba tare da shiri ba "
‎
‎Mur mushi yayi yad'an ja kumatun ta yace,
‎Oyoyo y'ar mitsitsiyar kyanwarmu ta girma.
‎
‎Dariya tayi"
‎Yaya bazaka dena kirana da wannan sunan ba koh?
‎
‎Ta fad'a tana dariya had'e da kar'bar jakar hannunsa,
‎Yaya na tsarabar me ka kawomin?
‎
‎Allah yasa waya ka sayomin Saboda wallahi na gaji da wayata inaso na canza '
‎
‎Ke umai ma...
‎Ki kyalemin d'a na ya huta,,
‎
‎Daga shigowar sa kin stare shi da surutu aide kin jira ya huta kafin ayi maganar tsarabar koh.
‎
‎Rafi 'a na durqushe a mawanki tana wanke wanke "
‎Dak'yar take iya wanke kwanunkan saboda tana fama da kakkare,
‎
‎Yatsar ta na hannu ta kumbura sosai tana yimata zafi da zogi '
‎
‎Dak'yar take iya saka hannunta a cikin ruwan domin duk abunda yatsar ta ta'ba ji takeyi kamar ranta ze fita saboda azaba ,,
‎
‎Amo ta fito daga d'aki tana fad'in '
‎Ke Rafi 'atu bazakiyi sauri ki kammala wannan wanke wanken ki tafi talle ba?
‎
‎Tun d'azu kike abu d'aya kamar cin kwan makauniya"
‎Maza ki kammala ki wuce ki d'auki tallen munafuka tsintacciya kawai.
‎
‎Ta qarasa maganar tana aikawa Rafi 'a da saqon harara '
‎Rafi 'a ta d'ago cikin hawaye tace,,
‎Amo dan Allah kiyi haquri wallahi yatsar nan tanayimin ciwo sosai '
‎
‎Bata qarasa ba Amo ta d'auki cokali ta kwad'awa yatsar seda ta fashe ta fara zubar da d"iwa ,
‎
‎Sannan ta d'auki ruwan omo ta kwarara akan ciwon.
‎Wani irin shid'ewa Rafi 'a tayi ta mimmiqe a guri numfashinta ya d'auke '
‎
‎Tsabar azaba duk da a sume take hakan be hana fitsarin wahala biyo qafafunta ba .
‎