27
by @rukyelmuaz
CIGABAN LABARI
Garin ya yi shiru banda carar zakaru babu abinda kake ji, wani sanyi me ratsa ƙashi da ɓargon jiki ya hana kowa fitowa, kasancewar an yi ruwan dare, ya sakar da sanyi, a cikin garin karfe 6:30. Amma garin babu zirga zirgar mutane, sai masu tafiya gona. Sai ƙarar motoci dake kake ji daga can guri titi suna wuce wa ƙilan matafiya ne da suka kwana a hanya.
Kwance yake a bed. ya takure wuri ɗaya ya rufe kansa da brown blanket.
Tunda ya dawo sallar Asubahi ya kwanta yake jin sanyi na shiga ko ina a jikinsa, duk san sanyi irin na Julaibib, ji ya yi sanyin ya masa yawa.
Wayarsa ce ta ɗauki ƙara, wanda hakan ya yi sanadiyar motawarsa, shi kam ya manta da zai kwanta bai saka wayar a silent ba.
A hankali ya ɗan buɗe jikinsa da duka ya rufe da blanket.
Hannu ya kai yana laluben wayar daga wurin da yake da tabbacin nan take, ba tare da ya buɗe ido ba ya ɗauki wayar kashe, ya koma ya kwanta,
Kwance take duk ta yaye blanket ɗin da kaka tasa ta rufeta da shi, ta yi irin kwanciyar da ake cewa kwanciyar faɗi, kayan baccin dake jikinta wata doguwar riga ce, duk ta tattareta ta dawo wurin ƙugunta.
Kaka ce ta shigo ɗakin riƙe da Flask , ta zubo ruwan zafi ciki ta a jiye ƙusa kusa da mirror, wurin gadon ta zo ta tsaya tana kallon irin kwanciyar da Haisu ta yi, wanda yanzu har pant ɗin jikinta kana gani.
"Ni Hafsatu na shiga ukku wannan yarinya sai kace suna dambe da Aljanu"
Kaka ta yi maganar tana dafe ƙirji, wani juyi Haisu ta ƙarayi ta yo gefen gado zata faɗo, da sauri Kaka ta tare ta, "Ke Hafsatu tashi kiyi sallah tun ɗazu nike tashinki kina komawa bacci."
Shiru Haisu tayi babu alamar zata motsa ganin hakan yasa Kaka ta tattaro ƙarfinta wuri ɗaya ta ɗagota, Kuka ta saki kamar wacce a kama duka.
"Ke Hafsatu bani son iya shege sallah ce baza kiyi ba ko me?"
Kuka take har yanzu bata kula Kaka ba, sai ma kwace hannunta da tayi ta koma zata kwanta.
"Hafsatu wallahi in kika koma baki wuce kin yi sallah ba ni da ke ne, Zuraibib zan je in kira ya miki fyaɗar ƴan kaɗanya."
Jin sunan da aka ambata yasa tayin saurin buɗe ido, yo ai ita tama manta Basamude na gidan nan.
Kafin kace kwabo ta ruga ta shige toilet ko takalmi babu a ƙafarta sai bayan ta shiga sannan ta ce.
"Kaka bani takalmi, kin ɗauke takalmin ki kawomin."
"Kai wannan yarinyar babu ranar da zata sauya"
Juyawa Kaka tayi ta bata takalmin kamar yanda ta nema, sannan ta juya ta fita ɗakin.
Ta daɗe a cikin toilet ɗin sannan ta fito, dogon hijabin Kaka ta ɗauka ta saka tayi sallah, tana gamawa ta cire hijabin.
Ko sallaya bata ɗauke ba, ta a jiye hijabin a saman sallayar ta koma gado ta ja blanket ta rufe jikinta, bacci mai daɗi ya ƙara ɗaukarta.
Sai ƙarfe wurin goma sannan ya tashi, yana tashi ya kunna wayarsa, sannan ya shiga toilet ya yi wanka.
Ya ɗauki lokaci sannan ya fito daga toilet ɗin, yana riƙe da wani ƙaramin towel, yana goge sumar kansa.
Ɗaure yake da blue towel, kansa jiƙe da ruwa, gargasar jikinsa ta kwanta a ƙirjinsa.
Wayarsa ce ta fara ƙara alamar kira na shigowa wurin ya ƙarasa ganin number ɗin bata Nigeria ba ce ake kira da ita yasa ya zauna a gefen gado sannan ya ɗauki kiran.
"Hello Uncle!"
" Son what happened to your phone?"
“Nothing happened to my phone, Uncle.”
“I called you, your phone was ringing but then I heard that it was switched off.”
"I was the one who switched it off I didn't know it was you calling."
"Alright."
"Princess ta tashi bacci ne?"
"Bansaniba yanzu na tashi na yi wanka, fitowa ta wanka kenan"
“Please, go and check if she’s awake give her the phone I just want to see her face.”
"Ok Uncle"
Uncle na kashe kiran, Julaibib ya tashi sai da ya gama shiryawa, jikinsa sai ƙamshin Perfumes iri da kala yake, duk da haka sai da ya ɗauko.
Creed Aventus, Royal Oud, Louis Vuitton, perfumes, ƙamshin turarukan sun haɗe suna fitar da wani ƙamshi na daban wanda yake jin sa tun daga kansa har cikin ƙasan zuciyarsa wata natsuwa tana saukar masa.
Wurin wardrobe ya ƙarsa ya buɗe ya ciro wata Egyptian cotton blue black jallabiya ya saka a jikinsa, ta yi masa kyau sosai ta zauna a farar fatar jikinsa, gaban mirror ya koma ya sake kallon kansa ya ɗan gyara sunarsa sannan ya koma wurin shoe cabinet ɗinsa ya ciro wani Navy blue sandal ya sanya a ƙafarsa wanda yama farar ƙafarsa kyau.
Wayarsa ce ta ƙara rings hakan yasa ya dawo wurin gadon ya ɗauka Mommy ce ke kiransa cikin girmamawa ya ɗauka,
"Mommy barka da safiya ina kwana."
"Lafiya lau Alhamdulillah, ina Kaka ta saka wayarta ina kiransu wayar bata shiga"
"To taya waya zata shiga bayan, kun san tana da birinya a cikin ɗaki"
"Wacece biranya?"
"Ɗiyarki mana"
"Wallahi zan ɓata maka rai, ka kaima Kaka wayar."
Mommy na faɗin haka ta kashe kiran.
Sai da ya koma gaban mirror, ya sake duba kansa ya ƙara gyara sumar kansa, kamar ba zai bar wurinba ya jima yana tsaye kamar mai tunanin wani abu, sannan ya nufo ƙofa ya buɗe ya fito.
Yana fitowa suka haɗu da Kaka a bakin ƙofar da alama shigowa wurinsa zata yi, murmushi ya yi mata yana ƙoƙarin yi mata magana yaga ta fara binsa da kallon zolaya tana tiƙe haɓarta alamar almara.
Ganinshi cikin kyakkyawar shiga da ƙamshin turarukan da yake tashi yasa ta ce, "A kwana a hantse sai kyakkyawa, sammako sai mummuna, an fito ne mai gidan da babu cefane?, kai ka huta na,urar baturen kewayenka bata samu matsala ba"
Ƙaramin murmushi ya yi mata wanda ya ƙara fito da kyaun da ya yi a fili, ya sake saka kayan suka ƙara haska shi, idonsa ya ɗan shigar ciki kaɗan.
"Amma so nawa zan ce miki ki daina cewa kewaye, ita kuma ba sunanta na,urar bature ba, shower a ke cewa"
Yana faɗin haka ya juya ya janyo ƙofar ɗakinshi ya wuce zai shiga ɗakin Kaka.
Bayanshi ta biyo tana mitar maganar.
"Kai bana son fitina irin ta masu jajayen kunnuwa, komi sun canja masa suna sun maida shi wani yare da ban"
"Shikenan na ji baki so, amma dole ki koya, daga yanzu zaki fara koya, barka da safiya amarya ta,"
"Barkanmu dai ya ka kwana?"
"Lafiya lau"
Yana faɗin haka kafin Kaka ta bashi amsa wayarshi ta fara ƙara alamar kira na shigowa, ganin me kiran yasa ya ce "Kaka ina wannan yarinyar"
"Wacce yarinyar kake nufi"
"Yarinyar ki mana"
"Bata da suna ita yarinyar"
"Wannan matsatstsakun yarinyar, suda uwar magana"
Ya gama kai Kaka wuya don ta lura baida niyyar faɗin sunan wanda yake nema ɗin, ita kuma ba zata bashi amsa ba in har ba zai faɗi sunan ba.
Juyawa tayi ta koma kitchen ta barsa a wurin ganin ta wuce yasa ya shige cikin ɗakin don nemanta da kansa, don baya da tabbas tana cikin gidan ganin bata parlour yasa ya shiga kicin bedroom ɗin.
Kwance take sai surutai take cikin barci kamar tana rigima da wasu rigar jikinta ta gama tattarewa har pant ɗinta ana gani.
"Wallahi kin taɓo masifa da kuɗinki sai na zubar miki da haƙora"
"Ke Mairo yi mana gata tsiya gata arziƙi"
Yanda take maganar zaka rantse ba bacci take ba don in baka kusa zaka ce rigima take da wani a cikin ɗakin.
Cikin ɗakin ya ƙarasa shigowa yana ƙare mata kallo yanda bakinta ke jaraba a cikin bacci, "Mtswwww" yaja tsaki yana maganar zuciya, wato ita wannan saboda tsabar bala'i a cikin baccin ma bata ƙyale fitina ta zauna lafiya ba,
Wayarsa ce ta ƙara sabon ƙara hakan yasa ya tuna da abinda ya kawo shi, yatsina baki ya yi, ya ɗan duƙo yana buga gefen gado alamar yana son ta shi ta ne, ganin taƙi tashi saima sake juyawa wani ɓarayin tayi, ganin kamar tana jinsa ne yasa ya bugi cinyarta da take a buɗe saboda yayewar rigarta.
Kamar wacce a ka kawo ma farmaki ko tayi mummunan mafarki, haka ta zabura ta tashi zaune, tana murza idonta dake cike da bacci, can kuma ta saki kuka "Wayyo Allah Kaka zaki ciremin cinyata, ki maidani musaka,"
"Zaki buɗe idonki ko saina zabga miki mari"
Da sauri ta buɗe ido tana nurzawa hawaye na sake fitowa daga idonta jin muryarsa kamar daga sama, kuma tabbas tasan zai iya kasancewar ba sonta yake ba, mugun banza kawai shine abinda take faɗa a cikin zuciyarta.
"Maza ki share wannan ruwan banzan dake fitowa a idonki, ko in canja miki kamanni"
Baki ta murguɗa tana wani wuri-wuri da ido, hannunta tasa ta fara goge idonta, kiran dake ƙara shigowa ya ɗauka ya miƙa mata wayar, ganin wanda ke saman screen ɗin yasa ta fashe da sabon kuka, harda yarfa hannu.
Da kallo kawai ya bita ganin yanda take kuka harda yarfa hannu, abin yana bashi takaici.
Yarinya tun tana ƙarama ta iya kaidi da makirci na manyan mata, shi manyan ma in suna wani makircin da shagwaɓa ji yake wannan iskanci ne kawai,
Ganin abin na ƙara bashi ta kaici yasa ya fita ya bar bedroom ɗin ya koma parlour ya zauna.
Kuka take sosai taƙi cewa komi,
"Doughter nayi laifi ne? Please stop cry"
Cikin kuka take ɗaga masa kai alamar ya mata laifi.
"Ohhhh my heart"
Ya faɗa yana dafe gefen zuciyarsa "Doughter kinga zuciyar Daddy ɗinki na bugawa da sauri saboda ya yi ma gimbiya laifi."
"Daina kukan ki faɗamin meye laifin nawa in wanke kaina"
Goge hawayen fuskarta tayi tana turo ƙaramin bakinta gaba, ta ɗan ɗauki lokaci taki cewa komi.
"Kina son Daddy ya yi kuka shima"
Da sauri ta girgiza kai alamar a'a.
"Daddy ka dawo ni ina son ganinka, kuma baka zo graduation ɗina ba, naga yara suna ɗaukar photo da Babansu da Mamansu, amma ni sai Kaka da Aunty Jannat da Mommy"
Yana kwance a kan gado na alfarma ya ɗan rufe ƙafarsa da blanket, yana sanye da White t shirt duk da sajen fuskarsa furfura ta ratsa shi amma hakan bai hana fito da kyaunshi ba, da farar fatarsa da hutu da jin daɗi ya gama ratsata ba.
Kalmar da ta faɗi na yara na photo da iyayensu sai yaji kamar ta fama masa wani rauni ne da ya daɗe yana jinya. Lokaci ɗaya yaji bugun zuciyarsa yana neman fara bugawa da wani salo wanda ya kwana biyu bai buga da irinsa ba, daurewa ya yi, ya hana zuciyarsa tarwatsewa ya tattaro duk natsuwarsa wuri ɗaya domin yana tare da sanyin Idanunsa farin cikin zuciyarsa ya ce.
"Daddy ya yi laifi shikenan ina bada haƙuri zan dawo, yanzu dai Happy birthday my princess"
"Ni fa bana son wannan birthday wishes ɗin naku"
" Haba Doughter dole in yi murna kina ƙara girma da hankali mana"
"To nagode Daddy yaushe zaka dawo"
"Yanzu dai me kike so birthday gifts"
Da farin cikin jin abinda Daddy ya ce tayi fari da ido tana murmushin jin daɗi, ita kuwa yau kakarta ta yanke saƙa, cikin farin ciki ta fara magana tana lissafawa da hannunta.
"Ina son gujiya, Ina son kifi, ina son kaza, ina son tsami gaye, Ina son ɗinya, Ina son, kashu, ina son zaitun, Ina son carbin tsohuwa, ina son hanjin ligidi.
Dariya sosai yake mata in ba ƙuruciyaba wannan aguguwan da take lissafawa duk a cikin wa zata zuba su, gashi kuma ta dage iya gaskiyarta abinda take so take lissafawa.
Julaibib da duk abinda take faɗi yana ji kasancewar tana magana da ƙarfi, maganar Uncle ɗinsa ce kawai baya ji,
Wannan yarinyar sam bata da hankali, birthday gifts ɗin shine za,a kawo mata wasu tarkace wanda wasu ma yanzu yaji sunansu a bakinta, gyara zaman shi ya yi, yana jin duk shirmen da take yi.
Ta cikin wayar Daddy ya ce' "Yanzu duka wannan aguguwan ke dawa zaki cinye su?"
"Ni da Mairo zamu cinye duka"
"Da wani bakin zaki cinye, don wannan bakin naki ya yi ƙarami"
"Daddy zan iya cinyewa Allah kuwa"
"To na yarda zaki iya cinyewa, kuma zan saya amma nima zakimin wani abu in kin yarda"
Wayar ta saki a saman gadon ta miƙe tana rawa da tsalle, in banda ƙafafunta babu abinda Daddy ke kallo, magana yake amma sam bata shi yake ba, sai da ta gama tsalle da murna sannan ta zaune, ta ɗauki wayar, murnushi yake mata, domin komi ta yi tana tuna masa da wata rayuwarsa ta baya ne.
"Yanzu Doughter ai saiki bari kiji me nike so ko, kafin ki fara murna."
"To Daddy mai kake so"
Gyaran murya ya yi sannan ya tamke fuska alamar babu wasa don yasan abinda zai faɗi dole sai an yi rigima da ita.
"Anjima yayanki zai kaiki a yi miki siyayyar school, sannan ina son kiyi gayu sosai a miki pictures masu kyau a turamin don in ga yanda Princess ta ƙara girma"
"Allah ba zan je da shi ba sai dai a bani kuɗin in je Mairo ta rakani"
"Doughter ni kike cema bazaki ba"
"A'a da basamude nike shine bazani dashi ba"
"Tun yaushe na hanaki kiransa da wannan sunan zan saɓa miki fa"
"Kayi haƙuri Daddy ni wallahi bana son zuwa dashi"
"Dole ki je tunda hidimar makaranta za'a miki"
Kuka ta fara ita a dole sai dai Daddy yasa a bata kuɗin su je ita da Mairo su sayo, da kyar Daddy ya samu ta yi shiru har ta amince zata je ɗin tare da shi.
"Daddy to ina son itama Mairo ka sakata a wannan makarantar da zaka sakani, mu ringa tafiya tare kaji"
"Daughter ba zaki yi karatu ba, baku tare ma baki maida hankali ina ga kun dawo tare"
"Ni ina son ka sata a school ɗin, Allah ni ina son a sakata a school ɗin muna tafiya tare"
Ganin zata tada masa hankali haka ya amince, yace za'a yi siyayyar school ɗin harda Mairo, ranar Monday Julaibib sai ya kaisu ya musu registration.
Murna sosai take yi "Ki tabbatar kin yi kyau sosai, kin ga yanzu kin zama ƴan mata"
"Da gaske na zama ƴan mata?
Ta faɗa tana kallon Daddy da yayi mata alamar Ehh da kai kawai.
Sun daɗe suna waya cike da farin ciki da tsantsar ƙauna tsananin uba da ɗiyarsa ji yake kamar ya ɗauketa ya dawo da ita gabansa domin ya bata duk irin soyayyar da ya dace da ita zuciyarsa kullum tana kukan rashin ganinta a kusa dashi.
Bayan sun gama wayar komawa ta yi cike da farin ciki ta kwanta ta a jiye wayar a gefenta.
Kira ne ya ƙara shigowa wayar hakan yasa ta miƙe ta ɗauki wayan ta fita parlour ta miƙama Julaibib wayar.
Ganin mai kiran yasa ya ɗauka ya bata muryan Mommy ta ji daga cikin wayar "Tun ɗazu nace ka kaima Kaka wayar mai ka zauna yi ne"
"Mommy ni ce"
"Hafsat ce"
"A'a Haisu ce"
Dariya mommy ta yi tace ohhhh "Haisu ƴan matan Mommy ce"
"Ehhhh ita ce"
"Happy birthday ƴan mata na, an girma sauran aure"
"Mommy ni bana son aure"
Dariya Mommy ta yi sosai sun daɗe suna magana Haisu na shirme.
Bayan sun gama waya ta kaima Kaka wayar, ta dawo ɗaki zata koma ta kwanta.
"Zo nan"
Ya yi maganar a daƙile kamar tayi masa dole, ƙafafuwansa ya miƙar a kan table ɗin dake kusa da kujerar.
Kamar bata ji ba ta yi banza zata wuce ciki.
"Wallahi kika ƙara tako ɗaya sai jikinki ya faɗa miki"
Juyuwa tayi tana tafiya tana turo baki, ɗauke kai ya yi kamar bai ga abinda take yi ba.
"Gani"
Ta faɗa tana kama ƙaramin Kwankwasonta da bai wuce cikin carbi ba.
"Kika tsaya kina riƙemin Kwankwaso kamar kwalbar Lacasera, zaki saki hannunki ko saina karyaki, ƙashin kwankwason ya zame da ga jikinki."
Kallon Kwankwason ta fara yi sannan ta ƙarasa wurin da yake, hannu ya kai ya riƙo kunnanta ya murɗe shi.
"Ni dodo ne da za'a ce zan fita dake kike aguguwa kamar ƴar bori?"
"Wayyo Allah kunnena don Allah ka yi haƙuri ba zan sakeba"
"Kima sake wallahi kiga yanda zan yi dake, ke ba abin alfaharin ki bane a ce na taimaka na ɗaukeki a mota na ƙazamar banza da wofi don Allah ƙalleki kamar dorinar ruwa"
Wani baƙin ciki ne ya gama tokare mata zuciya ta saki wani ihu wanda yasa Kaka dake waje shigowa da gudu tana salati.
"Kai Zuraibib saketa cire mata kunne zaka yi ne, ko kurma zaka mayar da ita?"
Shiru ya yi bai ce komi ba kuma bai saki kunnan Haisu ba, sai da ya tabbatar ta ji zafi sosai sannan ya saki kunnan, yana sakinta taja ajiyar zuciya ta ruga ta riƙe Kaka.
"Kuma an ce Basamude"
Yin ƙorowa ya yi zai tashi Kaka ta yi saurin ce wa "Wallahi zan kira ubanka in sanar masa ba zaka saka marainiya a gaba kana cin zalunta ba.
Komawa ya yi, ya zauna, Kaka ta shiga bedroom da Haisu.
Da wowa Kaka ta yi, ta miƙa masa wayarsa da ta gama waya da Mommy da ita, sannan ta koma ciki.
Wuce ki yi wanka ki zo ki karya ga shinan ina haɗa miki abin karin safe.
"Kunu ne?"
"A,a gero ne, don iyayenki"
Kaya ta fara cirewa Kaka ta fita domin ta zuba mata ruwan wanka daga kitchen.
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, ni Hafsatu, kai Zuraibib zo nan taimaka ka miƙama Haisu bokitin ruwan wankan nan, kaga miyata zata ƙone.
Yana jinta ya yi shiru shi wallahi ya rasa dalilin da yasa Kaka take masa irin wannan abun yanzu kamar shi zata ce ya zo ya kaima wannan yarinyar ruwan wanka.
Shirun da Kaka taji ne yasa ta ɗauko ruwan da kanta ta shigo dashi, tana shigowa idonta ya sauka a kansa hankalinsa na kan waya sai kallon labarai yake a ciki.
Bata ce masa komi ba ta wuce bedroom ta kai ma Haisu ruwa, sannan ta fito, ta koma kitchen.
Breakfast ta haɗo ta kawo masa yana zaune hankalinsa yana kan wayar da yake dubawa,
"Ga karin kumallo nan ka ci"
"Don Allah Kaka ki waye mana, meye wani karin kumallo?"
"Ki ce breakfast"
"Birezibaz"
Wata dariya mai sauti ya yi yana mamakin halin Kaka wai kawai breakfast ɗin ne bazata faɗa ba wai birezibaz.
"Don Allah Kaka meye wani birezibaz, just breakfast da zaki ce shine abun matsala"
"To shikenan na ce ga barebarifas ɗinka shikenan"
"Ohhhh my god."
"Shikenan koma kitchen Kaka nagode sosai Allah yaja da kwana"
Bata sake kulashi ba ta wuce ta fita.
Wayarshi ya a jiye sannan ya buɗe plates ɗin da ta ɗauro a saman tray ɗin breakfast da tace ta kawo masa ɗin.
Noodles with fish & Irish Potato chips ne, haɗin da yake so, numfashi ya ja ya rufe ido ya buɗe yana ƙara shaƙar kamshin, shi kam bai san me yasa yafi jin daɗin girkin ƙauye ba basa irin haɗin birni a yi ta zuba shirme a abinci.
A jiye wayar ya yi a kan kujerar da yake, sannan ya miƙe yana tashi ya fita, kitchen ɗin ya shiga ya iske tana ɗuma,ma sauran kazar da Haisu ta rage da dare.
"Kaka me kuma zaki yi da sauran kaza, ki bari in na fita sai a sayo miki wata mana."
"Kai Zuraibib Haisu nike haɗama nata abun karin, na san zata iya cin wannan kazar da sanyinta, shiyasa gwara in ɗan bata tsoro da wuta, ta kashe sanyi."
"Uhmmmm"
Ƙawai ya ce, ƙaramin kofi ya ɗauka ya fita ya barta a kitchen ɗin, yana komawa ya buɗe Flakes ɗin dake saman tray, ya zuba ruwan tea, da yake ta ƙamshin na'a na'a, sai fitar da ƙamshin kayan haɗi yake wanda ya gama cika wurin yake shiga cikin hancinsa zuwa tsakiyar maɗigar kansa.
"Ya salam" ya furta a hankali yana komawa da baya ya jingina sosai da kujera.
Ruwan tea ɗin ya ɗauka a hankali ya ɗan kurba ya a jiye ƙara lumshe ido ya yi a karo na babu a dadi don ƙamshi da daɗin har tsakiyar kansa yake ji.