KOWA DA RABONSA

Chapter 18

by @mamyywriter

╔══════════════════════╗
  🌺🌺 *KOWA DA RABONSA* 🌺🌺
╚══════════════════════╝

 🌺 A Story Filled With Lessons, Destiny and Love🌺

 ✍️
> BY MARYAM USMAN MAMYY WRITER (FULANIN JAJIRTATTU)

━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━

🏆 JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION

✨ FIVE STAR WRITERS✨

📞 ***

📚 BOOK 2

📖 Page 18
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ


Bismillahir Rahmanir Rahim.

> Wane lokacin kaddara ce take zaɓa maka rabonka, wani kuma rabon nasa ne kaddara. Duk abin da ya zama rabonka dole ne ka yi haƙuri da shi.

~NOTE: Ban yarda da wani ko wata su yi amfani da littafina ba. Ban yi littafin nan da wata ko wani ba. Duk abin da kuka gani mallakina ne, bana so wani ya yi min copy ba tare da sanina ba.~

━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━



Har cikin zuciyarsa ya ji maganarta, a hankali ya tashi, tare da ɗauko towel ɗinsa wanda ya yi cili da ya ɗaura, ruwan ya ɗauƙo mai ɗan sanyi ya bata,  sosai ta sha ruwan, sannan ta ce ya isa.

Sannu ya yi mata sai yanzu yake jin tausayinta kamata ya yi suka shiga toilet, shi ne ya yi musu wankan. Sannan suka kwanta baccin gajiya.

━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
Da asuba ma sai da ta sake shiga ruwan zafi sannan ta yi sallah bayan ta idar, ta zauna a gefen gado tana addu'a a hankali, Allah ya sa Abbanta ya bar ta ta ɗan huta, domin har yanzu tana jin gajiyar daren jiya.

Tana cikin tunani ne ta ji an buɗe ƙofar bedroom ɗin
M Madawaki ne ya shigo, sanye da farar jallabiya, hannunsa riƙe da wayarsa.

Kyakkyawan idanunwasa ya zuba wa Shatu yana murmushi har ya ƙaraso inda take, hannayenta ya kamo yana furta.
"Eshaa."

Ɗaga masa kai ta yi, tana lumshe ido alamun bacci bai isheta ba ta ce.
"Good morning Abbana."

Dogon hancinta ya ja tare da yi murmushi mai sauti, hijabin jikinta ya cire mata, suka kwanta babu jimawa bacci ya yi gaba da su.
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
Sai ƙarfe sha biyu sannan suka fito cikin shiga ta alfarma, tana riƙe da hannayensa, da almar magana suke yi, a harabar hotel ɗin suka haɗu da A Maina, shi da Yusuf zare jikinta ta yi tana kallon gefe ta ce
"Good morning Abbansu Nadiya and uncle Yusuf.."

A lokacin guda M Madawaki da A Maina suka kalleta, ganin tana turo baki ne ya sa M Madawaki janyota jikinsa yana kallon fuskar A Maina.
"MAMUB kun gama shirin tafiyar ta ku..?"

Murmushi Yusuf ya yi tare da komawa gefe, domin dariya ce take son kama shi, lamarin Uban gidan nasa sai addu'a yanzu duk ya sauya a duk lokacin da yake buƙata kasance a gida shi da Shatu baya duba abubuwan da suke gabansu.

Kame fuskar A Maina ya yi tare da kallon gefen Shatu, cikin nutsuwa ya ce.
 "Shatu M Madawaki shiga mota za mu yi magana.."

Cire hannunta ta yi tana nufar motar da Yusuf yake tsaye a jikinta, Shatu na tafiya A Maina ya fara dariya tare da dafa kafaɗar M Madawaki.

"MAMUB wai me yake damunka ne? Ka san tafiyar zuwa Spain dole ce, amma na fahimci ka saboda  Matarka kake ajiye mana aiki a gefe ko? To na shirya mata komawa Najeriya ita da Yusuf karfe takwas na dare......"

"Wait wait MAMUB Eshaa tana tare da Ni, ina so zan huta sai su biyo bayanka Spain ɗin, daga can sai mu wuce Saudiyya za mu haɗu da Shekyh Mohaj...."

Dariya A Maina yake sosai, yana tafa hannu haɗe fuska M Madawaki ya yi, zai tafi A Maina ya riƙo hannunsa tare da cewa.
"Okay MAMUB ina so ka yi haƙuri mu tafi Spain yau kasan mun gama magana da su sai wannan matsalar ta shigo, Ni ban da matsala za ka yi tafiya da Matarka, amma ba za ta takura min ba...."

Murmushi M Madawaki ya yi, tare da nufar mota key ɗin motar ya karɓa a hannun Yusuf suka fita shi da Shatu, domin su yi breakfast.

━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
London - Breakfast at Sushi Kanesaka, 45 Park Lane.

Restaurant ɗin yana boye ne a cikin Dorchester Collection Hotel. Kujeru 13 ne kacal, Lights ɗin ɗakin sun yi dim, itace mai tsada, kuma kowanne mutum ana yi masa hidima shi kadai.

Chef ɗin Japan, ne tsaye a gabansu yana murmushi,cikin harshen turanci ya furta.
"Welcome to Sushi Kanesaka. This is an intimate Omakase experience," 


Gyaran Shatu ta yi wacce take gefen M Madawaki, sanye da abaya mai sheƙi idonta na kallon yadda aka jera faranti na crystal. Abinci course by course ake shiryawa.
 First course _Hokkaido scallop with caviar and gold leaf, Main - A5 Wagyu beef with black truffle, seared for 12 seconds, Sushi -Bluefin tuna Otoro aged for 21 days.

Kowanne faranti £420 per person ne, amma M Madawaki bai damu da farashin ba, Shatu kawai yake yadda take murmushi mai ɗaukar hankali, cikin sanyin murya ya furta.

"Eshaa, how do you feel now?" 

Ɗagowa ta da kanta, tana murmushi mai cike da godiya.

" Abbana,Alhamdulillah!"

 "Eshaa, I want us to travel to Spain to meet someone, I know it won't be long, from there we will proceed to Saudi Arabia."

A hankali ta ɗaga masa kai, shi ne ya bata abincin har ta ƙoshi sannan ya ci.

 Wayo ya yi da ita tana ganin gari sai karfe bakwai na dare suka dawo hotel ɗin, A Maina da Yusuf suka samu suna jiransu a lobby, shirye da jakunkuna don tafiyarsu zuwa Spain da karfe takwas na dare.
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
SPAIN - Madrid - Mandarin Oriental Ritz.

Bayan jirginsu ya sauka a Barajas Airport da karfe 3 na yamma, wata Rolls-Royce Cullinan baki ce ta dauke su, zuwa Mandarin Oriental Ritz, Madrid.

Manager ɗin hotel ɗin da kansa ya tarbe su cikin farinciki, da sanin juna.
"Welcome, Mr. and Mrs. Madawaki. Your Grand Suite with private terrace is ready."

Murmushi kawai M Madawaki ya yi tare da kama hannun Shatu suka nufi hanyar da za ta sada su da masaukinsu, wani Falo ne mai fadin gaske da chandelier na crystal, bedroom da gado mai girman gaske da aka shimfida shi da fararen furanni da rubutun "Welcome To Your Honeymoon Retreat" da rose petals.

Terrace mai zaman kanta da ke kallon Prado Museum, akwai jacuzzi mai dumi da table don dinner na dare.

Shatu ce tsaye a bakin terrace, iskar Madrid mai sanyi na taɓa fuskarta a hankali ta juya tana kalli M Madawaki.

"Abbana, this place is... wow. Kamar mafarki."

A hankali M Madawaki ya karaso yana kamo fuskarta ya furta.

"After everything we went through in London, Eshaa, you deserve this peace, wannan ne ƙaramin kafin mu koma gida, Just you and me."

A ɓangaren A Maina kuwa da Yusuf, a kasa suka  sauka a Four Seasons Hotel, suka bar su su kadai a Ritz don su huta, don su fahimta M Madawaki ba aiki ya tawo ba soyayya ya tawo.

Da yamma aka kawo musu dinner
Candlelight dinner, lobster da Wagyu, da juice mai sanyi, da violinist da ke buga musu waka daga nesa.

A ranar babu inda M Madawaki ya fito ko sallar a ciki suka yi tare, sanyin wajen ya taimaka musu sosai wajen nuna wa juna zallar ƙauna domin Shatu mantawa ta yi da matsayin M Madawaki a wajenta kamar yadda shi ma ya manta da wacce yake tare.

Sai bayan sallar isha'i suka sararawa juna.
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
Misali karfe sha biyu na dare.

Violinist ɗin ya gama buga waka ya tafi, ya bar su da sautin iska da hasken kyandir guda 20 da aka kunna a terrace din.

Shatu ce zaune a kan kujera mai laushi, kafafunta a hade, tana kallon garin Madrid da ke haskakawa a kasa, M Madawaki na tsaye a bayanta, hannunsa a kafadarta.

"Abbana, sai yanzu na ji sanyin a zuciyata aka abin da yake faruwa da Ni."

A hankali ya ja kujera ya zauna gabanta, ya kama hannayenta biyu.

"Eshaa, look at me."

A hankali ta ɗaga idonta masu cike da hawaye masu sheki tana kallon fuskarsa.

"The doctor said there is hope. Ta ce 'Many women with this condition go on to have successful pregnancies.' Kin ji ta, ko? Wannan ba karshen bane, farko ne. And I will be with you, every step."

Hawayen farinciki ne suka gangaro mata, tana yi murmushi ta furta.

"Abbana."
Ɗaga mata gira ya yi yana murmushi.

Rufe fuskarta ta yi tana cewa.
"Duk kyawun hotel ɗin da abin da yake cikinsa bai fi ganinka a idana daraja ba, kabar aikinka ka zauna da Ni domin na yi farinciki, na gode sosai.

Hannayenta da ta rufe fuskar da su ya kamo yana murmushi tare da cewa.

"Because you are my everything, Eshaa, you know that."

Iska mai daɗi ce ta kada labulen terrace ɗin cikin sanyin jiki M Madawaki ya mike, tare da kamo hannayenta suka kwanta bacci.
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
Washegari - Madrid - Karfe 9:00 na safe.

Hasken rana ne ya shigo ta tagar terrace ɗin. Shatu ce ta farka tana ga kanta a lullube da blanket, M Madawaki na zaune a gefenta, waya a kunne, yana magana kamar baya so.

"Yes, tell the Spanish partners we will be at the Four Seasons for the meeting by 10:30. And make sure the documents for the Saudi deal are ready."

 Kashe wayar ya yi tare da juyo yana kallon fuskar Shatu, da take sheƙi, murmushi ya yi tare da furta.

"Good morning, my Eshaa. Did you sleep well?"

Tana murmushi ta furta.

"I slept like a baby, Abbana. Ina jina kamar sabuwar"

Tare suka yi wanka, suka sa kaya masu kyau, M Madawaki cikin suit mai tsada, Shatu cikin abaya mai ruwan hoda, sun yi kyau sosai.

Suna sauƙo ƙasa wata motar Rolls-Royce tana jiransu, suka shiga zuwa, Four Seasons Hotel Madrid - Meeting Room.

A Maina da Yusuf da wani mutum Bature dan kasuwar Spain, mai suna Mr. Carlos, suka tarar zaune a wani private meeting room da aka yi masa ado da gold da marble.

Tun shigowar M Madawaki da Shatu,A Maina da Yusuf suka kalle juna, domin sun yi tunanin a hotel ɗin zai barta, Mr. Carlos ne ya kalli Shatu, tare da cewa.

"Your wife is beautiful, Mr. Madawaki. You have a good eye for beauty, not only in business."

Dariya A Maina ya yi sosai yana kallon fuskar M Madawaki wanda ya haɗe rai, Yusuf ma sai da ya yi dariya domin lamarin Uban gidan nasa akwai gyara.

Shiru suka yi da dariya, suka fara Meeting ɗin a kan wani babban project na gidaje tsakanin Madrid da Riyadh. M Madawaki yana magana cikin nutsuwa Shatu na gefensa hanunsa cikin nata.

Sai bayan awa biyu, suka kammala, Mr. Carlos ya miƙa wa Shatu hannunsa, wacce take jikin M Madawaki.

"It's a deal, Mr. Madawaki. $45 million deal. Congratulations. And please, enjoy Madrid. You are staying at the Ritz, the best. Perfect for your honeymoon."

Kalmar honeymoon ce ta saka Shatu yin kasa da kai tana jin kunya, M Madawaki ne ya matse hannunta da yake cikin nasa yana mata magana da ido.

Bayan sati biyu, a cikin sati biyun irin soyayyar da suka sha ba'a magana, domin A Maina ma bai fiya ganinsa ba, daga shi sai Yusuf suke gudanar da harkokin kasuwancinsu, shi kuwa ogan yana ɗaki shi da Matarsa.

Yau ne aka yi sa'a ya fito, har ya zauna suka tattauna abubuwa masu mahimmanci, a hankali A Maina, ya kira shi da sunan da yasa babu maganar wasa ya ce.

"MAMUB, jirginmu zuwa Jeddah gobe da karfe 2 na rana. Sheikh Mohaj yana jiranmu a Makka."

Miƙa wa ya yi yana kallon wayar hannusa ya ce.
"Okay."

Murmushi Yusuf ya yi domin ya san ba da son rainsa zai tafi ba.

A daren, ya sanarwa da Shatu cikin farinciki ta dago hannayenta tana addu'a.

"Ya Allah, ka sanya wannan tafiya ta Saudiyya ta zama mafita, halin da muke ciki Ni da Abbana, ka biya mana dukkanin buƙatunmu."

Da Amin M Madawaki ya amsa yana rungumota.