MATAR SALMAN

Chapter 19

by @hauwa3030

*💫MATAR SALMAN 💫*



*➡PART ONE*
*PAGE 19*


Tun a satin da su Ummah suka tafi hajj Ib ya fara tunanin yanda zai samu ya shawo kan Amina ta amince dashi ba tareda yasha wahala ba.
Kasancewar a sashin su Ummah su Aminan kawai suka rage sai 'yan aiki, don haka rannan Ib ya ga bazai iya jurewa ba, hakurinsa ya kare, ya tafi kansa tsaye duk da ya sami su Ummi, amma haka ya korasu ya rage dagashi sai Aminarsa, yasha wahalar shawo kanta kam gaskiya.....


Su karima sai dai kawai suka jiyo ihun Amina rikicewa sukayi gabadaya, don haka
suka tashi lokaci daya suka tafi sashin Yayansu Nasir wanda Ibrahim ke bi, a gidan yake zaune da matarsa aunty sa'a nurse ce da yaransu maza biyar. Dama da Ummah suka zo tafiya wurin Aunty Sa'a tace Amina ta dinga zama gudun irin haka.

Ib kam bai saurarawa Amina ba saida ya tabbatar ya rabata da budurcinta ya maidata mace sosai, sannan ya kyaleta, amma gaskia tasha albarka gabadaya ya rikice ya fita hayyacinsa gaskia Aminarsa special ce rumgumeta yayi sosai a jikinsa yana rarrashinta hade da sa mata albarka.

Ya zuba mata ido cikeda kulawa "Am sorry my dear zakiji sauki in kinsha magani kinji? Allah ya miki albarka."

Ya shiga toilet din a gurguje yayi wanka ya dawo ya maida kayansa, sannan ya kalli agogo karfe sha daya saura da sauri ya kalli Amina yace "Ina zuwa dear."

Ya fita da niyyar ya je ya kira Aunty Sa'a, kawai sai ya ganta a Palo suna zaune da su ktarima sunyi jigum jigum. Koda ya fito duk ido suka zuba mishi.

Nan da nan ya tamke fuska kallo daya yayi wa Karima da Ummi suka mike sum sum suka bar Palon, don sunsan halinshi sarai yana wasa da su amma in ya juya ido baida daɗi sam.

Bayan fitarsu ya kalli Aunty Sa'a ya dan sosa kai ganin yadda ta sa mishi ido yace "Aunty dama nace don Allah kizo ki duba Amina.......

Aunty Sa'a ta katseshi da faɗin ”Haba Lamiɗo meyasa kayi haka saboda Allah? yanzu me zance da Ummah in ta dawo?"

Ya dan tausasa murya yace "Aunty ni a ganina tunda....

Bata tsaya sauraranshi ta tashi ta shiga dakin anan ta tarar da Amina kwance idonta rufe hawaye na bin kumatunta.

Ta kalli bedsheet din duk ya baci.
Da sauri ta karasa ta riko hannun Amina tana "Sannu Amina kinga ni ko? Shiyasa nace ki yi taka tsan tsan da Lamiɗo dama nasan bazai barki ba."

Ibrahim dai be bar gidan ba saida ya tabbatar Amina tasha magani tayi bacci sannan ya tafi. Ranar ya gagara bacci a gidan sa sai juyi yake domin ji yake kamar ya koma gaskia Amina ta dabance.

Tun ranar ya kasance Ib sai ya je ya biya bukatarsa, tun Amina na ki yau da gobe har ta saba. Sun mori amarcinsu a haka har su Ummah suka dawo sunji dadin samun kowa lfy, bama Amina da tayi kyau tayi fresh abinta.
Sai dai dawowarsu ko sati basuyi ba Amina ta soma laulayi wanda ya kasa boyuwa don duk wanda ya ganta sai ya fahimci cikine kawai.
Abinda ya bawa Haj Rumaisa da Haj Zubaida mamaki lallai yaran yanzu sai a barsu. Umma kam don tabbatar wa ta kira Aunty Sa'a ta yiwa Amina test sai gashi cikin ne.
Amina taji wani irin kunya da nauyin su Ummah kamar ta nitse ta kasa ɗaga kanta ta kalli kowa. Aunty Sa'a kam ta fara kame kame daga karshe dai ta gaya ma Ummah gaskia.
Umma ta kalli Amina ta ce ”kingani ko Amina shiyasa nace miki kar ki kula Lamido ba kunya ne da shi ba, yanzu kinga wannan laulayin shi zai hana ayi bikin nan tare dake, sai dai su Ummin kawai, shikenan tashi kije Allah ya raba lafiya."

Hawayene ya ciko idon Amina domin tana so ayi bikin nan har ita, saboda burinda sukaci na shagalin da za'ayi.
Amma Allah ya rigada yayi ikonsa.

Uban gayya kam ko a jikinsa da maganar bikinsu cikin jikin Amina kawai yake tattali yana ta addu'a Allah ya basu 'ya mace. 

Bikinsu Ummi sai matsowa yake ana ta shirye shirye.

Kwatsam Amina ta wayi gari da ciwon mara mai tsanani har sai da sukaje asibity anan kuwa jini ya balle cikin jikinta ya fita.
Sosai Ib yayi bakin cikin wannan ɓarin, ita kam Amina bayan ta warke ko a jikinta aka shiga hidimar biki da ita.
Duk abinda aka siyawa Karima da Ummi itama Amina sai da aka saya mata gaskia Amina taga gata da mutuntawa a familyn Galadima.
Amare duk sun tare gidajensu, Ummi a Abuja Karima a Maiduguri, Amina kuwa a gidan Ib dinta dake MAFIYAS QUATERS ana Yola
sunyita kukan rabuwa har wasu sun shiga tayasu.

Amina da Ibrahim suka shimfida rayuwar soyyaya cikin jin dadi da annashuwa, basuda matsalar komi. Nan da nan Ib ya soma kiɓa harda ajiye tumbi kayanshi. Ta tare da watanni biyu Jamila ta dawo don taga ba sarki sai Allah.
To haka dai zaman ya kasance da dadi ba dadi har Amina ta koma school.

Shekara biyar da aurensu gashi har ta gama makaranta shiru ba labarin ciki tun dai ɓarin da tayi da farko shikenan, nan Ummah ta shiga neman mata maganin haihuwa duk inda taji.
Jamila kuwa har ta haifi da bai zo da rai ba.

Su Ummi da Karima duk suna da yaransu har bibbiyu maza.
Tun Amina bata damuwa har ta abun ya fara damunta, yanzu sunje asibitoci da dama amma bincike ya nuna ba wani matsala da aka gani, rarrashinta Ib ya dinga yi.

Saida Amina tayi shekara tara cif a gidan ib sannan Allah ya amshi adduarsu ta sami cikin RUMAISA, Jamila ma kuma a lokacin ta haifi Hafiz.
Amma duk da haka Jamila tana matukar jin haushin cikin nan na jikin Amina domin ita anata son kar Amina ta haihu kwata kwata ne.

Anan fa zaman lfy yayi kaura a gidan don kullum Jamila sai ta kirkiro matsala ta hana Amina sukuni nan ma Ib na taka mata birki sosai. Da abin yaki ci yaƙi cinyewa Haj Rumaisa tace Amina ta dawo gida wurinta sai ta haihu.
Haka Amina ta kasance cikin kulawar su Haj Rumaisa har cikin ta ya kai wata tara. A lokacin ta fara nakuda a hankali har haihuwar yazo gadan gadan ba bata lokaci aka kira Ib suka tafi asibityn BOSHANG dake Jimeta Amina na shiga labour room sai ga kan baby, baba bata lokaci ta haifo babynta katuwar gaske wanda da ta kara kadan ma sai dai C.S.
Nurse ta fito lokaci guda Haj rumaisa da Ib da Aunty Sa'a suka mike har suna hada baki "nurse ya.....
Ta katsesu cike da fara'a ta ce ”Ku kwantar da hankalinku Amina ta sauka lfy Alhamdulillah."

Alhamdulillah suma suka fada lokaci guda kowa fuskarshi da farinciki. Haj Rumaisa tace "Ina fatan ita Amina tana lafiya da jariri?

Nurse tace "Ai Hajiya baby girl ce......."

Ib ya kalli nurse da sauri yace "Kikace mene Amina ta haifi baby girl?"

Nurse tace kwarai ma kuwa baby girl ce katuwa lafiyayyiya jajir da ita. Gabadaya hamdala suka dinga yi cike da farin ciki domin wnn itace jika ta farko 'ya mace a bangaren Galadima.

Ib cikeda murna yace wa Nurse "zamu iya shiga mugansu?"
Tace "A'a ana shiryasu sai sun fito tukunna

Ib yace "OK" sai kuma ya kalli Nurse din yace ”Bani account numbernki zan baki tukuicin wannan albishir da kika min."
Nurse ta washe baki tuni ta fara godiya tun ba'a kai ga bata ba, sannan ta bashi account number nan take ya saka mata kudi masu tsoka, ta dinga murna har ta rasa inda zata saka kanta don daɗi.
Amina kam bacci takeyi yayinda Ib yake rike da 'yarsa kamar zai maidata ciki.
Bayan Amina ta huta sosai aka sallamesu don kuwa tuni familyn Galadima sun soma cika musu asibity.

Tun randa aka haifi Rumaisa, Jamila ta shiga tashin hankali sosai har kuka ta yi dan bakin ciki, sai dai tashi alwashin raba Ib da Amina kota wani hali, wannan karon bazata kuma sake ba.

 Amina kam tun ranar da ta haihu ta fara karbar kyaututtuka daga wannan family masu karamci da sanin ya kamata, abun sai wanda ya gani masha Allah.

Ranar suna baby taci sunan Hajiya Rumaisa inda mahaifinta yace a kirata da IHISAN.
A daren da aka watse sunan Rumaisa ita ma Ummi mijinta ya kira yana ma su Ummah Albishir Ummi ta haifi 'ya mace, haba murna ba'a magana, Hajiya Rumaisa harda kuka tana godewa Allah a cikin sati guda ya bata jikoki biyu mata, sai tayata murna ake ta zuwa yi.
Wani karin farinciki ranar suna ita yarinyar aka saka mata suna RUMAISA.


A hankali rayuwa ke tfy Amina da 'yarta sun sami dukkan gata da kulawa har ta manta da matsalar rayuwa itakam. Sai dai hankalinta yayi gida duk sai kewar Yayyenta takeyi, in ta kalli su Auwal kuma sai ta tuno twins dinta Salman da Salim, musamman Salman da yafi manne mata, miskilancinsa na kara burgeta, kamar ba Shatu ta haifeshi ba.

Hmm koda tayiwa Ib maganar zuwa KD bai wani bata muhimmanci ba, ya dai amsata don a rabu lafiya.

Soyayyar da Ib yake nunawa ersa Rumaisa ya wuce duk yadda kuke tunani, abun a fili yake ɓaro ɓaro, har Amina sai da ta mishi magana, don Jamila ta gane, har ta janye ƴaƴanta.

Rumaisa Nada wata hudu ta fara rashin lfy kamar nimonia abinda ya dagawa Ib hankali matuka don yana wahalar da ita sosai musamman in anyi sanyi, don haka dole ya tashi tsaye wurin kula da ita sosai, Amina kanta bata tsira ba inde akan Rumaisa ce, sai ya rufe ido ya mata tass.

Jamila kuwa tana nan tana shige shigenta bata fasa ba sai dai sam bata nunawa Amina ko a fuska ba, yanzu zamansu lfy suke harda hira suke, don haka sosai hankalin Ib ya kwanta sosai.

A lokacinda Rumaisa ta kai shekara daya da wata bakwai Amina ta yayeta. Don ta girma ga wayo ba abinda bataci tana gudu ko'ina.

A wannan lokaci ne kuma Amina ta fahimci Ib ya fara sauya mata don ya daina kulata daga ita har ruymaisa.
Abin ya matukar baiwa Amina mamaki tayi ta tambayarsa amma sai yace mata aiki ne ya masa yawa baida lokacin kansa shima.

Wasa gaske abu sai gaba gaba yake har ya kasance baya cin girkinta kuma in taje dakinsa baya kulata haka Rumaisan ma ya daina daukarta in tana kuka ma baya damuwa sai dai yace ta dameshi.

 Amina ta shiga tashin hankali sosai, taso ace tana tareda wani nata a wannan lokacin domin ta koka masa halinda ta shiga.

Haka ta dinga rokon Ib akan ya fada mata laifinta inshaa Allah zata gyara.
Rannan kam ranshi a bace yace "Wai ke Amina bansan da wani yare zan miki magana ba ki fahimta, wai me yasa kike matsamin da tambaya ɗaya kullum ne? Kinga in bazaki iya zaman nan dani haka ba, ki kama gabanki, ke kinga kije na ma sawwake miki kawai ki dauki 'yarki ku bar min gidana.”

Cike da mamaki da tsoro Amina ta kalleshi tace "what? Ibrahim me kake nufi?"

Kai tsaye yace "Amina ina nufin na sakeki saki daya."

Yana fadin haka yayi ficewarsa a fusace, Amina kam jiri ne taji ya fara dibanta a hakali ta fara fadin "Innalillahi wa inna ilairrajiun!"
Da kyar ta dawo hayyacinta sai ta fashe da kuka mai tsanani ta rumgume Rumaisa tana jin wani nauyi a kirjinta.
Sai da tayi mai isarta sannan ta shirya kayanta ta tafi gidan Galadima anan ta sanar ma Ummah komai. Hankalin Haj Rumaisa ya tashi matuka don haka ba bata lokaci ta nemi Ib tayi masa tatass kuma tace dole ya maida Amina, kuma koda wasa kar ya kara maimaita irin wannan kuskuran.
Haka Ib ya hkr Amina ta koma gidansa, amma sam baya kaunar ganinta daga ita har erta, yayinda Haj rumaisa ta cewa Amina lallai ta dage da addu'a domin wannan al'amari babu lafiya.

Ita kanta Amina tasan da hakan ne duk wani sashi na zuciyarta kuma yaki amincewa. 

Wannan karon wulakancin Ib ya ninka na da sau dubu don ko girki ma Amina batayi bare kuma zuwa turaka.

Jamila da yaranta kawai ke cin karansu babu babbaka a gidan.
Wasa gaske Amina ya kasance sai tayi sati bata saka Ib a ido ba.
Abinci ma sai Jamila taso Amina keci a gidan don a yanzu ko 'yan aiki sun fita daraja.
Ranar cikin dare Rumaisa ba lafiya kirjinta na toshewa tana numfashi da kyar, daga karshe ma numfashin kamar zai ɗauke .....
Amina tayi maza taje tayita yiwa su Ib knocking, da kyar Ib ya bude kofar ya na kallon Amina cikeda haushi.
Rumaisa dake rumgume a jikinta ta mika masa da sauri tace ”Lamido Ihsan zata mutu."

Juyawa yayi zai koma cikin dakin tayi maza ta sha gabansa.
Durkusawa gabanshi tayi ta fashe da kuka mai ban tausayi tace "Lamiɗo don Allah don Annabi ka tausayawa rayuwata data Ihsan ko bacci ba muyi ba don Allah ka taimaka ba don halina ba ka kaita asibity."

Ba tare da ya ko kalleta ba yace "Ke ki kaita mana kawai meye sai kinzo kin matsa min anan ko bakisan hanyar asibitin ba?" 

Amina cikin matsanancin kuka tace "Don Allah Ibrahim ka gaya min abinda na maka kake min irin wnn horon ? Ko ka manta banda kowa a garin nan sai kai din ka tuna fa na bar garinmu yayyuna na bijire musu saboda kai yanzu ina kake so nasa ka raina?"

Murmushi yayi yace "Na godewa Allah da kika gane kuskurenki na rashin biyayya ga yayyunki Amina."
Ya sauke numfashi sannan yace "Amma karki damu lokaci bai kure miki ba kina iya zuwa ki nemi gafarar su indai nine matsalarki...... Amina kije daga yau na yanke igiyoyin aurena dake kanki ma'ana na sakeki saki biyu in kin hada da waccan ya zama uku kenan shikenan kowa ya kama gabansa."

Amina ta mike da sauri kuma a rude ta kalli Ib cikin bacin rai tace "Ibrahim kana cikin hayyacinka kuwa ko kasan me kakee fadi?"

Yace "Na sani sarai Amina, zama dake ya isheni gabaɗaya bana son ganinki daga ke har 'yarki ku fita ku bani wuri kuma na baki daga yanxu zuwa gobe ki tattara ku bar min gida. Kuma har abada ke da 'yarki kar wanda ya kuma dawowa gareni bana bukatarku."

Ya karasa fada cikin tsananin fushi irin wanda Amina bata taɓa ganin yayi ba.

Tashin hankali! Wannan dare Amina taga matsifar rayuwa haka ta sanyawa zuciyarta hakuri ta dauki ' yarta ta kaita hospital cikin daren kuma bata fadawa kowa ba don yanzu kam tsakaninta da Ib ya kare tunda babu sauran igiyar aure don haka babu amfanin taje ta fadawa su Hajia Rumaisa to me zasu mata?

Bayan sun dawo ta tattara kayanta da gwalagwalanta duka kudadenta kam dama suna banki.
Jamila kam kamar ta zuba ruwa a kasa tasha, sai walwalaarta takeyi da ƴaƴanta.

Kafin Amina ta bar Adamawa sai da ta tabbatarwa Ib itama tayi alkawarin bazata kuma dawowa ba daga ita har 'yarta sai ya nemesu da kansa in Allah ya yarda!

A wulakance yace mata "Alhamdulillahi haka nake son ji dama kuma nima bazan nemeku ba kuma har abada don bana buƙatar ku a rayuwata a sauka lafiya!"

Da wannan bakin ciki Amina ta bar Adamawa ba tare da sanin su Haj Rumaisa ba.
Gaskia Amina ta yanke wa kanta hukunci cikin fushi don saida ta isa Kaduna ta fara tunanin da wani ido zata kalli Yayyenta kuma me zatace musu?





*RUMAISA SALMAN BY HAUWA SALIHU USMAN MAMAN KAUTHAR 🥰👍🏻*