RU'UYAA (The dreams we never lived)
51. ...So much for nothing...🖊️
by @autum17
51. ...So much for nothing...🖊️
Na ɗauka wannan jarabawar zata kasance ta daban,duk wannan nauyin zuciyar da nake fama dashi idan muna jarabawa bazai zoba,i was gravely mistaken...Dan baƙin cikin dana ƙunsa a wannan jarabawar yafi na waec...
Allah yasa muna haɗuwa dasu Jay d akai akai ita take kwantar min da hankali.ya xanyi da raina idan wata rana akace babu ita a tare dani? jarabawar da sauri sauri muke yi ba kamar waec ba da sai mun kwashi kwanaki kafin muyi wata paper
Kuma a wannan jarabawar ma malamai suna karɓar cin hanci ..muda bamu biya ba sai su dinga rubuta sunayen mu da nambobin mu a paper daban na rasa dalilin hakan.
Yau bayan mun gama rubuta I R S da ƙarfe huɗu da rabi ina tsaka da tafiya naji ana kiran sunana har sai dana sha kwana na tsaya.macijin sari ka noƙe ne saye da matsatstsun ƙananan kaya...dama na lura sai wani kallona yake bini bini a exam hall
''kin iya tafiya da sauri. inata kiranki baki jiba'' yayi tsaye gabana yana haki kamar wanda yayi gudun marathon.ɗauke kaina nayi daga kallon shi dan haushin shi nake ji bana wasa ba
Tashi tsaye yayi da kyau da wani makirin murmushi a fuskar '' naga kamar da kanki kike rubuta jarabawar ko?" Juya idona nayi
'' uhm...''na amsa a gajarce
'' wow that's good kin burgeni wallahi.haka ya kamata ace students sunayi.they should learn from you!..." ya cigaba da zuba kamar redio nikam sai cika nake ina batsewa..na gyara hijabina
'' ina so in tafi!" Na furta ganin baida burki...kallona yayi da shegun idonshi kamar na mujiya yace '' toh muje in taka maki...'' girgiza kaina nayi
'' ka barshi kawai na gode...'' mutumin nan bai jini ba ya biyo ni yana cigaba da zuba
'' wato a gaskiya Abeedah bazan ɓoye maki ba,ke kyakkyawa ce ta gaske har kin fi yar uwarki kyau ga wanda ke da ido!"burki naci ba shiri na juyo na kalle shi rai a ɓace '' Malam dan Allah kayi tafiyar ka nima nayi tawa!" Na faɗa a ƙufule kafin nayi gaba
Da sauri ya cafko hannu na '' haba ai ban__'' fisge hannu na nayi
'' WAI MEYE HAKA!!!" na ɗaga murya tare da zaro mashi gray eyes ɗina da suka ƙara duhu dan tsanar shin da nayi ta sake tasowa bayan ya taɓani...yaja baya kamar ya tsorata
'' Abeedah ni kike ɗagawa murya?" Wani dogon tsuki naja...can ya ƙara matsowa zai cigaba da magana na ɗaga mashi hannu '' bana so inji koma meye zaka faɗa...ka barni kawai!"
Na Juya zan bar wurin idona ya sauka cikin na Khalil dake jingine da motarshi mukulli a hannu babu fara'a a fuskar shi...dum! dum! naji gabana ya shiga faɗuwa...
Malam Saminu yake bina ''.ki tsaya mana...magana nake so muyi..'' ya sake riƙo hannu na...Khalil kamar iska ya matso ya fisge hannunshi daga nawa...sai da macijin sari ka noƙe ya kusa faɗuwa
Idonshi a waje yace '' Malam meye haka? Ya zaka shiga tsakani na da ƙanwata?" Kallon da ban fahimci ma'anar saba Khalil ya jefa min,na haɗiye yawu...
Sai macijin sari ka noƙe yayi ƙoƙarin zagayowa bayan Khalil ya riƙe hannu na,wani wawan naushi Khalil ya sauke mashi a ƙirji...macijin sari ka noƙe ya saki baki da ido da alamu ya kasa numfashi
'' wayyo Allah na...Mallam,kasan ko waye ni kuwa?" Yayi maganar yana haki hannun shi dafe da ƙirjinshi...
Collar shi Khalil ya cakumo yana kallon shi cikin ido yace '' i don't care who you're,stay away from her!" Ya nuna ni,sannan ya wancakalar da macijin sari ka noƙe gefe ɗaya...ya juya ya shiga mota...sum sum nabi bayanshi...gefen shi na zauna nasa seat belt ya fara sharara gudu kamar yanda Roman yake...na tsorata sosai...
muna kawowa wurin traffic baki na rawa hawaye suka ciko idona na fara mashi bayani batareda ya tambaye niba... handkerchief ya zaro daga aljihun shi ya share min hawayen '' don't worry, it's okay!"
Kwanakin jarabawar suka zo suka wuce amma nauyin da suka zo dashi ya cigaba da zama a zuciya ta kamar wani ƙaton dutse da zuciyata ta gaza ɗauka...
har yanzu ban dena ji inama ace kada safiya ta waye da asuba ba,duk na shiga damuwa akan result ɗin mu duk da Khalil yace kada in damu amma na kasa dena damuwa...Roman ma yayi wahalar gani...
na cigaba da addu'oina da kuma sadaƙa ina roƙon Allah yasa in cinye jarabawar...ina magana dasu Mama akai akai sannan ina zuwa gida weekend
A cikin watan August result ɗin mu zai fito...na tsananta addu'a da komai ma, nake iya ƙoƙarina wurin ture damuwa da fargaba... Finally ranar duba result taxo,da yawa daga cikin yan gidan da masu aiki fatan su shine Allah yasa mun faɗi
Result ɗina aka fara dubawa amma yaƙi fitowa sai ayi ta cewa server timed out..ko missing page...tun ina yi da daɗin rai har hankali na ya fara tashi ga bugun zuciya ta dake haifar min da ciwo da gajiya a sauran sassan jikina
hawaye suka taru a idona..Khalil yake ta kwantar min da hankali..amma hankalina yayi nesa da kwanciya...
can dai aka ajiye nawa aka duba na diyaam...result ɗinta yayi kyau sosai daga A sai B ko C babu..Diyaam kamar zata zuba ruwa ƙasa tasha..na taya ta murna sosai...duk da banga nawa ba...
Mun kwashi kwana da kwanaki ana gwadawa kafin dai Khalil yace zai tafi cyber Cafe ya duba min...babu abinda zuciya ta take sai tsananin bugu
Yan gidan da suka ji Diyaam taci jarabawar ta,sai suka mayarda miyagun addu'oin su akaina Allah yasa kada inci tawa...
Maganganun suna tayar min da hankali ba kaɗan ba...da daddare bayan mun gama sallar Isha'i Khalil ya kira ni zuwa sashen shi,sanda na isa yana cikin ɗaki yasa na zauna ina jiran shi a parlor sai ga Roman ya shigo shima,kamar koda yaushe da baƙaƙen kaya
Can gefe ya zauna ya shiga danna wayarshi kamar bai ganni a wurin ba,can kuma ya fara magana da Yaren su a waya...
Bayan mintuna kaɗan Khalil ya fito saye da riga mara hannu da guntun wando hannunshi riƙe da paper dana ke tsammanin result ɗina ne... fuskarshi ba walwala...nan naji kamar jini na ya fara hawa...
shima wani gefen daban ya zauna yayi min alamar inzo...jiki a sanyaye na tashi ina tafiya ɗaya ɗaya a mugun tsorace...My mind was all over the place
gefen shi ya nuna min in zauna,na zauna kaina ƙasa ina wasa da yatsuna...hawaye sun samu mazauni a idona...
Paper ya turo min gabana...hannu na rawa na jawo bayan na karanto duk addu'ar data zo bakina kafin na buɗe idona dake lumshe na sauke akan grades ɗina. numfashi na ya ɗauke...bugun zuciya ta ya tsaya kafin na fara hyperventilating,jikina ya fara rawa... inata motsa baki amma na kasa cewa komai...
Roman da Khalil suka kafe ni da ido...hawaye wasu nabin wasu
'' Abeedah!!" Kamar jira nake na rushe da matsanancin kuka tare da wurgar da result ɗin.. Khalil ya matso kusa tare da riƙo hannu na
'' I...i have.. worked so hard ...na tabbatar...taya....how. ..taya...na faɗi jarabawa ta....yanzu sai...maimaita...yan ajin mu zasu barni...su Jadeedah..wayyo Allah...ya zanyi...zuciy...Ahhhh!'' nake sambatun tsakanin kuka da numfashi kamar zautacciya,na fisge hannu na daga na Khalil na riƙe kaina,nake ji kamar komai ya tsaya min..taya?...duk na ruɗe na shiga tashin hankali... jawo ni jikinshi Khalil yayi yana lallashina harda zufa a goshin shi,shima ya damu sosai'' kada ki damu idan baki ci waec ba akwai neco...''
girgiza kaina nayi murya a shaƙe nace '' idan fa na faɗi NECO ɗin itama...bani da sa'a, addu'oina....su Hansa'u... addu'ar su ta karɓu...meyasa hakan ke faruwa dani koda nayi iya ƙoƙarinaaaaa!!!!" Na faɗa tare da sake rushewa da kuka... numfashi na ya fara fita da ƙyar...tsabar baƙin ciki nama kasa cigaba da kukan, hawaye kaɗai ke sauka... ruwa Khalil ya zuba min a cup da ƙyar na sha
'' no,bazaki faɗi ba...and you're not unlucky don't say that...and I'm with you kada ki damu'' ya riƙe fuskata a hannunshi..lumshe ido nayi ina juya kaina...duk da ina ƙoƙarin tilasta kaina in yarda da abinda ya faɗa..ban faɗi NECO ba amma zuciyata ta yanke hukunci...
Naji kunya ta rufe ni ta gefen ido na sake kallon result ɗin
Math F9
English F9
Government F9
Economics E5
Literature in English D7
Islamic studies C6
CivicE5
HausaD7
PHE D5
wani irin tuƙuƙi zuciyata take tambayoyi na tafasa daga ciki na...kamar wacce batayi karatu ba... na tabbar da abinda na rubuta wallahi...subject ɗin dana tabbatar zan faɗi kawai shine math,the F9 was justified amma sauran subjects ɗin ko sama da ƙasa zasu haɗe ban yarda grades ɗina bane...
Can Roman ya miƙe '' talk tomorrow!" Ya fita sai lokacin ma na tuna ashe yana wurin..haɗiye kukan daya kawo maƙoshina nayi.. Khalil ya cigaba da lallashina sai wurin ƙarfe goma ya raka ni har ɗakin mu
Ina shiga na rufe ƙofar tareda cire hijabi na cikin duhu na isa bakin taga ina kallon waje, taurari sun cika sama,iska mai sanyi na kaɗawa a hankali...sai taune bakina nakeyi...
minti talatin nayi a wurin kafin na dawo na kwanta saman gado na lumshe idona...zuciyata da ƙwaƙwalwa ta suka shiga debate tsakaninsu sai dai dukan su suna a team ɗaya ne...meyasa bayan duk efforts ɗin dana sa,harda ƙin karɓar amsa dan kawai ina so in cinye jarabawar da kaina,me yasa na faɗi?da ace na biya an bani amsa da zan wuce kenan?
ranar dai ban runtsa ba dole bayan sallar asuba na koma na kwanta..wurin ƙarfe biyu su Mama suka kira suna tambaya akan result fashewa na sake yi da kuka
'' Ma..ma na faɗi jara...'' jefar da wayar gefe nayi batareda na iyar ba na cigaba da rera kuka...Mama babu abinda take faɗa sai Innalillahi wa inna ilaihi raji'una
tana ta lallashina cikin wayar haka ma Inna sarai da Anaam...bayan mun gama wayar Khalil ya shigo da abinci a hannun shi,da ƙyar naci bawai dan ina jin daɗin abincin a bakina ba...
Kwanakin da suka biyo baya suna ɗauke da wani irin duhu,nauyi da ɗaci gare ni...mutanen gidan ban san yanda akayi suka san na faɗi jarabawa ta..su Hansa'u harda zuba ruwa a ƙasa su sha...kenan tasu addu'ar ta karɓu ba tawa ba? basa bari in manta da wannan koda yaushe sai sun sake tunamin harda cewa '' wannan shine abinda zai cigaba da faruwa dake har abada!"
Ranar da akace NECO ɗin mu ta fito shiryawa nayi cikin riga da wando irin na indiyawa nasa hijabi ash color na wuce cyber Cafe dan dubawa..harda handkerchief na ɗauka...
Da kowane taku bugun zuciya ta ƙaruwa yake har na iso,akwai layi yasa dole sai dana jira wurin ƙarfe huɗu da rabi lokacina yazo
Paper da aka bamu sanda muke rubuta jarabawar na duba na copy details ɗina na shigar..da sauri result ɗin ya fito kowa dake wurin suka wani yi hah! Kamar nice ta farko dake da result mara kyau... wannan ma yafi WAEC ɓaci
Hakan ya ƙara sani a ƙunci na bar wurin da hawaye ina tafiya gefen hanya..iska na kaɗawa...naji kamar na dena jin ƙafafu na... zuciyar ma kamar babu a ƙirjina
Ina zan sa kaina? Idona sukayi ja suka ƙanƙance..nikam babu kalamai da zasu iya kamanta ɗacin ran dana shiga... yanzu yan ajin mu zasu yi graduating su barni... Jay d itama zata tafi makarantar gaba... zamu rabu...
ina tafiya iska na kaɗani...komai ya fitar min daga rai.. zuciyata ta sake tabbatar min dacewa da gaske fa banida sa'a komai zanyi babu abinda zai canja daga rayuwa ta...nake ji kamar in shiga coma ko in samu memory loss ko dai wani abu da zai taimake ni wurin rage raɗaɗin dake zuciyata
Ina tsaka da tafiya motar Khalil ta tsaya gefena,na cigaba da tafiya ta,da sauri ya iso ya riƙo hannu na,na juyo idona ya shiga cikin nashi..kamar wacce tasha wani abu ina murmushi hawaye na sauka daga gefen idona nace
'' addu'oina basa karɓuwa Khalil...ko mai zanyi abinda nake gudun ya faru kullum shi yake faruwa..bani da sa'a!!!!"
girgiza min kanshi yayi yana share min hawaye
'' it's not true... don't say that kitten!"jin shi kawai nayi.. wani irin rauni ya mamaye ni.. slowly yayi wrapping hannayen shi around me.. hugging me comfortingly...
'' we'll figure things out together...kada ki damu!" rufe bakina nayi kawai na dena kukan badan raɗaɗin dake zuciyata ya ragu ba....
Drop your comments like and share ..
((★Wa'yanda ke tambayar complete yanzu nake rubuta littafin
★Wa'yanda ke tambayar account number gashi nan a ƙasa don't come to my DM asking for it pls🙏
★idan banyi replying message ɗin mutum a Whatsapp ba pls banda kira send SMS...
★If you're not buying the book don't come
to my DM pls...
★Wayanda ke tambaya daga farko akwai shi a cikin links ɗin nan don't come to my DM
★Wa'yanda ke son yin comment zasu iya tafiya a shafina na Arewa pen suyi a can or you can get into the group..or Mi DM))
🌹 ❤️📖✨
***
RU'UYAA…📖
₦500 ne idan ya kammala zai koma 800
Biya ta wannan account ɗin ***..Salma Aliyu opay
Shaidar biya ta ***
Autumn writes 📖🖋️