KOWA DA RABONSA

Chapter 15

by @mamyywriter

╔══════════════════════╗
  🌺🌺 *KOWA DA RABONSA* 🌺🌺
╚══════════════════════╝

 🌺 A Story Filled With Lessons, Destiny and Love🌺

 ✍️
> BY MARYAM USMAN MAMYY WRITER (FULANIN JAJIRTATTU)

━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━

🏆 JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION

✨ FIVE STAR WRITERS✨

📞 ***

📚 BOOK 2

📖 Page 15
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ


Bismillahir Rahmanir Rahim.

> Wane lokacin kaddara ce take zaɓa maka rabonka, wani kuma rabon nasa ne kaddara. Duk abin da ya zama rabonka dole ne ka yi haƙuri da shi.

~NOTE: Ban yarda da wani ko wata su yi amfani da littafina ba. Ban yi littafin nan da wata ko wani ba. Duk abin da kuka gani mallakina ne, bana so wani ya yi min copy ba tare da sanina ba.~

━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━


Dr Maryama ya yi wa message ta zo ta duba masa Shatu, lokacin da ta zo Shatu bata ɓangarensa shi da kansa ya rakata falon Daada, a kwance ya sameta a cinyar Rahmah sai Daada da take faman faɗa.

Tana ganin Dr Maryama ta ce.
"Yawwa yarinyar kirki yanzu nake cewa Shatu ta kira miki ke, ki duba min ita domin ina zargin ciki ne da ita.."

Zaro ido su Nadiya suka yi, suna kallon juna, murmushi Dr Maryama ta yi tare da cewa.
"Yanzu Sir ya kira ni, Shatu tashi mu shiga ciki ko?"

Ɗago da kanta Rahamah ta yi, Daada ta yi saurin cewa.

"Inna Lillahi Wa'inna Ilaihir Raji'un Rahmah gano yarinyar nan ta koma wannan baccin."

Murmushi Rahmah ta yi tare da cewa.
 "Ai Daada yanzu ma zazzaɓin ne a jikinta, wannan bacci kuwa cikin ne yake sakata."

A Maina ne ya shigo wanda M Madawaki ya yi wa message ya zo saka Rahmah ta sauke Shatu daga cinyarta, kallon fuskar Shatu ya yi wacce ta ɗashe ta yi haske sosai, Dr Maryama ya kalla tare da cewa.
 "Ki dubata ciki ne ko?"

Murmushi Dr Maryama ta yi, domin tambayoyin nasu dariya suke bata, kowa so yake a ce ciki ne a jikin Shatu, a hankali ta girgiza kai ta ce.
 "Me zai hana muje Hospital domin tabbatar da komai."

Ɗaga mata kai duk suka yi Rahama da Daada suka kama shi Shatu zuwa mota, Yusuf ne ya ja motar zuwa Madawaki Hospital, mamaki sosai Dr Nadraa ta yi ganin sun zo da Dr Maryama.

Ita ce ta nunawa Dr Maryama inda kayayyakin aikin suke, tana komawa gefe, Dr Maryama ce ta duba Shatu cikakken ciki ɗan wata biyu ne ya bayyana a jikinta, cikin farinciki ta sanar da su.

Farinciki sosai duk suka shiga, A Maina kasa boye farincikisa ya yi har da hawaye, haka Daada da Baba Malam, M Madawaki kuwa iya murmushi saman fuskarsa za ka kalla ka san yana cikin farinciki marar misaltawa.

Meerah ce ta kamo hannun Nadiya da Rima gefen suka koma tana dariya ta ce.
"Ciki fa kai amma Shatu M Madawaki munafuka ce yanzu duk zaman da muke ba ta, taɓa nuna mata akwai wata alaƙa mai ƙarfi ta aurataiya tsakinta da Abbanta ba.."

Dariya Nadiya ta yi tana cewa.
 "Ai kin san Shatu akan lamarin Abbanta ba za ta taɓa faɗawa kowa ba."

Rawa Rima ta fara tare da cewa.. 
 "Ko babu komai nakusa zama uwa.."

A hankali Dr Maryama ta fito da Shatu, da sauri duk suka taso, cire hannunta ta yi daga na Dr Maryama ta nufi motocisu, dole sai bayanta suka bi, ƙasa Yusuf ya yi da kansa wanda ya gama murnar ƙaruwa da Uban gidan nasa zai samu, buɗe mata ƙofar motar ya yi.

Ta juya za ta shiga ta ji an yi sama da ita, saura kaɗan ta suma, a hankali ya shige da ita cikin motar tare da jan motar da kansa, shiru ta yi tana kallon gefen fuskarsa, har suka shiga Madawaki Dynasty bai yi magana ba ita ma bata ce komai ba.

A tare motocinsu suka shigo da sauri Daada ta zo gaban motar ta tsaya, M Madawaki na buɗewa Shatu ƙofa, ta kamo hannunta, zaunar da ita ta yi duk suna yi mata sannu, tambayarta abin da take so suka fara yi ta yi shiru tana kallon Dr Maryama da take bata magani.

Babu musu ta karɓa Rahmah ta bata ruwa ta shanye ko ajiyar cup ɗin ba ta yi ba, ta amayar da shi, sannu duk suka yi mata Baba Malam ya ce.
 "Ko akwai inda yake miki ciwo?"

Kallonsa ta yi da idanuwanta da suka yi laushi tare da miƙewa Rima hannunta, da sauri Rima ta kamata, suka shiga bedroom ɗinta wanka ta yi ta sauya kaya, a hankali ta fito ganin duk ita suke kallo ne ya saka ta yi ƙasa da kanta.

Har dare Dr Maryama tana gidan sai ƙarfe goma sannan Yusuf ya maida ita, har lokacin Shatu bata ci abinci ba, sha ɗaya na yi ta tashi, kallonta Anne da Daada suka yi ganin za ta fita.
Hajiya Safiya ce ta yi saurin cewa.
"Shatu lafiya?"

Girgiza kai ta yi tana ɗaukar wayarta.
 "Bacci nake ji, sai da safe..."

Baki sake suke kallonta har ta shige ɓangaren Abbanta, a falo ta same shi zaune yana aiki, sallamarta ce ta sa ya ɗago, hannunsa ya miƙe mata alamar ta zo babu musu ta ƙarasa, rungumeta ya yi tare da zaunar da ita a cinyarsa, hannunsa ya ɗora saman mararta yana shafawa..

Riƙe hannunsa ta yi tana shagwabe fuska, murmushi ya yi tare da maida hannunsa lumshe ido ta yi tare da ƙanƙameshi, hannayensa ya saka yana zagayeta a kunnenta ya furta.
"You are pregnant, I am so happy and I hope you will be happy too."

Zabura ta yi tana kallon fuskarsa idanunta na cika da hawaye bakinta na rawa ta ce.
 "Ni ciki Abba?"

Ɗaga mata kai ya yi tare da maida ita jikinsa cikin sanyin murya ya furta.
"May Allah show me the day I have been longing to see, I thank Allah and I hope you will join me in thanking Allah?."

Shiru ta yi na ɗan lokaci sannan ta ɗaga masa kai, murmushi ya yi tare da ɗago kanta.
"Will you talk to me with your mouth, or don't you want to have a sister?"

Dukan ƙirjinsa ta yi tana rufe fuskarta hannunta ya riƙe yana murmushi, cikin sanyin murya ta ce.
 "Na taya ka murna, Ni kuma gaskiya bana son na samu Yar uwar da zaka raba mana soyayyarka.."

Cikin sabon yanayi mai daɗin gaske ya ɗora bakinsa cikin nata, sun jima suna tsotsar juna, daga ƙarshe ma bedroom suka koma sai wajen sha biyu sannan suka sararawa juna bayan sun yi wanka ne ta ce za ta ci abinci, tare da ita suka shiga kitchen, tea ta ce za ta sha.

Da kansa ya dafa mata, a kitchen ɗin suka zauna tana cinyarsa yana bata ta sha rabi, rabi ta zuba masa a bakinsa, daga ƙarshe kasa jurewa M Madawaki ya yi ya cafko harshenta yana tsotsa kamar zai cire.

A haka suka koma master room ɗinsa, a can suka sake komawa ruwa, har biyu na dare sannan suka kwanta bacci da asuba kasa tashi ta yi, sai bayan ya dawo daga masallaci ne ya taimaka mata ta yi sallar asuba tana idarwa ya kwantar da kansa a cinyarta tare da saka hannunsa a cikin hijabin jikinta.

Cikin shagwaɓeɓiyar murya ta furta.
"A'a Abbana na gaji sosai...."

Dariya ya yi tare da shafu saman mararta sannan ya yi kissing ɗin bakin da ya yi maganar ya furta.
"Sorry mu yi bacci ko?"
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
A saman bed ɗin ma sai da ya ɗan yamutsata sannan suka yi bacci, har sha biyu, tare suka fito fuskarsu ɗauke da murmushi shi ɗaya ya yi breakfast ɗin ita kwanciya ta yi a jikinsa, sai bayan ya kammala sannan ya kama hannunta suka fita.

A ɓangaren Daada kuwa tun asuba ta tare Mallamai suka yi mata addu'a, ta yi sadaka, abinci ta saka Hajiya Maryam ta yi wa Shatu, ta zauna jiran fitowarta.

Tun suna ganin agogon har ta haƙura ganin sha biyu da rabi, Nimrah ma da take son ganin Shatun tun jiya da suka zo har ta gaji da yin tsaki, Zulaihah ce da Inayaa suka shigo sai Rahmah da Nadiya.

A haka falon ya ciki da ahalin gidan da yaransu, sautin takalminta suka ji, Banisha da Nimrah suka miƙe tsaye, da sauri gani M Madawaki a gefenta yasa suka zauna, Shatu kuwa gudu za ta yi, ya yi saurin riƙe ta yana murmushi da ido ya nuna mata cikinta.

Dariya ta yi tana rufe fuska, har tsakiyar falon ya rakota sannan ya juya ya fita duk gaida shi da suke yi babu wanda ya amsawa,yana fita Nimrah ta rungume Shatu Banisha ta faɗa kansu.

Faɗa Hajiya Safiya ta fara tare da korarsu daga jikinta, gaida su Shatu ta yi tare da tashi tana cewa.
 "Baby's ku tashi mu shiga ciki kafin Daada ta fara halin nata......"

Zaunar da ita Hajiya Safiya ta yi tare da cewa.
 "Sai kin yi breakfast ai Yaya Muhammad ya ce baki ci komai ba.."

Ɓata fuska ta yi tare da cewa.
 "Ni bana jin yunwa."
Duk yadda suka so ta ci abinci kasa ci ta yi dole sai haƙura suka yi.

━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
Bayan kwana goma da sanin tana ciki kullum sai ta zauna tana shafa cikin wai ko za ta ji motsin ku san kullum sai Dr Maryama ta zo, har lokacin kuma su Anne na gidan babu wanda ya tafi.

Tsakinta da Abbanta kuwa sai abin da ya sake gaba domin soyayya suke yi kamar babu gobe, ta haƙura ta karɓe shi a matsayin Miji, har lokacin A Maina bai daina shigo falon M Madawaki ba, amma duk zuwan da zai basa haɗuwa, domin ta san lokacin shigowarsa.

Yau da wuri M Madawaki ya tashi, falon Daada ya shiga domin yin breakfast ɗin cikin Yan Uwansa, gani Shatu bata fito babu wanda ya yi masa magana suna cikin yin breakfast ɗin suka ga ta fito,tana tsayawa a baƙin ƙofa tare da dafe bango, cikin ɗaga sauti ta furta.
"Inna Lillahi Wa'inna Ilaihir Raji'un! Abbana cikina wayyo Allah....."

Da sauri duk suka yi kanta tana ƙoƙarin zuɓewa a ƙasa M Madawaki ya zauna ta faɗi kansa rungumota ya yi yana ƙoƙarin ɗagata ya ji damshin a hannunsa a hankali ya ɗago hannun....

Ihun Daada ne ya saka duk suka kalli hannunsa.

"Inna Lillahi Wa'inna Ilaihir Raji'un! Muhammad kamar jini nake ganin Allah yasa ba wani abu ba ne ya samu cik....."

Bata iya ƙarasawa ba, domin ganin M Madawaki ya fita da Shatu wacce jini yake bin jikinta, cikin ƙanƙanin lokacin suka isa Madawaki Hospital, kafin su isa cikin ya gama fita ko da dr Nadraa ta dubata sanar da su ta yi cikin ya fita.

Daada ce ta nuna bata yadda, dole sai Yusuf ya kira mata Dr Maryama ta fi dr Nadraa iya aiki, ko da Dr Maryama ɗin ta zo abin da sanar da su kenan, tana mai tausayinsu domin a bayyana yake irin tsananin ƙaunar da suke wa ciki.

A Maina kasa boye damuwarsa ya yi tare da cewa.
 "Dr Maryama ko Shatu M Madawaki ta yi ƙarama ne da ɗaukar ciki? Kin ga wannan shi ne na biyu duk suna zuɓewa?"

"A'a Sir ana samun yara wanda ba su kaita shekaru ba, suna haihuwa, dole akwai abin yake kawo fitar cikin......."

Sayyid Madawaki ne ya gyara murya yana cewa.
 "Yanzu dai ki duba mana ita domin mu san abin da yake zubar da cikin sau biyu fa ai mun yi asara babba....."

Baba Malam da Baba Haruna ne suka haɗa baki wajen cewa.
 "Subbahanallhi! Abubakar! Sayyid! Wace irin magana ce wannan, Allah ne fa ya bata kuma ya karɓa don Allah ku zama masu karɓar ƙaddara mana, da fa ba mu samu wata a cikin Matansa ta yi Miscarriage ɗin ba, Allah yana sane da duk abin da yake faruwa, shi rabonsa a nesa yake ku yi haƙuri da abin Allah ya tsara.."

Maganar su Baba Malam ce ta saka jikinsu ya yi sanyi babu wanda ya sake tasa maganar sai bayan wani lokaci Shatu ta farka kafin wani ya sanar da ita, ita ce ta fara tambayar Dr Maryama ta ce.
"Aunty Maryama Miscarriage na sake yi ko?"

Hawayen da Daada take riƙewa ne ya ƙwace mata, ta fara kuka kamar ƙaramar yarinya, zama M Madawaki ya yi a gefen bed ɗin yana kama hannunta zai magana Shatu ta yi saurin cewa.
"Ai na san na yi ƙarama a haihuwa don Allah Aunty Maryam ki bani magani na na daina samun ciki kin ga zuɓewa yake, in na sake girma sai na haihu...."

Girgiza kai Baba Malam ya yi tare da cewa.
 "Allah za ki yi wa wayo kenan? Babu wani magani da za'a baki, haka za mu yi haƙuri har Allah ya kawo mai taka ƙasa.."
━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
Shiru ya mamaye room ɗin, a hankali Shatu ta ɗago jajayen idanunta tana kallon Baba Malam, sai kuma ta mayar da dubanta ga Dr Maryama.
"Aunty Maryam, ni dai ina so ki taimaka min bana son na sake shiga wannan halin ina shan wahala."

Cikin tausayawa Dr Maryama ta matso kusa da ita, ta riƙe hannunta.
"Shatu, ki saurare ni da kyau, abu na farko da nake so ki sani shi ne, ba ke kika jawo wannan abin da yake faru ba, kuma zubar da ciki sau biyu ba yana nufin cewa ba za ki iya haihuwa ba."