FreeArewaPen original
TSAƘANINMU
- 1views
- 15chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
’Whenever an idea lands in her head, she doesn't rest until she writes it out.’
Sample · 1. Meet Ashraf Muhammad Talba
TSAKANINMU _Abuja, Nigeria._ _2016_ Iska ne me ƙarfi yake kaɗawa. Hadari ya haɗu sosai yanayin gari ya canja ko wane lokaci ana iya fara ruwa.Tuki take tana me lura da irin hadarin dake akwai. Ganin yanda iskan ke ƙara ƙarfi yasa tayi gefen titi tayi parking. Shiru tayi tana tunanin yanda zata isa gida irin wannan iskan da ake yi. Hannun ta tasa ta dake steering wheel na motar ta haushi yana kara cika ta gashi gida ba wanda yasan da fitowar ta se me gadi. Wayar ta ta jawo ta kira Ashraf. Wayar be jima da fara ringing ba ya ɗauka. "Ina kusa da ku fa" ta faɗi mishi "A nan Wuse?" Ashraf yace tare da tashi daga kwancen da yake akan gado."Eh. Kaman iska ko ruwa ne zan ce....yana so ya tare ni""Ki jira ni yanzu ina tahowa se mu aje ki gida""Okay. Dan Allah se kayi ɗan sauri Ashraf. Gida ba'a san na fito ba"Tashi yayi tsaye yasa takalmin shi, ya sanya baƙin jallabiya. Fitowa daga ɗakin shi yayi be samu kowa a parlour ba se TV da yake kunne ba'a jin murya. Yana tafiya har ya fito daga cikin gidansu. Iska ne ke kaɗa mishi sumar kai yana yi yana sa hannun shi yana janyewa daga goshin shi, sakamakon shi me yalwar sumar kaine kuma be cika aski ba. Fuskar shi neutral tana me ƙara fitowa da kyawun shi. Shi ya kasance irin mazan nan ne masu haske. Yana da saje wanda yake gyarawa. Yana da tsawo daidai ba wanda ya wuce iyaka ba. Shi ya kasance Igala a kabilance wanda ya ɗauko haske a wurin mahaifinsa. Ashraf be jima da fitowa a gida ba ya hange motar Jawahir. Isa yayi wurin ta yayi knocking a glass na window'n ta. Ɗago kanta tayi ta buɗe murfin motar ana iska me karfi ta ɗan rufe idanun ta kaɗan tace "Kaga iskan da ake""Daga ina kika fito haka?"Fitowa tayi daga motar ta ta bashi makulli ta koma dayan bangaren shi kuma ya shiga inda ta fito yaja mota zuwa unguwar su maitama. "Naje ShopRite ne na siya whipping cream""Baki ga yanda ake haɗa hadari bane kika fito haka?" Ashraf yace tare da kallon ta ya kuma maida hankalin shi akan tuki."Na fito daga wani wurin ne""Okayyy! yau dai bani na saka ki fitowa gida ba kar a miki faɗa ki kirani kina complaining"Dariya Jawahir tayi "Ai dama ko kaine ba laifi nake ɗaura maka ba. Ina ɗaukar accountability ne ga duk abinda nayi""Allah yasa ki ɗauka wannan kar ki kirani kina kuka"Wata dariya ta ƙara yi ba tace komai ba har suka isa unguwar su.Hannun ta ta bashi suka hada knuckles nasu sannan tace "Zaka kira bolt ne?""Eh. Ki shiga gida kar faɗan da za'a miki ya ƙara tsawo"Murmushi tayi tukunna taja mota ta wuce cikin gida. Parking tayi ta wuce ciki da sauri saboda yayyafin da aka fara. Tana shiga cikin babban parlour'n su ta cire takalmin ta flat shoes ta fara tafiya ahankali kar a gano ta shigo gida. Daga stairs taji muryar Yayan ta, Khal...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.