Chapter 10
by @mamyywriter
╔══════════════════════╗
🌺🌺 *KOWA DA RABONSA* 🌺🌺
╚══════════════════════╝
🌺 A Story Filled With Lessons, Destiny and Love🌺
✍️
> BY MARYAM USMAN MAMYY WRITER (FULANIN JAJIRTATTU)
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
🏆 JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION
✨ FIVE STAR WRITERS✨
📞 ***
📚 BOOK 2
📖 Page 10
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
Bismillahir Rahmanir Rahim.
> Wane lokacin kaddara ce take zaɓa maka rabonka, wani kuma rabon nasa ne kaddara. Duk abin da ya zama rabonka dole ne ka yi haƙuri da shi.
~NOTE: Ban yarda da wani ko wata su yi amfani da littafina ba. Ban yi littafin nan da wata ko wani ba. Duk abin da kuka gani mallakina ne, bana so wani ya yi min copy ba tare da sanina ba.~
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
Domin shi a tunaninsa duk akan Hajara ne Shatu take gudun Abban nata, kallonsa kawai ta yi tare da buɗe baki tana kuka sosai, tausayinta ne ya kama shi, har ya yanke shawarar saka M Madawaki ya dawo da Hajarah, a falonsa ya barta yana fitowa umarnin ya bawa M Madawaki ya dawo da Hajarah.
Ita ma Daada wannan shawarar ta yanke, shi dai shiru ya yi bai ce komai.
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
Kwana biyu tsakanin su na cikin yin breakfast Shatu ta fito, duk kallonta suka yi sai yanzu kowa ya ga irin ramar da ta yi, M Madawaki kuwa kasa daina kallonta ya yi har ta buɗe baki a hankali ta ce.
"Abbana Good morning.."
Ƙasa amsawa ya yi, dalilin wani sanyin da ya ji har ya matan yaushe rabonsa da ya ji muryarta, su Daada ta gaida sannan ta zauna tana yamutsa fuska.
Cikin farinciki Daada ta ce.
"Me kike so na zuba miki?"
M.Madawaki ta kalla tana cewa.
"Na ƙoshi."
A hankali ya ɗago yana kallon fuskarta, ita ɗinma kallonsa take da idawnuwanta da suka yi laushi dalilin kukan da ya zama abokin rayuwarta.
Shigowar A Maina ce ta hana M Madawaki yi mata magana, da mamaki A Maina yake kallon Shatu da take zaune a dinning room ɗin, gaida shi ta yi cikin sanyin murya, amsawa ya yi tare da nunawa M Madawaki lokaci.
A hankali ya miƙe zai fita Shatu ta riƙe hannunsa duk tsayawa suka yi suna kallonsu, a hankali ta furta.
"Ina so magana da Dr Maryama yau.."
Idanuwansa ya zuba mata na ɗan lokaci sannan ya juya dama yana so a duba masa ita, ganin yadda ta koma lokacin guda, ga rama ga fari da ta ƙara sosai.
Ranar dai a farkon ta zauna, har yamma sai da Rima da Meerah za su fita ne ita ma ta ce za ta bisu, babu wanda ya hanata domin so suke ta warware ta dawo rayuwarta.
Tare suka fita, yawonsu har bayan sallar isha'i sannan suka dowa, lokacin M Madawaki yana zaune, bata jima da zama ba Dr Maryama ta shigo, da sauri Shatu ta rungumeta.
Gaida mutanan da suke falon ta yi, sannan Shatu ta ja hannuta suka shiga ciki, suna shiga Daada ta ce.
"Muhammad daga ina aka samu wannan?"
Tashi ya yi tare da cewa.
"Dr ce duba Eshaa za ta yi."
A ɓangaren Shatu kuwa, farinciki ganin Dr Maryama ya saka ta manta da duk wata damuwarta, ta saki jiki suna hira, kallonta da Dr Maryama take yi ne, yasa ta turo baki ta ce.
"DR Maryama ko na ƙara miki kyau ne?"
Cikin sanyin jiki Dr Maryama ta riƙe hannunta tana cewa.
"Shatu M Madawaki, me yake damumki duk kin rame?"
Shiru ta yi na ɗan lokaci sannan ta ce.
"Ni ma ban sanin ba, ko abinci bana iya ci tun lokacin nan na kasa manta wa da abin da ya faru da Ni.."
"Inna Lillahi Wa'inna Ilaihir Raji'una" Dr Maryama ta furta a hankali, tana kamo hannayen Shatu cikin ruwar murya ta ce.
"Shatu kin ga al'adarki tun bayan abin da ya faru"
"A'a Dr Maryama ban sake yi ba, dama a lokacin kwanana uku da gamawa.."
Shiru Dr Maryama ta yi tana maganar zuci.
'Na shiga uku ya tabbata kenan yarinyar nan ciki ta samu, Subbahanallhi! Ban san yadda Mahaifinta zai ji ba, ita ma ya yi za ta ji lamarin.."
Shatu ce ta katse mata maganar zucin tana cewa.
"Dr Maryama zazzaɓi nake yi sosai ga amai ko ban ci abinci ba kullum sai na yi da sassafe, ki ba ni magani."
Hawaye ne ya zubowa Dr Maryama har zuciyarta take tausayin Shatu, tashi ta yi tare da cewa za ta kawo mata maganin gobe, har baƙin ƙofar falon Daada Shatu ta rakata, za ta koma bedroom ɗin ne Daada ta kwantar da murya tana cewa.
"Allah yasa ba Abban naki za ki ƙwasuwa wata masifar ba, domin na ga soyayyar wannan matar a idanunwaki."
Murmushi kawai Shatu ta yi tana shiga bedroom ɗin Meerah, a can ta kwana washegari ranar ta tashi da zazzaɓin sosai, wanda sallar asuba ma, sai a zaune ta yi, cike da tausayawa Meerah ta take kula da ita, sai bayan zazzaɓin ya lafa ne, ta fara amai da ya zame mata jiki.
Meerah ce ta rakata toilet ta gyara jikinta domin hajijiyar da take yi, sun zo bakin ƙofa ta zame ta faɗa a ƙasan toilet ɗin, da sauri Meerah ta kamota za ta ɗagota sai jini taga yana bin jikinta.
Da gudu ta fito falon Daada tana ihun Shatu ta faɗa jini yana zubowa a jikinta, M Madawaki ne ya fara shiga bedroom ɗin sai A Maina, ganin jinin da take zubarwa ne ya saka A Maina cewa su tafi hospital.
Cak M Madawaki ya saɓuta a kafaɗarsa ya fito, kuka Daada ta fara ana rasa mai bata haƙuri domin kowa hankalinsa yana kan Shatu, Yusuf suka samu tsaye da waya a hannunsa ya kasa motsi, duk maganar da A Maina yake masa, domin message ɗin da Dr Maryama ta yi masa na Shatu ciki ne da ita ya sanar da M Madawaki kafin ya girma a zubar da shi, shi ya saka shi suman tsaye.
M Madawaki ne ya sakata mota A Maina ya ja ganin Yusuf bai kula da su ba,kafin sun je A Maina ya kira Dr Nadraa yana sanar da ita zuwansu, Baba Malam yau da kansa ya ja mota shi da Daada da take kuka, duk Hospital ɗin suka tafi babu wanda ya zauna ko Inayaa da ta shigo ta ga suna fita,gidansu ta koma tana sanar da su, ita ma ta bi bayansu.
Lokacin da suka isa duk jikinsa ya ɓace da jini da kansa ya kwantar da ita a room ɗin da Dr Nadraa ta nuna masa, wajen ya fito A Maina yana riƙe shi, dole sai zaunar da shi Aminu H Madawaki da Sayyid Madawaki suka yi, Daada ma zaunar da ita aka yi.
Su Meerah ma kuka suke sosai, zuwan su Rahmah ne Daada ta rungume Innayi suna kuka.Nadiya ma cikinsu Rima ta shiga suna kuka sosai.
A hankali Baba Malam ya yi musu magana a kan kukan da su yi, dole suka yi shiru suna tsayuwar tsammani, Yusuf ne ya shigo da sauri tare da faɗawa jikin M Madawaki yana hawaye, cikin sanyin murya ya furta.
"Sir,Miss Shatu is pregnant for you Sir, I'm so happy, ashe kana da rabon haihuwa a duniya."
Duk kallon Yusuf suka yi, domin babu wanda ya fahimci abin da yake nufi, a hankali M Madawaki ya cire shi daga jikinsa ya buɗe bakinsa.
"Me kake faɗa...."
Shiru ya yi yana kallon fuskar Dr Nadraa da ta fito jiki a sanyaye, duk kanta suka yi suna haɗa baki wajen tambayarta.
Hawaye ta fara domin ta san abin da za ta faɗa musu ba mai daɗi ba ne, Baba Malam ne ya ce.
"Dr Nadraa ki faɗa mana duk abin da yake faruwa, mun san ƙaddara za mu karɓi duk abin da Allah ya ƙaddaro mana."
Ɗaga mata kai Daada ta yi, tana goge fuskarta matsowa M Madawaki ya yi yana kallon fuskarta, cikin sanyin murya ta ce.
"Shatu is pregnant."
Zabura duk suka yi suna kallon fuskar Dr Nadraa, M Madawaki kuwa baya ya yi zai faɗa Abubakar Madawaki ya riƙe shi, Yusuf ne ya sake cewa.
"Alhamdulilah! Dama Dr Maryama ta yi min message I'm so happy...."
A Maina ne ya kalli fuskar Dr Nadraa yana nunata da yatsa..
"Ciki! Ciki kuma? Daga ina ya fito kin dubata da kyau kuwa?"
Cike da masifa Daada ta ce.
"Kaga Abubakar ɗauko mana ita mu sake asibiti dama daga ganin wannan Yarinyar ta samu ciwo a ƙwaƙwalwarta.."
Tashi M Madawaki ya yi tare da rungumo A Maina da yake tsaye bakinsa na rawa ya ce.
"MAMUB, Eshaa ce take da ciki? Na sha uku Hajarah ta cuce Ni, MAMUB ta yi min dafi a zuciya...."
Rufe masa baki A Maina ya yi, ganin yana neman fita daga haiyacinsa, cire hannun A Maina ya yi daga bakinsa yana hawaye cikin ɗaga sauti ya ce..
"MAMUB ka san cikin jikin Eshaa na waye? Inna Lillahi Wa'inna Ilaihir Raji'un MAMUB nawa ne, Ni Ni fa MAMUB na cutar da Esha...."
Riƙe shi Abubakar Madawaki da A Maina suke Baba Malam ya fara yi masa addu'a, cikin kuka Daada ta ce.
"Ba zan taɓa yafewa mai hannun a wannan lamarin ba, Allah ya isa tsakaninmu da wanda ya yi wa Shatu cik......"
Yusuf ne ya yi saurin cewa.
"Don Allah Daada kada ki ƙarasa wannan cikin fa na Mr Madawaki ne..."
Ja da baya Daada ta yi tana nuna Yusuf da hannu, Baba Malam ne ya gyara murya tare da cewa.
"Muhammad abin da Yusuf yake faɗa gaskiya ne?"
A Maina ne gyara tsayuwar domin tun fara maganganu M Madawaki ya fahimci komai, ba komai ne ya saka shi shiru ba, sai maganar cikin kenan dai M Madawaki yana haihuwa, hawaye farinciki ne suka zubo masa da saurin ya rungume Baba Malam yana cewa.
"Alhamdulilah Baba Malam MAMUB yana haihuwa, dama na faɗa na san yana haihuwa lokaci ne kawai bai yi ba..."
Maganar A Maina ce ta shiga jikinsu tun da ake maganar babu wacce suka fahima irin wacce A Maina ya yi yanzu, zaman yan bori Rahmah da Daada suka yi, Dr Nadraa kuwa suman tsaye ta yi.
Su Nadiya kuwa kukan da suke yi suka nema suka rasa, sai zaro ido suke tare da kallon bakin duk wanda yake magana, gyarawa M Madawaki zaman Abubakar Madawaki ya yi tare da kallon fuskar Dr Nadraa ya ce.
"Dr Nadraa ya jikin Shatu akwai abin da ake buƙata?"
Sai lokacin kowa ya san abin da ya kamata su fara tambaya kenan, cikin sanyin murya ta ce.
"Ina mai bada haƙuri Shatu ta yi Miscarriage....
Katse ta A Maina ya yi tare da cewa.
"Kamar ya ta yi Miscarriage kina nufin cikin ne ya zuɓe?"
"Eh ya zuɓ..."
Tashi Daada ta yi tana cewa.
"Karya ne bai zuɓe ba, cikin da ko sanni ba mu yi ba ki ce ya zuɓe..."
Shiru Dr Nadraa ta yi domin bata da abin da za ta iya faɗa, jikinta ya jima da mutuwa tun maganganu M Madawaki, kanta ma duk ya kulle ta rasa mai take ji.
Baba Malam ne da ya kasa magana yana kallonsu ya motsa bakinsa yana cewa.
"Ke Nadraa kin tabbatar ciki ne na gaskiya ko?"
"Eh Baba Malam ciki ne kuma ya zuɓe amma ƙarami ne bai fi wata biyu ba..."
"To Alhamdulilah ko yanzu na koma ga Allah na ji daɗi da Allah ya nuna min wannan ranar nan, Daada kamata ya yi fa mu yi wa Allah godiya magana fa ake ta Muhammad yana haihuwa, mu ga tabbace da idanunwanmu."
Maganar Baba Malam ne ya saka Daada hawayen farinciki, ita da Innayi suka rungume juna, A Maina ma rungume M Madawaki ya yi, haka Abubakar Madawaki da Sayyid Madawaki.
Sai bayan sun gama murnar su ne, sannan aka bari suka shiga room ɗin da Shatu take kwance, kasa magana duk suka yi ganin tana bacci sai ruwa da ake ƙara mata, Zulaihah ce ta fara fita daga room ɗin domin zuciyarta fashewa za ta yi saboda baƙin ciki.
Inayaa ma kuka take yi sosai, Baba Malam ne da ya fito daga room ɗin ya ce duk su koma gida, babu yadda suka iya haka duk Baba Malam ya kora su gida, iya A Maina da M Madawaki suka bari a Hospital ɗin.
Sai Yusuf da A Maina yake tambayarsa abin da ya faru, labari Yusuf ya bashi na yadda abubuwa suka fara har cikin ya samu, murmushi kawai A Maina.
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
Sai sha biyu na rana Shatu ta farka, kallon fuskar Abbanta ta yi wanda yake zaune a gefen bed ɗin, hannayensa ta kamo cikin sanyin murya ta ce..
"Abbana."
"Na'am Eshaa ya kike ji, ko na kira DR Maryama ta duba ki?"
Girgiza kai ta yi tana kallon fuskar A Maina da ya shigo shi ma zama ya yi gefenta yana riƙe hannunta.
"Shatu M Madawaki ya jikin? Akwai abin da kike so?"
Hawaye ta fara tare da cewa.
"Ka yi haƙuri Abbansu Nadiya ba zan sake bacci a ɗakin jarabawa ba, ba Ni da lafiya ban san abin da yake damuna ba, kullum sai na yi amai da sassafe amma Dr Maryama ta ce za ta kawo min magani don Allah ka faɗawa Abbana a maida Ni gida bana son Dr Nadraa ta duba Ni.."