Chapter 4
by @mamyywriter
╔══════════════════════╗
🌺🌺 *KOWA DA RABONSA* 🌺🌺
╚══════════════════════╝
🌺 A Story Filled With Lessons, Destiny and Love🌺
✍️
> BY MARYAM USMAN MAMYY WRITER (FULANIN JAJIRTATTU)
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
🏆 JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION
✨ FIVE STAR WRITERS✨
📞 ***
📚 BOOK 2
📖 Page 4
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
Bismillahir Rahmanir Rahim.
> Wane lokacin kaddara ce take zaɓa maka rabonka, wani kuma rabon nasa ne kaddara. Duk abin da ya zama rabonka dole ne ka yi haƙuri da shi.
~NOTE: Ban yarda da wani ko wata su yi amfani da littafina ba. Ban yi littafin nan da wata ko wani ba. Duk abin da kuka gani mallakina ne, bana so wani ya yi min copy ba tare da sanina ba.~
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
Jiki na rawa ta faɗawa Mamanta, abin da yake faruwa, cike da farinciki Zulaihah ta samu Rahama da take zaune a falo ita da Innayi, sai Muhammad da ya shigo, tana cewa.
"Wai Maman Muhammad, M.Madawaki ya raba auren da yake tsakaninsa da Shatu ne? Har ta fara kula Samari?"
Baki sake Rahmah take kallonta, Innayi ce ta yi karfin halin cewa.
"Wacce irin magana ce wannan? Dama kin ji labarin akwai rabuwar aure tsakaninsu? Kuma waye ya kawo miki labarin Shatu M Madawaki na kula Samari?"
Cike da rashin kunya Inayaa ta ce.
"Ni ce kuma ai da sanin Mummynta tun yaushe take kula Samarin yanzu ma Yaya Muhammad ya zo na nuna masa, ku tabbatar ba karya nake mata ba, Rahim Matawalle ne..."
Kallon Muhammad Rahmah ta yi tare da cewa.
"Ku je sannan ka ce Shatu M Madawaki ta zo."
Tare da Inayaa suka shiga Madawaki Dynasty, a lokacin Rahim Matawalle na ƙoƙarin shiga mota, Shatu da Meerah na tsaye suna ɗaga masa hannu.
Muhammad tsayawa ya yi har Rahim Matawalle ya fita daga gidan sannan ya ƙarasu inda Shatu suke tsaye, murmushi Shatu ta yi tare da cewa.
"Welcome Yaya Muhammad shi ne jiya na kira wayarka baka ɗaga ba ko?"
"Waye ya fita yanzu?"
Kallon juna suka yi ita da Meerah domin babu hanyar da za su yi masa ƙarya kamar yadda suka yi wa Shamsudeen da ya tambayesu Rahim Matawalle saurayin waye Meerah ta ce saurayinta ne.
Murmushi Inayaa ta yi, tana son ganin yadda za su yi, tun da kowa ya san Muhammad A Maina saurayin Meerah ne, murmushi Meerah ta yi tana kallon fuskar Shatu da kanta yake ƙasa ta ce.
"Yaya Muham..."
Kallon da ya yi mata ne ya hanata ƙarasa maganar, yana nuna Shatu, cikin ɗaga sauti ya ce.
"Shatu M Madawaki soyayya kike yi? Dukan da Abbanki ya yi miki shekarun baya bai shiga jikinki ba ko?"
"Ai a lokacin ban girma ba, yanzu kuma na zama buduwa, kuma na isa a yi min aure babu laifi dan na kula saurayi kuma kowa ya san waye Rahim Matawalle ba...."
Da gudu ta shiga cikin gidan ganin Muhammad yana ƙoƙarin dukanta,
"Inna Lillahi Wa'inna Ilaihir Raji'un!. Shi abin da Daada ta faɗa ganin Shatu ta shigo a guje, Shamsudeen ne ya tashi tsaye yana kallon Muhammad da yake ƙoƙarin kamo hannayen Shatu, fashewa ta yi da kuka tana cewa.
"Allah ba zan tsaya ka duke ni ba, ai babu ruwanka da Ni..."
Haɗe fuska Daada ta yi tare da ƙwace Shatu daga hannun Muhammad ta ce.
"Kai bana son rashin mutunci har gabana zaka zo ka dakar min Yarinya me ta yi maka?"
Sayyid Madawaki ne ya yi gyaran murya, tare da ƙarasowa cikin falon, kallon fuskar Muhammad ya yi tare da cewa.
"Muhammad lafiya me yake faruwa ne?"
Shiru ya yi na ɗan lokaci, domin tunanin abin da zai faɗa, dan ba zai yi faɗa musu abin da yake faruwa ba, baya so maganar ta fita yana so su gyara komai a tsakaninsu da mahaifiyarsu kafin M Madawaki da A Maina su san halin da ake ciki.
"Abban Rima babu komai Umminmu ce take kiranta shi ne take min hauka."
Tsaki Sayyid Madawaki ya yi tare da nunawa Shatu hanya, jiki a sanyaye ta fita tana ƙananu maganganu, Inayaa ce ta yi sauri riƙe hannunta tana cewa.
"Ke Yar gata ce, duk laifin da za ki yi Yaya Muhammad boyewa yake."
Cire hannunta ta yi tana rigasu shiga cikin gidan, Rahmah ta samu zaune a falon farko sai Innayi da take jan cerbi, Nadiya ce ta fito tana ganin Shatu ta fara dariya tana cewa.
"Wai har ya tafi? Yanzu fa nake cewa zan zo mu gaisa."
Kyakkyawan murmushi Shatu ta yi tana rungume Nadiya ta ce.
"Ya tafi Daddynsa ne yake kiransa."
Cikin sanyin jiki Rahmah ta kamo hannun Shatu tana zaunar da ita sannan ta kalle Innayi ta ce.
"Innayi kina jin abin da Shatu M Madawaki take aikatawa,da auren Abbanta a kanta take kula Samarin, da saka hannun Ummi(Nadiya)...."
Katse ta Shatu ta yi tana yin dariya.
"Wai Umminsu Nadiya, Abbansu Nadiya bai faɗa miki ba, ai babu wannan maganar tun yaushe aka rufe shafinta......"
"Shi M Madawaki ne ya raba igiyar auren da take tsakaninku?"
Kallon Maman Inayaa Shatu ta yi jin abin da take faɗa, baki ta turo tana kamo hannun Rahmah ta ce.
"Umminsu Nadiya, tun a satin Abbana ya tabbatar min babu wani aure tsakaninmu domin shayar da ni da Mummyna ta yi, kuma har Abbansu Nadiya ya san da wannan maganar...."
"A'uzubillahi minash-shaiɗanir-rajim! Yaushe ita Ruƙayyah ta shayar da Ke? To wai waye ma ya faɗa miki wannan maganar? Shi Muhammad ɗin ne da kansa?"
Duk kallon Innayi suka yi da take tambayar Shatu, kafin Shatu ta yi magana Zulaihah ta yi saurin cewa.
"To Alhamdulilah, dama abun da kunya a ce aure tsakanin Shatu da M Madawaki wanda duniya suke masa kallon mahaifinta,ai Innayi ba sai ana tune-tune ba, dama na san M.Madawaki ba zai taɓa karɓar Shatu a matsayin matarsa ba, ko da babu mata a duniyar nan......."
Cikin ɓacir rai Innayi ta ce.
"Ke! Zulaihah bana son hauka, Shatu M Madawaki waye ya faɗa miki?"
Nadiya ce ta yi saurin cewa.
"Mummynta ce ta faɗa mata kuma Abbanta ma ya ce haka ne ko Shatu?"
"Eh Abbana ma ya ce haka ne, har Daada, dama Baba Malam ne ban faɗa masa ba, ina jin haushinsa, ai duk shi ne ya yi komai.."
Shiru falon ya yi babu mai bakin magana, kowa da abin da yake tunani, murmushi dole Rahmah ta yi tana kallon fuskar Shatu ta ce.
"Shatu M Madawaki, ai duk da haka dole sai Abbanki ya raba igiyar auren da take tsakaninku, bai kamata kin fara kula Samari ba har sai kin san matsayinki, ban ji daɗin abin da yake faruwa ba, kuma bana so M Madawaki ya san maganar nan ki dakatar da shi Yaron har sai Abbanki ya ba ki dama.."
Shiru Shatu ta yi, kamar ba za ta yi magana ba, Muhammad ne ya zauna kusa da ita yana kama hannayenta cikin sanyin murya domin so yake su lallaɓata, ta dakatar da Rahim Matawalle kafin A Maina ko M Madawaki su san maganar.
"Shatu ki yi haƙuri, zan samu Rahim Matawalle na yi masa bayanin ya yi haƙuri ki kammala school ɗinki, Ni na fi son ki gama karatun sai ki yi duk abin da kike so, kin ga kafin sannan Abbanki ya sanar da Ke matsayinki."
Baki ta turo tana ɓata fuska.
"To na yadda amma in wata ta ƙwace min shi fa?"
Murmushi duk suka yi Muhammad ya ce.
"Ai Shatu KOWA DA RABONSA, duk abin da kika ga ba ki samu ba, to ba rabonki ba ne, ki yi haƙuri har sai Abbanki ya sanarwa duniya matsayinki."
Shiru ta yi alamar ta amince da maganar, su ma kowa shiru ya yi suna tunanin abin da zai faru gaba, Zulaihah ce ta katse musu tunanin ta hanyar cewa.
"Ni fa na yadda da maganar Shatu, tabbas Ruƙayyah ta shayar da ita, kuma Ni a nawa tunanin ai babu wani batun sai an jira M.Madawaki ya raba igiyar aure, dama babu auren, yanzu dai A.Maina za mu jira dawowarsa sai ya aurawa M.Madawaki Inayaa a maimakon Shatu....."
Cike da tsoron Shatu ta miƙe tsaye tana kallon fuskar Zulaihah bakinta na rawa ta ce.
"Mama, Inayaa kuma Abban nawa? Haba Allah ya rufa asiri wallahi ba zan taɓa amincewa ba, Inayaa fa Yarinyar cikinsa ai Abbana ya wuce nan kuma da kike wannan maganar yanzu da aure tsakanin Mummyna da Abbana, ba na buƙatar wata ta sake raɓarsa.."
Dariya Inayaa ta yi tare da cewa.
"Ni babu ruwana da Mummynki, ai namiji Mijin mace huɗu ne, dan haka ina son Abbanki zan iya zama da shi a matsayin Mij...."
Buge mata baki da Shatu ta yi ne ya hanata ƙarasa maganar.
"Ƙarya kike wallahi babu wata mace da za ta sake sharing one bed da Abbana kin yi kaɗan ba ki kai matsayin da zai kallonki a mace ba.."
Faɗa za su fara Muhammad ya yi musu magana, hanyar fita Shatu ta nufa tana cewa.
"Wallahi na sake ganin ƙafarki a Madawaki Dynasty sai na ba ki mamaki zan nuna miki Ni ɗin jinin Madawaki Dynasty ce.."
Murmushi Rahmah ta yi tana bin bayan Shatu da kallo, bayanta Muhammad zai bi Innayi ta hana shi, cikin kuka ta shigo tana kwanciya a cinyar Daada, Abubakar Madawaki ne ya kallon Baba Malam da yake cin abinci, babu wanda ya hanata kukanta har sai da Baba Malam ya gama cin abinci ya ce.
"Shatu M Madawaki me yake faruwa?"
"Baba Malam duk ranar da Inayaa A Maina ta sake shigo mana gida sai na ɗauki babban mataki a kanta.."
Girgiza kai Baba Malam ya yi tare da cewa.
"Ko da wasa bana son ki sake magana irin wannan...."
Cikin kuka Shatu ta ce.
"Wallahi sai na faɗa ai Abbana ba sa'anta ba ne, Allah ba zan sake yadda wata mace ta sake sharing one bed da shi ba...."
Daada ce ta riƙe hannunta tana cewa.
"Shatu M Madawaki me yake faruwa?"
Cikin kuka ta ce.
"Wai Abbana take so, Mamanta na cewa Abbansu Nadiya ya dawowa za ta saka ya aura mata shi."
Mamaki duk suka yi na jin abin da Shatu take faɗa, har Baba Malam da ya kasa motsi ya san Shatu ba za ta yi ƙarya ba, duk abin da ta faɗa ya faru, ganin duk sun yi shiru ne ya saka Shatu nufar ɓangaren M Madawaki da gudu.
A ɓangaren Shatu kuwa kuka ta yi sosai sannan ta shiga falon Mummynta tana sanar da ita abin da yake faruwa, ƙaramin hauka Mummy ta fara, wanda ya tsorata Shatu, hijabi ta ɗauko tana fita daga gidan.
Kwanciya Shatu ta yi domin ta san Mummy gidan A Maina ta nufa, Mummy kuwa na shiga ta samu Zulaihah, babu tunanin komai suka fara kokawa, duka Mummy ta yi wa Zulaihah tana shiga bedroom ɗin neman Inayaa.
Allah ya rufa musu asiri Inayaa bata gidan a lokacin, haka Mummy ta gama haukanta ta fita a gidan, Rahmah na kallonsu ba ta ce komai domin bata shiga harkokin Hajarah yanzu.
Mummy na shiga ta samu Shatu da masu aikin ɓangaren Mummy suna fito da kayayyakin Inayaa, da Mummy aka fita da kayan tana bada saƙo mai girma na kada ta sake ganin fuskar Inayaa duk ranar da suka haɗu, a ranar za ta kashe ta.
Shatu ma Baba Isah mai gadi ta samu, tana saka dokar duk wanda ya sake barin Inayaa ta shigo Madawaki Dynasty a bakin aikinsa, cike da girmamawa Baba Isah ya amsa yana sakawa sauran masu gaɗin dokoki, domin ciki umarnin zuciyar Uban gidan nasu.
Innayi ce ta shigo gidan domin jin dalilin da ya sa aka kawowa Inayaa kayanta, tun a bakin Gate ta jin dokokin da Shatu ta saka na hana Inayaa shigowa Madawaki Dynasty, duk abin da yake faruwa su Baba Malam babu wanda ya sani sai da Innayi ta zo.
Cikin ɓacir rai Baba Malam ya kira Shatu yana yi mata faɗa, yana farawa ta fara ihu tana kuka, dole sai rabuwa ya yi da ita.
━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
Cikin sati guda, Shatu ta hana Inayaa shigowa Madawaki Dynasty duk faɗan da Baba Malam ya yi mata a banza, Abubakar Madawaki ma ya yi nasa amma Shatu ta rufe ido ta ƙi fahimtarsu.
Sanin babu wanda take tsoro sai M Madawaki ne ya saka Innayi kiran shi a waya, yana ɗagawa ta fashe da kuka, ta shi zaune ya yi yana kallon fuskar A Maina da yake gefensa, cikin ƙaramin sauti ya furta.
"Innayi me yake faruwa?"
Cikin muryar damuwa Innayi ta ce.
"Muhammad Shatu M Madawaki ta hana Inayaa shiga Madawaki Dynasty,har da saka masu aiki su ƙwasu mata kayanta, jiya kuma a school ta ƙwace motar Inayaa.."
Katse Innayi ya yi ta hanyar cewa.
"Eshaa ce duk ta yi wannan? Akwai abin da yake faruwa ne?"
Shiru Innayi ta yi tana rasa abin da za ta faɗa masa, jin ta yi shiru ne, ya kashe wayar yana kallon Yusuf da ya shigo.
"Ina so mu koma gida yau."
Tashi A Maina ya yi tare da cewa.
"MAMUB yau fa muke da meeting da AA Shazalee.."
Kallon agogon hannunsa ya yi yana sake kallon Yusuf ya ce.
"Yusuf, a shirya komai sannan a yi wa AA Shazalee message mun ɗaga meeting ɗin sai next week."
"Okay Sir."
Yusuf yana juyawa,M Madawaki ya kalle A Maina, da idanuwasa wanda suke nuna zallar damuwa.
"MAMUB Eshaa bata jin magana ina tunanin sai na sake yi mata irin dukan da na yi mata shekarun baya.."
Murmushi A Maina ya yi tare da cewa.
"Ai kullum damuwarka Shatu M Madawaki ce, yanzu wani abu ta sake yi har kake ƙoƙarin saka kanka cikin damuwa? Ko ka manta wancan dukan da ka yi mata sai da ya taɓa ka, har da kwanciya a Hospital?"