KOWA DA RABONSA

Chapter 20

by @mamyywriter

╔══════════════════════╗
  🌺🌺 *KOWA DA RABONSA* 🌺🌺
╚══════════════════════╝

 🌺 A Story Filled With Lessons, Destiny and Love🌺

 ✍️
> BY MARYAM USMAN MAMYY WRITER (FULANIN JAJIRTATTU)

━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━

🏆 JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION

✨ FIVE STAR WRITERS✨

📞 ***

📚 BOOK 2

📖 Page 20
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ


Bismillahir Rahmanir Rahim.

> Wane lokacin kaddara ce take zaɓa maka rabonka, wani kuma rabon nasa ne kaddara. Duk abin da ya zama rabonka dole ne ka yi haƙuri da shi.

~NOTE: Ban yarda da wani ko wata su yi amfani da littafina ba. Ban yi littafin nan da wata ko wani ba. Duk abin da kuka gani mallakina ne, bana so wani ya yi min copy ba tare da sanina ba.~

━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━

Da saurin Baba Jamila ta matsa tana basu hanya, master bedroom ɗinsa ya shiga, tare da kwantar da Shatu, toilet ya shiga babu jimawa ya fito, ya taimakawa Shatu ta cire kayanta suka shiga toilet ɗin, shi ne ya yi mata wanka ta yi alwala shi ma ya yi suka fito.

Tana fitowa ta kwanta duk yadda ya so ta ci wani abu kasa ci ta yi, saboda baccin da yake idanuwanta, masallaci ya fita a can ya haɗu da Baba Malam da Baba Haruna, tare suka shigo falon suka samu Anne na faɗa.

Cikin sanyin murya ya gaida Anne, washe baki ta yi tare da cewa.
 "Muhammad sannu da dawowa wai ina Shatu ne, an ce ka ɗauketa....."

Katse ta ya yi ta hanyar cewa
"Bacci take yi."

Abubakar Madawaki ne da Aminu Madawaki da suke shigo suka haɗa baki wajen cewa.
"Ya kamata ta tashi babu kyau bacci irin wannan lokacin.."

Kafin ya yi magana Innayi ta shigo da kuka A Maina a bayanta, Anne ta rungume tana sake fashewa da kuka, Baba Malam ne ya gyara murya tare da cewa.
"Hajiya Nadiya wane irin kuka ne haka me yake faruwa.."

Da gudu Inayaa da Zulaihah suka shigo, Nadiya da Rahamah a bayansu, duk kallonsu suke yi, jiki na ruwa Daada ta ce.
"Abubakar ka yi magana mana......."

Rahmah ce ta rungumeta Daada tana cewa.
 "Daada ina Shatu M Madawaki Daada alhamdulilah! Ashe Shatu ciki ne da ita Allah yasa an yi aikin a sa'a........."

Zabura Daada da Anne suke yi, tare da cewa.
 "Ciki ciki dai Rahamah?"

Shiru Rahmah ta yi ganin kamar babu wanda ya san da maganar, a hankali A Maina ya zauna gefen Baba Malam yana kamo hannayensa ya ce.
 "Baba Malam alhamdulilah, Allah ya azurta MAMUB da samun ƙaruwa matarsa ciki ne da ita, kuma cikin nufin Ubangiji an yi mata aiki a mahaifarta, domin hana cikin fita, yanzu haka cikin yana lafiya.."

Duk kallon bayan M Madawaki suka yi da tun bayan fara maganar A Maina ya nufin ɓangarensa, murmushi Baba Malam da Baba Haruna suka, suna kasa magana saboda da farinciki, Abubakar Madawaki ne ya yi saurin cewa.
"Abubakar yanzu cikin yana lafiya, kuma za ta iya haihuwa da kanta?"

Murmushi A Maina ya yi tare da cewa.
 "Yaya Abubakar in sha Allahu za ta iya, addu'a kawai za mu yi mata...."

Daada ce ta miƙe tsaye tana ɗaga hannayenta.
"Allahu Akbar! Allahu Akbar! Ya Allah, na gode maka! Na gode maka!"

Su Nimrah ma ihu suka fara ganin M Madawaki ya fita, babu wanda ya yi musu magana akan ihun domin kowa yana cikin farinciki sosai.

Baba Malam ne ya tambayi A Maina abin da yake damun Shatu, bayanin ya yi musu na duk abin da ya faru har komawar da za su yi UK in cikin ya kusa haihuwa.

Kukan baƙinciki ne ya kama Inayaa, da gudu ta shige bedroom ɗinta, babu wanda ya kula da lamarinta domin sabon aiki da Daada ta saka kowa, na sake wa Shatu, abinci irin na masu juna biyu.

Har karfe takwas, babu wanda ya ga motsin M Madawaki, bare Shatu kuma har lokacin suna zaune zaman jiransu, sai takwas da rabi suka ji motsin buɗe ƙofar ɓangaren M Madawaki, duk ido suka baza har Baba Malam domin ganin waye zai fito.

Shatu ce ta fito ita da M Madawaki hannunsu cikin na juna, fuskarta ɗauke da murmushi, duk da ta rame sosai amma hakan bai hana kyawunta bayyana ba, magana suke ƙasa ƙasa, a hankali ta ɗago kanta tana murmushi tare da rufe fuska, murmushi M Madawaki ya yi yana sakin hannunta.

A hankali ta ƙaraso tana rungumar Daada, tare da kamo hannayen Rahamah, cikin shagwaɓeɓiyar muryarta ta ce.
"Daada irin wannan kallo sai ki saka mu faɗi, mun sauya muku ne?"

Cire jikinta ta yi tana kallon fuskar Baba Malam, tashi za ta yi, M Madawaki ya yi saurin riƙe hannunta yana kallon cikin idonta, turo baki ta yi tare da cewa.
"Sai na kira DR Emily na jin dalilin da yasa ta saka Abbana yake wahalar da kansa..."

Murmushi ya yi wanda ya bayyana a saman fuskarsa, yana zama daf da ita, tare da kwantar da kanta a kafaɗarsa, cikin sanyin murya ya furta.
"Daada a kawo abincin Eshaa bata ci abinci yau."

Abincin Hajiya Safiya da Hajiya Maryam suka kawo tare da shafa kan Shatu, a hankali ta gaida su, sannan ta kalli Baba Malam da Baba Haruna suka gaisa, ta so ya saketa ta rungume Rahmah amma yaƙi dole tana jikinsa suka gaisa da kowa.

A Maina ne ya shigo, ganin M Madawaki da Shatu a jikinsa kuma ga abincin a gabansu, ya yi murmushi tare da zama kusa da su shi ne ya zaba abincin kaɗan wanda ya san za ta iya ci, ya miƙewa M Madawaki.

Cikin nutsuwa M Madawaki ya bata abincin tana yatsine fuska tana ci har ta ci mai yawa, sannan A Maina ya ba shi maganinta wanda yake yawo da shi a aljihu, ko za'a samu matsala na wajan M Madawaki ya ƙare, to a ɓangaren Yusuf ma duk wani maganin da aka rubutawa Shatu yana da shi a wajensa gudun matsala.

Tana sha ta kallonshi cikin sanyin murya ta ce.
 "Abba su Nimrah nake so mu yi magana na yi missing ɗinsu.."

Kafin ya yi magana A Maina ya ce.
 "Yanzu lokacin kwanciyarki ya yi, da safe sai ku yi magana, MAMUB ya kamata ta kwanta yanzu."

Gyaran mata zama ya yi yana kallon wayarsa ya ce.
 "Jiya ma da ta kwanta sai da ta yi amai, a bari sai goma zuwa sha ɗaya sannan abinci ya bi jikinta."

Baki na rawa Anne ta ce.
 "Muhammad bata da lafiya kennn...."

Maganar ta tsaya ne sakamakon wanke M Madawaki da A Maina da Shatu ta yi da amai mai ƙarfi, sosai ta yi aman sannan ta kwanta a jikinsa tana lumshe idanuwanta da suka yi laushi.

Sannu A Maina ya yi mata sannan ya fita zuwa gidansa domin ya gyara jikinsa, cikin sanyin jiki Rahmah ta yi mata sannu ita da Zulaihah suka bi bayan A Maina, babu wanda ya kula da yaushe ya tashi sai ƙarar rufe ƙofa suka ji.

Ganin babu Shatu a falon ne ya basu mamaki sosai, domin ba su ga lokacin da ya tashi ba, bare Shatu da take jikinsa.

Suna shiga toilet ya nufa wanka ya yi musu, sannan ya bata ruwan tea mai ɗan cita, tana sha ta yi bacci sai a lokacin hankalinsa ya kwanta ya koma falon Daada, zaune ya same su har lokacin, abinci ya ci, suka fara magana da Baba Malam.

━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
Washegari.
Tun bakwai na safe ma'aikatan gidan suke aikin shirya abinci, har karfe sha ɗaya, a lokacin duk family suna dinning room ɗin, har M Madawaki da Shatu, da take murnar ganin su Rima.

Cikin nutsuwa suke breakfast ɗin, kowa abin da yake so yake ci, ban da Shatu da M Madawaki ya takura mata sai ta ci wani abu, idonuwanta cike da hawaye take yin breakfast ɗin, Daada ce ta kalleta cikin sanyin murya ta ce.
"Shatu M Madawaki, na ga kamar bakya so, ki faɗi abin da kike so sai a yi miki yanzu."

Kalle Shatu duk suka yi har M Madawaki domin jin ko akwai abin da take so ɗin, turo baki Shatu ta yi tare da cewa..
 "Daada Ni na ƙoshi babu abin da nake so."

Lumshe idanuwansa ya yi domin ya san abin da za ta faɗa kenan, kullum sai ya tambaye akwai abin da take so amma amsar ɗaya ce babu.

Tashi ta yi daga dinning room ɗin, tana shiga bedroom ɗin Meerah, Shatu na tashi duk Yan matan gidan suka fara fita ɗaya bayan ɗaya, ihun su kawai suka ji, a bedroom ɗin Meerah, fita M Madawaki ya yi zuwa office.

Hajiya Safiya ce ta shiga bedroom ɗin domin ganin abin da suke yi, gudun kada su yi musu asara, ganin Shatu a kwance ne hankalinta ya kwanta ta fito, tana fita Rima ta ce.
"Shatu wallahi mun yi kewarki, kika barmu da kewa! Abbanki ya boye ki a London ko?"

Dariya duk suka yi, Shatu ta ja bargo ta rufe fuskarta tana murmushi.
"London,Spain, Saudiyya duk nan mu ka je, na yi farinciki sosai kuma na yi kallo....."

Katse ta Nimrah ta yi tare da cewa.
 "Kuma an yi soyayya ba....."

Buge mata baki Shatu ta yi tana haɗe fuska, murmushi suka yi tare da kallon juna, sannan suka fashewa da dariya, Meerah ce ta shafa cikin Shatu a hankali, tare da cewa.

"Yana ciwo?"

 Girgiza kai Shatu ta yi tare da cewa
"Babu ciwo, sai dai amai kullum da safe idan na tashi, ga kasala sannan na ji duniyar tana juya min."

Cike da tausayawa suke kallonta, ranar tare suke yini, sai dare ta koma ɓangarensu, tun da suka fahimci irin wahalar da take sha duk suka koma hidimta mata, cikin na cika wata huɗu ta ji sauƙi ta daina yawan aman da take yi a lokacin ne bikinsu Rima ya tashi.

━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
 BAYAN WATA ƊAYA.
Tun bayan samun sauƙin Shatu, gidan ya dawo cikin annashuwa, cikin nata kuwa ya cika wata huɗu,har yanzu M Madawaki bai daina kula da ita kamar yadda likitoci suka umurce shi ba.

A wannan lokacin kuma, ana cikin shirye-shiryen bikinsu Rima da Omar Aminu Madawaki.
Gidan cike yake da hayaniya, ma'aikata suna kai-komo, yayin da matan gidan suka raba ayyukan da za su yi.

A ɗakin Rima kuwa, zaune suke a gaban madubi, Nimrah tana gyara mata gashinta, Meerah kuma tana zaune a gefenta tana duba wasu kayan da za'a yi amfani da su.

Shatu ce ta shigo ɗakin sanye da doguwar rigar atamfa mai kyau, ta riƙe cikinta da ya fito.
"Assalamu alaikum, amaryar gidan!"

Da sauri Rima ta juyo tana murmushi.
"Wa alaikumus salam, amaryarmu ta musamman."

Dariya Shatu ta yi tana zama a gefenta.
"Ni da na zo, in ga ko akwai abin da zan taimaka muku, amma na ga kamar an gama komai."

Dariya Nimrah ta yi.
"Ke dai ki yi zamanki, kada Abbanki ya same mu yana cewa mun wahalar da mai jego."

"Ni fa ba na son yadda kuke raina ni wai mai jego, babu daɗin ji."

Dariya suka yi, domin sun san Shatu bata so su kitara da mai jego.Suna cikin dariyar ne wayar Shatu ta fara ringing, sunan Abbanta da ta gani nema a fuskar wayar ya sa ta yi saurin ɗagawa.
"Hello, Abbana."

"Where are you?"

Murmushi ta yi tare da furta.
"In Rima's room."

"Have you taken your medication?"

Sai da ta lumshe idanuwanta sannan ta ce.
"Abbana, na sha fa."

"Are you sure?"

"Yes, Abbana."

"Alright. Don't stay too long. It's time for your lunch."

Tana murmushi ta ce,
"To, sai na zo."

Shi ne ya fara kashe wayar, sannan suka cigaba da maganganunsu, tsokanarta suke tana murmushi, har M Madawaki ya sake kiranta sannan ta fita.

━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━
M Madawaki da A Maina ne zaune a office, suna duba wasu takardu, da Yusuf ya kawo. 

 Wayar M Madawaki ce ta yi ƙara ganin Dr Emily ce ta kira shi, ya ɗaga yana cewa.
"Hello, Doctor."

"Good afternoon, Mr Madawaki. How is Shatu doing?"

Yana kallon fuskar A Maina ya ce.
"She's doing much better now. The vomiting has reduced, and she's eating better."

Dr Emily ce ta ce.
"That's good. Please make sure she continues her prescribed medication and attends her scheduled antenatal appointments. Also, avoid unnecessary physical stress."

"Sure, Doctor. Thank you."

Ya kashe wayar yana mai gyara zaman agogonsa A Maina ne ya sake kalle shi.
"What did she say?"

Murmushi ya yi tare da cewa.
"Nothing."
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
Washegari.Da safe aka daura auren su:

- Nimrah da Shamsudeen
- Meerah da Muhammad A Maina
- Rima da Omar Aminu Madawaki
- Banisha da Walid Makama 
- Nadiya da Yusuf

Baba Malam da Baba Haruna ne suka jagoranci daurin auren a babban masallacin gidan, M Madawaki ne ya karɓawa Yusuf aure, kuma shi ne ya yi masa komai, domin Yusuf ba shi da kowa Iyayensa sun jima da rasuwa.

Sadakin Nadiya dubu ɗari biyar, M Madawaki ne ya bada da hannunsa, Shamsudeen ma sadakinsa dubu ɗari biyar A Maina ne ya biya masa.

Sayyid Madawaki ne ya bigawa Muhammad A Maina, Abubakar Madawaki ya biyawa Omar Aminu Madawaki, murmushi Baba Malam ya yi yana kallonsu, cikin farinciki aka kammala komai, sai dai mu ce Allah ya bada zaman lafiya.

Shatu ce zaune kusa da Rahmah, tana juya takalmin wanda M Madawaki ya ce shi zata saka, Low heel ne shi yasa take turo baki, a haka ta saka tana fitowa falon, duk kallonta suke yi, domin cikin jikinta ya yi mata kyau ya fito sosai kamar me cikin wata biyar zuwa shida, ta yi kyau sosai yanzu babu rama ta yi kyau.

A daren aka kai raka kowacce amarya dakinta, wanɗanda suka sha kuka, saboda Banisha Abuja za'a kai ta, sai Nadiya da M Madawaki ya bawa Yusuf ɓangare ɗaya a private Quarters ɗinsu, sosai suka yi kuka har Shatu, sai da M Madawaki ya shigo ya fita da ita, zuwa private Quarters ɗinsu.
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
Tun shigarsu ta yi shiru dalilin bugawa da zuciyarta take yi, abubuwan da suka faru ne a gidan ya dawo mata, duk yadda M Madawaki ya so ta shiga cikin bedroom ɗin ƙin yadda ta yi, tana kwanciya a falo har ya yi wanka ya fito.

Zama ya yi yana ɗaro kanta a cinyarsa, hannunsa ya saka tare da shafo saman mararta, cikin sanyin murya ya furta.
"Eshaa."

Fashewa ta yi da kuka tana rugumeshi, cikin kuka ta ce.
 "Don Allah Abbana mu koma gida, Ni bana son nan zuciyata bugawa take yi."

Murmushi ya yi, domin ya fahimta tun shigowarsu ya kula ta rasa nutsuwarta, a hankali ya ɗauke tare da shiga bedroom ɗin da take tsoron, ihu ta fara yi masa tana dukan ƙirjinsa, murmushi kawai yake tare da kallon fuskarta.

Sai da ta gaji ta kwanta a jikinsa tare sauke ajiyar zuciya, a hankali har bacci ya ɗauketa, gyara mata kwanciyar ya yi, tare da rufe ƙofar gidan.

Kamar yadda ango Yusuf ya gwangwaje amarci haka M Madawaki ma, domin shi har ya fi sabon angwayen morewa, sosai Shatu ta sha kuka domin rabon da ta shiga hannun Abban nata tun suna Saudiyya, dalilin hutun da Dr Emily ta ce ya kamta Shatu ta samu.

Shagwabe masa ta yi, shi kuma ya fara aikin rarrashi, ranar babu inda ya fito suna tare, dare na yi M Madawaki ya sake komawa ruwa, yanzu kuma da gaske Shatu take kuka domin ta ji, jiki sosai a hannunsa.

━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━