BIYU A ƊAYA

Chapter 48

by @barista

BIYU A ƊAYA 
     ( Never judge someone according to the cover)


Book 2 
Page 48
Sayyada barrister 
 ~***~ 
Sabon number nah ***
YOTA 13 
The five ink legends 


BORNO STATE 

Maiduguri KIRAWA'S FAMILY

A daidai sakiyar katafaren farfajiyar gidan a ka yi parking na motocin, a lokaci guda kuma a jere kamar haɗin baki, sai da aka ɗauki kusan minti biyar sannan aka fito. Daddy ne da Alhaji babba suka fara fitowa, suka ɗan ja gefe suna tattaunawa a sakanin su, Dr Waahab da Ya Sa'eed suka fito suna sauke numfashi tare yin hamdala ubangiji ya nufa sun dawo gida lafiya. Alhaji ƙarami da Abbie da Abba su ma suka fito, wajen su Alhaji babba suka nufa suna sake shawara akan yadda za a tarɓi bakin Ghana da suka taho tare da kuma masaukin da za a basu...

ALAJA dake zaune cikin mota ta kurawa gidan idanu sai kalle-kalle take yi tana mamakin girman gidan, duk da saukan dare su ka yi amma tana iya karewa ko'ina kallo ta fitilun da suka haske gidan. Lallai fah sirikan Bilqees sun wuce tunaninta, yanzu daga cikin wannan daular suke, kuma suka tafi har Ghana tumbin Giwa neman auren Angel...

Ta ji aka yi nocking glass na mota na inda take zaune, ta zuge ganin Alhaji ƙarami ne yasa ba ta yi magana ba, ya ɗan rage tsawonsa yana kallonsu ya ce

"Ku sauƙo"

Suka fito ban da Angel da take cikin lulluɓi bata ma san in da suke ba, ita dai ta san suna sauƙa a airport suka shigo cikin mota daga nan kuma bata san inda suka nufa ba sai dai jin tsayuwar mota. ALAJA ta dubi Alhaji ƙarami ta ce

"To mun fito"

Ya ɗauke kansa a lokacin Aunty Nazeefa da wasu mata biyu suka taho tarɓansu, Alhaji ƙarami ya dubi matarsa ya ce

"Nazeefa ku kai su masaukin baƙi na bangaren dama"

"To Alhaji, sannun ku da zuwa"

Ta yi wa su ALAJA sannu da zuwa tana kare musu kallo tare da taɓe baki, ALAJA ta buɗe motar ta ce da Angel ta fito, ta fito suka wuce masaukin su, ya matuƙar haɗuwa yadda aka tsara wajen ya burge su, Aunty Nazeefa ta ce

"Ku saki jikinku kada ku damu, ai nan tamkar gida ku ka taho"

"To mun same ku lafiya?"

Cewar ALAJA tana zaunar da Angel kan kujera, ita ma ta zauna.

"Lafiya lau"

Suka fito Laraba ta ce

"Wai tab Angel ta shigo gidan daula"

"Baƙin ciki kike yi mata"

Cewar Jummai, ran Laraba ya ɓaci ta maida mata da

"Allah ya sawwaƙa, in nayi mata baƙin ciki samu zan yi, kawai don na yaba"

"A'a addu'a za ki yi mata"

"To ba zan yin ba ina ruwan ki"

ALAJA cikin ɓacin rai ta ce

"Sai kuma ku nuna halin, daga zuwan mu ko ruwa ba mu sha ba za ku tara mana mutane, a ce wasu irin baƙi ne"

Su ka yi shiru Majada ta zauna kusa da Bilqees ta riƙe hannunta tare da cewa 

"Ƙawata na taya ki murna"

"Na gode"

Kawai Bilqees ta ce, a lokacin aka shigo musu da kuloli kala daban-daban ana shirya musu dining, su dai sai kallo, Ya Sa'eed ya shigo ɗauke da manya manyan leda ya ajiye musu, ya sake yi musu sannu da gajiya sannan ya fice, Aunty Nazeefa ta shigo da wasu ƴan mata suka sake jera musu plates da spoons har da cups sannan ta ce

"Yawwa ɗakuna ne waɗan nan, zaku iya amfani da kowanne daga ciki, ku watsa ruwa sai ku ci abinci"

"To mun gode sannu da ƙoƙari"

"Ai ba komai mu nan gidan karamci ne"

"Ah to kun haɗu da ƴan karamcin, don mu ma ƴan karamci ne"

Cewar ALAJA, Aunty Nazeefa ta taɓe baki ta fice, dariya Laraba ta yi ta ce

"Sai dake ALAJA, kin yi min daidai"

"To ba wannan ba, Majada mik'o min leda nan na gani"

Jummai ta janyo su gaban ALAJA, duk abubuwan da suka shafi toilet ne waɗan da za su buƙata, sauran kuma kaji ne da drinks, Alaja ta ce

"Ta shi za mu yi mu duba ɗakunan kowacce ta watsa ruwa sai mu ci abinci don yunwa nake ji"

Suka mik'e, ɗakuna biyu kawai suka ɗauka, ALAJA da Bilqees za su yi amfani da ɗaki ɗaya, sauran kuma su zauna a ɗaki ɗaya. Bayan sun watsa ruwa sun fito kowacce ta shirya sannan suka fito palour suka zauna cin abinci sai santi suke yi, amma banda Bilqees da ƙyar ta watsa ruwa, ta sanya doguwar riga ta material multi color ce ta yafa mayafi sai da ta idar da sallah sannan ta zauna kan kujera, ta takure jikinta waje guda ta faɗa duniyar tunani, ALAJA ta ce

"Ke in za ki zage ki ci abinci to ki tashi ki ce, ki bar wannan miskilancin na ki"

Ta sauke numfashi a hankali ta ce

"Bani da yunwa Maa"

"To mu ne masu yunwa ko?"

Cewar Laraba, Jummai ta ce

"Ga alama"

"Kin ga ki daina shigar min hanci"

"Na shiga sai ki fece ni"

"Kun san Allah zan ci muku mutunci in ba ku daina min iya shege ba"

Sallama suka ji, Bilqees ta amsa tare da gyara mayafinta Alhaji ƙarami ya shigo tare da cewa 

"To ma sha Allah, a huta gajiya"

"Mun gode"

Cewar Laraba, ya dube Alaja ya ce

"Ku yi hakuri anan za ku kwana, bangaren amaryar ba a shirya shi ba, sai zuwa gobe za ayi mata siyayya"

"Ok ba damuwa Allah ya kai mu, amma nan ɗin ma ya yi"

Cewar ALAJA, ya ce

"Eh nan bangaren baƙi ne, sannan duk abinda kuke bukata ku sanar za a kawo muku"

"To ba komai ai an kawo duk abin da muke buƙata"

"To ma sha Allah sai da safen ku"

Ya fice ALAJA tana mamaki duk uban kayan ciye-ciyen da suka kawo musu har suna cewa in da abin da suke so su sanar, lallai Angel ta huta, tayi sa'a. Sun kammala cin abinci suna zaune a palour ALAJA ta ɗan jingine da jikin kujera tana gyangyadi suna yi mata dariya, Majada ta ce

"Ai ALAJA daga cikin ta ya ƙoshi take bacci"

"Ai haka take ko kuma ana kallo za ki ga ta bar gari, rannan fa har kusan kwanan zaune ta yi"

Cewar Jummai, dariya su ka yi Laraba ta ce

"Ballantana kuma an sha fresh milk ba"

Ƙasa ƙasa suke magana, suna dariya su ka ji muryar ALAJA tana cewa

"Sarai ina jinku ai ƴan iska"

Sit su ka yi, kowacce ta riƙe bakinta...

*****

Dr Waahab yana shigowa ciki ya wuce side na Mamie, ya tadda tana cin abinci da sallama ya ƙaraso, har ya zauna bata ce komai ba bayan ta amsa sallama. Ya sauke numfashi cikin sanyin murya yace 

"Mamie mun dawo"

"Babangida sannun ku da zuwa"

"Yawwa Mamie, ko wanka ban yi ba na shigo na gaishe ki"

"To ya yi kyau"

Jikinsa ya yi sanyi matuka, har zai mik'e ya ce

"Mamie ba ki tambayi Bilqees ba"

"Wacece haka?"

"Amarya"

Ya faɗa a hankali, ta ɗan dube shi sannan ta ce

"Ai ban santa ba"

"A ɗakin baƙi aka sauke su"

"To ya yi kyau"

Jiki a sanyaye ya fito zuwa ɗakinsa, ya faɗa toilet ya watsa ruwa ya jima a haka sannan ya fito ya shirya cikin ƙananan kaya yayi kyau sosai sai ƙamshi yake yi, ya idar da sallah. Yana fitowa ya wuce side na Mommie ya tadda tana zaune ita kaɗai tana shan fruits, murmushi ta yi a lokacin da ta ɗaura idanunta kan sa, ya fahimci dalilin yin murmushin ya zauna tare da cewa 

"Mommie ya jikin?"

"Ango"

Ya ɗan sosa keyarsa, cikin kulawa ya ce

"Da ita muka taho"

"Ai dole, to tana ina?"

"Ɗakin baƙi"

"Shi ne ba za ta zo ta gaishe ni ba?"

"Za ta zo, zan kawo ta nan ta gaishe ki"

"To da ya fi"

Ta tura masa plate ɗin alamun ya ci fruits ɗin ya ce baya sha'awa, bai jima ba ya wuce side na Ammie kamar yadda yake yi, ya tadda bata cikin palour ya yi sallama kusan sau uku sannan ta fito, cike da girmamawa ya gaishe ta amsa fuska a sake ta yi masa ya gajiyan baƙi sannan ya fito, ya tadda Sa'eed yana zance shi da Suhaima kamar ya wuce amma ya tsaya, Suhaima ta gaishe ya amsa ta yi saurin shigewa ciki, Sa'eed ya ce

"Kawai sai ka kora min mata"

"Yaushe ni? A'a"

"Eh mana tana ganin ka ta wuce ciki ta barni"

"Kawai dai ta yi shigewarta kada ka ɗaura min"

"To me labari?"

"Mu je na yi wa matata ban gajiya"

"To mu je duk da ka kora min tawa"

Bai ce komai ba suka nufa bangaren baƙi, suka shigo da sallama, aka amsa tare da basu wajen zama, ALAJA sama sama take iya gane komai ta ce

"Har kun iso restaurant? To madallah sannun ku da zuwa"

Dariya su Laraba su ka yi, Majada ta ce

"ALAJA ba a Ghana muke ba a Nigeria ne fah"

Ta ɗan buɗe idanunta ta ce

"Au Yallaɓai likita ne sannun ku da ƙoƙari"

"Yawwa sannu ALAJA, ki shiga ciki ki kwanta mana"
 
Cewar Sa'eed, Alaja ta ɗan watsake idanunta ta ce

"Yanzu zan shiga, kaganta nan ba abin da ta ci, ga cen mun ajiye mata rabonta"

Ya sauke numfashi ya kalli in da Angel take zaune ta rufe fuskarta tare da sunkuyar da kanta ƙasa, Alaja ta mik'e ta shige ɗaki, Dr Waahab ya masu kusa da Angel ya ɗan yaye mata mayafinta ya kalli fuskar duk da kanta a ƙasa yake, ya yi magana a hankali 

"Mon Ange ba ki ci abinci ba? Me ya sa?"

"Bana jin yunwa ne"

Ta faɗa masa a hankali, ya sauke numfashi tare da cewa 

"Ba fa abin da kika ci, taso mu je ki ci"

Ya kama hannunta zuwa dining area, Sa'eed kuma sai hira yake yi da su Laraba suna yaba garin Maiduguri har yake ce musu gobe zai fitar dasu su ga gari, suna ta murna. Dr Waahab ya zuba mata abinci ya yaye mata mayafinta ta sake sudda kanta ƙasa ta ce

"Ba zan iya cin abinci ba"

"Me kike so?"

"Ba komai"

"To ni ma ba zan bari ki kwana da yunwa ba"

Ta ɗan marairaice ta ce

"Da gaske Yallaɓai likita"

Ya sauke numfashi ya kura mata idanu, ganin duk jikinta a sanyaye ya sa bai takure ta sai ta ci ba, iya fresh milk ya bata, da sneaks da ƙyar ta ci, ya ce

"Shi kenan zan yi miki allura"

Ta ɗan waro fararen idanunta tana kallon sa, ya yi murmushi ya ce

"Eh mana tun da dai ba za ki ci abincin ba"

A kunyace ta ce

"Na ci ai yanzu"

Ya riƙe hannunta yana jujjuya shi a hankali yana sake kallon lallen ta sudda kai ƙasa, ya dubi in da Sa'eed suke yaga sai labari yake baiwa baƙin ya sa ya ɗaurata kan cinyarsa ya zaunar da ita sosai bai damu da kunyarsa da take ji ba, ya ji jikinta zafi sosai ya yi saurin cewa 

"Subhanallah! Mon Ange jikin ki da zafi, zazzaɓi ne?"

Ta gyaɗa masa kanta alamun eh, cikin tausayawa ta ce

"Sannu kin ji?"

"Thanks"

Ta faɗa, ya ɗan zuba Farfesun jan nama yana bata a baki yana kuma haɗawa da romonsa don ta samu ƙarfin jiki, duk da bata ci da yawa ba amma ya kyaleta ya goge mata baki da tissue, ya ɗauko wayarsa ya kira Sageer Mustapha KIRAWA bugu biyu ya ɗauka ya ce

"Zan tura maka text message yanzu ka je ka sayo min magungunan"

"Okay"

Cewar Sageer, Dr Waahab ya kashe wayar ya dubi matarsa da duk alamun gajiya ya bayyana a jikinta, ya turawa masa magungunan da yake buƙata, ya ɗago da haɓarta suna kallon juna ya yi mata magana a hankali 

"Ya kike jin jikin ki?"

"Zazzaɓi ne kawai"

"Shi kenan?"

Ta gyaɗa masa kanta alamun eh, Sageer ya shigo ya gaishe da su Laraba, Angel ta yi sauri ta zauna kan kujerar tare da gyara mayafinta duk da palour na da girma suna ɗan nesa da inda Sa'eed suke. Sageer ya ƙaraso tare da miƙa wa yayansa ledan magungunan ya dube amarya ya gaishe ta, ta amsa cikin sanyin murya, sannan ya juya ya fito, ganin Dr Waahab yana ƙoƙarin buɗe leda ya sa ta marairaice ta ce

"Bana son allura"

"Magunguna ne kawai za ki sha"

"To"

Ta faɗa ya ce, ya balle ya bata ta sha sannan ya ce ta shiga ciki ta kwanta, ta wuce ciki su Laraba ma suka shige nasu ɗakin. Dr Waahab suka fito Sa'eed ya ce

"Kai anya za ka jira ayi maka rakiya"

"Daman ban nema ba"

"Naga alama ai"

Su ka yi dariya kowannen su ya wuce side nasa. Angel ta tadda Alaja ta yi bacci nan ta kwanta ita ma bacci ya ɗauke ta...

*******
WASHE GARI

Gata iya gata ALAJA sun gani washegari kamar a goya su a baya sabar hidima, an yi musu lafiyayyun breakfast sun ci sun yi hamdala, suna zaune a palour wannan ya shigo wannan ya fice, haka suke shigowa ganin amarya suke ficewa. Angel ba um ba um um sai ido ta kasa sakin jiki, tana tunanin rayuwar da za ta yi da sabon ahali...

Ringing wayar ALAJA ta yi tana dubawa Maman Bilqees ce, tayi receiving tare da cewa 

"Sannu Maman Bilqees"

Jin ALAJA ta ambaci maman Bilqees ya sa ƙirjin Angel bugawa, jikinta ya soma rawa, a hankali ta runtse idanunta tana jin suna gaisawa a hands free ALAJA ta saka, ta ji muryar Mamanta tana cewa

"Yawwa sannu, kun sauƙa lafiya?"

"Sai godiya gamu a gidan Angel"

"Ina take?"

Ta tambaya ALAJA ta ce

"Ga ta nan"

Ta miƙa wa Bilqees wayar, hannunta na rawa ta karɓi wayar ba tare da ta ce komai ba ta ji Mamanta tana cewa

"Ki bata wayar mana ALAJA"

"Mama"

Shiru Mamanta ta yi da ta ji ta kirata da Mama, ta sauke numfashi tare da cewa 

"Har kin manta da ni?"

"A'a"

"Eh mana, ya gajiya"

"Alhamdulillah"

Kawai ta ce ba ta sake cewa komai ba, Mamanta ta ce 

"Ki bai wa ALAJA wayar"

Ta miƙa wa ALAJA, ta shige suna ci gaba da wayar, Bilqees ta sauke numfashi, a hankali ta lumshe idanunta, ta kwantar da kanta jikin seat, ta faɗa cikin duniyar tunani, ƙamshin turaren da ya ziyarci hancinta ne ya sa ta buɗe idanunta a hankali ta sauke su cikin nasa, sanye yake cikin manyan kaya shadda fari kal ɗinkin half jampa ya sanya hula da farin eye glass, ya zuba mata ido ko kiftawa ba ya yi, ya ɗan yi mintuna da shigowa ya yi sallama bata amsa ba har ya ƙaraso yaga kamar bacci take yi.

"Morning mon Ange"

Ta ɗan tashi ta zaune ta yi magana a hankali 

"Morning Yallaɓai likita"

Ya ɗan sakar mata da murmushi ya zauna kusa da ita sai a lokacin ta ankare ashe ita kaɗai ce a palour, kenan sun shige sun barta...

"Ya jikin?"

"Na daina jin zazzaɓi"

Ya ɗan lakuci hancinta ya ce

"To ba allura zan yi miki ba"

Ta ɗan yi murmushi, ya sake cewa 

"Kin sha magani?"

Ta gyaɗa masa kanta alamun eh, ya jinjina kai sannan ya ce

"Ina ALAJA?"

"Ta shiga ciki"

"Nazo ne mu yi magana, duba nan ki zaɓa"

Ya miƙa mata wayarsa ta zaɓe ɗaya daga cikin hotunan bed kala kala, sun matuƙar haɗuwa, sai dai ita ba za ta iya zaɓa ba ta ce

"Na mene?"

"Ki zaɓi wanda ya yi miki sai a saka miki a ɗakin ki"

"A'a bani da zaɓi"

Ya riƙe hannunta tare da wayar, yana kallon ta cike da so da kauna, ya ce

"Kina da zaɓi mana shi ya sa na kawo miki ki zaɓi na ranki"

"Yallaɓai likita kowanne ma a saka"

"Zan yi magana da ALAJA"

"To"

Ta mik'e ta shiga cikin ɗaki ta yadda Alaja zaune tana waya, kuma ta tabbatar da Mamanta suke yi tun ɗazu...

"Kin wani tsare ni da ido kina kallona, menene kuma?"

Ta ɗan sauke ajiyar zuciya ta ce

"Yallaɓai likita yana palour"

"To"

Kusan tare suka fito, ya gaishe da Alaja, sannan ya nuna mata hotunan bed ɗin ya ce ta zaɓa sai a kawo, ta ce duk wanda aka kawo suna maraba da shi, sannan ya ce iyayensa mata suna zaman jiran isowarsa su cikin gida, ta ce to za ta shirya Angel sai su taho, ya mik'e ya fice, ALAJA ta sanar da su Laraba akan za su yi wa Bilqees rakiya wajen sirkanta, suka shirya ba laifi sun yi kyau suka fito Dr Waahab yana tsaye da Teemah ya ce ta yi musu isowa. 

A palour suka tadda mata zaune suna jiran isowar su, sun tarɓe su ba laifi har kyaututtuka sun yi wa Bilqees, Hajjiya babban matar Alhaji babba ta ce

"To madallah Allah ya sanya alkhairi"

Aka amsa da

"Amin"

Sannan ta ci gaba da cewa 

"Ya kamata a daren yau a haɗa walima"

Mamie ta ce

"A'a ba za a yi wani shagali ba, kawai a yi wa amarya rakiya ɗakin mijinta"

Shiru aka yi, Aunty Nazeefa ta ce

"Aiko ga shi cen ana gyara ɗakin furnitures kawai ma ake jira"

"Menene abin wani jira ai yaro yana da ɗakinsa anan za su zauna"

Cewar Mamie, Hajjiya babba ta ce

"A'a a dai gyara mata sabon waje, nan ɗin ai ɗaki ɗaya ne ko kitchen babu"

"A shi ɗin za ta zauna, babu na gama magana"

Aunty Nazeefa ta ce

"To tun da ba a rakota da komai ba ai bata da zaɓi ko a store ne su zauna"

ALAJA ta ce

"To alamu sun nuna kuna so ku ci mana mutunci ne, kuma wallahi ba ku isa ba, muna da kuɗin da za mu yi mata kaya, mazan ku ne suka hana, don haka ba za a yi wa ƴata gori ba"

"Madam ki yi hakuri, Bilkisu da Nazeefa ba ku kyauta ba, bai da ce ki faɗi haka a gaban iyayenta ba"

ALAJA ta mik'e ta kama hannun Bilqees ta ce

"To wallahi ba za mu amince da wulaƙanci ba, sai na same mazan naku mun yi magana, in su suka ɗaure muku gindin ku ci mana mutunci sai mu sani"

Hajjiya babba ta mik'e tana bai wa ALAJA hakuri, da ƙyar ta amince ta zauna tare da cewa 

"Wacece uwar Yallaɓai likita?"

Aunty Nazeefa ta nuna Mamie ta ce

"Da ita kike magana"

"To ikon Allah mu da muka kawo miki ƴa amana shi ne kike faɗin haka?"

Mamie ta gyara zamanta ta ce 

"Ni ba abin da nake nufi ba, cewa na yi su zauna a ɗakin mijin nan ma ya ishe su"

Wata daga cikin su ta ce

"Ko gaisuwa ta surka ba ayi ba"

"ALAJA ta ce

"Ba ku nema ba"

Da ƙyar aka bar cece ku ce ALAJA ta ce

"Ai ko a ɗaki ɗayan suka zauna da mijinta ba matsala bane tun da dai suna tare babu me raba su sai Allah"

"A dai yi hakuri magana ta wuce"

Cewar Hajjiya babba, ta ce Teemah ta yayewa amarya mayafinta su kalli fuskarta, ta yaye sun yi mamaki ganin kyakkyawar yarinya, kanta na ƙasa ta kasa ɗagowa, masu sanya albarka suka sanya hatta Mamie jikinta ya yi sanyi ganin fuskarta, sai dai ba za ta bari hakan ya ɓata alaƙarta da ƴan'uwanta ba. ALAJA ta kama hannun Bilqees suka taho masaukinsu.

Zance kamar wasa ya karaɗe family, ba za ayi shagali ba kuma matar Dr Waahab a ɗakinsa za ta zauna, abin bai yi masa daɗi ba, musamman ma da aka yi zancen a gaban Angel, jikinsa ya yi sanyi, da ƙyar Daddy ya ba shi hakuri akan su zauna a ɗakin kamin a gyara bangaren sai su koma.

Dr Waahab ya shigo masaukin baƙi, ya yi nocking Majada ce ta buɗe, ya shigo da sallama Alaja ta amsa ya zauna ganin babu Angel a palour ya sa jikinsa sake sanyi ya ce da Alaja 

"Ku yi hakuri da abin da ya faru, zan sauya mata kayan ɗakina, sabo za a saka mata"

"Duk da ban ga ɗakin ba, ba zan ce ka sauya ba, ka bar shi haka ku zauna"

"Ina Angel?"

"Ta kwanta"

"Zan yi magana da ita"

"To ba damuwa tana ɗaki"

Ya mik'e ya shigo ya tadda tana kwance kan carpet idonta biyu, ya tako ya zauna kusa da ita, ƙamshin turaren da ta ji ne ya sa ta ɗago da kanta, ganin Yallaɓai likita ne ya sa ta tashi ta zauna, ya riƙe hannunta ya janyota kusa da shi, ya ɗago da haɓarta yana kallon fuskarta ya ce

"Jikin ne?"

Ta girgiza kanta alamun a'a, ya sauke numfashi sannan ya ce 

"Ki yi hakuri da...

"Yallaɓai"

Yana kallon ganin ta katse shi, a hankali ta ce

"Zan zauna a duk inda ka ajiye ni"

Tausayi ta ba shi, ya sauke ajiyar zuciya, ya shafi fuskarta a hankali ya furta 

"Na gode, mu je ki ga ɗakin, sai a sauya abin da ba ki so"

"A'a"

Ta ce ta sudda kanta ƙasa, ya ɗago da fuskarta ya ce

"An jima za mu je ki gaida Mommie tana tambayar ki"

"To"

Ta ce, ya mik'e tare suka fito palour ya yi musu sai an jima ya fice, Bilqees ta zauna a lokacin Laraba suka fito cikin shirin fita unguwa, ALAJA ta taɓe baki ta ce

"Ina kuma za ku je?"

"Yallaɓai Sa'eed ne ya ce zai kai mu unguwa"

"Lallai ku da amaryar ku bata samu matsuguni ba a cikin gidan har kuke zumuɗin fita yawo"

"Ai dole su bata wajen zama, kawai iya shege ne amma ai ba za su barta a gantale ba"

Cewa Laraba, jummai ta ce

"Matar nan Nazeefa ta ke ko mecece kan na bar gidan nan sai na koya mata hankali"

"A'a ba ruwan ki mu koma ƙasar mu lafiya, ita kuma taji da shi"

Cewar Laraba, ALAJA ta ce

"Ai ita ce ta sanar dasu ba ayi mata komai ba, kuma nasan a wajen mijinta ta ji"

Angel ba ta ce komai ba, ai laifin su ALAJA ne da ko ƙaramin set su yi mata na hana gori amma sun ki ayi mata suka amince da hakan. Sa'eed ya shigo ya gaishe su sannan suka fice da su Laraba.

*********

Daddy da ke tsaye ya zubawa Mamie idanu ya ce

"Kin kyauta wa ɗakin ki kenan?"

Mamie ta janye tagumin da ta yi ta ce

"Fushi dani Ammie ke yi, har da sauran akan ni na ɗaurewa Babangida baya ya auro wannan yarinyar, bayan tafiyar ku mun ta yi dasu"

"Hakan yana nuni da ba ki amshi matar Waahab a matsayin surka ba?"

"Bana ce ba amma kasan wancan bangaren tun asali mun yi magana na Ashfat ne don ba ayi da ita ba, ba zai yu wata ta shiga ba"

"Uhm Balkisu kenan, ina jiye miki abin da zai je ya dawo, kada don son farantawa ƴan'uwan ki yasa ki jefa ɗan ki cikin wani hali"

Ba ta ce komai ba ya ci gaba da cewa 

"Yarinyar marainiya ce shi yasa Abban Ashfat da Abbie suka ɗauki nauyin yin komai, amma ba don sun kasa ba, sannan a matsayin ki na uwa sam abin da ki ka yi bai dace ba"

Yana gama faɗin haka ya fice abinsa, ta sauke numfashi, nocking ta ji ta bada izinin shigowa, Dr Waahab ta gani tare da matarsa ya yi sallama ta amsa haka ma Bilqees, suka zauna ƙasan carpet Dr Waahab ya ce 

"Mamie ga Bilqees"

Ta ɗan dube shi ta ce

"Me hakan yake nufi?"

"Gaishe ki tazo yi"

"Ina amsawa"

Bai ji daɗin hakan ba, Bilqees ta ce

"Barka da dare"

"Yawwa sannu"

Cewar Mamie bata sake cewa komai ba, 
Jiki a sanyaye ya mik'e ya ce

"Mun tafi"

"Babangida"

Cewar Mamie ya zauna kansa a ƙasa tare da cewa 

"Na'am Mamie"

"Bana ƙin auren ka, Allah ya sanya alkhairi amma kuma a bangaren da kake nan za ka ajiye ta"

"Eh Mamie ai ta amince ma"

"Ko bata amince ba"

Ya ɗan runtse idanunsa ya mik'e tare da cewa 

"To"

Suka fito, ɗakin Ammie ya kaita ba laifi duk da bata sakar wa Bilqees fuska ba amma ta amsa gaisuwarta sannan ta sanya musu albarka. Suka fito zuwa ɗakin Mommie...

Ashfat dake tsaye bakin kofar ɗakin, tun shigowar su take kallon su har suka fice, da ƙyar ta koma ta kwanta, tun jiya da ta ji saukan su ta shiga tashin hankali sosai ta ci kuka har sai da ƴan team ɗin ta suka yi mata faɗa ta yi shiru. Shi kenan ta rasa Ya Waahab, mafarkinta bai zama gaske ba, burinta ba zai cika ba, shi kenan ta rasa farin cikin ta, an ya kuwa za ta iya juriyar zama a wannan Ahalin? An ya ba za ta nisanci ahalinta ba, don ba za ta iya juriyar ganin abin ƙaunarta maƙale da wata ba. Ta   fashe da kuka....

_________________








Comments and share fisabilillah