FreeArewaPen original
SALMA ELM
- 1views
- 10chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
I'm a writer at heart ❤️ Driven by the power of word cause words are my love language.🤩😍 Novelists 🖊️🌹
Sample · 1
**********University of Cambridge. Fitowar sa daga hall kenan ya kammala yiwa dalibai lecture suna tajin daɗi haka shima yana jin daɗin yarda yake koyar da su suna ganewa, yana murmushi ya fito zai wuce office ɗin sa dake kusa da inda suka yi lecture, sai kuma a hankali ya ja ya tsaya daga inda yake kafin ya tsaya yana ƙarewa wata yarinya kallo. Kafin ya kai ga duban ga mutanen dake wurin. Kowa ka duba zaka ga zallar farin ciki ce a tare da shi. Domin kyakkyawan labarin da aka ba su bayan fitowar su daga hall ɗin. Ba iya su wanda suka fito ba, kowa na arean yana cikin walwala da farin ciki. Basa tare da wata damuwa Kowa yana harkar gabansa. Sanann kusan kowa dake wurin yana tare da abokinsa suna tattaunawa, masu tafiya kuma sun tafi. Yayin da wata yarinya mai kimanin shekaru ashirin da uku ke zaune da documents a hannunta,amma ita fuskar ta sam babu alamar farin ciki a tattare da ita. Fuskarta fayau babu ko ɗigon kwalli, baƙin ta a bushe ƙayau babu alamar ana shafa masa lipgloss. Amma hakan be hana ta yi kyau ba abinta, Sam inda farin ciki yake bata kalla ba. Kasancewar ana sanyi yasa ta ɗaura babbar jacket a saman rigarta ta atampha yayin da tafa mayafi a saman ɗankwalin dake kan ta. Ƙaramar yarinya ce ta taho da gudu tana bin abin wasan ta ci karo da ƙafarta dake a harɗe, ko kaɗan bata ɗaga kai ta kalli yarinyar ba, bare ace wai ko saboda ita ne yasa yarinyar ta faɗi. Yarinyar har ta gurje saboda faduwar da ta yi amma hakan be sa ta ɗago ta kalle ta ba ko ta san da wani abu a wurin. Har sai da Maman yarinyar ta zo ta ɗauke ta sannan ta yi shiru.Kansa ne ya yi bala'in ɗaurewa sosai hakan yasa shi sake kallonta a tsanake yana sake karantar yanayin ta, tabbas ita ce, wacce ya sani ce, a sanda ya haɗu da ita ya haɗu da ita ne a lokacin tana shekara sha shida a duniya, sannan ya barta tana sha takwas, duka duka rayuwar shekara biyu suka yi. Amma a cikin wannan shekaru guda biyu babu abinda be sani ba na dangane da rayuwarta. Ya san komai, ya san komai dangane da ita, duk a yanzu ta sake girma amma hakan be sa ya kasa gane ta ba, domin ba yarda za'a yi ya ganta yace ba ita bace. Ba iya ita kawai ba kowa dake cikin gidan su zai iya gane su. Ta kasance wani babban gibi a cikin rayuwarsa....Office ɗin sa ya koma yana haɗa coffee da kan sa kafin ya bude ƙofar sa ta baya da zai sa shi ganin school ɗin, daga inda yake tsaye a saman building ɗin sa hawa na uku yana iya hangenta da take zaune an a jarabar cafe ɗin an kawo mata coffee amma bata ɗauka ba tana duba abu a babban littafinta. Yana shan coffee din sa yana tuno duk wata rayuwarta ta baya.....Sunanta Ummusalma, ana kiran ta da Ummu, yayinda wasu ke ce mata Salma, hanyar inda ji yake bata haɗa ba, sai inda tsokana da faɗa yake. Mahaifinta ya kasance mutum ne da baya san hayaniya da husuma, ...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.