LOKACI CHAPTER 38
by @fulani32
***
⏳🕛 LOKACI 🕛 ⏳
RABI'ATU KABIR ACHADU FULANI
YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION YOTA
Under Team Yota's Amazing Pen's.
FULANI ❣️
***
PAGE 3️⃣ 8️⃣
Tana zaune a kan kujerar cikin parlown ɗakinta, hannunta riƙe da carbi tana ja a hankali, duk da yanda take tazbiyi hankalinta yana kan Zay'd, ta san ɗanta, ta san irin son da yake yi wa Zahra, sosai taga ƙarfin halinsa, ba ta yi tunanin zai iya haƙurin da ya yi ba, amman kallo ɗaya ta masa ta san rashin nata yana taɓa sa sosai, sai dai duk da halin da ta gansa bata jin zata iya basa Zahra a yanzu, ajiyar zuciya ta sauke, a ranta tana yi musu addu'a da fatan alkhairi.
Ƙarar buɗe ƙofa ce ta katse ta daga tunanin da take yi, ta ɗago kanta, ganin wanda ya shigo ne ya sa ta ɗan gyara zamanta, fuskarta kuma ta yalwata da murmushi.
"Assalamu alaikum"
Abhie ya yi sallama yana shigowa cikin parlown, sannan ya mayar mata da martanin murmushin da take masa.
Kujerar da take fuskantarta ya zauna, sannan su ka gaisa, glass cup ɗin da ke gabansa ya ɗauka ya zuba ruwa kaɗan ya sha, bayan ya ajiye kofin ne ya mayar da hankalinsa kanta.
"Ammie alfarma na zo nema"
"Alfarma kuma Abhie, kawai ka bani umarni"
Murmushi ya yi kaɗan, ya na jin daɗin furucinta.
"A kan Zay'd da Zahrah"
A take ta haɗiye murmushinta, sauke carbin hannunta ta yi a kan cinyarta, ta jingina da bayan kujera. Wani murmushin ya ƙara saki, ya na jinjina ƙarfin halin matar tasa.
"Ɗanki ya kawo min ƙararki kin ƙwace masa mata"
Murmushin da ba tayi niyya bane ya ƙwace mata.
"Shi babban mutum ɗin ne ya ce na ƙwace masa mata?"
"Eh dan haka tunda har ya yi magana shiyasa nazo nema masa alfarma a basa matarsa, ai taji sauƙi kuma ya kamata a basa dama ya rarrashi matarsa"
"Toh Abhie naga dai sauran kwana shida sati biyun ya yi ko?"
Zama rarrashinta ya yi, har ya samu ta amince a kan zata basa matarsa a yau ɗin, amman ba dan ranta ya so ba, tashi ya yi ya fice daga parlown, ita kuma ta tafi kitchen dan babu abin da za ta yi koda taje, kawai dai zata duba me yaran suke ne.
Wayar Zay'd ya kira ringing biyu ya ɗaga.
"Abhieee"
Murmushi Abhie ya saki a ɓangarensa.
"Abhie kayi magana mana" ya ce cike da zaƙuwa.
"Ammie ta baka matarka, amman ta ce sai dare zaka zo ka ɗauketa"
Godiya ya fara yiwa Abhie, yana jin wani irin farin ciki na ratsa shi.
Daga kitchen bayan ta duba abin da Autah suke da Princess ta wuce part ɗin Zay'd, lokacin da ta shiga tana zaune akan daddamu tana karatu, tana kai ayar da take ta katse karatun, juyowa ta yi ta gaisheta, amsawa ta yi sannan ta ce ta zo kusa da ita ta zauna za suyi magana, rufe Kur'anin tayi ta taso ta zauna a wajen ƙafafunta.
Hannayenta ta riƙe a cikin nata.
"Za ki koma gidanki yau daughter, tunda naga alhamdullah jikin naki da sauƙi ko?"
Ta ƙarasa da tambayarta tana kallonta, saboda tana son ganin yanayinta.
Duk da yanda gabanta ya faɗi da maganar Ammien haka ta dake, ta yi ƙasa da kanta sai da tayi dagaske sannan ta iya magana.
"Tohm Ammie Allah ya kaimu"
Nasiha Ammie ta fara yi mata, da kuma nuna mata wannan shine auren, kar abin da ya faru ya sa ta ce za ta guji mijinta, mijinta yana sonta dan haka ta yi abin da zata ƙara shiga ransa, anan ta fara faɗa mata abin da Zay'd yake so da wanda baya so, sosai take bata shawara kamar ba uwar mijinta ba, dan sai da ta ƙara maimaita mata ita ba'a sirika take ɗaukarta ba, a ɗiyarta take ɗaukarta, dan haka ko wani abu ya yi mata tazo ta faɗa mata ita zata rama mata.
Sosai taji daɗin maganganun Ammie, kuma ita ma kanta ta sani yanzu me yayi mata saura, banda ta kwantar da hankalinta a can gidan nasa, bata da inda ya fi can ɗin, sai dai tsoronsa ne bata san ta ina zata fara ciresa ba.
"Ki shirya anjima za'a zo ayi miki gyaran jiki, kanki kuma zan saka ayi miki kitso, mai ƙunshi ma za ta zo"
"Tohm Ammie nagode sosai Allah ya ƙara girma da ɗaukaka"
Ta amsa mata kanta a ƙasa cike da jin kunya.
Fita tayi ta kira matar da zata mata ƴar meduguri ce, aure ne ya kawota garin kano, dake ta na yi mata daman, bayani tayi mata da duk abin da take buƙata, sannan suka yi sallama, bayan Ammie ta tura mata kuɗin aikin. Daga nan ta koma kitchen ɗin ta haɗa mata abubuwan da take bata tunda tazo gidan.
Bayan ta karya ta sha maganinta, wanka ta yi daga nan ta koma part ɗin Ammie dan har sunzo suna jiranta. Gyaran jiki aka fara mata da gyaran gashi, bayan an gama a ka saka mata ƙunshi, baƙi a hannu da ƙafa, saboda da sauran jan lalle na bikinta bai gama fita ba, a wajen kitso ne ta nuna ba sai anyi ba, saboda bata so, amman haka Ammie ta ce sai anyi, ba za ta iya mata musu ba, haka a ka yi mata kitso kamar zata yi kuka, sosai kitson yayi wani irin kyau kodan bata saba ba, haka su Teemah suka sakata a gaba da ɗaukar hoto, ana gamawa taje ta sake wanka da ruwan turare, koya ta gitfa ƙamshi ne yake tashi a jikinta.
Ga wasu irin itacen turare da tayi tsugunno a kansu wajen kala uku, humra Ammie ta saka aka haɗa mata da turaren wuta, duk wani abu na nau'in ƙamshi sai da Ammie ta siya mata, sosai kuma taji daɗi dan a rayuwarta tana ƙaunar ƙamshi.
Ammie kuwa duk sanda ta kalleta, wani irin farin ciki take ji ita da kanta tasan yaronta ya yi dace, shiyasa bata damu da irin son da yake mata, ita kanta ɗan zaman da tayi a gidan, wani irin so take mata, saboda tana da shiga rai sosai.
Wajen 6 suka gama, daganan ta koma can part ɗin, a gaban mudubi ta tsaya tana kallon kanta, ita kanta tasan tayi kyau, fatarta sai ɗaukar ido take yi, kitson kanta ta zubawa ido tana tunanin anya da wayonta ta taɓa ƙananun kitso haka, a ranta kuma wani irin girman Ammie ne ya ƙara samun matsuguni a zuciyarta, kamar yanda Ammie tace kallon ƴa take mata, ita ma da kanta kallon mahaifiya take mata, saboda kulawar da bata da soyayyar da ta nuna mata, dagaske ta na son matar sosai.
Wanka tayi da alwalah jin har an fara kiran magriba, sai da tayi sallah sannan ta shirya cikin baƙar doguwar riga, rolling ta yi ta haɗe kayanta a ƙaramin akwatin da aka zubo mata kayanta, jin an turo ƙofar ɗakin ne ya sa ta ɗagowa, Teemah ce da Salmah suka shigo, Teemah ta kalla ganin kamar kuka tayi.
"Me ya faru Princess?"
Ta tambayeta tana riƙe hannunta, jikinta ta faɗa ta fashe da kuka, Salmah ma kamar mai jira itama ta fara kukan, ƴar ruɗewa ta yi tana tambayarsu ko lafiya.
"Yanzu duk tafiya za ku yi ku barni, gashi can Yah Zay'd ya zo ɗaukarki, itama yanzu Yah Khaleel zai mayar da ita gida"
Tayi maganar tana fashewa da kuka.
Tabbas da ace a nutse Teemah take da taji yanda zuciyarta ta buga da ƙarfi, ƙoƙarin danne yanayinta ta yi ta ɗagota daga jikinta.
"Toh me abin kuka? Duk sanda kika so zuwa gidana ki haɗo kayanki ki tawo, haka idan gidan Mahmah ne, babu mai hanaki, kalli kina kuka ko kyau baiyi miki ba"
Ta faɗa tana share mata hawayen fuskarta. Kallon Autah tayi itama tayi mata magana suka dena kukan, akwatinta da na Salmah suka ɗauka suka nufi waje, basu shiga da su part ɗin Ammie ba, iya su kaɗai suka shiga part ɗin.
Ya na zaune a kujerar da take kallon bakin ƙofa, kuma idonsa yana kan ƙofar tunda Ammie ta aika a kira ta, tun kafin ta shigo ƙamshinta ya shigo cikin parlown, lokacin da ta yi sallama idonsa yayi luuu kamar zai lumshe sai kuma ya ƙara ware su a kanta, gani yayi kamar an canza masa ita, ya na kallonta ta zauna a ƙasan ƙafar Ammie, suka gaisa.
Abhie ne ya sakko daga sama, sai a lokacin suka gaisa da shi, Khaleel ne ya gaisheta ta amsa masa kanta a ƙasa, saboda yanda idanunsa da suke a kanta duk suka takura mata.
"Muje ko Autah"
Ya yi maganar yana barin parlown. Ta na miƙewa Teemah ta haye sama a guje tana kuka, duk da kallo suka bita, jaka Ammie ta bawa Salmah ta karɓa ta yi godiya, itama kamar za ta yi kuka, Abhie kuma kuɗi ya bata, daman tun shigowar Zay'd taga ya tura mata kuɗi a account ɗinta, godiya tayi musu sannan ta bi bayansa.
Ƙasa shima ya sakko ya zauna a ƙasan ƙafar Abhie, nasiha mai ratsa jiki Abhie ya yi musu, Ammie ma ta ɗora da nata, sanna suka sallamesu, har bakin mota suka rako su, sai da motar su ta bar harabar gidan Ammie ta koma, tana jin kewar Zahran na kamata.
★★
"Autah"
Ya kira sunanta a hankali, ya na rage gudun motar sa, ganin sai share hawaye take.
Ɗagowa ta yi ta kallesa ba tare da ta amsa ba.
"Kukan me ki ke yi?"
"Princess ce sai kuka take"
Ta basa amsa wasu hawayen na zubo mata, a zamanta sosai ta saba da ita fiye da yanda suka saba, yanzu ga shi za ta koma gida babu Big Sister babu Princess daga ita sai Mahmah.
"Share hawayen ki ji wata magana"
Ya faɗa yana miƙa mata hankachief ɗinsa. Karɓa ta yi ta share hawayen, fuskarta har ta yi ja.
"Ina wannan saurayin naki?"
Ya tambayeya yana tsareta da idanunsa.
"Bayan ka koresa ko number ta ban basa ba da ya ce"
Ta yi maganar cike da ƙuruciya.
"You are mine ta ya zan bari ki bawa wani number ki?"
Cikin rashin fahimta take kallonsa. Murmushi ya yi sannan ya ce.
"Zan aiko nima Abhie ya zo nema min aurenki, da dai naso kiyi candy, amman yanzu ba zan iya ba, saboda yanda nake jinki anan"
Ya ƙarasa ya na nuna mata saitin zuciyarsa.
Bata san sanda ta rufe fuskarta da hannunta ba, cike da jin kunya.
"Wow amman lallen ya yi kyau sosai, ya zama dole na biya kuɗin ƙunshi"
Da sauri ta janye hannun nata a fuskarta, sai kuma ta cusa kanta cikin ƙafafunta.
Dariya ce ta kamasa ganin ta kasa zama a waje ɗaya. Babu kunya babu tsoron Allah Khaleel ya saka Autar Mahmah a gaba da kalaman soyayya, ita kuma tayi tsit tana saurarensa, a haka suka zo ƙofar gidansu, bai barta ta shiga ba sai da ya tabbatar ya dasawa ƴar ƙaramar zuciyarta wani abu a kansa, shima kuɗi ya tura mata a account, sai wata ƴar ƙaramar jaka da ya bata, ya na tsaye har ta shige cikin gidan, sannan ya ja motar ya tafi yana sakin murmushi shi kaɗai.
Sai da ta daidaita yanayinta sannan ta shiga da sallama, gidan tsit da gudu ta rungume Mahmah cike da kewarta, itama Mahmah cikin jin daɗi ta rungumeta, ta na mata sannu da dawowa....
★★★
"Besty babu gaisuwa?"
Ya katse shirun motar da tambayarta.
"Ina wuni"
Ta gaishesa ba tare da musu ba. Juyar da kansa gefe yayi ya saki murmushi, amman bai yi magana ba.
"Ya jikinki?"
Ba ta bashi amsa ba, sai bakinta da ta turo masa gaba.
Bai ja ta da magana, saboda yaga a ɗaɗare take da shi, har suka zo gida babu wanda ya ƙara magana a cikinsu, horn ya yi a ka buɗe ya danna hancin motar cikin gidan.
Tun da suka shigo gidan gabanta yake faɗuwa da ƙarfi, wani irin yanayi ta tsinci kanta a ciki, kai tsaye ba zata ce ta na farin ciki da dawowarta ba, kuma ba zata ce tana baƙin ciki ba, gyara zamanta tayi ta zubawa harabar gidan ido, a hankali abubuwan da suka faru suka fara dawo mata, lokacin da ya kawo ta gidan bayan sun baro wajen dinner, yanda ya saka hannunsa ya ɗauketa, fitowarta daga wanka, yanda komai ya faru a gaggauce, ba za ta iya tuna lokacin da ta fita daga gidan ba, dan bata cikin hayyacinta, gashi yanzu ya ƙara dawo da ita cikin gidan da kansa.
Wani irin abu taji ya tsaya mata a ƙirji, da ta kasa tantance ko menene, amman dai ta na jin tsoro a ƙasan zuciyarta, na ƙara kasancewarsu su biyu a cikin gidan.
Buɗe mata ƙofar da ya yi ne ya katse mata tunaninta.
"Welcome home Besty"
Muryasa ta fito a hankali, cike da wani irin farin ciki a cikinta, da ya kasa ɓoyuwa har a kan fuskarsa.
A hankali ta ɗago idonta ta kallesa. Sosai kalmar home ɗin ta tsaya a zuciyarta, kasa amsa masa ta yi, sai idanunta da ta mayar ƙasa, tana ƙoƙarin ɓoye yanayinta. Hannunsa ya miƙa mata, ido ta zubawa hannun nasa ba tare da tayi ƙoƙarin basa nata ba, sai ma ɓoyesa da ta yi cikin cinyarta. Bai damu da abin da ta yi ba ya bata hanya ta fito daga motar, hannun dai da bata son ya riƙe shi ya riƙe, duk yanda take ƙoƙarin ƙwacewa bai barta ba, har suka ƙaraso ƙofar parlow, suna zuwa ya tsaya, itama tsayawa ta yi.
Kallonta ya yi ta ce.
"Besty rufe idon ki"
Ɗagowa ta yi ta kallesa, bata san sanda bakinta ya furta sunansa ba.
"Muhan"
"Please"
Ya katseta, cikin muryar rarrashi. Kallonsa ta yi sai kuma ta sauke numfashi, rufe idon tayi, hannunsa ya saka ya rufe mata idonta a hankali, sannan ya buɗe ƙofar parlown ya shigar da ita, tafiya suke a hankali hannunta a kan nasa dake kan fuskarta, a tsakiyar parlown ya tsaya, sannan ya yi shiru na ɗan lokaci.
"Are you ready?"
Ba ta amsa masa ba. Hannunsa ya cire daga fuskarta ya matsa daga kusa da ita. Ganin duhu a parlown ya sa ta fara lalubensa da hannunta, wani irin tsoro taji ya dirar mata.
"Muhan"
Ta kirasa a hankali muryarta ɗauke da tsoro.
"I'm here Besty"
Ya yi maganar a bayanta, a dai-dai lokacin hasken parlown ya kawo, bata san sanda ta ware manyan idanunta akan abin da ta gani ba, zagaye ta fara yi da idanunta ba tare da ta san ta na yi ba, wani irin decoration ne a parlown da ya ɗauki hankalinta, tsakiyar parlown ƙaton arch ne na balloons da aka tsara cikin kalar, cream, Champagne gold da soft white, sai wasu irin furanni da aka haɗa a jiki.
*WELCOME HOME BESTY*
Ta karanta a jikin wani babban sign me kyau, wanda aka saka a tsakiyar decoration ɗin, sai kuma daga can gefen parlown aka jera cushions da ƙananun furanni a gefensu.
*WELCOME HOME FALMATA*
Juyowa ta yi zata mata masa magana, kawai taga hotunansu a cikin frame tare a wajen dinner, sai kuma wasu na biki ita kaɗai shima shi kaɗai, hotunan basu da yawa, amman waɗan da aka saka sosai sukayi wani irin kyau, a tsakiyar babban table ɗin parlown wasu ƙananan gift boxes ne a jere, ta ɗauki lokaci tana kallon komai ba tare da ta ce uffan ba.
Lokacin ta ɗago kanta taga wani rubutun da ya ƙara ɗaukar hankalinta da kuma furucin da ya yi.
*WELCOME HOME WIFEY*
Bakinta ta buɗe kamar zata yi magana, amman ta kasa furta masa komai. Murmushin da yake kan fuskarsa ne ya ƙara faɗaɗa, koda ba ta yi magana ba, fuskarta ta nuna ya bawa da kuma jin daɗi, duk da ga mamaki nan rubuce akan fuskarta.
A hankali ya tako gabanta, hannunsa ya saka ya janyota jikinsa, ta baya ya rungumeta. Ba ta yi yunƙurin ƙwacewa ba, sai hannunsa dake kan cikinta da ta zubawa ido.
"Ya yi miki kyau?"
Ya raɗa mata a cikin kunnenta.
Kanta ta gyaɗa masa.
"Ina fatan kinyi farin ciki?"
Nan ma kanta ta gyaɗa masa.
Hannunta ya riƙe suka je wajen gift ɗin da ya tsara mata.
Tun kafin ya buɗe mata ta ce masa.
"Thank you Muhan"
Cikin sanyin murya.
Murmushi ya sakar mata. Ƙasa tayi da kanta. Hannunta ya riƙe suka fara taka stairs, ita dai kawai biye da shi take, zuciyarta na bugawa da sauri da sauri, suna ƙarasawa upstairs ya tsaya a ƙofar master bedroom, buɗe ƙofar ya yi ya kalleta.
Ganin ta tsaya cak tana ƙarewa ɗakin kalli, hannunta da yake cikin nasa ta zare, tsoro ne bayyane akan fuskarta, baya ta fara yi a hankali.
"Uhm.. ɗakina zan je"
Ta faɗa muryarta na ɗan rawa. Zuba mata ido ya yi na ɗan lokaci, sannan ya kalli cikin ɗakin ya sake kallonta, ba ya son ya takura mata ko kaɗan, mussamman da ya ga yanda take ta ƙoƙarin daidaita yanayinta, tunda suka baro gidan Ammien.
"Okay"
Ya ce mata ya na kallonta har lokacin, da hannunsa ya nuna mata ɗakin nata.
Ɗago kanta ta yi ta na kallonsa, ba ta yi tunanin zai ƙyale ta ba, kanta ta jinjina masa sannan ta nufi ɗakin da ya nuna mata, ya na tsaye har ta shige ta turo ƙofar, shima shiga ya yi ya rufe ƙofar.
Wanka ta yi da alwala sallar Isha'i ta yi, sannan ta saka kayan bacci riga da wando ta kwanta, sama take kallo tana tuna yanayinsu na ɗazu, taji a ranta zata basa dama, za kuma ta yi amfani da duk abin da Ammie ta faɗa mata in sha Allah, hasken ɗakin ta kashe ta ja bargo ta rufe jikinta, bacci ya na shirin ɗaukarta ta ji an buɗe ƙofar ɗakin, ba ta san sanda ta tashi zaune ba, ta na kallon ƙofar.
Rufe ƙofar ya yi ya nufi kan gadon, ba ta san sanda ta dire ta can ɓarin ba, tana kallonsa a cikin duhun gabanta na tsananta faɗuwa.
"Muhaan..."
FULANI
***