Chapter 22
by @mamyywriter
╔══════════════════════╗
🌺🌺 *KOWA DA RABONSA* 🌺🌺
╚══════════════════════╝
🌺 A Story Filled With Lessons, Destiny and Love🌺
✍️
> BY MARYAM USMAN MAMYY WRITER (FULANIN JAJIRTATTU)
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
🏆 JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION
✨ FIVE STAR WRITERS✨
📞 ***
📚 BOOK 2
📖 Page 22
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
Bismillahir Rahmanir Rahim.
> Wane lokacin kaddara ce take zaɓa maka rabonka, wani kuma rabon nasa ne kaddara. Duk abin da ya zama rabonka dole ne ka yi haƙuri da shi.
~NOTE: Ban yarda da wani ko wata su yi amfani da littafina ba. Ban yi littafin nan da wata ko wani ba. Duk abin da kuka gani mallakina ne, bana so wani ya yi min copy ba tare da sanina ba.~
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
Bai yi magana ba, sai miƙewa da ya yi tare da kamo hannayenta suka nufi ɓangarensa, baki sake Anne take kallinsu, sannan ta juyo kan Daada ta ce.
"Daada wai Muhammad bai san mace sai ta yi arba'in take komawa wajen Miji ba?"
Shiru Daada ta yi domin bata da bakin magana tun suna London take fama da M Madawaki, a kan Shatu ganin babu cigaba ne yasa ta zuba musu ido.
Ganin Daada ba ta ce komai yasa Anne yin shiru, ganin ƙarfe sha ɗaya da rabi ne Daada ta ce,Hajiya Safiya ta kai wa Shatu RIZQ KARIM domin shi ne yake kukan dare.
Lokacin da ta shiga ɓangaren nasa ta same shi a falo, yana aiki, RIZQ KARIM ya karɓe har za ta fita ya ɗago yana kallon fuskarta.
"Safiya"
Juyowa ta yi tana da cewa.
"Na'am Yaya Muhammad."
"Umh ki kawo MOHAAJIR AMEEN ya sha kada ya kwanta da yauwa."
Murmushi ta yi tana fita, babu jimawa ta shigo da MOHAAJIR AMEEN da yake bacci, a hankali M Madawaki ya fito daga master room ɗinsa, ya karɓi MOHAAJIR AMEEN, zama ta yi a falon har ya fito da shi.
Cike da farinciki ta karɓe shi tare da cewa.
"Yaya Muhammad, ina so ka bani NI'IMATUL RAHMAN mu kwana tun da ita bata kuka.."
Ɗaga mata kai ya yi alamar ya amince, MOHAAJIR AMEEN ta kaiwa Daada domin tun haihuwarsu a wajen Daada yake kwana, sannan ta koma a zaune ta same shi da NI'IMATUL RAHMAN, miƙe mata ita ya yi sannan ya fara tattara kayansa.
Bai rufe ƙofar ɓangarensa ba, domin ko wani a cikin yaran zai tashi, a hankali ya shiga bedroom ɗin yana kallon Shatu da take bacci cikin nutsuwa, kwanciya ya yi tare da rungumesu ita da RIZQ KARIM.
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━━
Washegari ranar suka yi taron suna,wanda ya tara manyan masu kuɗi da manyan ƙasa, da manyan yan jaridu, a ranar hotunan M Madawaki da yaransa babu inda bai zagaya ba.
Mummy tana school ta ji ana labarin taron sunan da ake jiya a Madawaki Dynasty, da sauri ta juyawa tana tambayar abin da yake faruwa, wata daga cikin Malaman ce ta bata labari tare da nuna mata hotun M Madawaki da yara, domin M Madawaki bai yadda an ɗora hotun Shatu ba.
Jikinta ne ya fara rawa, idanuwanta na zubar da hawayen baƙinciki, da gudu ta fita daga school ɗin da kallo Malamn suka bita wasu suna taɓe baki.
A daren da ake yi bikin sunan Inayaa ta samu Shatu tana bata haƙuri akan abin da yake faruwa tsakaninsu tare da sanar da ita ta haƙura da M Madawaki, dan ya yi mata nisa ta san A Maina ba zai aura mata shi ba.
Wannan kalaman ne suka Shatu kallon Inayaa da idanun rahama, sannan ta bata shawara, ita ma ta kawo Miji a yi mata aure, cikin kuka Inayaa take sanar da ita Rahim Matawalle take so, shi ma yana sonta amma A Maina ya shiga tsakaninsu.
Kwantar mata da hankali Shatu ta yi, tare da cewa zata yi wa Abbanta magana ya samu Abbansu Nadiya su yi magana, cikin farinciki Inayaa ta rungume Shatu.
A ranar Shatu ta yi wa M Madawaki maganar Inayaa, da farko bai magana sai ta takura masa sannan ya ɗago kansa, yana kiran number A Maina maganar ya yi masa, tare da kiran Muhammad A Maina ya ce ya turo masa Rahim Matawalle.
A satin M Madawaki ya gaba bincike akan Rahim Matawalle tare da saka ranar auran sati mai zuwa, A Maina dai bai ce komai ba, kallo kawai yake yi.
Zulaihah ce ta zo har gida ta yi wa Shatu godiya akan maganar da ta yi M Madawaki har aka saka ranar auren Inayaa, sannan ta sami Rahmah tana bata haƙuri abubuwan da ta yi mata.
━━━━━━━━━━━★━━━━━━━━━━
Bayan sati ɗaya, cikin satin aka yi bikin Inayaa, Shatu da yaranta suna samun kulawa sosai, sun yi kyau sosai NI'IMATUL RAHMAN ce ma take fama da zazzaɓi, M Madawaki bai sani ba sai da ya dawo.
Zazzaɓin da ya ji sosai a jikinta, ya ɗauƙota suka tafi Hospital, Safa da Maira ne suka ɗauki su RIZQ KARIM da MOHAAJIR AMEEN wanda M Madawaki ya ce duk a zo da su domin a duba masa lafiyarsu.
DR Maryama ce ta duba NI'IMATUL RAHMAN domin yanzu ta dawo aiki a Madawaki Hospital, maganin zazzaɓin ta bawa NI'IMATUL RAHMAN, tare da duba lafiyarsu RIZQ KARIM kamar yadda M Madawaki ya buƙata.
Bayan Dr Maryama ta gama duba su ne suka fito, a harabar asibintin ta ga Mummy ciki mummunar yanayin ita da Dr Nadraa, Mummy na jin muryar Shatu ta ɗago kai cikin rawar jiki ta nufo Shatu.
Security ɗin M Madawaki ne suka tare ta, a hankali Shatu ta ɗaga musu hannun tana nuna Mummy da yatsa bakinta na rawa wajen cewa.
"Mummy!Mummy!Mummy! Ke ce haka?"
Fashewa da kuka Mummy ta yi za ta rungumi Shatu, M Madawaki ya janye Shatu zuwa jikinsa, cikin kuka Shatu ta ce.
"Abbana, ka ga Mummy don Allah ina so mu yi magana."
Cak ya ɗagata zuwa mota, sai da ya sakata a cikin mota sannan ya ce.
"Eshaa bana son abin da zai sake haɗa mu da Hajarah..."
Hannayenta ta haɗa wajen guda tana roƙansa, girgiza kai ya yi tare da yi wa ɗaya daga cikin security ɗinsa magana ya kira masa Hajarah.
Da gudu Mummy ta zo, tana tsayawa a bakin ƙofar motar da ya buɗe, cikin kuka ta ce.
"Shatu M Madawaki don Allah ki yafe min dukkanin abin da na aikata miki ko zan samu sauƙin a rayuwata....."
Katseta Shatu ta yi tare da cewa.
"A'a Mummy babu wani abun da kika yi min, koma kin yi Ni na yafe miki.."
Goge hawayen fuskarta Mummy ta yi tare da cewa.
"Na gode sosai Shatu, zan so ki bani Yarinyar wajenki na ɗauka in babu matsala?"
NI'IMATUL RAHMAN Shatu ta miƙewa Mummy, M Madawaki ya kawo hannunsa zai karɓe Yarinyar Shatu ta turawa Mummy ita, sannan ta juyo tana rungume M Madawaki.
Fashewa da kuka Mummy ta yi tana juya NI'IMATUL RAHMAN a hannunta wacce take bacci dalilin zazzaɓin da yake damunta, cikin sanyin murya Mummy ta ce.
"Shatu wannan Yarinyar M Madawaki ce? Shi ya haifeta, na shiga uku rashin haƙurina ne ya sa na kasa gane wa KOWA DA RABONSA, na kasa fahimtar hakan Shatu idanunwan sun rufe na manta da cewa rabonka baya wuce ka, duk tsawon lokacin in kana da rabo zaka samu...."
"Haka ne Mummy mutane suna mantawa da hakan suna kasa haƙuri su ga abin da Allah ya zaɓa musu, Ni na san KOWA DA RABONSA, ba kowa ke zaɓar rabonsa ba, wasu rabonsu ne yake zaɓarsu, Ni wana rabon ne ya zaɓe Ni, ƙaddara ita ce ta sadani da rabona, wanda a nan Madawaki Dynasty suka san akwai rabon da Allah ya bawa Abbana, da kike kasa haƙurin jiran lokaci.
Irinku ne masu bin ZAƁIN ZUCIYA, da nufin samun FARINCIKI RAYUWA, amma daga ƙashe abubuwan suka cakuɗe har ku zo kuna neman WAYE GATANA, bayan tun farko kun bara shi a baya lokacin da kina MATAR AURE CE, amma duk da hakan bakwa fahimtar KOWA DA RABONSA..
Alhamdulilah! Alhamdulilah! Alhamdulilah!
A nan na kawo ƙarshen littafin KOWA DA RABONSA.
Ina so na yi amfani da wannan lokaci domin na sanar da mu, wani abu ɗaya.
Littafi KOWA DA RABONSA littafi ne da na yi domin tunatar da Yan Uwana mata da maza, wani abu da muke mantawa da shi, da yawan mutane sun ganin matar da bata haihu da wurin ba, suna kiranta da taba haihuwa, kuma da yawan matan ba rashin haihuwar ne ba sa yi ba, lokacin ne ba yi ba.
A haka ma ɓangaren maza, namiji yana auran mace ɗaya zuwa biyu indan babu wacce ta haihu za'a fara kisan da baya haihu, muna mantawa da KOWA DA RABONSA a duniya in dai mutum ya je asibiti suka tabbatar masa da cewa lafiya yake babu wata matsala da take damunsa, zai iya samu rabonsa a gaba duk tsawon lokaci.
Sai babban matsalar da muke fama da ita mu mata, akwa wanda Allah yake jarabta da matsalolin, wanda dole suna buƙatarta kulawar likitoci, Misali irin matsalar da Shatu ta fuskanta da yawa a cikin mata akwai masu fama da irin hakan rashin kulawa da rashin haƙuri ke jefa su cikin wata matsalar.
Domin mace na yin Miscarriage sau ɗaya zuwa biyu za'a a fara ƙananun maganganun, ana matar wanne bata iya ɗaukar ciki, yawan ɓari ne da ita, in kuma ta taɓe yin family planning za'a fara cewa ai daga yin planning ta fara shi kenan mahaifarta ta samu matsala.
In kuma aka samu wata ta samu irin wannan matsala har ta samu damar zuwa Hospital, likitoci suka bata damar hutawa, ana iya samun namiji da ba zai iya yi mata aiyaukan gida ba, kuma ba zai bari ta nemo wace za ta taimaka mata ba, ko ya yadda ta tafi gidansu, da yawa irin wannan na faru, sai da Allah ya kawo mana mafita a cikin lamarukan mu.
Allah ya bamu iƙon cinye duk wata jarabawa, ya ƙara mana haƙuri da juriya. Ya ba mu iƙon fahimtar duk abin da haƙuri bai baka ba, rashinsa ma ba zai baka ba. ✍️✍️
MAMYY WRITER CE ✍️ ✍️
Shin kun san WAYE Ra-si Amjad da Ayrah? To ku nemi littafina mai suna ZAƁIN ZUCIYA.
Na san baku san WAYE AA Shazalee ba, ku nemi littafina mai FARINCIKI RAYUWA.
Amma dai kuna da labarin Shekyh Mohaj dai, wanda ya zama gatan Aneelah a cikin littafina mai suna WAYE GATANA.
A littafina mai suna MATAR AURE CE, za ku ji yadda Prof Muhammad Zaid yake bulayin neman matarsa wacce suke tare da ita a cikin inuwa ɗaya amma babu wanda ya san, da ɗan Uwansa.
Na san yanzu haka KOWA DA RABONSA ya iso gareku, ina so bayan kun kammala karanta duk waɗannan littafan za mu haɗu da ku a cikin littafina mai suna FANSAR RAI.
Ina godiya sosai da bibiyata, babu abin da zai ce da ku masoyana sai dai Allah ya biyawa kowa buƙatarsa, ku ne Garkuwar hannun da nake yi rubuce-rubuce da shi in babu ku To babu MAMYY WRITER