SALMA ELM

3

by @hijjartabdoul06

*********Ko da aka fita break kwasar ƴan aji ta yi wanda ba su zo jiya ba wai su zo su ga sabon Malamin su dan be shiga ya yi musu karatun da aka ce ya je ya yi ba, wani malamin yaga ya shiga, shine ta kwaso su za'a je a ganshi, su je wai Malamin da baya dariya. Suna bayan staff room yanzu dake rana ta ɗan ɗaga. Suke leƙa shi idan sa a rufe yake yayinda sauran malamai suke cin abinci banda shi dake kan kujera.

"Kun san sunansa?

"Sunansa Mufeed".

"Shi wannan ɗin aka sawa sunann yara?

Maryam ta faɗa tana taɓe baki.

"Amma de sunan ya yi daɗi, Maryam bana son hassada".

"Ai bance be yi dadi ba".

Sake leƙawa ta ga Malaman har sun watse, suna me suka tafi ba su gan su ba. Sai shi kadai a wurin amma yanzu idan sa a buɗe yake. Tana juyowa taga babu su Maryam sai ita kadai sun kwasa da gudu sun shige aji. Maimaikon ta shiga ajin itama sai ta cigaba da leƙa shi. Idan ya ɗago zai kalleta sai ta yi saurin ɓoyewa tana dariya. Haka ta ringa yi a karo na ba adadi tana laƙa shi, abin daɗi yake yi mata yarda baya ganinta a duk sanda ya ɗago da kan sa.

Murmushi ta saki sosai tana ɗaga girarta alamar abin ya yi mata sugar, tana sake leƙawa kawai taga bayanan, hakan yasa ta fitowa dakyau taga to ina ya yi? Tana juyawa ta gan shi a bayanta. Da wani irin bala'in saurin ta juya masa baya gabanta yana faɗuwa sosai. Sai kuma a hankali ta juyo tana kallon sa tare da sakar masa wani shegen yaƙe. Yayinda ya naɗe a hannunsa a ƙirji yana kallonta.

"Sorry".

Ta faɗa a hankali tana kama kunnenta. Bata jira cewarsa ba ta zagaye shi da bala'in sassarafa tana tafiya ajinsu da kallo kawai ya bita yana girgiza kan sa. Koda aka tashi ita ce ta fara fitowa da gudu, shi de a saninsa ance masa ƴan ajin sune ajin sauka, kuma ya ga duk wayancinsu ƴan mata ne masu hankali masu ji da kan su, amma wannan kam ta fita daban acikin su ko dan ita ce ƙaramarsu be sani ba. Amma de tabbas akwai sauran hauka a cikin kan ta wannan kam.

"Dan Allah Malam Mufeeeed, ko zaka taimaka ka rage min hanya gidan mu ata can yake ba nisa ka ji? Na hau?

Ta faɗa tana ɗaura jakarta a machine ɗin sa, bata jira cewarsa ba, ta dafa kafaɗarsa ta ɗane machine ɗin nasa. Sai da ya kalli hannunta dake kan kafaɗarsa sannan ya kalle ta ta madubin machine ɗin sa. Anya ya taɓa ganin yarinya irin wannan yarinyar kuwa a cikin duniyarsa gaba ɗaya?

"To Malam na hau, mu je?

"Ke Maryam gobe muka dawo ki tabbatar sai na ci uwarki amma ba Umma ba".

Maryam ta ce, "Yoo akwai wata uwar da nake da ita banda Umma?

"Wannan matar Baban naki mai mugun hali da baƙin hali shegiyar wannan ita nake nufi, kuma ai uwarki ce...

Duka ta kawo mata da sauri ta ƙanƙame shi tana cewa, "Malam muje dan Allah zata dakeniiiik".

Ta faɗa tana sake ƙanƙame shi har ta taɓa ta.

"Dan Allah mu tafi, idan ba zaka rage min hanyar ba, sai na sauka, amma ka bari kowa ya tafi dan kar a dizgani".

"Sauka".

Yace da ita a takaice.

"Ehh ?

Be maimaita ba, haka be tafi ba.

"Ka ce na sauka? Wai yanzu kai Malam ko kunya sai ka sauke ni bayan na hau?!

"Sauka".

Ya sake maimaita mata a takaici yana haɗe fuskarsa. Taɓe baki ta yi kafin ta sake dafa shi ta sauko.

"Bakomai da sanin Allah".

Sai ga Ya Ibrahim ya zo zai wuce.

"My Heartbeat wait mana gani nan, ba ni ka zo ɗauka ba?

Sai da ya zuba mata harara sannan ya tsaya yana gaisawa da Mufeed. Suna kama sosai da shi da ita amma ya fita haske.

"Ya Ibrahim ina yini? Ya aikin? Andace? Ka samu aikin? Wanda irin position aka baka? Sannan ya yanayin aikin yake? Akwai kuɗi sosai da zaka siya min motar? Ka yi magana dan Allah".

"Kin bani damar na yi magana ne?

Murmushi ta yi masa, kafin a hankali ya gyara mata machine ɗin yarda zata iya hawa sannan ta dafa shi ta hau ya riƙe mata jakarta. Kafin ta ƙanƙame shi tana saƙalo da hannunta ta cikinsa ta yi lamo a bayansa yana jin sautin surutunta har suka ƙulewa masa. Hawan machine ɗin da aka yi ne yasa shi juyawa ya kalla wanda ya hau ɗin.

"Ya M muje".

Be yi magana ba suka ce a hanya suka haɗu da su ta tsayar da shi a wurin mai siyar da awara wai yunwa take ji.

"Kai Fahad wallahi gobe ka tabbatar sai na wuceka kasan ba'a ja da ni".

"Idan kin fasa wuceni, ni nace kar ki zo".

Ƙwafa ta yi zata yi magana Mufeed ya danna machine suka yi gaba.....

"Wash Dadda nagaji".

"Sannu kinji? Bari na zubo maki abinci sannu".

Daada dake kishingiɗe ya miƙe yace.

"Ki kawo mata fura da mai sanyi ki bar wannan abincin ba ci ba zata yi tunda ga fura nan ko?

"Ehh Daada".

Ibrahim ne ya shigo da sallama yana miƙa mata jakarta.

"Kika sake barmin jaka a jikin machine ki tabbatar a wurin zan barta ko na yi sadaka da ita wawiyar yarinya kawai".

"Ban hanaka zagar min yarinya ba ne Ibrahim?

Zama ya yi yana zare necktie din wuyansa be yi musu magana ba.

"Ina tawa furar?

"Ka ce zaka sha ne?

Daada ya mayar masa da amsa.

"Ita haka tace zata sha?

Dadda tace, "Saboda ita tana so ne, kai kuma sai ka ga dama ka ke sha".

Rasa abin cewa ya yi kawai ya yi shiru, ya tabbatar ya fita dan furar nan amma shine za su ce masa haka saboda kawai yace mata wawiya.

"To nima ba zanci abinci ba, furar zan sha".

"Sai ka bari idan ta kammala sai ta rage maka".

"Ni fa awara ma da zan ci, zaka ci awarar?

Be kulata ba ya yi mata banza, tsuke baki ta yi ta ce.

"Ya Ibrahim Pad ɗina ta ƙare fa yaushe zaka siyo min?

"Mtsw, ke ko kunya bakya ji a rayuwar ki wai?

"To idan baka so na tambaye ka sai ka siyo ka ajjemin....

Dadda tace, "Ta ji kunyar Yayanta tace ta ji kunyar wa? Idan bata faɗa maka damuwarta ba waye zata samu ta faɗa masa?

"Ke kuma Dadda abinda kike ba....

Sai kuma ya yi shiru yana zuwa ya bude Fridge be ƙarasa ba dan kada maganar ta yi tsayi. Furarar sa ya ɗauko da ya tabbatar da tashi ce ya zauna suka fara sha. Tana kammalawa ta kwanta ta fara bacci a wurin....

********UMSAL Café aka rubuta a wurin ya jima yana kallon wurin tare da kokonton ya shiga ko har ya shiga? Kafin a hankali ya ƙarasa ya yi parking motar sa a wurin ya fito. Wurine da yake da tsaro gashi shiru babu wata haniya sannan ba cafe ne ba da yake haɗa irin maza da mata ana disco da sauransu. Wurin de ya yi masa yarda kuma komai na su yake a tsare cike da burgewa. Be shiga ciki ba, dan haka akan barandar wurin da aka ƙawata ya samu waje ya zauna yana kallon tsirarun mutanen dake a wajen wasu kuma daga ta ciki.

Menu ya aka ɗauka yana dubawa basu da wasu abinci, zallar beverages ne kala kala sai ɗan snacks da Cookies ɗin da ba'a rasa ba. Ganin waiter a kan shi yasa shi sanar da ita abinda yake so ya maida hankalinsa ga wayar sa. Aka kawo masa coffee harda abinda be buƙata ba. Kallon coffee din ya yi ya ga heart da kuma emoji na murmushi a ciki. Hakan yasa shi ɗagowa ya zubawa Salma ido da ta zauna a kujerar dake kallon sa tana masa cute murmushinta.

"Shi murmushi da ka ke ganinsa wani abu da yake sanya mana nutsuwa a ƙirajenmu. Haka nan, fuskar mutum ta kasance cikin murmushi ya fi ta kasance cikin ɓacin rai".

"Bansanka ba, amma ina so na daura murmushi akan wannan kyakkyawar fuskar na ka".

"Kome ka ga mutum yana yi, a duniyar nan babu dalili, nasan there's most be a reason behind this face. Can you please tell me why? Even if you didn't tell me the reason. Na san ya taɓa maka zuciya sosai. Amma ka sani, akwai Allah, idan zaluntar ka aka yi, baka sani ba ko hakan shine mafi Alkhairi a tattare da kai".

"Malam Mufeed sunana Ummusalma".

Ta faɗa a hankali tana miƙa masa hannu.

"If you don't mind, ina so na zama budurwarka ta wata biyu kacal. Domin naga na sanya ka a cikin farin ciki mai ɗorewa. Ina so naga na sanya mutane dayawa farin ciki, hakan na sani daɗi, shine favorite abinda nake so a duniya. Sannan ina son naga na yi tsokana....

Ta faɗa tana dare bakin ta.

"You know tsokana akwai daɗi, amma ina fasawa mutane baki fa".

Ta sake faɗa tana dunƙule hannunta.

"Ni ce Shalelen Daada Shalelen Dadda bame ja dani".

Ta faɗa tana ɗan sakin murmushi mai kyau.

"Oya tell me, me ka ke tunani a akai na?

Kawai kallonta ya ke yi batare da ya ɗauke idan sa akan ta. Tana sanye da farar riga sai baƙin wando, ta ɗaura apron akai na shagon sai hular dake kan ta. Kana ganinta ka ga yarinya sosai.

"Sunana Ummusalma, Shekaruna 16, na kammala secondary. Ina neman admission amma bansan wanne abu zan karanta ba kasancewar burina kawai na ga na yi karatu a turai Cambridge ina son garin irin sosai ɗin nan. Ance Londonne wai haka ne?

"Daada ya mallaka min wannan Cafe din, nawa ne halak malak. Ina ɗan zuwa amma na fi zuwa Juma'a da Asabar ranakun da ba school. Yanzu kuma nakan ɗan zo idan ta kama saboda ina gida ne kawai. Amma da daddare fa idan aka jima zuwa 11 Yayana zai zo ya ɗaukeni badan yana so ba, sai dan dokar Daada ce hakan".

"Abu na gaba kar ka ganni ƴar ƙarama, ina da samari shida, ina son hudu daga cikin su, biyu kuma bana son su. Sai kai yanzu da idan ka bani dama, zan sanya ka a cikin jerunsu".

Ajiyar zuciya ta sauke tana kallonsa.

"Ka yi haƙuri na....

Bata ƙarasa ba ya ga ta tashi da gudu tana nufar inda wani ƙaramin yaro ya faɗi ya fara kuka. Ɗaukan yaron ya yi ta sanya a jikinta tana jijjigashi, kafin ta ƙwala kiran a kawo mata first aid ta yi treating inda yaron ya ji rauni. Ya samu ya yi shiru sai ririta shi take yi tana masa abubuwa wasa. Ko da zata yi treating din nasa cikin hikima da dabara ta yi.

"Dan Allah ku dena barin sa shi kaɗai. Gudun faruwar matsala".

Ta faɗa cike da ladabi tana miƙa iyayen yaron na su. Kawai zuba mata ido ya yi shi akan sa a lokacin be san wanne irin tunani yake yi ba, game da ita. The way take magana kai ka ce wata uwar mata ce.

"Yauwa na dawo gareka masoyin wata biyu".

Ta faɗa tana zama.

"Ina cewa me ye ne?

Be bata amsa ba ya ɗauka tea spoon ya kwashe wannan kumfar da aka yi hotan emoji da heart a sama. Ya zuba a mini plate ɗin cup din yana kallonta.

"Idan aka ce kin rasa Daada da kuma Dadda a lokaci guda, sannan baki yi sallama da gawar su ba ya zaki ji?

Sai da zuciyarta ta buga ta dawo jin abinda kunnenta ya ji mata. Gaba ɗaya jikinta sai ya yi sanyi. Yana kallonta ya ce.

"Watana uku a asibiti bansan inda kai na yake ba. Mun yi accident ina farkawa aka ce min sun rasu har sun rufe su, wannan ya sa Ni shiga damuwar da bansan adadinta ba. Fahad told me everything akan ki. Ya ce min sune suka shagwaɓaki sune komai na ki. Nima hakan take, ba abinda ba sa min, ba kuma kalar shagwaɓa nin da basu yi ba har na yi wannan girman nawa na mallaki hankalina. Kwatsam ace sun tafi sun barni?

Ya faɗa a hankali yana kallon ta, ganin yarda ƙwalla ta fara zarya a fuskarta.

"Ka yi haƙuri. Bansan haka zan ji ba. Dan Allah ka yi haƙuri".

Girgiza mata kai ya yi a hankali.

"Dan Allah ka gafarceni".

"Ka yafe min".

Ta sake faɗa innocently tana share hawayenta.

"Nevermind".

Tashi ta yi ta koma wata kujerar ta yi shiru ta zuba tagumi tana wasa da deco ɗin kan table ɗin.....