Chapter 1
by @khairatup01
INUWAR JIYA
NA
UMMULKHAIR S PANISAU
*Wannan ƙirƙiraren labari ne,ban yi shi don rayuwar wani ko wata ba,idan an samu wani kamanceceniya arashi ne kawai.*
O1
"Ba za ki je Jos ba."
Ta ɗaga kanta daga kallon wayar da take yi ta kalli mahaifin ta. Da irin mamakin nan kamar bata ji abin da ya faɗa da kyau ba.
"Daddy?"
"Cewa nayi ba za ki je Jos ba."
Ta sauke wayar a hankali kan cinyarta.
"Amma,Daddy aiki zan je."
"Koma mene ba za ki je ba."
Tayi shiru na wasu ya sakanni. Dama tun safe ta lura da irin kallon da yake ta mata tunda ta sanar masa da tafiyar ta zuwa Jos.A lokacin bai ce mata ƙanzil ba sai yanzu da ya gama saita kan shi. Tunda editan ta ya gaya mata zata je Jos wani aiki ta san cewa akwai ƙura. Abin da ya sa ma take mamakin abinda ya faɗa saboda ta san ba wai damuwa ce irin ta uba ga yar shi ba ne don zata yi tafiya ba, Wanann wani abu ne na daban da take gani a cikin idanunsa.
"Daddy gaskiya wanann ba daidai ba ne."
Ya ja numfashi ya gyara zamansa yace "Ba za ki je ba." A karo na ba adadi."
"Why?"
"Sabo da bana so."
Ta sauke ajiyar zuciya.
"Daddy wanann ba amsa ba ce ba gaskiya, ka gaya min me yasa ba ka son na je Jos."
A tsawace yace "Rania."
"Daddy don Allah kar ka sa abin nan ya yi wani iri. Ni fa yanzu ba ƙaramar yarinya ba ce na wuce munzalin da za ayi min kulle."
"Ba maganar shekarun ki nake miki ba magana ce na ke miki saboda na isa kuma ni ke da iko da ke."
"Daddy da me yasa baka yi ikon ba?"
Ya yi shiru.
Rania ta kalle shi. Ta lura da yadda ya matse hannunsa a kan armrest ɗin kujerar.
"Bana son garin Jos kin sani kuma kin san dalili."
"Ni ma Daddy bana son zuwa, kuma dalilin da ya sa ba ka son garin nima ya shafe ni."
Ya kalle ta yace "Then don't go."
Ta ɗan yi murmuhshi haɗe da tsugunnawa a gaban shi kusa da ƙafar shi.
"Daddy aiki ne zai kai ni ba wai hutu zan je ba."
"Na fi so ki gayawa Editan ki ya aika wani ba ke kaɗai ba ce kike aiki a can ba."
"Daddy ba zai yiwu ba."
"Why?"
"Saboda aikina ne."
"Dole sai ke?"
"Daddy the Meridian Post fa." Ta dafa goshinta sai kuma ta sauke ta ci gaba da magana."Ni ce investigative journalist da aka tura, so yes it is my case."
"Ba ki fahimta ba har yanzu."
"Daddy ka fahimtar da ni."
Daddy ya yi shiru ya kasa cewa komai. Tun da can Rania na da taurin kai komai zata yi zata kafa maka hujja kai ma kuma in zaka yi sai ka kafa mata hujjar da zata gamsar da ita har ta ji Yes kana da gaskiya. Ya riga da ya bata freedom ɗin yin duk yadda take so saboda wasu dalilai na shi. Baya daga cikin iyayen nan da suke hana yaransu yin abinda suke so amma yau ya kafa ya tsare saboda garin da aka tura ta wanann karon yana da tsohon tabo da shi.
Wata murya daga bayan su ta ce "Tun farko na gaya maka ka bar wanann maganar Rania ba zata saurare ka ba."
Rania ta juya tayi mici-mici da idanunta. Matar mahaifinta ce daga haka bata da wata alaƙa da ita.
Daga kitchen ta fito tana goge hannu da towel. Tun tana kitchen take jin takkadamar uba da yar wanda ta san babu yadda za ayi yar ta rusuna daga na ta muradin.
"Ke Rania kina ɗaukar komai kamar wasa ba kya jin magana Jos ba Lagos ba ce."
Rania ta kalle ta.
"Ban tambaye ki ba, bana buƙatar shawarar ki."
Ta tsaye tana kallon ta ba mamaki take ba inda sabo ta saba jin fiye da haka.
"Rania!" Daddy ya kira ta da ƙarfi.
Bata ganin zata iya janye idanunta daga cikin na ta saboda bata gama da ita ba.
"Daddy, kai ne mahaifina wannan batun babu ja kuma babu wai amma wannan." Ta faɗa tana nuna ta da yatsa.
"Bana son tana shiga maganata da kai."
"Sai na shiga ai ni matar mahaifin ki ce."
"Haka nake son ji dama. Ke matar mahaifina ce ba mahaifiyata ba." Falon ya yi tsit kamar anyi ruwa an ɗauke.
Ta sunkuya ta ɗauki wayarta da ke kan sofa ta sake ce mata "Saboda haka ki zauna a matsayin ki na matar Daddy,ni kuma zan zauna a matsayin ɗiyar sa."
Da tsananin damuwa Daddy yake kallon Rania ransa ya kai ƙololuwa wurin ɓaci."
"Rania, wanann ba ɗa'a ba ce, ba haka ake magana da babba ba."
"Na sani." Ta faɗa a sanyayye ta gama gajiya da muhawarar.
"Ita ce ta shiga abinda bai shafe ta ba ta sani bana son tana shiga abin da ya shafe ni amma bata ji da gayya take yi don ta saka ni magana, na gaji."
Ta buɗe baki zata yi magana. Rania tayi saurin tarar numfashi ta tace "Please. Ba ruwan ki don Allah. Ki bari mahaifina ya gaya min ba ke ba."
Ta juya ta kalli Daddy tace "Daddy zan tafi Jos magana ta ƙare."
"Rania..."
Amma bata tsaya ba tana hawa sama tana magana "Ba tarewa zan yi a can ba zuwa zanyi nayi aiki na dawo ka kwantar da hankalin ka I'll be fine kuma ina son ka."
Ta shige ɗakinta. Ta rufe ƙofar a hankali, ta dauko handbag ta ajiye a kan gado,sannan ta buɗe wardrobe ta ɗauko wata ƙaramar jakarta ta ajiye a kan gado ita ma.
Bata san ya aka yi ba sai gani tayi Daddy ya shigo ɗakin.
"Tunda ba za ki ji abinda na ce da ke ba. Muryar shi ta daki kunnuwanta ta ajiye hijab ɗin da ta ɗauko ta juya.
"Daddy!"
"Na fi son ki Saurare ni. Bana son ki je can bana so."
"Na sani Daddy amma wanann fa dama ce na samu wasu damarmakin kuma ba kasafai ake samun su ba wannan babban al'amari ne zan je na binciko kamata ya yi kayi alfahari da ni muna da yawa amma ni aka zaɓa it's an honour."
"Don Allah yata ina son ki bar wanann assignment ɗin."
Ta wangale baki tace "Daddy na bari fa ka ce."
"Eh ki bari."
Saƙo ya shigo mata daga The Meridian Post Travel Desk.
*Your ticket and travel details have been confirmed.*
Passenger:-Rania Sulaiman.
Route:Lagos-Jos.
Departure: 2:15pm.
Flight:AS 217
Seat:14A
*Your colleague,Hamza Bello,has been assigned to pick you from the airport and assist you upon arrival in Jos.*
Ta sake duba saƙon ta buɗe attachment ɗin. Ticket ɗinta ne. CONFIRMED.
Ta saka wayar cikin handbag ɗin ta.
"An turo min details komai ya kammala am going kayi min addu'ar samun nasara."
Ta saka after dress kan wando da rigar da ke jikinta ta yafa mayafin a kan. Ta ɗauki handbag ta saka a kafaɗa ta sauke suitcase ɗin tace "Hamza zai zo ya ɗauke ni daga airport."
"Kin riga kin shirya komai kenan?"
Ta ɗan yi murmuhshi. "Daddy aiki ne."
Ba yadda ya iya haka ya sauke ajiyar zuciya yace "Idan kin je ki kirani, kafin ku tashi ma ki kira ni."
Ta yi murmuhshi ta kama hannun shi tace "Daddy ka fi kowa."
Ya shafa kanta. Ya karbi suitcase ɗin ya saukar mata da shi har mota ya kai mata.Ita dai Matar shi Hajiya Sa'a ta bi bayansu da kallo haɗe da taɓe bakinta. Inda sabo ta saba ganin yaƙinsu cikin mintuna kaɗan kuma su shirya ta saki tsaki ta koma kitchen don ƙarasa girkinta.
Ya zura kan shi ta bayan motar yace "Kar ki manta ki kira ni."
"Zan kira ka Daddy in sha Allah."
"Allah Ya tsare."
"Amin."
"Aminu ka tafi da ita a hankali."
"An gama yallaɓai."
Har suka fita daga gate yana ɗaga mata hannu.
*
Ta jingina bayanta da kujerar da ke kusa da taga,idanunta a kan agogon bangon cafe ɗin.Mintuna ashirin ne suka rage kafin lokacin boarding,amma kamar yadda ta saba rashin haƙuri ya riga da ya fara kamata.Ta ɗaga cup ɗin coffee ɗinta zuwa kan leɓɓenta,sannan ta yi tsaki.
"Wannan airport ɗin kamar ana azabtar da mutum da gangan."
"Me airport ya miki?"
Ta ji wata murya daga sama. Ta daga kai sama ta ga wani matashi tsaye a gabanta,yana kallon kujerar da ke gafenta.
"Zan iya zama a nan?"
Ta ɗaga masa kafaɗarta.
"Idan baka da damuwa za ka iya zama a kusa da wadda take fushi da airport."
Ya yi murmuhshi. "Zan iya jurewa."
Ya zauna.
Ta sake kallon agogon.
"Flight ɗin makara ya yi?"
"Ban sani ba."
Ta juya ta kalle shi.
Ya kalle ta yace "Ta yaya mutum zai zo airport bai san Flight ɗinsa yaushe zai tashi ba?"
Ta watsa masa harara sannan tace "Ce maka nayi ban san lokacin da zan tashi ba ko duk jan magana ne?"
Ya yi dariya a hankali.
"To ai kin ce baki sani ba."
"Ban ce ban san lokacin Flight ɗina ba cewa nayi ban sani ba ko zai makara ba."
"Oh!"
Ta cigaba da sabgrta da waya. Tana ƙunkunai.
"Duk lokacin da mutum yake da wani appointment ɗin sa sai suyi ta yin delay kamar ba su san kana da aiki ba. Mtsw."
"Maybe akwai dalili ne."
"Duk lokacin da suke cewa akwai dalili sai ka rasa meye ma dalilin."
"Ke ba kya son tafiya a jirgi ne?"
"Ba haka ba ne."
"To me ne?"
"Bana son jira ne."
"Ah. Jiran boarding,jiran take-off,jiran lauggage...komai jira ne."
"Amma idan jirgin ya tashi fa?"
Sai tayi shiru kamar ba zata iya magana ba sai kuma tace "Shi ma ba na so."
Ya sa dariya a hankali.
Ta kalle shi.
"Me?"
"Nothing."
"Ka yi dariya?"
"Na yi saboda yadda kika yi maganar."
"Ai gaskiya nake faɗe."
"Na gane."
Ya jingina bayansa.
"First time ɗin ki ne?"
"Not at all."
"Then ya kamata ki saba."
"Mutum zai saba da rashin haƙuri ne?"
"Ya girgiza kai yana murmuhshi."
"Maybe."
Aka soma announcement daga nesa cewa boarding zai fara nan da mintuna goma sha biyar.
Ta kalli wayarta.
"Finally."
Ya tashi.
"Looks like it's time."
"Your flight?"
"Yeah!"
Ta yi masa sallama da kai.
"Safe journey."
"Same to you."
Ya juya zai tafi,sai kuma ya tsaya yace "By the way..."
Ta daga kai.
"Hmm?"
"Ki rage fushi da airport."
Ta ɗaga girarta.
"Ban da tabbacin zan iya."
Ya yi murmuhshi.
"Try." Ya faɗa ya juya da sauri ya tafi.
"Waye wanann haka?" Ta tambayi kanta.
*
Ta shiga cikin jirgin tana duba wayarta,handbag ɗin ta a saƙale a kafaɗarta.
Saƙon editan ta take dubawa.
"Don't come back without something."
Ta ja numfashi.
"Ta sani wanann ba irin sauran tafiye-tafiyen da take yi ba ne .Wannan tafiya ce da ta shafi wani babban al'amari. Al'amarin da aka shafe babinsa shekaru da suka wuce,al'amarin da an san farkonsa amma ba a san ƙarshen sa ba." Ta saka wayar cikin jakarta,sanann ta duba boarding pass ɗinta.
Seat 14A.
Ta shiga cikin aircraft ɗin,ta zauna kusa da taga,ta ɗaura seat belt,sannan ta fito da ƙaramin notebook ɗinta.
Sunaye,dates,adresoshi,tambayoyi ,komai yana ciki. Ta buɗe wani page da aka yi wa alama da jan biro.
CASE FILE:2019.
Ta ɗan dakata tana kallon rubutun. Sai kuma ta ji ance "Miss."
Ta ɗaga kai ta kalli mai mata magana cabin crew ce tsaye kusa da ita.
"Would you mind putting your notebook away for take off?"
"Oh,sorry."
Ta rufe notebook ɗin.
Bayan yan mintuna aircraft ya soma cika da matafiya.
Rania na kallon masu shigowa ɗayan bayan ɗaya,har sai da idanunta suka tsaya kan mutumin da ya shigo daga baya.
Uniform,Captain's stripes,fuska cike da nutsuwa. A hankali tace "Kai wannan ai shi ne mutumin nan na cafe."
Rania ta lumshe ido sau ɗaya.
Sai kuma tace "No way."
Ya wuce ba tare da ya lura da ita ba.
Muryarsa ta fara tashi daga cikin speaker.
"Good afternoon ladies and gentlemen.This is your captain speaking.."
Rania ta zauna shiru cike da mamaki tace "Ita ce muryarsa ce ba mafarki nake ba." Ta faɗawa kanta a hankali.
"Captain Rayyan Zayd speaking..."
Ta buɗe baki kaɗan.
"Captain?"
Sai kuma tayi murmushi a hankali."Mutumin da yace da ita ta rage fushi da airport shi ne zai tuƙa su zuwa Jos." Ta girgiza kanta.
""Allah Ya so ni ban zage shi ba."
"Good afternoon ladies and gentlemen. Muryarsa ta cika aircraft ɗin cike da confidence.
"This is Captain Rayyan Zayd speaking from the cockpit. On behalf of the entire crew, I'd like to welcome you abroad. We are currently preparing for depature ,our estimated Flight time will be approximately one hours and fourty minutes." Ya ɗan dakata kaɗan sai ya ci gaba.
"The weather along our route is expected to be fairly clear,with some light turbulence Possible during the flight.So,Please remain seater with your seat belt securly fastened whenever the seat belt sign is on."
Rania ta kwanta jikin kujera jikin ta ya mata sanyi muryarsa ta banbanta a nan ba kamar ɗazu da ya zo mata a matsayin matashi mai barkwanci ba. Yanzu akwai authority a cikin muryarsa,wanda dole ne a saurare shi.
"We understand that some of You may not be the biggest fans of flying..."
Wasu daga cikin passengers suka yi dariya. Ta ɗaga gira tace "Wait."
"But,i promise You are in good hands."
Ta kalli gabanta ta runtse ido.
"Except ,of course,those of you who are still angry with airport."
Rania ta buɗe idanunta tace "Me?"
Tuni ta gane da ita yake. Ita yake aikawa sako a sauƙaƙe.
"Seat back,relax,and enjoy the flight."
Aka sake yin dariya.
Bata yi aune ba ta ji yace "And the lady from the cafe..."
Sai Rania ta daskare.
"I hope You have a better opinion of airports by the time we land."
Ta sa hannu ta rufe fuskarta da tafin hannunta.
"Ya Allah..." Ta faɗa a hankali cike da kunya.
Cabin crew dake gefen ta tace "Do you know the Captain?"
Rania ta sauke hannunta.
"Unfortunately."
Tayi dariya.Rania ta kuwa ta maida kai sama tana kallon ceiling ɗin aircraft ɗin.
"This is going to be a long one hour and fourty minutes." Ta faɗa a hankali. Sai kuma ta mayar da kanta kan wayarta.
Ta buɗe email ɗin da editanta ya aiko mata da safe.
*SUBJECT:JOS FILE." Ta danna shi.
"Ina son draft ɗin ki na farko na binciken nan ya kasance a cikin kwana biyar. Kar ki laru da iya tsofaffin bayanai. Ki nemo original record,kiyi magana da wanda kika samu a wurin, sannan abu mafi muhimmanci,find out me yasa maintenance reports was altered. Ana son a binne wannan labarin ko ta halin ƙaƙa ,ki binciko waye kuma meye dalili." Ta kashe wayar tana nazarin saƙon ta sa hannu a kan haɓa tana kallon taga.
Clouds sun fara bayyana daga nesa yayin da aircraft ɗin yake shirye-shiryen tashi.
Shekaru bakwai da aka binne wannan case ɗin.
Shekaru bakwai da iyalan waɗanda suka mutu suke rayuwa da tambayoyin da ba su samu amsa ba. Kuma yanzu,the Meridian Post na son ta tono komai.Rania ta buɗe handbag ɗinta ta fitar da ƙaramin notebook.
A shafin farko ta rubuta.
*AURELIA SKIES FLIGHT 217.*
Daga ƙasa kuma ta rubuta *JOS---2019*
Ta ɗan dakata da rubutun sai kuma ta kara rubuta wa.
*Waye ya yi ƙarya?*
Ta Kalli rubutun. A daidai lokacin aircraft ɗin ya fara motsawa. Ta dafe seat belt ɗinta.
"Okay." Ta gayawa kanta ,ta jingina da kujerar,tana kallon runway ta taga.
Aircraft ya fara gudu sai ya tashi sama. A zahiri ba ta jin tsoron jirgi sosai.
Abin da ba ta so shi ne rashin iko a cikin jirgi, ba ita ke da ikon sanin abin da ke faruwa ba.Ta rufe idanunta na yan daƙiƙu. Daga baya ta ji muryar wata yarinya tana tambayar mahaifiyarta.
"Mummy jirgin faɗuwa zai yi?"
Rania ta buɗe idanunta. Mahaifiyar yarinyar ta yi dariya.
"A'a sweatheart."
Rania ta kalli ceiling ɗin aircraft.
"Hopefully." Ta furta.
"Me kika ce?"
Ta juya da sauri.
Wata tsohuwa ce da ke zaune a kan kujerar gefenta.
Rania ta murmusa.
"Ba komai."
Tsohuwar ta kalle ta na ɗan lokaci sai kuma tace da ita "Yau kika fara hawa jirgi?"
"A'a."
"Amma me yasa kike a tsorace."
"A'a bana tsoro."
"Kina yi."
Ta yi murmushi tace "Ni yar jarida ce,a bisa ka'idar aikinmu dole ne ki dinga ganin mu a cikin damuwa."
Tsohuwar tayi dariya sanann tace "Wow, journalist?"
"Eh."
"Me za ki rubuta a Jos?"
Sai Rania tayi shiru.
"Tambaya ce mai sauƙi amma ba zata iya bata amsar ba."
"Kawai wani tsohon labari."
"Wasu lokutan tsofaffin labarai sun fi dukan zuciyar mutum."
Rania ta kalle ta sosai maganar ce ba ta yi tsanmanin za ta ji daga baƙuwa a cikin jirgi ba."
A hankali tace da ita "Maybe."
Ta sake buɗe notebook ɗin ta.
Sai dai kafin ta rubuta wani abu suka sake jin muryar Captain Rayyan daga speaker.
"Ladies and gentelmen,we are now cruising at thirty thousand feet. The weather sheds looks clear,so you can sit back and enjoy the rest of your journey."
Rania ta murmusa.
Sai kuma ta ji ya sake cewa.
"I checked the airport is no longer angry with you."
Wasu daga cikin passengers still suka saka dariya wasu kuma suka murmusa.
Ta girgiza kai tace "Arrogant."
Tsohuwar da ke kusa da ita yace "Waye?"
"Captain."
"Me yasa?"
"Saboda yana tunanin ya iya barkwanci."
"Watakila hakan ne."
Rania tayi saurin cewa "Don Allah kar ki goya masa baya."
*
Bayan Awa ɗaya da mintuna arba'in.
"Ladies and gentelmen,we have bugun our descent into Jos."
Rania ta rufe notebook ɗin ta.
Wannan karon ta haɗe rai tace "WHO LIED."
Ta saka a cikin jakarta.
Jos,garin da ta sani tun yarinyar ta. Garin da mahaifinta ya koya mata son sanyi da safe, tsaunuka,da dogayen hanyoyin da suke sa mutum ya yi tunani. Sai dai yau ta zo ba don ziyara ba sai don tono abin da wasu suka kashe shekaru bakwai suna ɓoyewa.
Aircraft ɗin su ya sauka lafiya. Passengers suka fara tashi.
Rania ta tsaya tana jiran mutane su rugu ta ɗauki jakarta.
Ta yi wani ɗan motsi tana ƙoƙarin sauke jakar daga overhead compartment.
"Let me help you."
Ta gane mai muryar ta juya.
"Rayyan."
Wannan karon yana sanye da uniform ɗinsa. Ya ɗaga jakar kafin tace komai.
Tace "Na gode."
"Ba komai."
Ya kalle ta yace "Ra'ayin ki ya sauya a kan airport yanzu?"
Ta karɓi jakarta tace "Ina nazari a kai dai."
Ya yi murmushi.
"Fair enough."
Ta wuce shi.
Bayan tayi taku kaɗan sai kuma ta tsaya ta juya tace "Captain."
"Na'am."
"Baka iya bada dariya ba."
Ya yi dariya sai ya shafa kansa yace "Zan ɗauki hakan a matsayin wani ci gaba." Ta girgiza kai ta juya ta tafi.
Ya bi bayanta da kallo ya ɗan jima a cikin aircraft ɗin Rania kuwa ko waiwaye bata yi ba.
Saboda tana da aikin da ya fi muhimmanci fiye da barkwancin Captain.
Rania na jan ƙaramin suitcase ɗin ta fita waje. Wata iska ta kaɗa a kan fuskarta kamar ta taɓa fuskarta ta wuce. Ta tsaya ta lumshe idonta a hankali.
Wani sanyi ya taɓa ta, Jos kenan.Ta gyara gyalen ta da ya zame a hankali. Ta ci gaba da tafiya. Sai da ta isa arrivals sannan ta tsaya. Ta fara zare idanu cikin mutane inda ake jiran fasinjoji.
Ta buɗe wayarta. Nan ta ga saƙon Hamza.
"Ina waje ,Baƙar Toyota. Kar dai ki ce kin manta fuska ta."
Tayi murmushi.
Ta ɗaga kai tana neman motar. Sai ta hango shi a jikin wata baƙar Toyota,yana riƙe da wayarsa.
Ya ɗaga mata hannu.
"Rania!"
"Hamza!"
Ta tura suitcase ɗin ta gaban shi.
"Dan da ƙyar." Ya faɗa. Ya ja suitcase ɗin.Finally, kin iso mintuna talatin na ɗauka ina jiran ki a nan."
"Ba laifina ba ne flight ɗin ne ya yi delay."
Ya buɗe trunk ya saka suitcase ɗin a ciki.
Rania ta shiga cikin mota.
Hamza kuma ya shiga ya zauna a driver's seat,ya kunna engine,sanann ya kalle ta.
"Barka da sake shigowa Jos."
Ta kalle shi.
"Bana so."
"Me ne ba kya so?"
"Kar ka fara."
Ya yi dariya.
"Har kin fara complain duka mintunan ki nawa da zuwa?"
"Ban yi complain ba."
"Ga shi nan kin ce min don't."
"Ai na san ka ne da tsokana shi ya sa."
Ya girgiza kai "Ba za ki canja ba kina nan a Rania ɗin ki."
"Unfortunately." Ta faɗa tana dage kafaɗarta.
Ya fitar da motar daga parking area. Sai motar tayi tsit na ɗan lokaci ba wanda yace komai.
Rania na kallon waje ta ciki bayan ta zuge tagar. Wasu wuraren sun canja,wasu kuma ba zasu taɓa canjawa ba.
Ta ga layin da ta saba bi don zuwa makaranta. Wani murmushi ya ƙwace mata. Hamza ya lura da hakan yace da ita.
"Memories?"
"Hmm."
"Kin fara murmushi."
"I am allowed to."
"Na zata kin tsani garin Jos?"
"Ban tsani Jos ba."
"Amma Daddy ya tsane ta."
"Haka ne."
Ya kalle ta na ɗan lokaci kafin ya mai da kan shi kan titi.
"Har yanzu bai gaya miki asalin dalilin ba?"
"Har yanzu."
"Na san ba iya wancan dalilin ba ne kawai."
"Na sani."
"Intresting."
"Very."
"Ki matsa mai da tambaya."
"Ba kalar tambayar da ban yi ba."
"To."
"Ko ka san wani abun Hamza?"
Ya kalle ta da sauri yace "Wanann investigative instincts ɗin na ki sun fara aiki kenan?"
"Ka bani amsa."
"Da gaske ban san komai ba."
"Ya yi." Ta faɗa tana mayar da kanta jikin taga.
Hamza ya ɗan kara saurin mota.
"Anyway an gama komai na masaukin ki, the hotel is ready. Your room has been booked na kwana biyar."
"Biyar."
"Haka Editor ya faɗa."
"Na sani."
"Gobe zamu fara."
Rania ta buɗe handbag ɗinta ta fito da notebook ɗin ta.
"Actually,yau zamu fara."
Hamza ya kalle ta.
"Da daddare kuma?"
"Zamu duba tsofaffin files."
"Rania."
"Hmm?"
"Baki gaji ba? Tafiyar awa ɗaya da mintuna arba'in fa kika yi."
"Sai me?"
"Ya kamata ki huta."
"Idan na samo gaskiya sai na huta."
Ya yi dariya.
"Shi yasa suka zaɓe ki suka aiko ki."
Ta ɗaga masa gira.
"Me yasa?"
"Saboda sun san kina da taurin kai."
"Ya zama jinina."
"Nima haka."
Ta buga masa notebook ɗin a kafaɗar sa.
"Ka yi tuƙi malami."
Ya yi dariya.
"Okay ma."
Ya ci gaba da tafiya a kan titi.
Ta jingina da jikin kujera idanunta na kallon kan tituna.
Duk yadda take ƙoƙarin mayar da kanta a kan assignment ɗin ta ,sai ta ji tana son sanin dalilin da ya sa mahaifinta ya tsani garin da aka haife shi,garin da suka taso. Me ya faru shekaru bakwai baya wanda bata sani ba? Me yasa baya son ta zo garin? Duk waɗanan tambayoyin sun cika mata kai tun fil'azal ga shi wanda zai bata amsar su ya mata katanga da sanin su.