Chapter 3
by @mamyywriter
╔══════════════════════╗
🌺🌺 *KOWA DA RABONSA* 🌺🌺
╚══════════════════════╝
🌺 A Story Filled With Lessons, Destiny and Love🌺
✍️
> BY MARYAM USMAN MAMYY WRITER (FULANIN JAJIRTATTU)
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
🏆 JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION
✨ FIVE STAR WRITERS✨
📞 ***
📚 BOOK 2
📖 Page 3
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
Bismillahir Rahmanir Rahim.
> Wane lokacin kaddara ce take zaɓa maka rabonka, wani kuma rabon nasa ne kaddara. Duk abin da ya zama rabonka dole ne ka yi haƙuri da shi.
~NOTE: Ban yarda da wani ko wata su yi amfani da littafina ba. Ban yi littafin nan da wata ko wani ba. Duk abin da kuka gani mallakina ne, bana so wani ya yi min copy ba tare da sanina ba.~
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
Lumshe idanuwansa kawai ya yi ba tare da ya ce komai ba, domin ba shi da abin faɗa, ya san Hajarah ta yi nasarar rage masa tarbiyyar Shatu, kuma yana tsaron ta ƙarasa, shi ne dalilinsa na dawo da Shatu ɓangarensa, yana kula da duk wani motsita.
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
Bayan kwana biyu, Hajarah ta kasa gane kan Shatu duk hanyar da tabi domin ta shiga ko da falonta ne sai Shatu ta zame, kuma ta tambayi Inayaa inda Shatu take kwana ta ce bata sani ba.
Daga ƙarshe ma sai Daada ta tambaya, tana nuna damuwarta a kan lamarin, ta yi sa'a kuwa Daada ta karɓe zancen ta yafa, a lokacin Shatu bata nan sun fita da motucin da M Madawaki ya siyawa su Nimrah.
Sai bayan sun dawo ne Daada ta saka Shatu a gaba tana faɗa, Hajarah kuwa har da hawaye tana nunawa Shatu bata jin daɗin rashin ganinta a ɓangarenta.
Rima ce ta kalle Daada da take zuba faɗa tana cewa.
"To Abbanta ne ya saka mata dokar zama a ɓangarensa, ko Shatu?"
Gogewa Mummynta hawaye ta yi tare da cewa.
"Mummy ki yi haƙuri, Abbana ne ya hana ni zama a ko'ina ya ce ko karfe takwas na dare ka da ta sake min a falon Daada."
Bakin Daada ne ya mutu, jin abin da Shatu ta faɗa, Mummy ma shiru ta yi da kukan munafurcin da take yi, jikinta ne ya yi sanyi, zuciyarta kuwa ta fara raya mata wasu abubuwan da sauri ta kalle Shatu baki na rawa ta ce.
"Kuma a can kike kwana?"
Ɗaga mata kai Shatu ta yi, tana kallon screen ɗin wayarta da kira yake shigowa, da sauri ta ɗaga waya tana kwantar da kanta a cinyar Daada.
"Assalamu alaikum Abbana."
Murmushi ta yi mai kyau tana cewa.
"To shi kenan abin da za ka ci?"
Dariya ta yi tare da cewa.
"Okay yawwa ka faɗawa Abbansu Nadiya ya zo ya ci abincina..."
Suman zaune Mummy ta yi tana kallon fuskar Shatu da take nuna zallar farinciki, so take ta tabbatar abin da kunnuwanta suke ji gaskiya ne, M Madawaki ne zai ci abincin da Shatu za ta dafa, da alama ma kamar ba yau ne farko ba.
Tunaninta ya katse ne sakamakon tashi da Shatu ta yi tana kallon fuskarsu Nimrah.
"Baby's good night."
Murmushi duk suka yi, suna ɗaga mata hannu, ɗan rungumo Daada ta yi tare da cewa.
"Daada na iya abinci jiya na girka wa Abbana kuma ya ce ya yi daɗi yau ma na girka masa wani.."
Farinciki ne ya bayyana a fuskar Daada tana riƙe hannayen Shatu ta ce.
"Ma sha Allah, Shatu M Madawaki ta fara girma, sai da safe maza tafi ki yi wa Abban naki aikin da ya saka ki."
Murmushi ta yi tana nufar ɓangarensa, a falo ta ajiye wayarta sannan ta shiga kitchen.
A ɓangaren Mummy kuwa ita ma tashi ta yi daga falon jiki a sanyaye, tana shiga bedroom ɗinta Amina ta kira tana bata labarin abin da yake faruwa.
Cike da masifa Amina ta ce.
"Hajarah wai ke har yanzu ba ki koma ɓangaren nasa ba dama? Ba dai wacce shegiyar Yar riƙon ta saka shi ya maida auren ba?"
"Amina ba za ki fahimta ba, tun daga ranar da muka yi magana da ke M.Madawaki yake rufe ƙofar ɓangarensa, ban yi tunanin wacce shegiyar Yar riƙon tasa a karkashinsa take kwana ba."
"To ke wane matakin kike ɗauka yanzu? Na san dai M Madawaki yanzu ba zai taɓa nemanki ba, tun da ba shi ne yake son zama da ke ba, Yar riƙonsa ce, shawara ɗaya ita ce ki yi amfani da wannan maganin in sha Allahu sai ya neme ki mundun ya sha.."
Dariya Mummy ta yi tare da cewa.
"Wallahi na manta da maganar shi ai da tuni ba wannan maganar ake ba, yawwa kin ce ɗaya za'a ba shi ko?"
"Eh ɗaya ya isa duk taurin kansa sai ya nemi mace mundun ya sha ɗin."
"Shi kenan sai kin ji labari domin sai na saka masa biyu na haukata masa ƙwaƙwalwa yadda ba zai iya jurewa ba..."
Dariya Amina ta yi tana sake bata shawara har sukai sallama.
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━
Karfe takwas da minti ashirin ya shigo, shiru da ya ji a falon ne kamar babu mai rai a ciki ya saka nufar bedroom ɗinta.
A tsaye ya sameta da kayan bacci a jikinta riga da wando masu tsayi sosai, ɗauke idanuwansa ya yi daga kanta zai juya ya ji sautin muryarta.
"Welcome Abbana way is Abbansu Nadiya har da shi fa na yi muku abincin?"
Murmushi ya yi yana yi mata alama ta zo, hular kanta ta gyara tana ƙarasowa gabansa, hannayenta ya kama, cikin ƙaramin sauti ya furta.
"Waye ya saka ki wahalar da kanki? MAMUB ba cin abincin zai yi ba, wai baki iya ba...."
Turo baki ta yi, tare da cewa.
"Gaskiya Abbana sai ya ci, ai har da shi na yi,kuma Allah ai na iya ko?"
Ɗaga mata kai ya yi yana cire hannunsa daga nata, ya fita daga bedroom ɗin, yana fita Shatu ta fito falon tana ɗaukar wayarta numbar A Maina ta kira, za ta fara magana ta ji muryar Zulaihah.
Kashewa ta yi tana kiran number Rahmah, ko sallama babu ta fashe da kuka, shiru Rahmah ta yi tana murmushi.
"Waye ya taɓa Shatu M Madawaki a wannan daren?"
Goge hawayen fuskarta ta yi tare da cewa.
"Ba Abbansu Nadiya ba ne, na yi musu abincin shi da Abbana, shi ne ya ce wai shi ba zai ci ba."
Murmushi Rahmah ta yi, tare da cewa.
"Gaskiya bai kyauta ba, ki yi haƙuri ki saka Abbanki ya kira shi zai zo."
Kashe wayar Shatu ta yi jin ƙamshin turaren M Madawaki, zuba masa ido ta yi har ya zauna a kusa da ita yana goge mata hawayen fuskarta, wayarsa ya ɗaga yana kiran A Maina, cikin sa'a kuwa ya ɗaga.
Shiru M Madawaki ya yi bai yi magana, har sai da A Maina ya yi dariya tare da cewa.
"Amma za ka raka ni Hospital in cikina ya ɓace ko?"
Murmushi gefen baki ya yi tare da kashe wayar magana ya yi wa Shatu da ido yana sanar da ita A Maina zai zo, kayan abincin ta kawo tsakiyar falon ta sake shirya musu abincin.
Knocking ɗin da aka yi ne ya sa ta kallonshi domin neman izinin buɗewa, tashi ya yi yana nufar ƙofar wasu number's ya nanna ƙofar ta buɗe.
Shigowa A Maina ya yi ba tare da ya rufe ƙofar ba, murmushi Shatu ta yi tana gaida shi. Abincin ta zuba musu tana komawa gefe ta zauna tana chatting, kamar wasa A Maina ya fara cin abincin yana mai yin bismillah.
A ɓangaren M Madawaki ma bismillah ya yi suka fara cin abincin cikin nutsuwa domin M Madawaki hankali kwance yake cin abincin ba kamar A Maina ba, da aka takura masa.
"Na san Abbansu Nadiya ma ya ji daɗin abincina ko...?"
Shiru ta yi ganin Mummy ta shigo cikin kayan bacci masu kyau, murmushi ta yi, za ta miƙe M Madawaki ya saka hannunsa yana zaunar da ita.
Murmushi Hajarah ta yi tana shigowa cikin falon, zama ta yi a kujerar da take kallon wacce M Madawaki yake, murmushi ta yi tana kallon fuskar M Madawaki ta ce.
"Masha Allah! Ashe Shatuna ta girma ta iya abinci, ƙamshin abincin ne har falona shi ne na fito na ga me ake yi."
Farinciki ne ya kama Shatu ta washe baki, tana dariya.
"Allah Mummy na iya? Jiya na fara yi."
Murmushi ta yi tana satar kallon M Madawaki, wanda yake goge baki, tashi A Maina ya yi shi ma yana goge bakinsa, kallonsu Shatu ta yi tare da cewa.
"Abbansu Nadiya na iya abincin ko?"
Ɗaga mata kai ya yi, yana nufar hanyar fita, yana fita M Madawaki ya tashi ya shiga bedroom ɗinsa.
"Mummy, kina son abincin ne?
Da sauri Hajarah ta girgiza kai tana miƙe wa tsaye, tare da shafa kanta.
"Ki kwanta da wuri, zan shiga domin Abbanki na buƙatar kulawa, kin fahimta?"
Dariya Shatu ta yi tana rufe fuskarta, dariyar Mummy ce ta sakata buɗe ido tana cewa.
"Good night Mummyna."
Shafa kanta Mummy ta yi tana turo ƙofar master bedroom ɗinsa, har ta shiga Shatu na kallonta, tana murmushi, sai da ta gyara inda suka ci abincin ita ma ta shiga nata bedroom ɗin, tana magana da Meerah a waya.
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
Lokacin da Mummy ta shiga M Madawaki yana toilet, kallon room ɗin ta tsaya yi, ganin ya sauya komai na ciki, hawaye ta ji sun zubo mata, ta yi missing ɗin room ɗinsa, yau shekararta ɗaya da rabi kenan.
A gefen bed ɗin ta zauna tana duba takardun da suke saman bed ɗin, har M Madawaki ya fito Mummy tana duba takardun ƙamshinsa ne ya sa ta lumshe idanuwanta da suke cike da hawaye ta yi dana sanin kashe aurenta da ta yi.
M.Madawaki kuwa bai san da zamata a room ɗin ba, domin yana fitowa gaban mirror ya zauna tare da ɗaukar phone ɗinsa yana kiran Yusuf, bayanin Yusuf ya yi masa wanda baya ƙarewa, kullum ka ga M Madawaki yana waya da daddare to da Yusuf yake magana, ya jima suna magana sannan ya kashe wayar yana shafa lotion ɗin dake saman mirror ɗin.
Tun da ya zauna Mummy ta kafe shi da ido ta so ta rungumeshi, amma sai ta bawa kanta haƙura tana son ganin irin karɓar da zai mata.
Yana gama abin da yake, ya tashi tsaye mutum ya ga zaune ya zuba masa ido, abun ya bashi mamaki sosai amma sai ya nuna bai kula da ita, kayan bacci ya ɗauko yana komawa toilet ɗin ya shirya yana tunanin tun yaushe Mummy ta shigo bai sani ba.
A hankali ya fito fuskarsa ya haɗe, hanyar fita ya nufa Mummy ta yi saurin riƙe hannunsa tana fashewa da kuka.
"M Madawaki, ka yafe min Allah na tuba, kuma na gode sosai da ka amince har aka maida mana aurenmu, na yi maka alƙawarin a wannan zama ba zan taɓa saɓa maka ba....."
Shiru ta yi sakamakon hannunsa da ya cire yana fita daga room ɗin, bayansa ta bi tana masa magana, zama ya yi a kujera yana lumshe idanuwansa, sai yanzu ya fahimci matsalar da A Maina ya gano masa.
Zama ta yi daf da shi, za ta kama hannunsa ya yi karfin halin cewa.
"Is okay, ina buƙatar hutawa..."
"Haba M Madawaki yanzu akwai wata hutawa da ta wuce wannan matarka ce fa Ni, na zo gareka ya kamata ka saurare Ni, ko da ba zaka sauke nauyina da yake kanka ba ai....."
Ɗaga mata hannu ya yi, yana tashi daga wajen bedroom ɗin Shatu ya shiga domin ganin abin da take yi, chatting ya samu tana yi wanda ya ɗauke mata hankali har ya shigo bata sani ba, sai da ya karɓe wayar hannunta.
Cusa kanta ta yi a cikin blanket, bai yi mata magana ba, sai remote ɗin AC da ya ɗauka yana rage mata karfin AC, sai da Shatu ta ji ya rufe ƙofa sannan ta tashi zaune wayarta ta duba ta ga bai ajiye ba, dole sai haƙura ta yi tana kwanciyarta.
Yana fitowa suka bugi juna shi da Mummy da take kallonsu, ta gefenta ya bi yana shiga nasa bedroom ɗin tare da rufewa, haƙuri Mummy ta baka kanta ta shiga bedroom ɗin Shatu suka kwana tare.
Haka washegari ranar ma Mummy ta sake shiga master bedroom ɗinsa, a lokacin yana kwance, dole sai fitowa ya yi, ya barta a ciki.
Haka Mummy ta saka M Madawaki a gaba tana bibiyarshi, shi kuma ya saka faɗa mata gaskiyar maganar cewa babu aure tsakaninsu, da ta takura masa ne ya sauya password ɗin ƙofar master room ɗinsa.
Yin hakan da ya yi ne ya samu lafiya ta daina shiga masa, sai dai ta tsaya iya falo, kuma tun ranar take kwana a room ɗin Shatu.
A ɓangaren Shatu kuwa bata san halin da suke ciki ba, domin ba zaman gidan suke yi ba,kullum suna hanyar school, daga boko sai islamiyya, suna dawo gida kuma a falon Daada suke zama har sai takwas na dare sannan take shiga ɓangarensa.
Suna cikin hakan ne, ya yi tafiya Lagos, tafiyarsa ce ta saka Mummy komawa nata ɗakin,kwana biyu tsakanin ta yi tafiya, wacce babu wanda ya san inda ta tafi.
A ɓangaren Baba Malam da Shatu kuwa yanzu bai fiya yi mata magana a kan irin shigar da take yi ba, ya haƙura ya zuba musu ido, ita da Abban nata, yin hakan da ya yi ne ya saka Shatu komawa asili Shatu M Madawaki da kowa ya sani Yar gayu mai ji da kanta.
Duk ranar juma'a sai sun fita, yawonsu a can ne ta samo wani saurayi mai suna Rahim Matawalle, shi ma Yaro ne matashi mai ji da gata da kuɗi, ya jima yana bibiyarta bai samu shiga ba, sai yanzu gani duk su Rima na da saurayi ita ma ta saka wa ranta yin saurayi, sai kuma Rahima ya bayyana.
Babu tunanin komai ta amince da shi, suka fara soyayya, duk Madawaki Dynasty babu wanda ya sani sai Mummynta da Rima, Meerah, da su Nimrah da suka koma Abuja, sai ranar da ya zo Inayaa ta gansu tare.
Jiki na rawa ta faɗawa Mamanta, abin da yake faruwa, cike da farinciki Zulaihah ta samu Rahama da take zaune a falo ita da Innayi, sai Muhammad da ya shigo, tana cewa.
"Wai Maman Muhammad, M.Madawaki ya raba auren da yake tsakaninsa da Shatu ne? Har ta fara kula Samari?"