INUWAR JIYAFree

ArewaPen original

MysteryFreeOngoing

INUWAR JIYA

  • 1views
  • 6chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

ongoing

No synopsis yet.

About the author

My name is Khairi, and I am a passionate writer who finds life in words. Writing is not just a hobby for me; it is my voice, my escape, and my power. I specialize in emotional and dramatic storytelling, especially stories centered around love, jealousy, deep affection, and human ...

More from @khairatup01

Sample · Chapter 1

INUWAR JIYANAUMMULKHAIR S PANISAU*Wannan ƙirƙiraren labari ne,ban yi shi don rayuwar wani ko wata ba,idan an samu wani kamanceceniya arashi ne kawai.*O1"Ba za ki je Jos ba."Ta ɗaga kanta daga kallon wayar da take yi ta kalli mahaifin ta. Da irin mamakin nan kamar bata ji abin da ya faɗa da kyau ba."Daddy?""Cewa nayi ba za ki je Jos ba."Ta sauke wayar a hankali kan cinyarta."Amma,Daddy aiki zan je.""Koma mene ba za ki je ba."Tayi shiru na wasu ya sakanni. Dama tun safe ta lura da irin kallon da yake ta mata tunda ta sanar masa da tafiyar ta zuwa Jos.A lokacin bai ce mata ƙanzil ba sai yanzu da ya gama saita kan shi. Tunda  editan ta ya gaya mata zata je Jos wani aiki ta san cewa akwai   ƙura. Abin da ya sa ma take mamakin abinda ya faɗa saboda ta san ba wai damuwa ce irin ta uba ga yar shi ba ne don zata yi tafiya ba, Wanann wani abu ne na daban da take gani a cikin idanunsa."Daddy gaskiya wanann ba daidai ba ne."Ya ja numfashi ya gyara zamansa yace "Ba za ki je ba." A karo na ba adadi.""Why?""Sabo da bana so."Ta sauke ajiyar zuciya. "Daddy wanann ba amsa ba ce ba gaskiya, ka gaya min me yasa ba ka son na je Jos."A tsawace yace "Rania.""Daddy don Allah kar ka sa abin nan ya yi wani iri. Ni fa yanzu ba ƙaramar yarinya ba ce na wuce munzalin da za ayi min kulle.""Ba maganar shekarun ki nake miki ba magana ce na ke miki saboda na isa kuma ni ke da iko da ke.""Daddy da me yasa baka yi ikon ba?"Ya yi shiru.Rania ta kalle shi. Ta lura da yadda ya matse hannunsa a kan armrest ɗin kujerar."Bana son garin Jos kin sani kuma kin san dalili.""Ni ma Daddy bana son zuwa, kuma dalilin da ya sa ba ka son garin nima ya shafe ni."Ya kalle ta yace "Then don't go."Ta ɗan yi murmuhshi haɗe da tsugunnawa a gaban shi kusa da ƙafar shi."Daddy aiki ne zai kai ni ba wai hutu zan je ba.""Na fi so ki gayawa Editan ki ya aika wani ba ke kaɗai ba ce kike aiki a can ba.""Daddy ba zai yiwu ba.""Why?""Saboda aikina ne.""Dole sai ke?""Daddy the Meridian Post fa." Ta dafa goshinta sai kuma ta sauke ta ci gaba da magana."Ni ce investigative journalist da aka tura, so yes it is my case.""Ba ki fahimta ba har yanzu.""Daddy ka fahimtar da ni."Daddy ya yi shiru ya kasa cewa komai. Tun da can Rania na da taurin kai komai zata yi zata kafa maka hujja kai ma kuma in zaka yi sai ka kafa mata hujjar da zata gamsar da ita har ta ji Yes kana da gaskiya. Ya riga da ya bata freedom ɗin yin duk yadda take so saboda wasu dalilai na shi. Baya daga cikin iyayen nan da suke hana yaransu yin abinda suke so amma yau ya kafa ya tsare saboda garin da aka tura ta wanann karon yana da tsohon tabo da shi. Wata murya daga bayan su ta ce "Tun farko na gaya maka ka bar wanann maganar Rania ba zata saurare ka ba."Rania ta juya tayi mici-mici da idanunta. Matar mahaifinta ce daga haka bata da wat...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters6
premium0

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play