Chapter 8
by @mamyywriter
╔══════════════════════╗
🌺🌺 *KOWA DA RABONSA* 🌺🌺
╚══════════════════════╝
🌺 A Story Filled With Lessons, Destiny and Love🌺
✍️
> BY MARYAM USMAN MAMYY WRITER (FULANIN JAJIRTATTU)
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
🏆 JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION
✨ FIVE STAR WRITERS✨
📞 ***
📚 BOOK 2
📖 Page 8
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
Bismillahir Rahmanir Rahim.
> Wane lokacin kaddara ce take zaɓa maka rabonka, wani kuma rabon nasa ne kaddara. Duk abin da ya zama rabonka dole ne ka yi haƙuri da shi.
~NOTE: Ban yarda da wani ko wata su yi amfani da littafina ba. Ban yi littafin nan da wata ko wani ba. Duk abin da kuka gani mallakina ne, bana so wani ya yi min copy ba tare da sanina ba.~
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
Sai karfe sha biyu na rana ta farka, da kuka Dr Maryama ce ta taimakata zuwa toilet, zama ta yi a toilet ɗin tana fashewa da sabon kuka, Dr Maryama ce ta sake komawa toilet ɗin cike da tausayawa take kallonta cikin sanyin murya ta ce.
"Sir Mijinki ne ko Babanki?"
Ɗago jajayen idanuwanta ta yi tana kallonta domin bugawar da zuciyarta take, shiru Dr Maryama ta yi tana haɗa mata ruwan wanka, dole sai Dr Maryama ce ta koya mata yadda za ta kula da kanta.
Lokacin da suka fito M Madawaki suka samu a room ɗin,kasa kallon fuskarsa Shatu ta yi,sai sabun hawaye da suke zubu mata, shi ma a ɓangarensa kasa maganar ya yi, sai hanyar fita da ya nufa.
Shopping ɗin da M Madawaki ya ajiye Dr Maryama ta buɗa tare da zaɓawa Shatu kaya, sallar asuba Dr Maryama ta ce ta rama, sannan ita kuma ta fita, a zaune ta same, kitchen ta tambaye shi inda yake ya nuna mata tea ta haɗa wa Shatu, da abinci mai sauƙi.
A zaune ta samu Shatu na hawaye, tea ɗin ta fara bata, a hankali Shatu na fara sha ta amayar da shi, gyara room ɗin Dr Maryama ta yi, sannan ta sake haɗa mata wani, zazzafan zazzaɓin ne ya rufe ta, wanda ya tsorata Dr Maryama fitowa ta yi tana kallon fuskar M Madawaki ta ce.
"Sir kamata ya yi mu je Hospital domin jikin nata sake rikicewar yake...."
Bai yi magana ba, sai room ɗin da ya shiga a kwance ya samu Shatu jikinta na rawa hannunsa ya ɗora saman wuyanta, duk halin da take ciki bai hanata gane hannunsa ba.
Zafin da ya ji ne a jikinta, ya gyara mata kwanciyar ya fito, Dr Maryama ya kalla tare da cewa.
"Akwai Hospital Quarters ɗin nan duk abin za'a buƙata akwai."
Wata ƙaramar waya ya ɗaga yana kiran Yusuf, babu jimawa Yusuf ya shigo Dr Maryama ce ta yi masa bayanin zuwa Hospital ɗin domin jikin Shatu da ya rikici, magana ya yi wa Uban gidan nasa da ido sannan ya yi wa Dr Maryama jagora zuwa Hospital ɗin.
Suna fita ya shiga bedroom ɗin, yana ɗauko Shatu cak rufe idannuta ta yi dalilin tunu irin ɗaukar da ya yi mata jiya, da abubuwan da ta ji yana ƙoƙarin aikata mata, har ya kwantar da ita a room ɗin bata buɗe ido ba, Yusuf kuwa tun shigowarsu ya yi ƙasa da kansa tare da fita waje.
Shi ma fita ya yi, domin bawa Dr Maryama damar dubata sosai. Dr Maryama ce ta kula da ita har dare lokacin ta samu sauƙi sai abin da ba'a rasa ba, M Madawaki ta kira ta yi masa sallama, tana sake jaddadawa Shatu yadda za ta kula da kanta.
Yusuf ne ya maida ita tare da kyakkyawar kyautar da M Madawaki ya ce a yi mata, sosai Dr Maryama ta yi farinciki tana sanar da Yusuf in suna buƙatarta su kirata kowanne lokaci.
Shatu kuwa M Madawaki ne ya maida ita ɓangarensa, tun shigarsu bedroom ɗin babu wanda ya iya cewa komai, kowa zuciyar da abin da take kitsa masa.
Abincin da Yusuf ya kawo masa ne ya shigo mata da shi, zai fita ta riƙe hannunsa tana fashewa da sabon kuka mai ratsa zuciya, dawowa ya yi tare da zama gefenta yana riƙe hannunta da kyau.
Cikin muryarta da ta dashe saboda da kukan da take yi ta ce.
"Na san haka ne ƙaddarata amma ta yi min nauyi kirjina kamar zai fashe, na so na mutu kafin zuwan wannan ranar..."
Kuka ne ya ci karfinta, dole sai kwantar da kanta ta yi a kafaɗarsa tana dukan ƙirjinsa da iya ƙarfinta, shiru ya yi yana saurarenta har ta gaji da kanta ta daina dukan shi, goge hawayen fuskarta ta yi tare da cewa.
"Na rasa kimata na rasa darajar da kowacce mace take da ita, ban san abin da zan sanar da Mijin da zan aura ba, ba zan iya faɗawa kowacce halitta cewa Abbana Mahaifina ya yi raped ɗina ba wannan mummunan ƙaddarar ta yi muni da yawa."
Shiru ta yi tana kallon fuskarsa, da ya zuba mata ido yana kallon bakinta da yake sarrafa kalmomi da suke shiga cikin zuciyarsa, lumshe idanuwansa ya yi, domin jin kalmomin da suke fitowa yanzu a bakinta.
"Na yafe maka, ina rokon Allah ya yafe mana wannan barnar da muka aikata, ka yi min addu'a Allah ya manta da Ni komai...."
Ƙasa ƙarasa maganar ta yi tana rungumoshi, sun jima a haka har ta ji sauƙi zafin da zuciyarta take yi, sannan a hankali ta dafa shi, tana tashi zaune tare da zuro ƙafafuwanta ƙasa ta miƙe tsaye ta fara takawa a hankali ta shige toilet, tana shiga ta shige ruwan zafi sai a lokacin ta ɗan sauke numfashi tana rintse ido tare da hana kanta tuna komai, domin kuwa tsautsayi ne ya gifta tsakaninsu, da kuma mummunan ƙaddarar da take a rubuce a littafin ƙaddararsu.
Ba za ta bar zuciyarta ko gangar jikinta su sake tuna abin da ya faru ba, alƙawarin ta yi wa kanta na za ta manta komai kafin ta fita daga toilet ɗin.
Hawayen da take riƙewa ne suka balle mata ta kasa riƙe kukanta tana ƙanƙame jikinta da har lokacin take jin raɗaɗin abubuwan da Abban nata a aikata mata, ta Jima sosai a toilet ɗin, sanin babu mai rarrashi ne ta bawa kanta haƙura ta karɓi ƙaddarar da ta same su, sannan ta fito ɗaure da towel da idanuwanta da suke a kumbure ga fuskar ta yi jajari da ita.
Miƙewa tsaye ya yi jiki a sanyaye yana yi mata kallo ɗaya ya dauke idanuwansa ya juya yana ficewa, da kallon ta bi bayan shi, tana mai jin tausayinsu na sake shiga zuciyata, ta san duk zafin da take ji Abbanta ya fita ji, magana ce ba zai iya yi ba.
━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━
Madawaki Dynasty.
Mummy tun bayan fitar Shatu take shirin tarbar M Madawaki da Amina ta shadda mata zai dawo a haukace, kallon agogon ta fara yi,ganin sha ɗaya na dare ga sai faman kira wayar Shatu take ba'a ɗagawa.
Hankalinta ne ya tashi ta ɗauko key ɗin motar Shatu sabuwar ta fita, private Quarters ɗin ta nufa da mugun gudu, lokacin da ta zo Yusuf ya fito daga cikin gidan yana tsaye a harrabar Quarters ɗin, cike da damuwa.
Mamakin ganinta ya yi,amma sai bai nuna mata ba, ya nufin gidan da yake kusa da na M Madawaki, dakatar da shi ta yi ta hanyar cewa.
"Yusuf tsaya."
Tsayawa ya yi ba tare da ya juyo ba,
"Yusuf ina M Madawaki? Ina Shatu?"
Kamar ba zai ce komai ba, sai kuma ya juyo yana kallonta.
"Mr Madawaki yanzu suka tafi Hospital shi da Mr Maina, Miss Shatu kuma ta jima da komawa Madawaki Dynasty.."
"Inna Lillahi Wa'inna Ilaihir Raji'un! Hospital kuma? Kai amma dai Allah ya tsinewa Maina, A.Maina ne matsalata sai na yi maganinsa kafin ya rabo da M Madawaki, uban waye ya faɗa masa Hospital za su iya magance matsalolinsa..."
Murmushi takaice ya yi, yana sake tabbatar da abin da yake zargi, dama tun safe da Dr Omar ya ce maganin ƙara ƙarfin sha'awa aka sakawa M Madawaki, ya fara zirgin Hajarah ce kawai za ta iya aikata wannan abun, sai kuma kalaman Shatu da ta ce Mummynta ce ta ba da magani a saka masa.
Ƙofar gidan ya buɗe ya shiga ba tare da ya ce mata komai ba, domin babu wani abin da zai iya faɗa mata, sai yanzu ne ya yi farinciki hukuncin da ya yi na tura Shatu, bedroom ɗin M Madawaki, duk da ya san Uban gidan nasa bai karɓi auren da yake tsakaninsa da 'Yar tasa ba.
Cike da ɓacir rai Mummy ta ja mota, lokacin da ta isa Madawaki Dynasty karfe sha biyu saura, kwanciya ta yi a falonta tana kurma ihu, masu aikinta ne suka fito har Inayaa da take bacci, tambayar abin da yake faruwa Baba Jamila ta yi, tana rufe baki Mummy ta fara zuga mata ashar.
Duk shiru suka yi ganin tana zagin Baba Jamila, komawa bedroom Inayaa ta yi tana kwanciyarta, suma ɗaya bayan ɗaya suka koma ɗakunansu.
Ranar Mummy sai a falo ta kwana, asubar fari ta nufin ɓangaren M Madawaki tana duban Shatu, rasa Shatu da ta yi ne ya sake ɗaga mata hankali, cikin kuka ta fito tana zuwa falon Daada, ta samu mazan gidan a zaune.
Duk kallonta suke ganin irin kukan da take yi, bakin na rawa Daada ta ce.
"Ke! Hajarah wane abun ne ya faru ne..."
"Daada na rasa Shatu, ga shi ma Abban nata tun jiya da safe bai dawo ba.."
Baba Malam ne ya kalle Daada yana cewa.
"Dama ba Shatu ba ce ta dawo karfe sha biyu saura?"
Sallamar A Maina ce ta hana kowa magana, zama ya yi tare da gaida su, yana cewa.
"Daada lafiya na ga damuwa a fuskarki?"
"Abubakar ina Muhammad ina Shatu wai Hajara ce ta fito tana kuka bata ga Shatu ba, kuma wai Muhammad bai dawo ba tun jiya da safe."
"Daada MAMUB ya tafi Abuja, shi da Shatu M Madawaki, ya ce na sanar da ku...."
"A Maina, a ina M Madawaki ya kwana? kuma Shatu ma tun juya ba ta dawo gida ba..."
Cike da masifa Daada ta ce.
"To ke ina ruwanki, ba dai kin ji inda su tafi ba? Sai ki haƙura har sai Shatu M Madawaki ta dawo sai ta baki labarin abin da kike son ji."
Shiru Mummy ta yi, tana komawa ɓangarenta Amina ta kira tana kuka sosai, tare da faɗa mata abin yake faru.
A ɓangaren A Maina kuwa har school ɗinsu Shatu ya kira tare da sanar da su, ta yi tafiya, su Rima tun ranar suke kiran numberta amma bata shiga, Daada ma da ta kira sau uku bata shiga, sai ta koma kiran number M Madawaki ita ɗin ma bata shiga.
_____________________________________
Tsawon kwana biyar wayoyinsu ba sa shiga, A Maina ma ya shiga damuwa, daga ƙarshe ne ya gwada kiran Yusuf, cikin sa'a ya same shi, abu na farko da ya fara faɗa shi ne.
"Yusuf ina MAMUB wai me yake yi a Abuja? Na kira wayoyinsa duk babu mai shiga, na yi magana da office ɗinmu da ke Abuja sun ce bai zo ba lafiya kuwa?"
Shiru Yusuf ya yi tare da kallon fuskar M Madawaki da yake zaune yana breakfast, nuna masa fuskar wayarsa ya yi da number A Maina ta bayyana, shiru M Madawaki ya yi yana karɓar wayar.
"Uhm."
Ajiyar zuciya A Maina ya sauke tare da cewa.
"Wai lafiya Ni fa na fara zirgin baka da lafiya ne shi ne ka gudu domin baka so na sani.."
"I'm okay."
Murmushi A Maina ya yi zai yi magana M Madawaki ya kashe wayar tare da bawa Yusuf wayarsa, karɓa Yusuf ya yi tare da yin ƙasa da kansa.
Miƙewa M Madawaki ya yi yana kallon fuskar Yusuf sanin da akwai magana a bakinsa.
"Sir Dr Maryama ta bada shawarar Miss Shatu ta koma gidan cikin mutane ko za ta rage damu..."
"Okay sai ta sake jin sauƙi sosai."
Yana gama faɗar haka ya shiga bedroom ɗin da Shatu take rayuwa a ciki, tsawon kwanaki biyar bata taɓa fitowa ba, komai a bedroom ɗin take yi, sai da ya shiga ya fita, sai Dr Maryama da take zuwa kullum sai dare ta tafi.
A kwance ya same ta ta yi tagume, tana jin motsinsa ta tashi zaune tana gyara rigar jikinta, zama ya yi a gefen bed ɗin yana kallon breakfast ɗin da ya kawo mata tun ɗazu, ganin babu abin ta ci ne ya saka shi matsowa kusa da ita ya fara bata.
Tana yatsine fuska ta cin abincin ya san bata so amma dole ne ya bata abinci, tun ranar da ƙaddara ta same su, Shatu bata sake cin abinci cikin kwanciyar hankali ba, kullum sai ya bata ko Dr Maryama wani lokaci ya zauna wani lokaci ta amayar da shi.
Kawai da kai ta yi alamar ta ƙoshi, kwashe kayan abincin ya yi yana fita da su, har ya dawo tana zaune, shi ma zama ya yi gefenta tare da kamo hannayenta, hawaye ta fara tana ƙasa da kai, tun ranar har yau ta kasa daina hawaye, ko magana mai tsayi bata sake yi ba, sai dai kallo.
Goge mata hawayen ya yi ta riƙe hannunsa cikin dasheshiyar muryata ta ce.
"Abbana ina so na koma gida bana ƙaunar zaman Quarters ɗin nan don Allah ka maida ni na ji sauƙi babu abin da yake damuna zamana a Quarters ɗin nan shi ne yake ƙara min ciwon zuciya, musamman bedroom ɗin nan a dole nake zama a cikinsa..."
"Okay sai ki koma wacan Ni na dawo nan, ba za ki koma gida ba, har sai na daina ganin wannan hawayen."
Ƙasa magana ta yi sanin ba zai sauya shawara ba, bedroom ɗin ya sauya mata, tare da bata wayarta ko za ta rage mata damuwa, shi ma wayoyinsa ya kuna, A Maina ya fara kira suka yi magana.
Sannan ya kira su Daada yana haɗa su da Shatu, daga gaisawa babu abin da Shatu ta iya cewa sai wayar ya kashe, yana fita daga bedroom ɗin, ta kunna wayarta, Nimrah ce ta fara kira, kiran ne ta samu ta ɗan sake suka yi magana, har ta ji sanyi a zuciyarta.
Da yamma kuwa sai gata ta fito falo, da mamaki suke kallonta shi da Yusuf da yake zaune suna magana, har ta zauna M Madawaki bai ɗauke idanuwansa a kanta ba, Yusuf ne ya sauke kansa cikin ƙaramin sauti da girmamawa ya ce.
"Barka da fito ya sauƙin jikin?"
Bata amsa ba, sai ma tashi da ta yi ta nufi hanyar kitchen, suna zaune ta fito da ƙaramin cup a hannunta, tana zama a dinning room, a hankali take shan abin da yake cup ɗin, ƙarar wayarta ne ya saka M Madawaki ɗago da idanunwansa yana kallonta.
Murmushi ya ga ta yi tana ɗaga wayar, bai gama tabbatar da waye ya kirata ba sai da ya ji tana cewa.
"Meerah bana son munafurci in ruwanki.."
Dariya ta yi tana yin shiru da dukkan alamu maganar Meerah take sauraron, miƙewa ta yi tana cewa.
"Allah a cikin satin nan zan dawo, kuma a shirya komai da Ni, ɗazu ma Nimrah ta kira Ni.."
Zaman da ta yi a kujerun falon ne ya saka shi ɗauke idanuwansa, farinciki da ya ga a saman fuskarta ne ya sanyaya zuciyarsa, ya fara sauke ajiyar zuciya a jere.
Tana kashe wayar ta kallo shi cikin sanyin murya ta ce.
"Abbana ina so fita waje na zauna."
Hanya ya nuna mata da hannunsa, a hankali ta tashi ta ɗaukar gorar ruwan da yake gaban shi, da kallo duk suka bita har ta fita, ajiyar zuciya ya sauke tare da lumshe idanuwansa sai yanzu hankalinsa ya fara dawowa jikinsa, Yusuf ma ya yi farinciki sosai ganin ta fara warwarewa, ya san ita ce ta zaunar da Uban gidan nasa a Quarters ɗin tsawon wannan kwanaki har yake ƙaryar baya gari.
Ko da Dr Maryama ta zo a waje ta sameta ita ma sosai ta yi farinciki tana rungumeta, tare suka zauna har M Madawaki ya fito sallar Magriba, kallon ɗaya ya yi wa fuskarta da take murmushi a lokacin da ya fito.
Ganin su fito ne Dr Maryama ta ce su gashi suma su yi sallah, tare suka yi sallah, Dr Maryama na bata labarin Uban gidanta AA Shazalee da matarsa Nabihah, da irin rigimar da ta yi lokacin da take da ciki na bata son Ɗa namiji sai mace. (FARINCIKI RAYUWA) Kenan.