TSAƘANINMU

16. The Intentional Man

by @zainabb

TSAKANINMU

Khalil ya gama siyayyar da yake yi ShopRite ya fito. Yana fitowa se ga Jawahir ta fito daga cikin motar ta. Kallon ta yayi da kyau domin ya tabbatar itace har ta shiga ciki. 

Yana gama confirming itace yaje jikin motar ta ya jingina yana jiran ta fito daga ciki. 

Bata wani jima daga ciki ba ta fito. Ganin mutum ta yi tsaye a jikin motar ta. Tana mamaki amma bata nuna a fuska ba ta isa wurin. 

"I have been waiting to meet you, Ma'am" 

Kallon shi take da confused look tace "Ni kuma? Saboda me?"

Sauke ajiyar zuciya Khalil yayi yace "Mama na ce ta nuna tana son cupcakes da baked meat pie naki"

Murmushi Jawahir tayi tace "Nagode"

"Rana biyu ina zuwa gidan ku amsar saƙo na kina turo min wata mace" Khalil ya faɗi mata yana kallon ta cikin idanu. Irin mazan nan ne masu confidence 

Murmushin ɗazu na kan fuskar ta ba tace mishi komai ba. 

"Ban taɓa cin kaya irin naki hakan ba. Mama na cewa tayi jikin ta be mata nauyi ba bayan ta gama ci kuma basu da zaƙi irin na sugar"

"Nagode sosai, I'm really grateful"

"You deserve it"

Nodding Kai tayi tana son shiga mota ta wuce. 

"Yaushe zan zo a koya min irin yanda ake?" yace yayi folding hannuwan shi a broad chest nashi yana kallon ta. 

Jawahir tsayawa tayi tana kallon shi tace "Duk ranar da kake so"

"Kin yarda? To yanzu kuwa zan bi bayan ki se ki koya min"

"A'a, ba fa yanzu ba"

Dariya Khalil yayi yace "Bari na kyale ki ki tafi. Amma kafin ki tafi, ki bani number ki. Zan samu?" Yace ya miƙa mata wayar shi. 

Amsa tayi daga gare shi ta rubuta mishi number ta.

"Se na sake ordering wasu kaya amma kar a turo min wata"

Jawahir ba tace komai ba yace "Gashi na kira wayan naki. Save my number"

Wayar ta dake cikin mota ta buɗe ta ɗauko. Sabuwar number ta gani ta san nashi ne, Khalil ya matso sosai wurin ta domin yaga ko zata yi saving. Yana gani tayi haramar saving yace "Sunana Khalil__Khalil Alhassan Waziri"

"Zan rubuta Khalil Waziri" ta faɗa mishi tana ƙoƙarin saving number shi.

Bayan tayi saving yace "Thank you, Jawahir"

Nodding kai kawai ta mishi ta shiga mota ta wuce zuwa gida.



Later in the day, da ƙarfe shida na yamma kafin a fara haramar kiran Sallah Maghrib, se ga Khalil da abokin shi sun taho gidansu Jawahir su tambaya izinin fara zance da Jawahir. 

Ita dai taga Abba yayi baƙi har parlour'n shi aka kai su. Kuma Khalifa ma na tare da Abba amma gabaɗaya bata gane Khalil ba saboda bayan su kawai ta gani ta wuce ɗakin ta. 

Da yake Abba yasan mahaifin shi, yaro ne a wajen minister'n ilmi Alhassan Waziri, sun jima inda yake kafin su faɗi buƙatar su. 

Abba yana sauraren su ya yarda da abinda suka zo dashi se de kuma shi ba shine ze bada izinin zuwa inda Jawahir zance ba. 

Suna nan zaune a wurin, Khalifa ya kira Hamdan ya ba Abba suyi magana. 

Abba ya faɗa mishi abinda ke faruwa duk suna sauraro. Hamdan yace indai Abba ya yarda dasu, then they should go on Kuma idan da gaske suke, kuma dashi da Jawahir sun daidaita kansu, a fara maganar aure kar a tsaya ana dating juna lokaci babu adadi. 

Kamar yadda Hamdan ya faɗi, haka Abba ya faɗa musu kuma suka amince ya basu izinin zuwa inda Jawahir neman yardar auren ta. 

Bayan sun gama magana suka tashi suka tafi ba tare da sun haɗu da ita ba. 

Bayan sun fita, Abba yace Khalifa ya kira mishi Jawahir. 

Tun daga chan ɗakin ta yake zolayar ta ai yau ta samu masoyi me son auren ta. Share shi tayi ba tace komai ba har suka isa inda Abba.

Gaida Abba tayi ta zauna a kusa dashi a kujera. Hannuwan ta biyu yasa a nashi ya fara mata maganar Khalil. 

Yana faɗin sunan shi ta gane shi nan take kuma tayi mamaki sosai da irin abinda ya taho ma Abba dashi. 

"Give him chance and see where it takes you" Abba ya faɗa daga ƙarshe 

"Yaya ya sani, Abba?"

"Yaya ne ya bada izinin shi akan wannan maganar, ƴar Yaya" Khalifa yace se ta kalle shi kaman tayi kuka

Murmushi Abba yayi yace "Kuma duk abinda Yaya yace shi Jawahir ke yi"

"In sha Allah zan duba, Abba"

"Allah yayi miki albarka. Ina miki fatan alheri"

Murmushi tayi tace "Amin, Abba. Nagode sosai"

"Ka gani Abba? Tana so tana kaiwa kasuwa kuma dama ta girma ai wacce zata shiga aji uku" 

"Khalifa ya isa fa, kar ka takurawa ɗiya ta"

"Lallai Abba. Na yarda Jawahir ce kawai a gaban ka"

"Kai kuma a baya na" Abba yace. Dariya Khalifa yayi sosai akan abinda Abba yace ita kuma Jawahir tayi murmushi.



Bayan haka da kwana biyu, Khalil be kira ta ba kuma be tura saƙo ba. Da kanshi ya taho gidansu. Aka mishi iso har cikin parlour'n su. 

Ahmad ne ya faɗa mata tayi baƙo yana parlour yana jiran ta tukuna ya wuce gida. 

Haka ta fito daga ɗakin ta babu komai akan fuskar ta. Abaya ce take sanye da, da mayafin ta ta ɗaura akanta. 

Murmushi ne akan fuskar shi yace "Ga Khalil ga Jawahir"

Itama Jawahir murmushi tayi tace "Haka kuwa" 

Zama tayi daura dashi a kujera daban. 

"Ka zo lafiya?"

"Alhamdulillah. Kuna lafiya?"

"Lafiya, alhamdulillah"

"So you were planning to come to my house and ask them about me?" 

"Ask them about you on what exactly?" Khalil yace kamar be gane abinda take faɗa ba.

"To seek for my hand" ta bashi amsa saboda ta samu kanta very comfortable with him, he's outspoken and she could even sense the vibes 

"I would want to make you my wife. That's the reason, Jawahir. I don't want someone to come before me"

"Allah ya baka sa'a"

"Sa'a? Na samu sa'a daga gare ki fa"

"Tukunna dai. You will have to try and try and try"

"Really?" Khalil yace yayi tagumi yana kallon ta "Kenan ina da aiki a gaba na"

"Idan ka ɗauka ma harda bayan ka"

Dariya Khalil yayi yace "Za ki ga yanda zanyi winning naki da dukkanin zuciyar ki"

"I'd love to see you try that"

"I'm on it already, baby girl"

Dariya Jawahir tayi akan abinda yace. Tun kafin su je ko ina ta gane shi mutum ne da kake saurin sakewa dashi.

"Ki faɗa min wasu muhimman abubuwa a game dake"

Ɗaga idanunta tayi ba tace komai ba na tsawon wasu sakanni tukuna tace "I'm a baker and I take pride in what I do. And of course, a university student of Nutrition and Dietetics. This young woman right here opposite you is a great dreamer because she dreams big"

Murmushi Khalil yayi yace "And as long as we're together, I'll make sure you fulfill every one of your dreams, that's a promise"

Hannu ta ɗaura a chest nata tace "Thank you. I'm grateful"

"You deserve it. What's more?"

"There's nothing actually. I'm a very simple person"

Nodding kanshi yayi yace "I'm pleased"

"What about you? What do I need to know about you before I continue on listening to you"

Dariya Khalil yayi yace "I'm a good man. There's no doubt about that"

"Ba zaka ma bari mutane su faɗa ba?"

"Ba zasu faɗa ba, yafi ni na faɗa"

Dariya suka yi su biyu yace "Ba ki faɗa min wace iri kike ba amma nasan you're a good woman"

"Ya akayi ka sani? Ka sanni dama ne?"

"No, but I know how good your cakes taste , that makes you a good woman"

Murmushi kawai Jawahir tayi ba tace mishi komai ba. 

"So, let's talk. Should I be coming everyday?"

Wani irin kallo ta mishi shi kuma yayi dariya yana kallon ta "Twice a week haka dai ko kuma once. Kaga I'm a student and I run a business"

"What if nayi order cake kullum? Idan na taho zaki fito na gan ki?"

Kaɗan tayi rolling idanun ta "Let's be honest with each other. Kana zuwa sau biyu a sati"

"A sati na uku se ayi min neman auren ki. Yayan ki yace kar na ɓata miki lokaci"

Murmushi tayi tace "Yes if we are compatible"

"Kina gani ba zamu zama compatible ba? I'm already seeing my children in you, Jawahir"

Murmushi Jawahir tayi har kafaɗar ta se da ta motsa. Yau Allah ya haɗa ta da mutum. 

"Kaman chemistry mu yayi matching"

"Yes, it does. And we'll be one beautiful couple"

"Really?" tace tana kallon fuskar shi. Tayi haske tun ɗazu se murmushi yake da dariya. Sumar kanshi very neat, beard nashi ma haka, he's of dark skin me kyau dashi haɗaɗɗen mutum. 

"Really"