KADDARAR ZUCIYA

THE CHAT

by @jiddaahbarkum

*KADDAR ZUCIYA*

*CHAPTER SIXTY-TWO: 62*

THE CHAT đź’¬ 


Washegarin dawowarsu daga Madina… tun da sassafe gidan Alhaji Kabeeru ya fara motsi kamar yadda aka saba. Masu aiki suna kai da komowa cikin nutsuwa, ƙamshin tea da gurasa na fita daga kitchen yana gaurayawa da ƙamshin turaren oud da ya mamaye falon gidan. Inteesar da Humaira kuwa… bayan sun gama shirinsu na safe, suka fito daga sashensu tare. Inteesar sanye take da doguwar abaya mai launin blue black, ta daura mayafin abayar a kanta, babu wata kwalliya a fuskarta sai hasken da kwanciyar hankalin kwanakin nan ya fara dawo mata. Humaira kuwa tana sanye da dark green abaya, tana taɓa wayarta tana bin bayan Inteesar. Kai tsaye suka nufi ɓangaren Daddy. Da suka isa… Inteesar ta tsaya bakin ƙofa, ta yi sallama cikin ladabi, “assalamu alaikum wa rahmatullah.” Muryar Daddy ta fito daga ciki cikin nutsuwa, “wa alaikumus salam… ku shigo.” Suka shiga tare. Alhaji Kabeeru yana zaune kan babban kujerarsa yana karanta wasu takardu, gilashin karatunsa na zaune a kan hancinsa. Da ya ɗaga kai ya gan su… sai fuskarsa ta washe da murmushi, “Princess…” Inteesar ta ƙarasa kusa da shi, ta durƙusa ta gaishe shi, “ina kwana Daddy.” “lafiya lau, Princess ɗina.” Ya ɗora hannunsa kan kanta cikin kauna. Humaira ma ta gaishe shi, ya amsa cikin fara’a. Sai ya kallesu, “yaya gajiyar hanya?” Inteesar ta yi murmushi, “alhamdulillah Daddy… mun huta sosai.” Humaira ta gyada kai, “eh Daddy, mun huta.” Alhaji Kabeeru ya yi murmushi mai cike da godiya, “alhamdulillah.” Ya ɗan yi shiru kafin ya ce, “Allah ya karɓi ibadunku.” “ameen,” suka amsa tare. “Allah ya ƙara muku kusanci da shi.” “ameen.” “Allah ya sanya albarkar wannan tafiyar cikin rayuwarku.” “ameen ya rabb.” Daddy ya jingina da kujerarsa cikin natsuwa, “na ga fuskokinku ma sun canza.” Humaira ta yi dariya, “Daddy… ai Madina daban take.” Ya gyada kai, “hakane.” Inteesar kuwa murmushi kawai take yi, tun daga dawowarsu… har yanzu zuciyarta na cike da wani irin natsuwa da ba taɓa ji ba. Ba ta ma san yadda za ta bayyana shi ba, sai dai… ta san Madina ta bar mata wani abu mai kyau a zuciya.

Ba da jimawa ba… Mommy Haleema ta shigo falon, sanye take cikin elegant sky blue abaya itama sai hijabi fari wanda ya sauko sosai. Ta yi musu murmushi, “ashe kun rigaya kun zo wajen Daddy.” Inteesar ta miƙe, “ina kwana Mommy.” Mommy ta rungume ta cikin ƙauna, “lafiya lau Princess.” Ta juya ta kalli Humaira, “kin tashi kenan?” Humaira ta yi dariya, “Mommy ai yunwa ce ta tashe ni.” Duk suka yi dariya, “mu je ku karya.” Suka nufi dining room tare. Breakfast ɗin ya kasance cikin annashuwa, tea mai ɗumi, omelette, bread, fresh fruits, da kuma fresh orange juice. Daddy yana ta ba su labarin wasu abubuwan da suka faru a katsina lokacin da ba su nan, Humaira kuwa lokaci zuwa lokaci tana saka dariya, Inteesar kuma tana sauraro cikin nutsuwa. A irin waɗannan lokutan… sai take jin daɗin kasancewa tare da iyalinta. Bayan sun gama breakfast… Daddy ya nufi office ɗinsa, Mommy kuma ta shiga kitchen tana duba wasu abubuwa, Inteesar da Humaira kuwa suka koma sashensu domin su huta.

Da yammacin ranar… karfe uku daidai, rana ba ta da zafi sosai, iska mai laushi tana shigowa ta window tana motsa labulen ɗakin. Inteesar tana zaune gaban dressing mirror, a gabanta akwai nail care set, a hankali take gyara farcen hannunta. Humaira kuwa… kwance take a kan gado, laptop na kan cinyarta, ta nutsu sosai cikin kallon wani korean movie. Wani lokaci tana murmushi, wani lokaci kuma tana yi wa jaruman dariya ita kaɗai. Sai wayar Inteesar da ke kan dressing table… ta fara ringing, screen ɗin ya haska, “My Amor ❤️.” Tun kafin ta ɗauki wayar… wani daddadan murmushi ya bayyana a fuskarta, ta ɗauke ta, ta kai kunnenta, “assalamu alaikum…” A ɗaya ɓangaren… Aliyu ya lumshe idanunsa, muryarta… kullum sai ta sake masa wani sabon tasiri. Ya yi murmushi, “wa alaikumus salam…” ya ɗan yi shiru, sannan ya ce cikin wata murya mai laushi, “wife…” Inteesar ta lumshe idanunta na ɗan lokaci, har yanzu… duk lokacin da ya kira ta da wannan sunan… sai zuciyarta ta buga da ƙarfi, “uhmmm…” ta amsa cikin murmushi, “ya ka yini? Ya aiki?” Aliyu ya jingina da seat ɗin motarsa, “alhamdulillah, komai lafiya.” Sai ya sauke wata ajiyar zuciya, “ke fa… kewarki kawai ce ta dame ni.” Inteesar ta yi murmushi, ɗan jingina da jikin mudubin, “nima… cike nake da kewarka my amor, I just can’t wait to set my eyes on you.” Aliyu ya yi wata yar dariya mai sanyi, “wow… really?” Inteesar ta lumshe ido, kai kawai ta jinjina kamar yana kallonta. Aliyu ya yi shiru na wasu daƙiƙu, sannan ya ce, “okay… guess what, darling.” Ta buɗe idanunta, “what?” Aliyu ya yi murmushi, “ina ƙofar gida yanzu.” Inteesar ta zaro ido, “what?!” Da sauri ta miƙe tsaye, ta ƙarasa window, ta buɗe curtain, ta leƙa compound ɗin gidan, sai dai… saboda inda motar take… ba ta hangota sosai ba. Ta sake komawa wayar, “really?” Aliyu ya yi dariya, “yes wife.” Ta saki curtain ɗin, ta turo baki, “toh ka… shigo mana, Daddy yana compound, kazo ku gaisa, zan fito yanzu.” Aliyu ya amsa cikin murmushi, “okay, my love.” Sai ya kashe wayar.

Inteesar ta sauke wayar a hankali, na wasu daƙiƙu… ta tsaya cak, sannan… wani irin farin ciki ya mamaye ta. Ba tare da ta shirya ba… ta fara juyawa a tsakiyar ɗakin tana dariya, “my babe is here… ohhh… I miss you darling…” Humaira ta ɗago daga kallon movie ɗinta, ta kalleta, sai ta fashe da dariya, “lalle intee… sannu fa.” Inteesar ma ta yi dariya, ba ta tsaya ba, kai tsaye ta nufi wardrobe, ta ɗauko towel, ta juya tana kallon Humaira, “let me shower first… my hubby is here.” Da gudu ta shige bathroom, ta rufe ƙofa. Humaira ta ci gaba da kallon ƙofar bathroom ɗin, ta girgiza kai tana dariya, “soyayya kenan,” sai ta maida hankalinta kan movie ɗinta… amma murmushin da ke fuskarta yana nan.

Bayan kusan mintuna ashirin… ƙofar bathroom ta buɗe a hankali, ƙamshin sabulunta mai kamshi ya fara cika ɗakin kafin ma ta fito gaba ɗaya, ruwan da ta yi wanka da shi ya bar fatarta tana wani irin haske mai sanyi. Pink cotton gown ɗinta ta sake sanyawa, towel kuma tana gogewa a hankali kan dogon gashinta da ke ɓoye ƙarƙashin sleeping cap. Ta ƙarasa gaban dressing mirror, ta tsaya tana kallon fuskarta, na wasu daƙiƙu… sai ta yi murmushi ita kaɗai, a hankali ta furta, “yau kam…” ta ɗan cije lips ɗinta cikin kunya, “…bari na yi kwalliya sosai.” Ba don wani biki ba, ba don fita wani waje ba, sai saboda… Aliyu. Wannan tunanin kaɗai ya sa fuskarta ta cika da annuri.

Ta buɗe drawer ɗin dressing table, ta fito da makeup pouch ɗinta. Da farko… ta shafa moisturizer mai laushi a fuskarta, ta jira ya zauna sosai kafin ta shafa primer domin fatar ta yi laushi. Daga nan… ta ɗauki foundation ɗinta, a hankali ta zuba kaɗan a bayan tafin hannunta, beauty blender ta ɗauka, ta fara daddanna foundation ɗin a kumatunta cikin nutsuwa, ta haɗa shi da fatar wuyanta har ya zauna tamkar ba wani abu ta shafa ba. Natural finish, babu nauyi, sai dai ya ƙara fito da kyawun fuskarta. Ta ɗauki concealer, ta shafa ƙarƙashin idanunta, a gefen hanci, da kuma tsakiyar goshinta, ta sake blending cikin nutsuwa, fuskarta ta ƙara yin haske. Sai ta ɗauki loose powder, ta seta makeup ɗinta cikin sauƙi, ba ta son makeup mai yawa, simple… elegant… kuma classy. Ta ɗauki eyebrow pencil, a hankali ta gyara gira ɗinta, ba ta cika shi sosai ba, sai dai ta ba shi shape mai kyau. Daga nan… ta ɗauki eyeshadow palette, ta zaɓi peach mai laushi da ɗan light brown, ta haɗa su a saman idanunta cikin salo mai sauƙi. Sai ta ɗauki black eyeliner, da hannunta mai natsuwa… ta ja siririn layi a gefen idanunta, nan take idanunta suka ƙara bayyana. Ta ɗauki mascara, ta shafa a gashin idanunta na sama da na ƙasa, dogayen lashes ɗinta suka ƙara tsawo da kyau. Ta ɗan yi murmushi, sai ta ɗauki blush, peach blush mai laushi, ta shafa kaɗan a kumatunta. Daga ƙarshe… ta shafa nude glossy lipstick, sai ɗan lip gloss kaɗan a saman leɓanta. Ta ajiye brush ɗin, ta sake kallon kanta cikin mirror. Na wasu daƙiƙu… ba ta motsa ba, sai murmushi mai cike da jin kunya ya subuce mata. Ita kanta… ta san yau ta yi kyau, ba wai saboda kwalliyar ba… sai saboda farin cikin da ke cikin zuciyarta, kuma idan ita kanta ta ga haka… to balle Aliyu idan ya gan ta.

“Wowww…” muryar Humaira ta katse mata tunani. Inteesar ta waigo, Humaira har ta buɗe baki, idanunta a buɗe suke sosai, “subhanallah… fatabarakallah… ahsanal khaliqiin.” Inteesar ta yi saurin sunkuyar da kai, “Humaira…” ta faɗa tana hararta. Humaira ta girgiza kai, “a’a wallahi, ki tsaya, ki bari na gama kallonki.” Inteesar ta yi dariya a hankali, sai ta juya zuwa babban wardrobe ɗinta, ta buɗe shi, idanunta suka fara yawo kan jerin kayanta, atamfofi, laces, abayoyi, dogayen gowns. Ta tsaya tana nazari, “wanne zan saka?” ta furta a hankali. Can… sai idanunta suka tsaya kan wata atamfa, peach da purple, sai ɗan baƙin design mai kyau a jikinta. Straight gown ce, mai sauƙi, amma cike da tsari da elegance. Ta zaro ta, ta cire gown ɗin da ke jikinta, ta saka sabuwar rigar, ta gyara zip ɗin bayanta… sai rigar ta zauna a jikinta tamkar a jikinta aka ɗinka mata. Ta fito da siririn waist ɗinta, dogon tsayinta ya ƙara bayyana, ta sake komawa gaban mirror, ta gyara rigar kaɗan. Sai ta buɗe jewelry box ɗinta, ta fito da ƙaramin necklace na azurfa mai ɗan pendant mai kyau, ta saka shi, sai matching earrings ɗinsa, ta ɗan karkatar da kanta, ta tabbatar sun zauna da kyau. Daga nan… ta ɗauki zoben sarkar, ta daidaita clasp ɗin da ke bayanta, ta gyara shi har ya zauna yadda ya kamata. Sai ta ɗauko peach veil ɗinta, ta shimfiɗa shi cikin tsari, ta ɗora shi a kafaɗunta cikin salo mai matuƙar kyau, ta ɗan gyara gefensa, ta sake kallon kanta. Komai ya yi matching, peach, purple, silver accessories, simple makeup, komai ya haɗu cikin nutsuwa. Sai ta miƙa hannu, ta ɗauki turarenta… parfums de marly delina exclusif, ta fesa kaɗan a wuyanta, kaɗan a bayan kunnuwanta, kaɗan a wuyan hannunta, sai ɗan kaɗan a kan veil ɗinta. Nan take… ɗakin ya cika da wani irin ƙamshi mai daɗi, mai taushi, ba mai ƙarfi da yawa ba, sai dai mai barin mutum yana son ya sake jin sa. Ta juya tana kallon Humaira, ta buɗe hannayenta kaɗan, “hey… yaya kika ganni?” Humaira ta rungume hannayenta a ƙirji, har yanzu murmushi yaƙi barin fuskarta, ta girgiza kai, “inaga… …Aliyu yau zai sa Daddy ya ɗaura auren nan kawai ya tafi da ke.” Inteesar ta yi saurin dariya, “Humaira…” Humaira ta ɗaga hannu, “a’a, ki bari na gama, saboda kinganki kuwa… oh my god, wallahi… kin yi masifar kyau, intee… yau kam…”

Ta sauke idanunta ƙasa, sai murmushi kawai take yi, ba ta ce komai ba. Ta ɗauki wayarta, ta kalli Humaira, “tasho.” Humaira ta ɗaga gira, “ina?” “ki raka ni don Allah, saboda?” Inteesar ta ɗan murɗa yatsunta cikin jin kunya, “yana wajen Daddy a compound, wallahi… kunya nake ji.” Humaira ta fashe da dariya, “lallai…” Ta ɗauki manyan ledunan tsarabobin da tayi masa, ba Aliyu kaɗai ba… har yaran gidansa, har safiyya, har hafsa, matansa. Kowa ta tanadar masa nasa. Inteesar ba ta son nuna bambanci tsakanin mutane, ta yi imanin cewa idan za ta ba da kyauta… to a yi ta da zuciya ɗaya. Humaira ce ta ɗauki mafi yawan ledunan saboda sun yi mata yawa, “tasho mu je.” Inteesar ta gyada kai a hankali, suka fito daga cikin gidan. Da suka sauko zuwa compound… sai suka hango Daddy da Aliyu zaune ƙarƙashin bishiyar da ke gefen falon waje, suna cikin hira cikin nutsuwa. Aliyu ne ya fara ɗaga kansa, daidai lokacin da idanunsa suka sauka kan Inteesar… sai ya tsaya. Na ɗan daƙiƙu… kallonsa bai motsa ba. Peach veil ɗinta na kaɗawa a hankali da iskar yamma, simple makeup ɗinta ya ƙara fito da kyawun fuskarta, straight gown ɗin peach da purple ya zauna a jikinta tamkar a jikinta aka dinka. Aliyu ya sauke idanunsa kaɗan, sai wani murmushi mai cike da natsuwa ya bayyana a fuskarsa. Daddy ma ya waigo, ya bi Inteesar da kallo, sai ya yi murmushi cikin jin daɗi. A hankali ya miƙe tsaye, ya dubi Aliyu, “Allah ya yi albarka.” Aliyu ya miƙe cikin girmamawa, “amin Daddy.” “Allah ya ƙara girma.” Daddy ya jinjina kai, “amin.” Bai sake cewa komai ba, ya wuce a hankali ta gefensu ya shiga cikin gida.

Da Daddy ya wuce… Inteesar ta ƙara sunkuyar da kanta, har yanzu kunyar kasancewar Daddy a wajen ba ta gama barinta ba. Humaira ta kalli yanayin, ta yi murmushi, da ƙarfi kaɗan ta kamo hannun Inteesar, “taho.” Ta jawo ta har zuwa inda Aliyu yake, ta zaunar da ita a kujera, ita kuma ta tsaya a gefenta, ta kalli Aliyu tana murmushi, “ina yini?” Aliyu ya ɗago daga kallon Inteesar, “lafiya kalau.” “ya kike Humaira? Ya gajiyar saudi?” Humaira ta yi murmushi, “gajiya ya bi lafiya, alhamdulillah.” Suka gaisa cikin mutunci, sai ta juya ta ɗauko ledar, ta ajiye ta gaban Aliyu, “ga tsarabarku nan… …daga amarya.” Aliyu ya sauke idanunsa kan ledar, sai ya sake kallon Inteesar, “harda tsaraba?” Humaira ta ɗaga gira, “eh mana.” Aliyu ya yi murmushi, “toh… nagode sosai.” Humaira ta yi dariya, ta sake kallon Inteesar, “ni bari na koma,” ta yi wata dariya, “asha soyayya lafiya.” Inteesar ta harare ta, Humaira ta ƙara dariya, ta juya ta shiga cikin gida.

Shiru ya sauka tsakaninsu, Aliyu ya maida dukkan hankalinsa kanta, Inteesar kuwa… har yanzu kanta a sunkuye yake, yatsunta biyu tana ta haɗawa da rarrabawa saboda kunya. A hankali… ya kira, “Babygirl…” ta ɗaga kanta cikin natsuwa, idanunsu suka haɗu, na ɗan daƙiƙu… babu wanda ya yi magana, sai ta kasa jure kallonsa, ta sake sauke nata idanun ƙasa. Aliyu ya yi murmushi, “kin yi kyau… sosai.” Murmushi ya bayyana a gefen lips ɗinta, amma ba ta ce komai ba. Shi kuwa… ya lumshe idanunsa na wasu daƙiƙu, wani irin abu ne yake yawo cikin zuciyarsa. Kafin ya sake magana… sai suka ji kiran sallar la’asar daga masallacin unguwar, “Allahu Akbar…” Aliyu ya buɗe idanunsa, ya sake kallonta, “bari na yi sallah, ko sai mu yi hirar da kyau idan na dawo.” Ta ɗago ta kalle shi, “toh…” ta ce cikin sanyin murya, sai ta miƙe, “bari na kawo maka ruwa daga ciki.” Ya bi ta da kallo, sai ya girgiza kai, “no babygirl, bari na yi alwala a fanfon can,” ya nuna fanfon da ke gefen compound. Suka taka zuwa wajen tare, da suka isa… Inteesar ta matsa kusa da shi, a hankali ta ce, “kawo… na cire maka cufflinks ɗin, sai ka yi alwala.” Aliyu ya tsaya yana kallonta, idanunsa sun ɗan kankance, “uhm… no babygirl.” Ta ɗago tana kallonsa, “why?” Ya rage murya, “I am very sensitive, idan kika taɓa ni… something might happen,” sai ya ɗan karkata kansa, “kuma kinga… nan gidanku ne.” Ya ƙarasa yana kafeta da ido, numfashin Inteesar ya ɗan tsaya, ta turo baki cikin jin kunya. Aliyu ya yi dariya a hankali, sai ya cire wayarsa daga aljihu, ya miƙa mata, “riƙe min, bari na yi alwala.” Ta karɓa, ta tsaya gefen fanfon, har ya gama alwala, ya goge fuskarsa, “bari na shiga masallaci.” Ta gyada kai, “toh.” Ya juya, ya nufi masallaci cikin nutsuwa. Inteesar kuma… ta dawo ta zauna kan kujerar da suke zaune ɗazu, ba za tayi sallah ba, tun safiyar yau… ta karɓi baƙonta, saboda haka… ta zauna tana jiran dawowarsa, wayarsa tana hannunta. Compound ɗin ya yi shiru, sai sautin kiran sallah da ya fara raguwa. Can… wayar ta yi ƙaramar vibration, drrr… Inteesar ta sauke idanunta. Notification ne, da farko ba ta yi niyyar dubawa ba, sai dai… wani suna ya ja hankalinta, “Exx Aishaa ❤️.” Gabanta ya ɗan buga. A saman notification ɗin kawai… ta ga rubutun, “hahaha wallahi tana sonka taabbb… ni tausayinta nake ji.” Numfashinta ya tsaya, ta daɗe tana kallon notification ɗin, zuciyarta ta fara bugawa da sauri, “me yake nufi…?” ta furta a hankali. Hannunta ya fara rawa, ta san bai kamata ta buɗe wayarsa ba, ta san sirrin mutum amanarsa ne, amma… wani irin tsoro ya fara shiga zuciyarta. Da hannun da yake rawa… ta buɗe wayar. WhatsApp ɗin ya buɗe, chat ɗin yana buɗe, ta fara scrolling sama a hankali… sai rubutun ya fara bayyana.

Aliyu: “ke wallahi yarinyar nan kadara ce, kin san cewa ita kaɗai mahaifinta ya haifa, na bincika, duk mazan nan ba yaransa ba ne, agololi ne ki duba mansion din da mahaifinta ya bani, a very huge one.” Inteesar ta haɗiye wani abu mai ɗaci, ta ci gaba da karantawa. Exx Aisha: “taab lalle ka tsinci dami a kala, ga kuma 17m, ka ga ko kayi retire kana da hanyar income, hankali a kwance.” Idanunta suka fara rawa, sai ta ga amsar da ta biyo baya. Aliyu: “eh mana… ai tana sona.” Numfashinta ya fara nauyaya, ta ci gaba. Aisha: “tana sonka… amma kai kana sonta kuwa?” Amsar ta bayyana. Aliyu: “wallahi ina sonta sosai, amma kuma ba zan ce banason kuɗinta ba, tsakanina da Allah… besides yarinyar fa ta haɗu, ga jiki mai kyau, ga kuɗi, ga kuma… uwa uba… masifar sona take.” Inteesar ta ji kamar wani ya doka mata guduma a ƙirji, amma ta kasa tsayawa, ta ci gaba da scrolling. Aisha: “hahaha, ni abin da yake bani mamaki ma… karama ce, kai kuma kana 50s yanzu, lokacin da za ta buƙace ka… kai kuma abin naka ya gaji, yaya za a yi lokacin?” Inteesar ta ji hannunta ya fara sanyi, sai amsarsa ta bayyana. Aliyu: “toh kinga… a lokacin ne son da take min zai yi aiki, she will endure.” A wannan karon… da ƙarfi… Inteesar ta dafe ƙirjinta, numfashinta ya fara fita da sauri, da sauri, da sauri. Idanunta suka cika da hawaye, wayar ta fara rawa a hannunta, kalaman da take karantawa suna cakudewa a idanunta, ta ji kamar ƙasa tana juyawa. Wani irin ciwo… mai tsanani… ya taso daga tsakiyar zuciyarta, har ya bazu zuwa dukkan jikinta. Ba ta iya kuka ba, ba ta iya magana ba, sai zuciyarta da take ta maimaita kalma guda… “she will endure…” “…amma kuma ba zan ce banason kuɗinta ba…” “…masifar sona take…” A karon farko tun bayan Ahmad… Inteesar ta ji kamar wani ya sake riƙe zuciyarta… …ya murƙushe ta da hannu biyu.