FreeArewaPen original
UQUBA
- 1views
- 1chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · Introduction
UQUBA CHAPTER 2BYFATIMA USMANSHA LELEN TERAWAN GAMJI......Washe gari da safe baffa da kansa yayimata wanka ya bata madara ta sha sannan ya bawa Ajimal renon ta Domin lokacin Ajimal ya kai shekaru sha takwas a duniya 'naja 'atu Kuma shekarar ta biyu.Baffa na fita Amo batayi qasa a guiwa ba ta d'auki mayafin ta ta nufi gidan babbar aminiyar ta salame "Kai tsaye suka shige cikin d'aki 'Amo ta kwashe labarin komai ta fad'awa salame,Game da maganar tsinto yarinyar da baffa yayi,,Ta qara da cewa...Ai ba hauka nakeyi ba wallahi bazan iya renon y'ar wasu ba 'Nawan ma kawai dan sun zamamin dole ne abarni da iya su sun isheni,,Haba salame Da wanne zanji?Naji da talaucin malam ne ko naji da riqon yara na kokuwa naji da renon waccar shegiyar y'ar tsanar?Ta qarasa maganar tana riqe ha'bar ta had'e da ta'be baki.Se da salame ta d'an numfasa sannan tace"Amma Amina bakida wayo wallahi,Ai ko baki kar'bi yarinyar nan dan Allah ba kya kar'beta ko dan gudun maganar mutane,,Kinsan fah yanzu an dena kiwon dabba mutum ake kiwo 'Kowa ya shiga gidan yaga malam ko Ajimal suna renon jaririya ke za a fara zagi ace bakida tausayi kinqi ka'bar jaririya.Da mamaki Amo ta kalleta tace 'Yanzu salame kece kike magana akan tausayi?Yaushe kika fara tausayin y'a y'an wasu kuma?Kin manta murjanatu y'ar marigayiya indo abokiyar zamanki irin wahalar da ta sha a hannunki?Kode bakiji labarin da na baki da kyau bane?Yarinya ce fah aka kawo ta akace na riqe ta Kuma bansan kowa nata ba "Wani shu umin dariya salame tayi sannan ta kalli Amo tace,Sarai na fahimci labarin Kuma na gane me kike nufi 'Sannan Kuma nid'in ce de da kika sani kirarina yana nan"Turnuqu fad'an ibilisai yaro be ganiba balle ya raba,Jani muje ko daban daban ma dawo Mugu shi yasan makwancin mugu 'To amma meyasa kika ce na kar'bi wannan tsintacciyar yarinyar?Amo ta fad'a fuskarta d'auke da mamakin kalaman salame 'Sosai salame tayi dariya sannan tace,Saboda ta hakane kad'ai zaki iya jifan tsun tsu biyu da dutsi d'aya,,Ke ban ganeba kin qara sakani a duhu...Bari nayimiki gwari gwari yadda zaki gane.Amo tayi saurin gyara zaman ta tace,Ina sauraronki fayyacemin yadda zan gane"Dariya salame ta sakeyi irin dariyar nan na qeta Sannan tace ,Qin kar'ba yarinyar nan ze saka kowa ya dinga yimiki kallon muguwar mace marar imani"Amma idan kika kar'beta za a dinga kallonki a matsayin mace me kirki da tausayi,Ko shi kansa malam se kinfi samun abunda kikeso a gurin sa,,Sannan Kuma yarinyar nan macece 'Da zarar ta fara tasawa zaki iya jaura da ita,Ki dinga kasamata talla kullum,,Sannan kuma ki dinga 'bata ta a idon malam da na mutane,Hakan ze saka mutane su dinga yimata kallon shed'aniyar yarinya marar tarbiyya "Ke kuma kowa ze dinga tausayamiki da tunanin yarinyar tana cutar da ke Itada y'a mace ce,Duk rintsi bazata ta'ba kaucewa umarni...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.