2.
KATANGA!
HADIZA D. AUTA.
BIYU.
Tsam na yi da raina saboda tuno halin Iya da matsalolinta. Jiki babu kuzari na kira ta a waya, aka yi sa'a tana kusa ta ɗauka, saɓanin wasu lokutta da take jefar da wayar ta yi ta sabgoginta, ko an kira ba ta sani.
"Hello, Iya."
Na faɗa ina ƙoƙarin danne kukan da yake turnuƙe mini zuciya.
"Lafiya? Na ji muryarki wata iri." Ta tambaye ni cikin muryar faɗa.
"Abban yara ne ya sake ni."
Na yi maganar cikin kuka duk da jarumtar da na so yi kada na yi kukan amma sai da na yi shi. Shiru kawai ta yi mini tana sauraron sautin kukana kamar ta rasa abin cewa. Kafin ta ja numfashi cikin fusata ta yi magana.
"Ya sake ki fa kika ce? To kansa ya yi wa don ke ba ki saku b..."
Cikin sauri na katse ta ina cewa, "Wallahi Allah Ya sake ni Iy...."
"Na ce ba ki saku ba!"
Tsawar da ta buga mini kenan kafin ta ɗora zancenta da cewa,
"Ko ba ki jin yaren da nake magana da shi ne? Wallahi daga ke har shi ba ku isa ba! Ki hanzarin share wuri ki zauna zama daram, babu inda za ki je kuma ko da wasa kada na ji labarin kin bar gidan nan."
A take na ji kukana ya ƙaru, babu shiri na yi magana cikin sautin kukan ina cewa, "Ya fa sake ni Iya, kuma kin san babu sauran igiyar aure a tsakaninmu yanzu duka sun ƙar..."
"Don na sani sai me to? Ai duk abin da ya faru ke kika jawo. Tun da kin kasa yi masa biyayyar da zai zauna da ke lafiya, duk da kyautatawar da yake yi miki ba kya gani, wadda yake yi mana mu ma ba ki godewa. To, ki sani ko auren ya mutu babu inda za ki je, don ban ga gidan uban da za ki zauna da yara uku ba. Idan ma zaton kike za ki ji daɗi don kun rabu; to babu mai aurenki a wannan lokacin da waɗannan yaran. Saboda haka zama gidan ubansu ya kama ki ko babu aure, don duk inda za ki je bai kai gidansu ba."
Kit ta kashe wayar ta bar ni da sharar ƙwalla wata bayan wata, don na kasa sauke wayar daga kunnena ballantana na yi wani abin kirki. Saboda takaicin mari da tsinka jakar da Abban yaran yake yi mini tana ƙara masa ƙaimi.
'Ni kam ya zan yi da rayuwata ne wai?'
Na tambayi kaina don na kasa sarrafa tunanina ballantana na gano mafitar rayuwata da ta yarana. Na yi ƙuri da ido ina kallon jakar da nake haɗa mana kaya tsawon mintuna ban iya motsawa ba.
'Duk na kalli ƙirjinki, ji nake yi tamkar na mutu tsabar baƙinciki. Kowace mace tana da nono a ƙirjinta amma ke komai ya shafe kamar allo. Ta ya zan ci gaba da zama da ke a haka ina kallon ki raina yana ƙara ɓaci?'
Kalaman Abban yaran kenan da suka faɗo nini a raina, waɗanda ko don su ya dace na yi nesa da shi kada na sake funkantar wani sabon tozarcin da wulaƙanci ya zarce wanda ya saba yi mini.
Daidai lokacin 'yata ta fari mai shekara bakwai ta shigo ɗakin tana kawo mini ƙarar Fahat ƙaramin yarona. Tana faɗin,
"Mama kin ga Fahat ya ƙi bari a saka masa rig... innalillahi me kike yi wa kuka Mama? Abba ne ko?"
Ta ƙaraso kusa da ni tana ɓata fuska alamun ita ma kukan take shirin yi, tare da saka hannu tana share mini hawayen da ya kasa barin fuskata. Sauyin yanayinta ya sa na yi hanzarin zuƙe majinar kukana ina cewa,
"Ba kuka nake yi ba Aunty Ummi. Tafi ki saka masa rigar kafin mai yi muku lesson ya ƙaraso ku kai masa kujera. Saboda mun fasa tafiyar sai wani lokaci."
"Mama, me ya sa ba za mu je ba to? Abbanmu ne matsala ko?"
Na yi hanzarin girgiza mata kai, saboda sanin halinta da yadda take nuna jin haushin sa ƙarara idan ya yi mini abu, a gabanta ko idan ta ji labari.
Zame jikinta ta yi daga jikina cikin wani kalar yanayi ta nufi ƙofa da nufin fita tana cewa, "Ni wallahi ba na son sh...."
"Ummi!"
Na kira sunanta da ƙarfi tare da zabura na isa gabanta ina nuna ta da hannu cikin ɓacin rai ina cewa,
"Ko da wasa na sake jin kin maimaita irin wannan maganar sai na saɓa miki!"
Sai da na gyara tsayuwata sannan na sake cewa, "Tukunna ma, sau nawa zan ce da ke ba na son kina faɗar magana mara daɗi a kansa?"
"Ba zan sake ba."
Ta faɗa cikin kuka tana ficewa daga ɗakin tana goge hawayen da ke gangarowa a saman fuskarta. A take na ji wani sabon abu ya riƙe mini wuya. Hannu na ɗora a ka ina matsar ƙwalla, a raina ina jin kamar na yi ta zunduma ihu.
Fahat ɗan shekara uku ya shigo ɗakin da gudu ya faɗa jikina yana dariya, sai ga Nawal mai shekara biyar ta biyo shi da riga a hannunta tana faɗin,
"Idan ba ka caya na saca maca yigar nan ba sai na da'e ka."
"Mama-mama ki foye ni!" Fahat ya faɗa yana ƙara shigewa jikina tare da ruƙunƙume ni. Hannu na miƙa mata alamun ta ba ni rigar ni na saka masa da kaina. Amma ta kauce ta dinga ƙoƙarin saka masa rigar ta ƙarfi tana faɗin,
"Sai na saca maca ita walla'i"
A take na ji tausayin yarana ya kama ni. Saboda ganin tana saka masa yana zillewa. A ƙarshe ta kai masa duka tana miƙo mini rigar cikin haɗe fuska ta sake cewa,
"Mama, saca maca na gaji da ci ni."
Na karɓa ina 'yar dariyar yaƙe na saka masa ina dungure masa kai ina cewa, "Shi fa wannan Fahat ɗin rigima gare shi."
Ita ma ta dungure masa kai tana cewa, "Da ma ci ai ba ya cin majana. Anci Ummi ma aka ya yi mata."
"Ina Aunty Ummin?" Na tambaye ta don na san halinta sarai da nuƙurcinta, don faɗan da na yi mata ya isa ta dinga jan fushi tana kumbura fuska har washegarin safiya.
"Ni ma ban gani ta ba ai." Nawal ta faɗa tana birkice hannuwa da yamutse fuska.
Tsam na miƙe jiki babu kuzari na dinga ƙwalakiran sunanta a cikin gidan amma ban ji alamunta ba. Sai da na fito haraba sannan na hango ta bayan ɗakuna ta haɗa kai da gwiwa wuri ɗaya tana shesshekar kuka.
"Aunty Ummi meye haka wai? Ke shikenan ba damar a yi miki faɗa sai ki dinga yi wa mutane kuk....?"
"Ni wallahi Allah ba ne son muna zama gidan nan." Ta faɗa yayin da ta ɗago kanta bayan ta gama zancen ta mayar da kan nata cikin cinyoyinta tana ci gaba da yin kukan cikin sauti.
"To, idan ba mu zauna ba ina kike so mu je ne?"
Na yi maganar cikin sanyin jiki saboda gabaɗaya ta ƙara lalata mini jarumtar da nake ƙoƙarin nunawa. Musamman maganar da na ji ta sake faɗa, wadda ta yi matuƙar ɗaga mini hankali har ta so zauta ni.
"Ai sai Auncle Ali ya tafi da mu wurinsa mu huta."
Daram-dam! Shi ne sautin dukan da ƙirjina ya yi. Musamman sunan Aliyu da na ji ta faɗa, wanda a take ta sauya mini yanayi zuciyata ta hau tafarfasa, na isa kanta tamkar zakanya. Babu jinkirin komai na wanke ta da wani kalar mari ina numfarfashi. Raina a matuƙar ɓace na nuna ta da yatsa ina cewa,
"Ko sunansa na sake jin kin faɗa a cikin gidan nan sai na yanka ki na jefa gawarki cikin rijiya."
Ta durƙushe tana wani irin kuka, yayin da na ja hannunta ƙi tana magiyar ta bari ba za ta sake ba, amma hakan bai hana ni saka ta ɗakinsu na kulle ba. Sannan na durƙushe bakin ƙofar ɗakin ina wani irin kuka tamkar numfashina zai shiɗe. Nawal da Fahat ma suka rungume ni suna taya ni kukan, wanda alamunsu ya nuna cewa kukana ne ya saka su yin nasu su ma.
Shin ne yake damun wannan family? Ku ci gaba da bibiyar alƙalamina domin na warware muku zare da abawa.
D. AUTA ✍🏻
***.