Furen Zuciya. Flower of the heart.

Chapter 7.

by @nasreelrl

🌸🌹🌺FUREN ZUCIYA.
 Flower of the heart.

   By Nasreel R.L.
      🤍A hausa love story…….

Chapter 7;


Round zuwa round na inspection akayi musu da saida suka shafe wajen 45minutes. Tun daga kan wayoyinsu da aka sasu cikin wani machine aka sasu sukayi signing permission form na inspection akayi scanning wayoyinsu, sannan aka koma kan kayansu gabadaya babu abunda aka bari sannan aka dawo kansu. 

Physical check aka fara musu sannan aka shiga dasu wani instant exray vision machine dan a duba har cikin jikinsu koda sun shigo da wani abu. Bayan an gama wannan sannan aka tafi dasu department of health inspection a same bus data kawosu. Nan aka dauki jininsu akayi musu test na infectious diseases, dakuma test na ciki domin ba’a bari mace me ciki data kusa haihuwa shiga kasar dan basu bada citizenship bakuma sa bari a haifi yaronda iyayensa ba residential citizens bane na kasar. Tests din sundau  wajen 1 hour sannan akayi referring dinsu zuwa department of immigration. Nan sukayi signing contract na shiga kasar.

Extensive contract ne dayake dauke da abubuwa daban daban. Tun daga kan dokoki da dole mutun yabi dakuma hukunce hukuncen su, dakuma lisense na anfani da wasu abubuwa da citizens kawai ke amfani dashi da sauransu. Za’a saka mutun ya karanta tun daga farko har karshe wajen 35 pages sannan yayi rantsuwa cewa yagane kuma zaibi duk abunda yake a takardar, idan aka samu akasin hakan toh zai anshi hukunci daidai laifinsa. Duk wannan ma saboda su citizens ne badan haka ba da tsaurin tsaro da inspection din yafi haka. 

Suna gama wannan sukayi signing aka daukesu zuwa border to border Airport na kasar da zakayi boarding zuwa garin dakake so. ta cikin bordern ake shigarta. aka hadasu tareda kayansu aka dawo musu da wayoyinsu. Ummi taso su samu lounge su huta dan sunsha gajiya ga 18 hour flight gakuma wannan grueling inspection din na wajen 3 hours saidai plane dinda akayi musu assigning yanzu zai tashi, tasan a Ghair Muaddal magana daya ake tazauna basa alfarma basa tankwarawa kowa.

A haka suka shiga plane din. karamar plane ce compared to commercial plane amma kuma ba karama kamar normal private jets ba, saidai cikinta sosai you will think a private jet kake ko’a first class lounge. Basa using manyan jets a cikin kasar for wanda suke shigowa kasar dan a rana baifi mutun 12 suke bari su shigo kasar ba, sannan kwana uku a wata kadai ake shigo da mutane dan haka 36 people a month kadai suke dauka. 

Miral kuwa koda sukayi boarding plane din dukda opposite dinsu Ummi da Hanat take dan gurin mutun hudu ne kowani dan lounge dayake a zagaye offering privacy da bazakaga wani a cikin plane din ba kowa a zagaye yake yanayin zamar bai dameta ba. Da on a normal occasion ne bazata saki jiki ta zauna dakyau ba suna kallonta tana kallonsu, saidai yanda takejin gajiya a jikinta batasan sanda ta kwantar da kanta a headrest ba ta rufe idanunta tana jan dogayen nunfashi tana fitarwa a hankali. 

Ummi da Hanat kansu a gajiye suke dan suna zama ko 5 minutes basuyi ba Hanat tahau bacci. Ummi kuwa bacci ya kafe a idanunta tunane tunane kawai ke yawo a kwakwalwanta. 

3 hours sukayi kafin su isa capital of Ghair Muaddal wato ‘SARMRUL QUWAA’, da mutanen kasar ke kira da SARM. 

Kasar GHAIR MUADDAL kasa ce da babu wanda zaice ga lokacinda ta kafu. Kasace da shekaru dasuka wuce ita ta mulki duniya cikin salon da ba’a taba yinshi ba. Ta kafu ta wanzu ta kafa mulki da iko a fadin duniya baki daya, tayi yaki da mallakar manya manyan kasashe zuwa kasanta, kasar da tunda aka kafata da babu wanda zaice ga lokacinda ta kafu har yau babu wanda yacita yaki, sannan tunda ta kafu gaba takeyi bata baya. 

Kasace da tarihinta dakuma mulkinta yadade da shafewa ga mutanen dake wajenta. Bakuma dan ta fadi bah, ko karfin mulkinta a duniya ya ragu bah, saidai dan ta cire kanta daga sauran kasashe, ta kafa kanta a matsayin duniyar kanta da bata bukatan sauran duniya, saidai duniya ta bukace ta. Mutane daidaiku ne shugabannin manya manyan kasashen duniya kadai sukasan da zamanta, dan ta bayan fage take mulkinta takuma cire kanta daga maps gabadaya. 

Ta kasance tanada landspan of approximately 40,000kilometer square. Kusan girman Asia gabadaya. 

Tanada states guda 12 da girman kowannenshi kamar wani country nakanshi yake, Monarch nation ne da Royal familyn kasar wato The TAUFEEQ BIN SAHIR Zaydeen Family ke mulka daga cikin capital state dinta SARMUL QUWAA datafi kowace state a ciki girma dakuma zama advanced. Duk wasu masu fada aji a kasar suna cikin capital dinta. 

Ta kasance tana karkashin mulkin Taufeeq Bin Sahir Zaydeen royal family tun daga kafuwanta babu fashi. Familyn Taufeeq sun kasance family dakeda kalilan mutane a cikinta, duk wani Vael Sultan( Sarkin kasar kenan) dayayi mulki baya haifar yara dasuka wuce Uku, duk yawan matanshi dakuma kuyangu basa wuce wannan Ukun. Yawancin yaran duk maza ne. Ba’a cika samun ya mace ba. Sannan namiji daya cikin su ke rai, dan sauran babu wanda ke haura shekara ashirin. Dan haka kwata kwata basuda yawa. 

Duk wani Vael Sultan dake mulki a kasar yasamu wani irin intense training da lokacin daya ansa mulki daga babansa zai kafa nasa mulkin mai nashi salon daya shafe na bayanshi. Mulki suke kafawa na gani na fada a aikace dan akan kasar zaka gane cewa mai rike da ita basa wasa. Tun daga kan yanda doka take aiki dakuma rapid advancement na essential areas of life and wellness na mutanen kasar zakasan akwai justice da kula daga masu mulkinta. Saidai kada kaso ka shiga baƙin su dan zaka gwammace bakazo duniya ba. 

Kasar Ghair Muaddal ta kara kafe sunanta shekaru talatin dasuka wuce lokacinda wata kasa dake wajenta ta kulla rebellion tareda samun goyonbaya da support daga manya manyan kasashen duniya sukayi kokarin shafe kasar Ghair Muaddal wanda a cikin hour biyu babu ragi ba kari da Vael Sultan Abdulmalik yayi musu alkawarin kammala yakin ya shafe kasar gabadaya da wasu irin drones da nuclear weapons da kasar Ghair Muaddal kadai ke kirkira da sarrafawa. 

Hakan yayi matukar tasar da hankalin shugabannin kasashen duniya dan basu taba ganin irin weapons da sukayi anfani da ita ba, dakuma zallar zalunci a cewarsu dan kasar gabadaya da wayanda ke cikinta suka shafar, sannan suka dauki shugaban kasar da duk wasu dasukeda hannu a cikin yakin zuwa kasar Ghair Muaddal har yanzu babu wanda yasan meya faru dasu. 

Tun daga ranar babu wata kasa data kara kokwanto ko tunanin zata kara da Ghair Muaddal dan Vael Sultan Abdulmalik ya isar musu da sako a aikace.

Mutane kasar dayawansu sunsan Fuskokin Mutanen royal familyn, mutun daya ne banda mutanen dake da manyan mukamai a kasar sukasan face dinshi shine Vael Rahem ( wato crown prince na kasar), harsai lokacin daya ansa kasar sannan mutanen kasar zasusan face nashi, haka dokar kasar ta tanada. 

Kasace datake so advanced on technology and medicine da wani abun bazaka so ka yarda cewa gaskiya neba. Wasu mutanen suna daukar hakan a cewar tsafi sukeyi, musamman ma akan technology. 

Miral tunda suka sauko daga plane zuwa private cars da The Zahir family suka turo musu latest edition bentley guda biyu white color a daukesu take bin airport din da kallo. Dukda shekaranta 16 a kasar tun haihuwanta saidai tama kasa gane koina da komai datake gani. Wani mahaukacin architecture ne akayi gine gine a kasar. A cikin shekaru biyu datayi bata zo kasar ba saitaji kamar bata taba sanin kasarba.

Komai daban ne a cikin kasar from the outside world architecture din kasar straight out of Sci-fi kamar wata futuristic city. Buildings din are specialized high rise skyscrapers masu wani round angles with complex interior da zakaji kamar zasu fado dan wasu are bendy. Ga historical style buildings kuma kamar domes manya manya ga drones dake yawo a sama. 

Specialized robots ne ke zagaye, kowanne na abunda akayi programming dinshi yayi, wasu driverless luggage cars ne dake daukar mutane daga exit na plane zuwa wajen airport din inda mutun zaihau mota, wasu kuma are stationed suna raba ruwa da snacks kamar fridge zaka gansu saidai sunada motion sensor dake detecting mutane dan haka one after another suke gungurawa da tires a kasansu kamar vending machine zakayi choosing a option abunda kakeso saisu ciro maka.

Hanat kanta dake feeling big girl bin komai take da kallo bakinta a sake, kasar ta hadu ba kadan ba as this is her second time a Ghair Muaddal first time dinta was two years ago datazo tayi spending 1 month saidai ji takeyi kamar bata taba zuwa ba yanda komai yayi advancing. 

Boarding wannan specialized driverless car din sukayi da luggage dinsu ya kawosu har waje sannan daya daga cikin securities da aka turo su daukesu ya gane face din Miral yayi musu magana tareda escorting dinsu zuwa motocin suka shiga. 

One hour drive ne from the Airport to the Zahir’s family residence. Mansion ne hadadde dayake cikin District 4 estate. Ungowoyin capital state din ana kiransu da District-District. Iya asalinka iya District dinda kake zama. District One dayake a tsakiyar Capital state din is reserved for the royal family. Palace din kasar anan yake da gidajen sauran royal family din. 

District Two kuma shine na manya manyan kasar, basuda sarauta saidai rike suke da duk wani harkar Oils da refineries na kasar dakuma wani bangaren cybersecurity na kasar dayasa daga royal family sai su a mukamai dakuma fada aji a kasar . Duka duka a district two family Daya ne kachal. Saidai sunada yawa sosai a cikin familyn, dan haka sun cike duk wai lungu da sakon district din. Sannan duk matan sarakunan kasar matansu daga district 2 suke. 

Sai kuma district three, shine na familynda tsofaffin generals na kasar, saidai yanzu kusan shekara 100 kenan basu rike wani mukami a military bah. familys ne masu asali dakuma kima. Sannan family biyu ne saidai sunada mugun yawa. 

District four kuma shine last district na manyan kasa. Shine na manya manyan yan kasuwa masu asali da suka rike spot dinsu tun kakan kakanni. Familys biyar ne a cikin district din, daya daga cikin familyn sannan kuma wanda yafisu arziki, fada aji dakuma asali shine familyn Zahir. 

Familyn Zahir sun kasance suna harkar gold dakuma diamonds dama sauran rare gems a kasar, babu kamarsu a harkar. Ba iya kasar suke business dinsu ba hatta sauran kasashen duniya sunayi. 

Districts din girma girma ne, ba kuma girma na wasa ba dan district daya ka shiga saikace wani state dinne na kanshi, district 1 dayake na royal house yafi kowanne girma dan zaiyi wajen 10 times the size of district 2, sannan district two yayi biyun district 3, hakama district 3 yafi district 4 girma. Dan haka manya manyan gidaje dake kowanni district ba girman wasa garesu ba. 

A harkar Arziki batareda wani mukami na military ko royalty ba babu family a Ghair Muaddal kamarsu babu kishiyarsu dan haka suna samun maximum respect sannan suna taka kujerarsu yanda yakamata. 

Cikin estate din Zahir family suka shiga dake zagaye da bishiyoyo buildings din ciki kamar an hada chinese style buildings da persian style architecture ne. Babban estate ne sosai with heavy security. Security men ne armed with guns ke patrol a cikin gidan. 

Wani irin kwalla ne suka ciko idanuwan Miral takasa yarda wai yau itace ta dawo gidansu. Ranar da tadade tana jira tana mafarki. Saidai yanzu ji kawai takeyi dama ta koma riyadh tacigaba da rayuwarta cikin kunci da tsangwamar su Hanat akan dawowarta nan. Sai yanzu da memories da 2years ago suka dawo mata kwakwalwarta kamar sabo taji danasanin dawowa dukda batada zabi. Inama ace kasa ta bude ta shanyeta  ta huta da wannan kuna da zuciyarta kemata. 

Tun ranar da abun ya faru bata kara bari memories din sundawo mata ba. Duk yanda tunanin ta yayi tsanani bata yarda ta tuno abubuwan dasuka faru. Ta burne su a bayan kwakwalwarta da whispers dinsu kadai takeji badai tajisu ba. Tayi tsammanin cewa ta riga ta birnesu, saidai dawowanta dakuma ganin yanda gidan yake yanda ta barshi saidai yan chaje chanje da ba’a rasa ba yayi mata wani mugun radadi a zuciyarta. 

Hannu takai ta share hawayen dake zarya a idanunta tareda sa mayafinta ta goge hawayen sosai tana jan dogayen nunfashi. Wani extreme anxiety ne ya diran mata lokacin da aka bude kofar motar ita batamasan an tsaya ba. Daidai gaban main entrance din main mansion din gidan dake a tsakiyar gidan aka tsaya. 

Kasa koda motsa idanunta that are glued to the people standing at the terrace tayi. Mutane uku ne a tsaye gefe da gefen junansu sai masu aiki dake cikin black and white dasuka fara ansan kayayyakinsu daga securities suna shigarwa ciki. 

Idanun Miral kan Mommynta ya fara sauka datake of average height tana kama da Miral saidai ba chanchan ba sannan Miral tafita kyau nesa ba kusa ba. Tana sanye da wata persian drape clothes dake jan kasa anyi mishi ancient persian sultanas design kamar wata sarauniya, face dinta dake under heavy make up daukeda wani sweet smile a lips dinta dayasha bright red signature lipstick dinta tana jiran fitowar big sister dinta dasuke uwa daya uba daya wato Ummi da niece dinta Hanat.

Gefenta kuma wata yarinya ce dabazata wuce 18 years ba suna kama sosai da Hanat saidai tafi Hanat kyau dan idanunta sun banbanta dana Hanat sunfi na Hanat girma sannan she looks slimmer tanada wani adorable beauty. Tana kuma kama da Miral sosai saidai still Bazaka hada kyansu da Miral ba dan Miral tafita kyau. 

Tanada tsawo dan zasuyi tsawo daya da Miral face dinta ba makeup jikinta sanye da silk pyjamas gashin kanta dayake wavy brown a sake har bayanta tana wasa da wani strand da yatsanta sai hamma takeyi face dinta babu alaman murmushi she looks bored tana taunan gum a hankali ko kallon inda su Hanat dake tahowa gurinsu batayiba. 

Gefenta kuma wata yarinya ce bazata wuce 18 ba itama kamanninta daban kana ganinta kasan tahada jini da europeans saboda mediem sized almond blue eyes da delicate features irin wayanda idan ka kallesu they look so innocent dakuma hasken fatarta yafi na mutanen Ghair Muaddal haske. 

batada tsawo sosai saidai bazaka kirata da gajeriya ba. Tana sanye da pink top daya kama jikinta tanada dan jiki da big boobs, tana sanye da wani baggy jeans face dinta da makeup tasa pink blush da pink lipstick sai glistening lips din nata keyi. A kanta idanun Miral suka tsaya ta kasa matsar dasu tarasa mema takeji ne. Da kyar tasamu ta dauke idonta akanta aranta tana tunanin ya akayi kuma Layla tazama family? A iya saninta family members ne kawai suke zuwa tarban baki. 

Daidai lokacin su Ummi da Hanat suka isa gabansu Mommy bayan sunhau steps din terrace din. Hugging juna Ummi da Mommy sukayi deeply kafin su saki juna Ummi tace “gosh! munaya bakya tsufa, har wani kara yarinta kikayi daga last time dana ganki”. 

Wani classy murmushi Mommy tayi sannan cikin siririyar murya tace “ Big sis karki koɗa ni, ke kanki look at you kamar bake kika haifi Hanat ba, how have you been?”. Murmushi Ummi tayi ta ansa mata da Alhamdulillah sannan ta juya ta kalli Solail da still hamma takeyi tana wasa da gashinta har a lokacin bata kallesu ba tace “ Solail babyn Mommynta da Daddy, you baza’a kulamu bane? Don’t tell me bakiji dadin zuwanmu ba? Musamman saboda ke nazo Sarmul Quwaa”. 

Juyowa Solail tayi ta kalli Ummi sannan tayi mata wani dan smile da kana gani kasan it’s fake tace “ welcome Ummi, kunzo lafiya?”. Ansa mata da lafiya lau Ummi tayi sannan ta kalli Layla dake murmushi tace “ oh My layla kece kika girma haka in just two years? Who could have thought layla zatayi kiba haka? Come let me hug you”. Tafada tana dariya. Zuwa layla tayi tay hugging Ummi sannan tayi hugging Hanat data gama gaisawa dakuma hugging da Mommy. Dan hira sukafara da Layla sannan ta juya takalli Solail tace “ Solail why so unhappy? Inbakiso muzo you should have said so earlier”. 

Smiling Solail tayima Hanat Sannan tace “ Hanat welcome”. Daga haka ta juya ta shige cikin gidan. Sosai ran Hanat ya baci ganin rashin mutuncin da Solail ke musu saidai bata nuna ba ta rike hannun layla suka bi bayan Solail. Mommy ce tace da Ummi su shiga ciki harsun juya Ummi ta tsaya tace “ wait, ina Miral ne?”. 

Wani irin juyowa Mommy tayi ta kalli Ummi tace “ bangane ina Miral ba. Ai wannan ke za’a tambaya bamu ba”. Harta kara gaba kuma ta juyo ta kalli Ummi ranta adan bace tace “ sis dont tell me yarinyar nan kika dawomin da ita gidannan?”. 
Daga mata gira Ummi tayi daya tabbatar ma da mommy Miral tadawo. 

Wani kallo takema Ummi na tsawon yan mintuna sannan tayi wani dariyar gefen baki tace “ no, sis no. Bazata dawomun gida ba. Wai kin manta me yarinyar nan tayi ne kokuwa? Ki dauketa kisan nayi da ita ba anan ba gaskiya”. Tana gama fadar haka ta juya ta shige cikin gidan. 

[ Toh Fah guys. Kunji meke faruwa anan? Mommy dai tace a fitar mata da Miral a gida. Shin wai metayi ne haka da uwar data haifeta zata kyamace ta haka?].

For more information ga WhatsApp number na ***