RU'UYAA (The dreams we never lived)
50. ...never want him to let go...🖊️
by @autum17
'' Abeedah...'' ya kira sunana da laushi...sai hawaye suka fara sauka daga idona ɗaya bayan ɗaya
'' b..bana so naje ko ina,dan Allah ka barni...'' na ƙarashe maganar tare da sakin wani sabon kuka. Ya zauna daga baya na murya a lallashe yace '' faɗa min,meya faru? wani yace maki wani abune?" share fuska ta nayi na tashi zaune nayi ƙasa kaina. kallon shi yayi min nauyi sai nake wasa da yatsuna
'' UHM?" Ya riƙo hannu na, girgiza kaina nayi har lokacin ban kalle shi ba '' bana so in tafi...dan Allah...'' nayi nesa dashi kaɗan
Cire hular shi yayi ya ajiye gefe
'' then I will stay with you!" Ba shiri na kalle shi,ya lumshe idonshi a wani irin slow na tabbatar wa...sai naga ya ƙaramin kyau...duk yafi sauran mazan gidan kyau.amma na yau daban ne,lips ɗinshi kamar ya shafa lipstick, idonshi kuma kamar ya shafa kwalli da mascara lashes ɗinshi sunyi zaƙo zaƙo, hancin shi dogo kamar pencil...he's so perfect... ƙamshin turaren shi na haifar min da wani irin feelings a zuciya da gangar jikina...hannun shi mai taushi yasa yana share min hawaye na...na sadda kaina ƙasa
''kizo mu tafi,idan mun dawo zan kaiki wani wuri..we won't come home for sometime...'' na tsaya tunani...ina wasa da ƙarshen rigata...bana so in fita saboda duk abu ɗaya ne,dole sai ina tafiya ina ƙare hijabi na...amma kuma bana so yayi missing sallah saboda ni...tashi nayi shima ya miƙe ya ɗauko hijabi na dake yashe can gefe ya samun da kanshi...
Ya ɗauka handkerchief mai taushi ya share min fuskata...yana komai ahankali da kulawa...
Tare muka fito daga ɗakin..ya rage sauri dan yayi matching taku na... Da kowane taku sai zuciyata ta buga kamar in koma...dakewa nayi har muka isa motar shi...na zauna gefenshi tare da sa nawa seat belt...
Badaɗewa ba muka iso masallacin har an kusa fara sallah,sashen mata ya tsaya na sauka sannan ya wuce sashen maza...
A sanyaye na shiga Masallacin na zauna daga baki baki... minti biyar bayan nan aka fara gyara sahu.zuciyata empty babu abinda nake ji a ciki...bayan an gama sallah nice ta farkon fita daga masallacin ina tafiya a hankali na isa wurin motar Khalil na jingina haɗe da lumshe ido hasken ranar ko damuna baiyi ba.
'' har kin iso...'' ya buɗe motar ya ajiye babbar rigarshi ciki. Na kaɗa kai .ina nan tsaye wasu maza su biyu suka iso suma sun ɗau wanka,da alamu ƙawayen shine. Suka kalleni suna murmushi suna cigaba da magana tsakanin su...nikam koda babu abinda ke damuna ba murmushin zan musu ba.IB ya fito daga motar
'' shine baka gaya mana ka samu Madam ba!"wanda ke saye da shadda brown ya faɗa yana naɗe hannu a ƙirji... murmushi Khalil yayi ya kalleni batareda ya basu amsa ba ya zagayo ya buɗe min seat ɗin baya na zauna
'' well,dana faɗa maku the suprise would have been ruined right?" Ya jefa masu mukulli.wanda ke saye da shadda milk color ya cafe. suna dariya dukan su .. Khalil ya shigo ta ɗayan gefen.su biyun suka zauna gaban mota..
suna cigaba da hira tsakaninsu..nikam nayi gefe da kaina ina kallon waje
'' bazaka gabatar mana da Madam ba?" Mai shadda brown ya faɗa
'' manta dashi Umar,kasan shi da shegen nawa!" Ɗayan mai saye da shadda milk ya furta.Khalil baice masu komai ba yana shafa gemun shi yana ta murmushi har suka ja motar muka fita...ko sau ɗaya ban motsa baki na ba da sunan magana
'' she's not my Madam happy!" Khalil ya faɗa daga ƙarshe,yana ɗan kallon gefena
'' Oh...hakane kaji shi ko Adnan" Umar yayi maganar yana taɓa wanda ke tuƙi... adnan burki ya taka hakan yasa dukan mu munyo gaba harda ni dake kallon waje
Da sauri Khalil ya riƙo kafaɗuna tare dasa hannun shi gaban goshina
'' careful man!" ya harare su '' yi haƙuri wancan driver'n ne ya shigo gaban mu...''
'' Hmph!" Khalil ya zaunar dani da kyau '' kina lafiya?" Ya tambaya da damuwa a fuskar shi..na gyaɗa kai
'' awwn...ka gani ko so much affection!" Umar ya faɗa yana cupping fuskarshi kamar mace
'' IB you're in love just admit it!" Adnan ya faɗa shida Umar suka sa dariya ,share su Khalil yayi...
Sai can kuma ya nuna min su,'' they're my friends,Umar da Adnan...'' juyowa sukayi briefly suna kallona da yake mun kawo traffic '' and she's Abeedah!" Ya furta kamar an matse bakin shi ganin sun kafe ni da ido
Sukayi dariya '' ka shinshino wani abu Umar?" Adnan da Umar suke shinshinar motar...mamaki nake ko mai suke ƙoƙarin shinshinowa can suka haɗa baki ''Ohhh.. it's jealousy...'' suka fashe da dariya
gyara zaman shi Khalil yayi '' ba haka bane bafa!" Ya shafa kanshi..sun dai cigaba da zolayarshi...ni har lokacin ban saki raina ba
can muka kawo wurin wani park inda ake carnival...ga mutane da yawa ga tents..da sauran abubuwa harda wasar doki...duk na hango ta cikin glass
Parking sukayi, suka fita Khalil ne ya zagayo ya buɗe min ƙofa na fito...
Ina tafiya a hankali..bugun zuciyata har kunne na...tsabar yanda hankalina yake a tashe saura kaɗan in faɗi..da sauri Khalil ya taro ni jikinshi
'' careful!" idon mu ya haɗu '' na gode..'' na furta slowly ya tsayar dani da kyau
'' awwn..so Romantic!" su biyun suka haɗa baki kamar mata...anya wa'yannan...
'' bana son sa ido!" Khalil ya ɓata fuska...sai ya juyo gently gefena ''.ina kike so mu tafi?" Nuna mashi wurin wasan doki nayi,muka tafi can ɗin...yan mata da yawa sun ɗau wanka cakuɗe da maza sai ihu ake ana cheering wa masu wasan dokin amma ni ko ganin su banyi sai dai naji anata kiran DI CAPRIO' kawai...nake mamakin ko waye shi?
Wayar Khalil tayi ringing hakan yasa yabar wurin bayan ya faɗa min kada in ɓace cikin mutane...
Ina ƙoƙarin kutsawa wani gaye ya jawo ni baya da ƙarfi ya wurgar na faɗi ƙasa.. ido na suka ɗuri ruwa..da sauri na tashi kada a tattake ni
wurin wata bishiya na nufa nayi zaune ina kallon wasannin da ake...rana ta fito da haske sosai tana bugun green grass ɗin dake wurin sai yanayin yake min kamar garin ya zama faint green
Share hawaye na nayi na zauna saman bencin dake wurin ihun masu cheering wa masu wasan dokin ya karaɗe wurin...can gefe kuma akwai wani abu da aka maƙala wa ice da ake halbawa da kibiya..babu mutane da yawa wurin kuma nima ban iya halbin kibiya ba dana gwada
Can gaba anyi displaying kayan wasa na yara wurin ya cika sosai...haka haka abubuwan suke jere...
Can na hangi wannan ƙatom abun mai Rollin kamar taya ferris wheel 🎡...
Da looptie loop➿ da jirgin nan mai gudu da sauri...nayi murmushin kaɗaici dasu Jay d na nan da babu abinda zai hana mu hawa a tare...
'' kina so kije can ne?" Khalil ke kallona da murmushi..gyaɗa kai nayi
'' talk to me,don't gesture!" ƙasa nayi da idona hawaye suka fara ɗiga ya sauke numfashi
'' yi haƙuri, taso mu tafi...'' girgiza kaina nayi '' okay then,I will pick you up!" Ya shiga tattare hannun rigar shi da sauri na miƙe ina gaba yana bina baya har muka iso
Matan dake wurin suka kafe shi da ido wasu gungun ƴan mata suna kallon shi suna dariya kun dai san abun nan da yan mata suke yi...
Haushi naji yana kamani...na dake har ya siya ticket biyu ya bani ɗaya naga yana kalle kalle a karo na farko nace '' me kake nema?" Ya kalleni tare da shafa kanshi '' ehmm,i can't do this...''
waro ido nayi '' tsoro kake ji ne...''girgiza kanshi yayi da deep voice yace '' kawai dai this is too childish..bari in kira wani...''
yayi baya tare da kara wayar shi a kunne yayi magana kaɗan kafin ya katse kiran, murmushin kunya ya sakar min daya ga ina kallonshi...naydariya '' waih ashe dama kana da tsoro?" ya cigaba da shafa kanshi ba tare da yace komai ba..yan matan nan kuwa kamar zasu cinye shi da idonsu..ba daɗewa wurin ya ƙara cika da hayani ana kiran DI CAPRIO'...na waiga amma banga kowa ba na cigaba da kallon gabana ina wasa da ticket ɗin hannu na
Badaɗewa naji tsayuwar mutum kusa damu...iska ya dinga kwasar ƙamshin turaren shi zuwa hancina koda zan ɗago naga Roman saye da baƙaƙen kaya casual kamar yau ba sallah ba. Face stoic
Naji zuciyata ta buga da ƙarfi
'' Oh Rome...kitten tana so tayi wasa a ferris wheel and looptie loop..ina ɗan da abinda zanyi attending pls be with her..'' da sauri Khalil yayi maganar kafin Roman ya samu damar amsa mashi yabar wurin.. har zai bi bayanshi wasu yan mata suka ƙaraso
'' mr CAPRI dan Allah zamu iya yin photo da kai...?" Roman na goga haƙoranshi a baki yace '' sure!" Yan mata suka wani tsaya kusa kusa dashi.
'' lokaci yayi fa!" Na faɗa da takaici ina nuna mashi mune akan layi
'' toh ki tafi ke kaɗai!" Yaban amsa yana cigaba da ɗaukar hoto da yan matan... raina yayi baƙi...barin wurin nayi gaba ɗaya
Ina tafiya like a lost lamb ina wuce masu ɗaukar hoto da masu yin video..ƙuncin wannan sallar daban yake dana koda yaushe... Wannan ba duniyata bace...wurin da ake halbar kibiya na isa na ɗauki kibiyar bawai dan na iya halbawa ba,but anything to keep my tears from spilling..naja numfashi as the tears roll on my cheeks like beads hannu na na rawa
Kamar in saki kibiyar in kurma ihu
Sai na saita inda tsinin na kallona cikin rashin sani..idan na halba tsaf mashin zai cake ni amma waya damu? Na share fuskata
Na ɗaga hannu na zan saki arrow'n naji tsayuwar shi baya na tare da ɗaura farin hannun shi saman nawa ya gyara saitin arrow'n a hannuna yaja hannun nawa Ni kuma naja arrow'n...zuciya ta babu abinda take sai uban gudu... muryar shi take shiga kunne na like the sweetest melody...
'' don't be stiff.. relax...saki...'' saki nayi absentmindedly..a mamakina ya daki target na juyo dan in kalle shi,our faces were so close na yan daƙiƙu na manta da damuwar da ranar yau ta haifar min,na manta da duniyar baki ɗaya...a wannan lokacin,ni da shi kaɗai ne...
Ɗage gira yayi hakan ya ƙara mashi kyau ba kaɗan ba kamar fantasy characters
'' da matsala ne?" Ya tambaya...da sauri na ɗauke kaina tare da matsawa daga kusa dashi...
Sai ga wasu maza su uku saye da baƙaƙen kaya..shugaban su na ma Roman mugun kallo yana mokaɗe mokaɗen wuya yace ''you won the horse ride, come to the arena and we will beat your sorry butt! '' muryarshi ba daɗi ko kaɗan... idonshi jawur...suma na bayan shi sai huci suke...
ƙasa da idon shi Roman yayi da murmushin gefen baki yace '' we'll see then!" Ya riƙo hannu na muka bar su tsaye..na kalli hannunsa dake riƙe da nawa...i don't ever want him to let go...munayin nesa dasu ya sake ni immediately the void in my heart opened...
wurin wata wasa da ake kira bowling ya kawo Ni,abun a ido kamar da sauƙi sai mutum yayi ƙoƙarin yi yaga ashe ba haka bane...kafin in sani murmushi ya wanzu a fuska ta..ya kaini wurare daban daban harda wurin cin abincin wurin amma shi bai ciba duk da nayi mashi tayi...
Mutane sai zuwa suke suna gaishe shi
'' dama kaine CAPRI SUN?"
'' CAPRIO'!" Ya gyara min yana juya ido
'' ai duk ɗaya ne! dama kana da wani suna bayan Roman?"
'' hmm... surname'' ya amsa a gajarce
'' Roman Di caprio?" Na sake tambaya
'' yeah...'' na taɓe baki..wai CAPRIO' juice ɗin CAPRI SUN na tuna na fara dariya
muka zagaye wurin har muka koma wurin looptie loop ɗin nan...ashe rayuwa da Roman akwai daɗi...kodai addu'a tace ta karɓu? Na kalli gefenshi..he's so kind to me... kuma gashi kusa dani..so close
ɗan ƙaramin farin ciki naji daya ɓace da sauri saboda wani tunanin daya faɗo raina...'' put on the seat belt..'' ya nuna min.. Gyaɗa kaina nayi na saka seat belt ba daɗewa kuwa ya tashi...wani irin jiri naji
ban san sanda na ƙanƙame Roman ba,hannu cakume da gaban rigarshi..fuskata a gefen wuyanshi...ina ta ihu...
Bawan Allah duk ya ruɗe sai rarrabar ido yake....abun na tsayawa na sauka da gudu na koma gefe sai amai...
ruwa ya karɓa ya miƙo min,'' na gode!" Na furta bayan na kuskure baki na wanke fuska..
'' should have told me ..'' ya faɗa yana girgiza kanshi
''.ai wannan ne karo na farko dana hau '' na bashi amsa
'' hmm..'' yayi gaba hasken ranar data kusa faɗuwa ya faɗa bayan shi...dogo ne shi sosai, yana tafiya a nutse kamar babu abinda ya dame shi a duniya..amma,he looks lonely to me...
Sai wurin ƙarfe bakwai muka koma gida..shigewa ɗakin mu nayi na canja kaya nayi sallar Isha'i,muka gaisa dasu Mama kafin na kwanta...
Tun daga wannan ranar rayuwata ta sauya sosai...bana fitowa bana yawan magana..kullum ji nake kamar kada safiya tawaye kamar mu cigaba da zama da asuba kada haske ya mamaye ko ina...bana son tashi daga gado...
Dan na riga da nasan ranar zata zo ta wuce ne da nauyi mai wahalar ɗauka a zuciya ta...
Kullum alla alla nake dare yayi...i was so miserable...
Bayan sallah da kwanaki muka koma makaranta domin zana jarabawar NECO...
Drop your comments like and share ..