17. The Abortion
by @zainabb
TSAKANINMU
_United States of America._
_Bethesda, Maryland._
Ringing bell akayi a ƙofar su. Madina naji tace wa Gumsu "Go and get the door, baby"
Tashi Gumsu tayi ta buɗe ƙofar. Olivia ta gani tsaye a ƙofar tace "Hey"
"Hey" Olivia ta amsa "Is your mom around?"
"Yes" Gumsu ta amsa mata se ta ɗaga murya tace "You've a visitor here"
"Get her in, Gumsu" Madina itama tace da ɗaga murya domin Gumsu taji.
Shigowa da matar Gumsu tayi ta zauna a living room ita kuma ta wuce ɗakin ta.
Madina ta sauko ta taho inda matar. Bayanin kanta matar tayi wa Madina , Madina tace ta gane ba 3 houses away from each other suke ba.
Nan take tun kafin ta fara faɗa wa Madina abinda ya kawo ta idanunta suka cika da hawaye. Hannuwan Madina ta riƙe ta fara magana.
"I want you to help me, doctor"
Gyaɗa kai Madina tayi tana kallon ta.
"I have been married for 13 years with my husband. We met in high school and immediately after our high school, we got married to each other"
"I have two beautiful kids with him and I'm pregnant with my third right now"
"He was everything I could ask in a man , he was my happiness" tace tana kuka "But not anymore___ because I caught him in his car cheating. I saw him with someone and they were doing it right before my eyes. I couldn't ___the scene is still in my head and eyes, vividly. I'm so wrecked"
Sosai Madina taji tausayin ta ta aza kanta akan laps na Madina tana kuka.
Daidai lokacin Hamdan ya sauko daga home office nashi ze ɗauka ruwa. A daidai lokacin kuma ta ɗago kanta ta dena kuka tace wa Madina "I don't want this pregnancy. I want to abort it and I need your help for that seeing you're a doc"
From behind Hamdan ya kalle su su biyu ya ɗan haɗe girar shi guda biyu se kuma ya ji Madina tace "I'm sorry you had to see your husband and someone in that act. And about your abortion. Don't worry about it, I'll see what I can do about it, Olivia"
"You promise?" Olivia tace tana kallon Madina da desperate eyes
"I promise" Madina ta amsa tare da squeezing hannun ta. Hamdan wucewa yayi ko juyowa be yi ba.
Bayan sun gama magana Olivia ta tashi zata wuce and Madina see her to the door ta dawo ciki.
A house office na Hamdan ta tafi.
"You have been working all day , Hamdan"
"I got to, Madina"
"But are you done? Let's go to our room" tace ta rike hannun shi ya tashi ya rufe system nashi suka wuce ɗakin su.
"So you were going to help abort someone's child?"
Taji tambayar daga Hamdan.
"Wha___No__no, i only said I'll see what I can do"
"But you were promising things, Madina. So kike ki shiga gaba ki zubar wa wata ciki ki sa kanki a matsala? Idan mijinta yayi suing naki fa? Kina da labarin kina iya rasa licensed naki?"
"No one will know about it, Hamdan" Madina tace mishi cikin sanyin murya da tausayi ga Olivia
Wani irin kallo ya mata ya rufe walk-in-closet nashi yace "Kin mance ana samun complications a wurin zubar da ciki? What if she bleeds to death? You'll be cooked in this country, Madina"
"She caught her husband and someone doing it in his car" she tells Hamdan emotionally
Matsowa yayi kusa da ita a bedside yace "I didn't ask you that. I'm here right before you telling you how dangerous it is to do what you promised"
"I'm a doctor fa, idan ban taimaka ba, wa ze yi, Hamdan?"
Ranshi ne ya ɓaci saboda yana nuna mata nan, amma chan take kallo. "Zubar wa wata ciki taimako ne?"
Itama Madina nan take taji haushi tace "Na faɗa maka fa abinda mijin ta ya mata. Ya kake so ka kawai duba irin abinda take son yi kana nuna makanta ga irin cin mutuncin da mijin ta ya mata? Wannan adalci ne?"
"I told you, I'm not asking you for what her husband did to her. I want you to see how grievous it is to help in aborting someone's child"
"Then why don't you see what the husband did?" Madina ta ƙara faɗa cikin faɗa saboda yanda take jin haushi kuma take cikin fushi
"Ko ni aka aikata irin wannan abun akaina, kuma ina ɗauke da ciki, zubar wa zanyi kuma na bar auren nan tunda ba dole ne ba. Ya an dake ka kuma a hana ka kuka? Da wanne zata ji to?"
"Oh! Yanzu kika faɗi abinda kike so ki faɗa tun ɗazu. Gani kike nima ina kusa da miki abinda aka mata ne?"
Tashi tsaye Madina tayi daga bedside tana kallon Hamdan cikin ɓacin rai tace "Yaushe kuma nace Hamdan ze yi irin wannan abun? Kar fa ka fassara min magana ta akan abinda ba shi nake nufi ba"
"Me kike nufi da har zaki bada misali da kanki? Akwai wani namiji da kike aure bayan ni ne da zanyi tunanin bani kike nufi ba? Daa misali kike son badawa, da kin kama sunan wata amma ba dai kiyi magana akanki ba"
Muryar ta ahankali take magana amma cikin ɓacin rai kuma idan kana saurare zaka san ɗaga murya ne take saboda ba wannan ce muryar ta ba tace "Da kai nake, Hamdan. Faɗa min, are you immune to cheating on me ne? Can't you do it?"
"Yes, I said so" he smiles bitterly "That's what you've been thinking of me for the 17yrs we spent as couple. And it's good you came open about it"
Haushi sosai Madina taji saboda yana fassara mata maganganu ta yanda ba haka take nufi ba kuma yasa ta faɗin abinda ba shine a cikin ranta ba.
Fita tayi ta bar mishi ɗakin harda banging ƙofa.
Ƙofar ɗakin yake kallo yana tunanin irin maganganun da Madina ta faɗa mishi. Zama yayi a couch ya ɗaura hannuwan shi a gefen kanshi yana tapping ƙafar shi a ƙasa.
He was just trying to call her out on this abortion and she was just blowing things out of proportion. And who does that? he's only trying to protect her.
A stairs ta haw ta koma ɗakin dake next to na Gumsu.
Kwantawa tayi akan gado bata san lokacin da ta fara kuka ba. Tana nan tana kuka aka fara ruwa.
Hamdan kuma na main ɗakin su yana ta tunanin ta.
Hawayen ta ta share ta shiga bathroom ta wanke fuskar ta. Bayan ta fito daga bathroom ta fito ta zauna a kujera tasa hannuwan ta duka tayi tagumi ta kuma buɗe ƙafafuwan ta daga zaunen da take.
A ranar da aka ɗaura mata aure, kafin akai ta gidan Hamdan a Abuja, abokiyar zaman maman ta, saboda itama tun tana yarinya ƙarama ta rasa mahaifiyar ta, take mata nasihar cewa kowane irin faɗa kika yi da mijin ki, kada ki taɓa bari saboda wannan saɓanin da kuka samu yasa ku kwana a mabanbantan ɗaki. Ta ƙara faɗa mata kada ta yadda tayi bacci ita da mijinta suna fushi da juna se de idan babu yanda zata yi, tayi iya kokarinta amma sun kasa shirya kansu.
Hawaye taji sun zubo a fuskar ta saboda ganin take wannan nasihar da aka mata, ita ta tauye mata wasu abubuwa da take son yi a gidan ta, kamar koda sun samu matsala da Hamdan, dole su kwana a daki ɗaya saboda itace a kodayaushe take barin ɗaki idan sun samu matsala amma shi baya taɓa bari. Kuma duk yanda suka samu matsala dashi, bata so suyi kwana suna fushi da juna kuma shima yana kokarin danne fushin shi ya bawa zuciyar shi haƙuri su shirya without them sleeping while angry at each other.
Hawayen ta ta share ta tashi zuwa ɗakin su.
Tana murɗa ƙofa Hamdan ya ɗago kanshi yana kallon ƙofar se gata tayi appearing.
Shigowa tayi gabaɗaya ta wuce bathroom tayi wanka. Bayan ta fito ta shirya cikin kayan baccin ta ta dawo ta kwanta akan gado ba tare da sun cewa junan su wani abu ba.
Ya jima zaune a couch kafin shima ya tashi ya shiga bathroom yayi wanka ya fito ya shirya ya kwanta a gado. Ita ta bashi baya amma shi bayan nata ya maida gaban shi.
Idanun ta na buɗe tana jin kamshin turaren shi. Idanun ta se sun cika da hawaye amma ta danne taƙi bari su fito.
Sun kai minti goma a haka babu wanda yayi magana. Chan Hamdan ya kai hannun shi a jikin ta se ta kwaɓe hannun shi, ya ƙara kaiwa ta ƙara kwaɓewa, ana ukun yace "Madina, stop this" Ƙyale shi tayi bata yi komai ba ta rufe idanun ta.
"You made me angry. Did you know?" she tells him
"I'm sorry"
"Bayan ka gama ɓata min rai" ta faɗa mishi
"Ke kika faɗa min, idan mutum ya ɓata maka rai ya baka haƙuri, haƙurin da ya baka yana iya goge maka duk ɓacin ran da ka samu. You told me how powerful a simple 'I'm sorry' can be"
"Okay, you want to tell me I was lying?"
"Ban faɗa ba, Madina. Kar ki sa min magana a cikin baki"
Shiru tayi ba tace komai ba.
"Turn around please Madina"
Shiru bata juyo ba.
"I said please"
"Okay, for the sake of please" ta faɗa ta juyo da dukkanin jikin ta.
Kwaikwayon ta yayi se ga Madina na dariya.
"Maybe you're using charms on me, Hamdan, and the time I catch you, you won't be happy with what I'll do to you"
"What can you possibly do?"
"I told you!"
"What is it that you can do to me?"
Raɗa tayi mishi a kunne and he smiles ya jawo ta a jikin shi and he pecks her forehead.
"Let's get a little wild today" he tells her and Madina gives out a soft giggle and she holds him tightly.
Da safe suna shirin zuwa wurin aiki a kitchen take tambayar shi. "Me zan faɗa wa Olivia?"
"Who?"
"The woman that came yesterday"
"Ohh! You tell her that you'll refer her to a clinic"
"I'll. Thank you. I love you and I'm sorry for what happened yesterday"
"Se yau zaki faɗa sorry? To ki jira amsar i love you naki zuwa gobe"
Dariya Madina tayi ta kai mishi dukan wasa a kafaɗa.