KOWA DA RABONSA

Chapter 5

by @mamyywriter

╔══════════════════════╗
  🌺🌺 *KOWA DA RABONSA* 🌺🌺
╚══════════════════════╝

 🌺 A Story Filled With Lessons, Destiny and Love🌺

 ✍️
> BY MARYAM USMAN MAMYY WRITER (FULANIN JAJIRTATTU)

━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━

🏆 JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION

✨ FIVE STAR WRITERS✨

📞 ***

📚 BOOK 2

📖 Page 5
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ


Bismillahir Rahmanir Rahim.

> Wane lokacin kaddara ce take zaɓa maka rabonka, wani kuma rabon nasa ne kaddara. Duk abin da ya zama rabonka dole ne ka yi haƙuri da shi.

~NOTE: Ban yarda da wani ko wata su yi amfani da littafina ba. Ban yi littafin nan da wata ko wani ba. Duk abin da kuka gani mallakina ne, bana so wani ya yi min copy ba tare da sanina ba.~

━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━


Murmushi A Maina ya yi tare da cewa.
 "Ai kullum damuwarka Shatu M Madawaki ce, yanzu wani abu ta sake yi har kake ƙoƙarin saka kanka cikin damuwa? Ko ka manta wancan dukan da ka yi mata sai da ya taɓa ka, har da kwanciya a Hospital?"

Tashi ya yi ba tare da ce komai ba ya shiga bedroom, murmushi A Maina ya sake, domin ya san duk abin da Shatu za ta sake aikatawa M Madawaki ba zai iya sake dukanta ba, kawai ya faɗa a bakin ne.
━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
Cikin lokacin ƙanƙanin Yusuf ya gama shirya musu dawowa, karfe goma na dare kuwa suka sauka, A Maina bai shiga Madawaki Dynasty gidansa ya nufi Yusuf ma, M Madawaki cewa ya yi, ya tafi gidansa.

Shi ɗaya ya shiga ta ƙofar baya wacce za ta sada shi da ɓangarensa, lokacin da ya shiga shiru ya ji falon kamar babu mai rai da yake rayuwa a ciki, bedroom ɗinsa ya shiga domin a gajiye yake.

WASHEGARI.
Babu wanda ya san M.Madawaki ya dawo sai a sallar asuba da mazan gidan suka ga motocinsa da shi kansa bayan an idar da sallah.

Cikin girmmawa suka gaisa da Yan uwansa, a tare suka shiga falon Daada, da mamaki Daada ke kallon fuskarsa, gaida ita ya yi, ya zauna a falon kamar yadda sauran suke zaune.

Sai bakwai na safe ya shiga bedroom ɗinsa ya yi wanka, cikin sauri ya shirya domin yana son ya haɗu da Shatu kafin su fita school.

Duk saurin da ya yi bai sameta ba, ko da ya tambayata, shiru duk suka yi masa, sai hawaye da ya ga a fuskar Daada, zama ya yi kusa da ita yana dafa kansa, domin ya san wani abu yake faruwa.
"Shatu M Madawaki ta daina yi wa kowa magana ko abinci bata ci a cikinmu,duk haushinmu take ji, duk saboda kai."

Ɗaga kansa ya yi tare da nuna kansa, Abubakar Madawaki ne ya ce.
"Eh saboda da kai ta daina zama a cikinmu, Baba Malam ya yi mata faɗa amma ba ta ɗauka ba, yanzu ma ba ta san ka dawo ba, na san da babu inda za ta fita domin jiran dawowarka take."

Fita ya yi daga falon, zuwa gidan A Maina domin a nan ne zai samu cikakkiyar amsar tambayoyinsa duk abin da yake faruwa Innayi ta faɗa masa, tana cire maganar Rahim Matawalle, shiru duk suka Zulaihah ta fashe da kuka tana cewa.
"Shatu M Madawaki ta yi wa Inayaa cin mutuncin a gaban jama'a duk a kan M Madawaki....."

Cikin tsawa A Maina ya ce.
 "Ke! Rufe min baki,ba duk laifinki ba ne, da kin ɗauki mataki da kike ji Inayaa na maganar ai duk hakan ba zai faru ba, shi MAMUB sa'an wasanta ne ? Kenan Ni ma za ta iya cewa tana son ta aure Ni ko? Shi ba Ubanta ba ne, rashin mutuncin nata har ya kai ta buɗe baki tana cewa shi take so?"

Shiru Zulaihah ta yi, kamar ruwa ya cinyeta, M Madawaki kuwa bai ce komai ba, sai fita da ya yi daga gidan sanin Shatu za ta yi abin da yafi haka akan wannan lamarin.

Har Shatu ta dawo daga school yana bedroom ɗinsa bai fito ba, ita kuma bata kula da motucinsa ba, kuma yau ta falon Daada ta wuce kuma babu wanda ta yi wa magana har Baba Malam da yake zaune.

Abincin da ta shigo da shi ta zauna ta ci a room ɗinta, sannan ta kwanta tana waya da Rahim Matawalle, tun bayan daina cin abincinta take siyowa.

Karfe uku ta fito da shirin zuwa Islamiyya, idanuwanta ne suka sauka a kan Inayaa da take zaune gaban M.Madawaki, a hankali ta ƙaraso a gabansu tana kamo hannayen Inayaa, cikin kuka ta ce.
"Zo ki fita waye ya baki damar shigo mana gida ban hanaki ba, ko yanzu ma biyo shi kika yi domin ki sanar da shi abin da yake zuciyarki?"

"Eshaa."

Juyowa Shatu ta yi da hawaye a fuskarta tana kallon fuskar Abban nata, sai a lokacin ta ga A Maina a zaune, janyo Inayaa ta yi tana kawota gaban A Maina ta ce..
"Abbansu Nadiya ka san abin da yake zuciyar wannan? Wai Abbana take so kuma Mama ta goya mata baya, Abbana sa'an wasanta ne? saboda ita bata da kunya,Ni zan iya cewa ina son Abbanta...."

"Eshaa."

Shiru ta yi tana fashewa da kuka, a hankali M Madawaki ya tashi yana kamo hannayenta, zaunar da ita ya yi kusa da Inayaa, sannan ya kallesu yana gyaran murya.
" Fatimah, Eshaa, I don't like this rashin hankali, na ji everything da ke faruwa. I want it to be na farko da na karshe, then Eshaa ki bata all the things da kika sani mallakinta ne, and ki sanar da waɗanda kika saka suka kwashe mata kayanta su je su dawo da su."

Cikin kuka Shatu ke kallon fuskar Abban nata, sai da ya sake magana sannan ta tashi da gudu nata shiga bedroom ɗin, key ɗin motar Inayaa ta ɗauko tare da ajiye mata a gabanta.

Gyaran muryar da ya yi ne ya sa ta nufar hanyar falon Mummynta, a zaune ta samu Mummy da Amina, sai Baba Jamila da take aiki iya Baba Jamila ta yi wa magana tare da sanar da ita, su je gidan A Maina su kwaso kayan Inayaa, tana rufe baki Mummy ta ce.
"Inji wane shegen? Ban hana ki zama a cikinsu ba, da har aka samu wani ya zugaki Inayaa ta sake shigowa Madawaki Dynasty?"

Cikin muryata da kuka ya gama cinyeta ta ce.
"Abbana ne ya dawo shi ne ya ce yanzu sai na saka an dawowa da Inayaa kayanta....."

"Kan uba yaushe M Madawaki ya dawo?"

"Ni ma ban sani ba yanzu na ganshi tare da Inayaa a falonsa........."

"Inayaa kuma? Shi M Madawaki? Shi kenan Shatu na san A Maina sai ya zuga Abbanki ya auri Inayaa ai mun shiga uku.."

Kuka ne ya ƙwace wa Shatu da gudu ta koma inda ta fito, lokacin da ta shiga Inayaa bata falon iya shi da A Maina ne, kallon bayanta A Maina ya yi yana girgiza kai har ta shige bedroom ɗinta.

Lumshe idanuwansa ya yi, yana kallon agogon hannunsa, sannan ya miƙe tsaye, hannayensa A Maina ya riƙe shi tare da zaunar da shi.
"MAMUB ka rabu da Shatu M Madawaki ta huta dole za ta ji babu daɗi, ka yi haƙuri har sai ta wuce....."

"Eshaa fa bata jin magana, ka san abin da Daada ta faɗa wai bata cin abinci a cikinsu ba ta zama a cikinsu, narasa abin da yake damunta......"

"Kishinka take yi, ai na jima da sanar da kai Shatu M Madawaki ba Hajarah take tayawa kishi ba, kanta take yi wa......"

Tsaki M Madawaki ya yi yana shiga bedroom ɗin Shatu, a kwance ya sameta tana kuka, jikinsa ne ya yi sanyi, ganin fuskarta ta sauya kala saboda da kukan da take fama da shi, a hankali ya zauna a gefen bed ɗin.

Shiru ta yi tana kallon fuskarsa, hannunsa ya miƙe mata alamar ta zo, jiki a sanyaye ta kamo hannun nasa, tana yin ƙasa da kanta.

Shafa kanta ya yi yana kallon fuskarta tausayinta ne ya kama shi sosai, ganin duk ta rame ga damuwa kwance a fuskarta.
"Eshaa what happened."

Goge hawayen fuskarta ta yi tana nuna shi, cikin shagwaɓeɓiyar muryata ta ce.
"Abbana don Allah ka yi min alƙawarin ba za ka sake auran kowacce mace ba, Ni bana so iya Mummy ta isa bana so wata ta sake shigo mana gida a matsayin matarka, duk ranar da hakan ya faru mutuwa za......"

Hannunsa ya ɗora saman lips ɗinta yana girgiza mata kai. Kwantar da kanta ta yi a jikinsa tana sauke ajiyar zuciya tare da cewa.
"Wai Inayaa ce take sonka, duk ranar da na buɗe ido na ga wata mace a matsayin matarka na san a ranar zan koma ga Allah...."

"Stop it Eshaa, bana so I don't want to hear bakinki ya sake ambaton waɗannan maganganun. Ni ba zan yi aure ba, and even if zan yi auren ma, ba zan auri yarinya ba, No, I can never aurar da yarinya kamar diyata. Do you understand?"

Shiru Shatu ta yi tana sauke ajiyar zuciya, a hankali ya fara yi mata faɗa a kan, abin da ta yi wa su Daada, sannan ya ce sai ta bawa Kowa haƙuri.

Tare suka zauna a bedroom ɗin, tana bashi labarin iri-iri duk da ba magana yake ba, ba ta daina bashi labarin ba, ta san yana ji maganar ce ba zai yi ba, kiran sallah ne ya saka shi fitowa ya tafi masallaci, ita kuma ta yi sallar a room ɗin sannan ta yi wanka.

Lokacin da ya dawo ita da Mummy ya samu a falo, bedroom ɗinsa ya shiga ba tare da ya yi magana da su ba, har ya gama abin da zai yi suna zama jiran shi, a hankali ya fito cikin farar jallabiya, wacce ta sake bayyana zallar kyaun fuskarsa.

Ita da Mummy duk sakin baki suka yi suna kallonshi, hanyar falon Daada da ya nufa ne, suka tashi suna bin bayansa, a tare suka shiga, kallon fuskar Shatu Baba Malam ya yi.

Maganar da Abbanta ya faɗa mata ne suka dawo mata, ƙasa ta yi da kanta tana cewa.
 "Baba Malam ka yi haƙuri ba zan sake ba."

Murmushi kawai Baba Malam ya yi yana kallon fuskar M Madawaki, rungume Daada ta yi tare da cewa.
 "Na tuba Daada ba zan sake ba...."

"Babu komai Shatu M Madawaki komai ya wuce."

Abubakar Madawaki ta kalla tana ba su haƙuri shi da sauran, duk murmushi suka yi, babu wanda ya ce komai, abincin suka ci, cikin nutsuwa da kwanciyar hankali. 

Suna gamawa su Shatu suka shiga bedroom ɗin Rima a can ta zauna har tara na dare.
━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
A ɓangaren M Madawaki kuwa yana tashi Mummy ta bi bayanshi, kallonta ya yi lokacin da ya zauna a falonsa, kashe murya ta yi tare da cewa.
 "Sannu da dawowa M Madawaki."

"Yawwa."

Da mamaki take kallonshi jin abin da ya faɗa, farincikin ne ya kamata ta sake matsowa kusa da shi za ta taɓa shi ya miƙe tsaye yana kallon wayar hannusa.

"Ko da wasa ne, I don't want to hear wani mummunan abu ya faru da Inayaa, ki yi a hankali."

Yana gama maganar ya barta a falon yana shiga bedroom ɗinsa, baki sake Mummy take kallonsa har ya rufe ƙofa.

Murmushin mugunta ta yi tare da tashi tana komawa falonta, Inayaa ta gani zaune tana waya, tsaki ta yi tana shiga bedroom ɗinta, wayar Amina ta kira tana cewa.
"Amina wai ya ake amfani da wannan maganin so nake na koyawa M Madawaki hankali na ga ya gama raina ni...."

Dariyar Amina ce ta katse mata maganar, cikin dariya ta ce.
"Ai ke ce kike sanyin jiki, da tuni mun wuce wajen yanda kike sha gyaran nan ai M Madawaki hannunki zai dawo, amma kin tsaya wasa.."

"Amina kenan Ni bana son cutar da shi ne, shi yasa na san tabbas zai cutu in dai na saka masa wani magani....."

"Ke! Bana son wani munafurci to shi kuma yake cutar da Ke, kawai Malama ki zuba masa tun da bai yi don Allah ba, a wahala za ta kawo shi.."

"Haka ne fa, zan saka masa ɗaya a tea gobe na san 
yau ya gama cin abincin.."

"Yawa yar gari in dan ya sha da safen ki sake ƙara masa wani da rana na san duk ƙarfin jininsa zai haukace kamar yadda muke so, ya zo gareki."
━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
Lokacin da Shatu ta dawo bata same shi a falon ba, ita ma bata neme shi ba, sanin ya shige, haka ta kwanta bacci, cikin bacci ta ji ya shigo bai jima ba ya fita.

Washegari ranar kuwa karfe bakwai ta tafi school, ko gaisawa ba su yi, shi ma bai fito ba sai takwas, Mummy ya samu zaune a falo gaida shi ta yi ya amsa yana nufar hanyar dinning room ɗin, da sauri ta tashi tana riga shi shiga.

Yana zama ta zuba masa tea ɗin da ta haɗa masa wanda yake tashin ƙamshi,karɓa ya yi yana fitowa daga dinning room ɗin, a kujerar ya zauna sai ga A Maina ya shigo magana suka fara yana shan tea ɗin.

M Madawaki ne ya ajiye kofin tea ɗin bayan ya sha rabi dalilin, zafi da kirjinsa ya fara domin citar da take cikin tea ɗin, kalle A Maina ya yi tare da cewa.


"AA Shazalee ya sauka karfe tara zamu zauna da shi."

"Okay sai mu tafi ko?"

Tashi M Madawaki ya yi suka fita, Yusuf na ganinsu ya buɗe mota, domin fitowarsu yake jira ganin lokacin ya tafi kuma ga AA Shazalee ya zo.

Ko da suka isa motocin AA Shazalee na shigowa, a tare suka shiga ciki.
━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━