Chapter 6
by @mamyywriter
╔══════════════════════╗
🌺🌺 *KOWA DA RABONSA* 🌺🌺
╚══════════════════════╝
🌺 A Story Filled With Lessons, Destiny and Love🌺
✍️
> BY MARYAM USMAN MAMYY WRITER (FULANIN JAJIRTATTU)
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
🏆 JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION
✨ FIVE STAR WRITERS✨
📞 ***
📚 BOOK 2
📖 Page 6
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
Bismillahir Rahmanir Rahim.
> Wane lokacin kaddara ce take zaɓa maka rabonka, wani kuma rabon nasa ne kaddara. Duk abin da ya zama rabonka dole ne ka yi haƙuri da shi.
~NOTE: Ban yarda da wani ko wata su yi amfani da littafina ba. Ban yi littafin nan da wata ko wani ba. Duk abin da kuka gani mallakina ne, bana so wani ya yi min copy ba tare da sanina ba.~
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
Tashi M Madawaki ya yi suka fita, Yusuf na ganinsu ya buɗe mota, domin fitowarsu yake jira ganin lokacin ya tafi kuma ga AA Shazalee ya zo.
Ko da suka isa motocin AA Shazalee na shigowa, a tare suka shiga ciki.
━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
Mummy kuwa M Madawaki na fita ta fito daga inda take tsaye ta fara dariya tana kiran number Amina, labari ta bata, suka fara dariyar farinciki.
A ɓangaren M Madawaki kuwa tun bayan gama meeting ɗinsu da AA Shazalee ya ji wani yanayi na daban, kasa banbanci abin da yake ji ya yi, shiru ya yi yana tunanin abin da ya sauya masa lafiyar jikinsa.
Gumi ne ya fara karyo masa a goshi, zuciyarsa ce ta fara bugun, numfashinsa ya fara karuwa, murɗawar da mararsa ta yi ne ya saka shi kiran number Yusuf.
Da sauri Yusuf ya shigo, ganin M Madawaki ya lumshe ido, ga gumi da yake fita a goshinta ya ƙaraso cikin rawar jiki.
"Sir a You okay?"
"Yusuf mu koma gida sannan ka kira min Dr Omar."
Amsawa Yusuf ya yi, yana gyara masa kayan office ɗin sannan suka fito.
Cikin minti 15 suka koma Madawaki Dynasty da mugun gudu masu gadi suka bude gate a firgice ganin yadda motocin suka shigo da gudu.
Yusuf ne ya tallabe shi domin a lokacin ya fara rasa sauran nutsuwarsa, ta ƙofar baya suka shiga, Yusuf ne ya buɗe ƙofar domin ya san duk password ɗin ƙofufin inda yake rayuwa, a falon ya kwantar da shi yana sake kiran Dr Omar.
Cikin minti 20, Dr. Omar ya shigo da jakarsa. Babban likita ne, shi ne yake duba M Madawaki, Babban mutum ne kamar M Madawaki, zama ya yi tare da fara duba BP ɗinsa, fuskar M Madawaki Dr ya lalle tare da cewa.
"M Madawaki, me kake ji a jikinka exactly?"
Shiru ya yi na ɗan lokaci sannan ya buɗe bakinsa a hankalin ya ce.
"Omar ban iya banbance abin da nake ji ba, amma marata..."
Yusuf Dr Omar ya kalle tare da cewa.
"Wani abu ya sha. This is not normal fever ko gajiya ba ne wannnan kamar reaction ne na wani abu da ya shiga jikinsa, ya ci wani abu ne ko ya sha wani abu, domin maganin da na bashi satin da ya wuce na san zai ɗauke tsawon lokaci bai shiga irin wannan yanayin ba.."
Shiru Yusuf ya yi, yana tunani halin da M Madawaki ya shiga da suna Lagos, kamar zai mutu sai da Dr Omar ya rubuta masa magani sannan ya samu nutsuwa.
A hankali M Madawaki ya furta.
"Tea! Na sha da safe."
Miƙewa Dr Omar ya yi tare da cewa.
"Ina kofin? Ina sauran tea ɗin? I need that cup. Dole na gani, don na yi test, a nan zan gane me aka zuba maka a ciki."
Dinning room ya nuna wa Yusuf, da sauri Yusuf ya shiga cikin sa'a kuwa cup ɗin yana nan akan table, da sauran tea ɗin har lokacin a ciki.
Dr Omar ne ya karɓa cup ɗin ya fita,
Tun bayan tafiyar Dr Omar hankalinsa bai kwanta ba. Abin da ya fi damunsa shi ne yadda jikinsa ya sauya lokacin ɗaya, Yusuf ya kalla tare da cewa.
"Bana so Eshaa ta dawo ta same ni a wannan hali, mu je MAMUB Quarters."
Cike da girmamawa Yusuf ya taimaka masa suka fita, har suka isa Quarters ɗin M Madawaki na gumi, da taimakon Yusuf suka shiga ciki.
Yana shiga ya wuce bedroom yana sakarwa kansa ruwa,ko zan samu sauƙin abin da yake ji, mintinan goma sha biyar tsakanin ya fito, a zaune ya samu Yusuf yana waya da A Maina yana sanar masa M Madawaki yana private Quarters ɗinsu.
Yana zama Dr Omar ya yi knocking, Yusuf ne da ya sanar da shi inda suke, ya tashi yana buɗe masa ƙofa, yana zama M. Madawaki ya gyara zamansa.
"Doctor, sakamakon binciken ya fito?"
"Yes, Mr. Madawaki. A sakamakon mun samu sinadarin VX-17, sinadari ne mai karfi gaske da yake saurin fitar da mutum a haiyacinsa, shan irin wannan magani ga mai irin yanayinka babban haɗari ne..."
"Doctor Omar, please help me with something, I can't bear the condition that I'm in."
Gyaran zama Dr. Omar ya yi yana kallon fuskar M Madawaki, tare da bude jakarsa a hankali ya dauko wani karamin file.
"Mr. Madawaki, ka kwantar da hankalinka, this VX-17... sinadari ne da aka hada da gangan to affect you, duk da kana da ƙarfin jiki, the substance has had an effect, yanzu hanya ɗaya ce zan iya taimaka maka."
Lumshe idanuwansa M Madawaki ya yi, yana ciza lips ɗinsa.
"Omar... my body... like fire, and my private part is like a stone, help me."
Dr. Omar ne ya gyaɗa kai cikin fahimta, dama ya san abin da M Madawaki zai faɗa kenan.
"Na sani, that's why I brought you this medicine, zai kwantar da bugun zuciyarka, and reduce this heat da kake ji. Amma dole ne ka yi hakuri, it will take a little time."
Allura ya dauko guda biyu daga jaka da ya zo da ita sai wani magani guda ɗaya.
"The injection zai rage karfin wannan sinadarin a cikin jininka, and the medicine zai sa ka samu damar yin bacci mai nauyi na awanni biyu. If you wake up, zaka ji sauki sosai."
Yusuf ne ya matso kusa da Dr Omar cike da damuwa ya ce.
"Doctor, akwai matsala ce babba? I don't want Sir to enter the same condition like that of last week."
"No, babu matsala mai girma if we do this Injection, Amma... Mr. Madawaki, daga wannan lokaci the Injection zai daina aiki a jikinka, mafita ɗaya ce, which is you have to get married, duk waɗannan Injections jikinka ya saba da su."
Shiru Yusuf ya yi domin ya san Uban gidan nasa babu maganar aure a tsarinsa, Dr. Omar ne ya yi masa allurar, a hankali M Madawaki ya sauke wata ajiyar zuciya mai karfi, tare da lumshe idanuwansa.
Yusuf ne ya kawo masa ruwa mai sanyi ya sha maganin, bayan kamar minti goma, idanuwansa suka fara nauyi.
Dr. Omar ne ya mike yana hada jakarsa.
"Yusuf, ka zauna anan, kada ka bar shi kadai, idan ya farka, ka bashi wannan maganin sannan a kiyaye ka da ya sake shan makamancin maganin nan."
"Okay Doctor."
Dr. Omar na fita, baccin wahala ya ɗauke M Madawaki,Yusuf ne ya zauna a kujerar kusa da M Madawaki yana kallonsa, wayarsa ce ta yi kara, sunan A Maina ne ya bayyana.
Cikin sanyin murya ya ɗaga a hankali kada ya tashe shi.
"MAMUB Quarters muke, Dr Omar ya zo ya bashi magani, yanzu yana bacci. Lab ɗin ya bada result VX-17 ne."
Daga ɓangaren A Maina ya gyara tsayuwar yana cewa.
"VX-17? Meye haka?"
"Sinadari ne aka zuba masa a tea, wanda zai ƙara masa ƙarfi sha'awa,Dr ya ce da gangan aka yi."
A Maina ne ya yi shiru na dan lokaci, cikin sanyin murya ya ce.
"Ka kula ina zuwa."
━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
Sai yamma A Maina ya shigo private Quarters ɗin masu, tun shigowarsa ya zuba M Madawaki ido, sai biyar saura M Madawaki ya farka, babu wanda ya kalla a cikinsu ya shiga cikin ɗaya daga cikin bedroom ɗin.
Mintinan ashirin tsakanin ya fito, zama ya yi tare da karɓar wayoyinsa missed calls guda 17 ya samu 9 daga Shatu, girgiza kansa ya yi.
Kafin ya yi motsi kira ya sake shigowa, dafa kansa ya yi da yake masa ciwo yana ɗaga wayar.
"Abbana?"
Shiru ya yi na ɗan lokaci sannan ya amsa cikin ƙaramin sauti.
"Abbana na dawo daga school amma kai har yanzu baka dawo ba, kuma na yi maka abincin."
"Eshaa ina private Quarters bana son hayaniya....."
Kafin ya ƙarasa maganar ta kashe wayar, kallonsa A Maina ya yi tare da tambayar yananin jikin nasa.
"I'm okay na ji sauƙi, Yusuf kai ma ka tafi gida.."
Shiru A Maina ya yi ba tare da ya sake magana ba, Yusuf ma ƙasa ya yi da kansa cikin ƙaramin sauti ya ce.
"Sir ba zan iya tafiya ba, na saka an gyara min ɓangaren can...."
Kallon Yusuf ya yi da idanunwansa da suke jajir da su har lokacin, zaman shiru duk suka yi har lokacin sallar isha'i sannan A Maina ya tafi bayan ya sake kiran Dr Omar ya duba M Madawaki ya gabansa.
━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━
Madawaki Dynasty.
Mummy tun bayan fitar M Madawaki, Amina ta zo suka tafi gidan wata mata yar Nijar da take gyaran jiki, kuɗin Mummy ta sake sosai wanda ta karɓa a hannun Shatu.
Sai yamma suka dawo, da nufin sake sakawa M Madawaki sauran maganin da ya rage, tana shigowa Madawaki Dynasty ta fara duba motocin M Madawaki, ganin babu motocinsa ya saka ta kiran Mamman tana tambayar ko M Madawaki bai dawo ba.
Sanar da ita ya yi bai dawo ba, tun safe domin lokacin da M Madawaki ya dawo gidan, Daada ta aike shi, tsaki ta yi tana shiga ciki.
Wayarshi ta so kira Amina ta hanata, har Shatu ta dawo daga islamiyya, ganin Mummynta cikin damuwa ne ya ɗaga mata hankali, ta zauna tana tambayarta.
"Mummy me ke faruwa?"
Hannayen Shatu ta kamo cikin damuwa sosai ta ce.
"Shatu Abbanki tun safe da ya fita bai dawo ba, kuma ba cikakkiyar lafiya ce da shi ba......"
Baki na rawa Shatu ta ce.
""Inna Lillahi Wa'inna Ilaihir Raji'un! Me yake damun Abbana ina yake?"
Tsaki Amina ta yi, tana kallon fuskar Shatu da, damuwa ta bayyana sosai.
"Ban san inda yake ba, kuma ko na kira wayarshi bata tafiya, ina son sani inda yake ko dan lafiyarshi..."
Shiru Shatu ta yi tana kiran number Abbanta,sai da ta yi kira tara sannan ta kira number Yusuf, kiran farko ya ɗaga, yana yin shiru, sanin M Madawaki take nema kuma yana ganin kiran da take yi a wayoyin M Madawaki da suke hannunsa.
Ɗaga ce bai yi ba, domin baya ɗaga kiran Shatu in ta kira M Madawaki, sanin matsayinta a wajen Uban gidan nasa.
Cikin sanyin murya ta ce.
"Uncle Yusuf ina Abbana? Me yake damunsa?"
Gyaran muryarsa ya yi tare da cewa.
"Sir yana hutawa, kuma yana lafiya."
Kafin ta sake magana ya kashe wayar, kasa zama Shatu ta yi tana ɗagawa Daada da Baba Malam hankali, wai Abbanta ba shi da lafiya kuma ba'a san inda yake ba, sai da Abubakar Madawaki ya kira A Maina, yana tambayar shi abin da yake faruwa.
Boye musu A Maina ya yi, tare da cewa.
"Yaya Abubakar, MAMUB lafiya yake waye ya ce ba shi da lafiya ne? Waya ce ba zai ɗaga ba yana ganawa da baƙi."
Sai a lokacin hankali Daada ya kwanta, Baba Malam kuwa Shatu ya kalla yana cewa.
"Ai kin ji abin da Abubakar ya faɗa ko? To ki yi haƙuri har ya gama abin da yake na san zai kira ki."
Bata yi magana ba sai ɓangaren Mummynta da ta koma a can ta zauna har dare, Mummy na tsara mata abubuwan da suke damu M Madawaki, tare da bata magani ta ce, ta zabu masa a coffee.
Karɓar maganin Shatu ta yi tana sake kiran numbersa cikin sa'a kuwa ya ɗaga, yana sanar da ita inda yake,ta miƙe tsaye tare da kallon Mummy ta ce.
"Mummy, Abbana yana private Quarters ɗinsu kawo abincin na kai masa, sai ya sha maganin zan dawo.."
Jiki na ruwa Mummy ta raka Shatu mota tana sake jaddada mata yadda za ta sakawa M Madawaki maganin in ta isa ba tare da M Madawaki ya sani ba.
Murmushi Shatu ta yi tare da komawa cikin gidan falon Daada ta shiga ta same su suna cin abinci, Daada ta rungume tare da cewa..
"Na tafi private Quarters ɗin Abbana, ashe yana can."
Dariya Omar Aminu Madawaki ya yi tare da cewa.
"Har na bada cikiyarshi a gidajen rediyo...."
Dariya ta yi tana nufar hanyar fita, Baba Malam ne ya ce.
"Ki yi tuƙi a hankali, ko ki tsaya Shamsudeen ya raka ki..."
"Ni babu mai raka Ni kuma sai na gudu."
Murmushi manyan suka yi tare da kallon fuskar Baba Malam da ya nuna kamar bai ji abin da Shatu ta faɗa ba.
━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
Karfe tara da rabi ta isa Quarters ɗin, Quarters ne mai kyau sosai, babu motsi kowa, motoci ma ba kasafai suka fiya fitowa ba, har ta isa ba ta haɗu da mota ko ɗaya ba, dama babu wasu mutane a Quarters ɗin daga shi sai A Maina, duk da shi A Maina bai fiya zama a ciki ba.
Zaune suke shi da Yusuf domin ya ji sauƙi sosai, har aiki ya samu damar yi, motsi buɗe ƙofar da suka ji ne ya saka Yusuf tashi tsaye,domin ganin waye, ya san password ɗin ƙofufin gidan da yake ƙoƙarin shigo falo.
Shatu ya ga ta shiga da kayan abinci a hannuta da sauri ya karɓi kayan abincin yana ajiyewa a gaban M Madawaki. Yana karɓar kayan ta yi saurin ƙarasawa jikin M Madawaki da yake zaune.
Lumshe idanuwansa ya yi, ganin ta faɗo jikinsa, tana kuka gefen da Yusuf yake ya kalla, wayam babu Yusuf murmushi ya yi tare da cire Shatu daga jikinsa.
"Eshaa kunneki ba ya jin magana ko?"
Goge hawayen fuskarta ta yi, tana murmushi.
"Sorry Abbana ya jikin ya yi sauƙi? Ka sha magani? Uncle Yusuf ya kira Dr Nadraa ta duba ka?"
Dogon hancinta ya ja, tare da miƙewa tsaye.
"Who said I am sick?"
Kamo hannayensa za ta yi, ya yi saurin shiga bedroom yana murmushi, zama ta yi a kujerar da ya tashi tana dariya, kiran wayarta Mummy ta yi, cikin saurin Shatu ta ɗaga tare da cewa.
"Mummy, na zo kuma babu abin da yake damun Abbana....."
Katse ta Mummy ta yi tana cewa.
"Ina M Madawaki? Shi da waye a gidan?"
"Shi da Uncle Yusuf ne, Abbana kuma yanzu ya shiga bedroom.."
"Shatu don Allah ki rufa min asiri ki saka wa M Madawaki maganin nan Allah ba shi da lafiya sannan ki tabbatar ya sha, yana sha sai ki dawo gida.."
Amsa wa Shatu ta yi tare da tashi tana haɗawa M Madawaki coffeen da ta zo da shi, maganin da Mummy ta bata ta juye duk sannan ta zauna tana juya coffee ɗin.
Fitowar M Madawaki ce ta sakata yin murmushi, zama ya yi a kusa da ita yana karɓar coffee ɗin, a hankali ya fara domin shi yake buƙata, tun safe bai iya cin komai ba.
Yana sha tana yi masa magana, sai da ya kusa shanyewa ya ji ɗanɗon tea ɗin da ya sa da safe ne, da sauri ya zuba da na bakinsa yana duba cikin cup ɗin, maganin ya ga kwance a ƙasan cup ɗin wanda bai ƙasara narkewa ba.
Shatu ya kalla da idanuwasa wanda suke nuna zallar ɓacin rai, cup ɗin hannunsa ya nuna mata tare da cewa..
"Eshaa me a cikin coffee ɗin nan?"
Zaro ido Shatu ta yi tare da cewa.
"Maganinka ne wanda kake haɗawa da coffee...."
Rufe idonunsa ya yi, yana ciza baki cikin ɗaga murya ya ce..
"Eshaa waye ya baki? Waye ya dafa tea ɗin da na sha da safe?"
Cikin tsoron Shatu ta ce.
"Mummy ce ta ce baka da lafiya dole sai ka sha wannan maganin za....."
"Inna Lillahi Wa'inna Ilaihir Raji'un! Eshaa kin san abin da kika shayar da Ni? Inna Lillahi Wa'inna Ilaihir Raji'un!.."
Hawaye Shatu ta fara tana riƙe hannunsa, cire hannunsa ya yi tare da nuna mata hanya.
"Eshaa fita daga gidan yanzu bana so na fito na same ki..."
Yana gama faɗar haka ya shiga bedroom yana faman kira wayar Dr Omar, Shatu kuwa yana shiga bedroom ta fashe da kuka, tana kwanciya a ƙasan carpet sosai take kuka domin ganin zallar ɓacin rai a fuskar Abban nata, wanda bata taɓa ganin ba.
━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━