NI DA YA NABIL

013

by @swrites22

_ NI DA YAYA NABEEL _



  _YOUNG WRITER✍️



* 013 *



A kwana ukun da Nabeel yayi a dakin Asum wani irin riritata yake kamar kwai, wadda ko a lokacin da suke Germany bai mata haka ba. Ya hanata zuwa scul shi ma kuma yaki fita, duk da yadda ake neman sa wurin aiki amma yayi buris dasu. Komai shi yake mata, ko gyaran bangaren sa da dakin ta saida ta tada masa rigima sannan ya barta ta gyara bangaren nasa dakin ta kuma yasa masu aiki suka gyara, girki kuwa tare suke shiga kitchen ɗin suyi.

Ranar da ya koma dakin Jumaymah sosai Asum ta sha kuka har tana jin anya kuwa zata iya wanna zaman, tana bukatar wanda zai taushe ta ya bata shawara amma kuma bata son tattauna wa da kowa kan rayuwar auran ta, ganin ta kasa bacci ya sata tashi ta dauro alwala ta fara nafilfili tana kaiwa mahallicin ta kukanta, tana roqon ya rage mata zafin kishin nan.





************




Jumayma ce ta shigo dakin taci kwalliya cikin wata fitinanniyar gown red mai hannu daya, gabadayanta bata wuce guiwar ta ba, gashin nan ya sha gyara dukda bashi da yawa sai daukan ido yake, bayanta kuma ma'aikatan dake musu aikin share² da goge ² ne biye da ita. Fitowar sa kenan daga wanka yana tsaye gaban mirror yana shiryawa ya hango shigowarsu ta cikin mirror ɗin, karasowa tayi tare da hugging dinsa ta baya ta ɗaura kanta a kafaɗarsa tana ƙoƙarin magana saidai a yadda ya juyo ya hanata faɗin abinda tayi niyya, rai bace ya kalli ma'aikatan tare da nuna musu kofa ya ce, "Get outtt".

 Ba shiri suka kwashe kayan sharar sukayi waje da sauri har dayan na tuntube. Da mamaki Jumayma ta dawo da kallon ta kansa tare da faɗin, "Babe ya zaka koresu kuma? Gyaran ɗakin naka fa?". Kallon ta yayi da idon sa da ya fara canja kala tsabar bacin rai ya ce, "Daga yau Kar na ƙara ganin wani ma'aikaci a bangarena da sunan yazo gyara, in har ke ba zaki zama mace ba ki san menene rayuwar aure to abar dakin a haka. Sannan kuma zan fada miki kar na qara ganin kina yawo da wa'annan bingalallun kayan gaban wasu garada, ni kadai ke da ikon ganin ki da kowacce irin shiga ba wasu ba. Miye amfani kwalliyar da a ƙaramin tunanin ki ni kika yiwa amma wasu banzaye can sun rigani gani a bagas. Mtwee". Ya karashe yana jan tsaki ya juya ya cigaba da shirin sa.

Baki buɗe ta bishi da kallo cike da tsananin mamaki, daƙyar ta haɗiye mamakin nata tace, "Babe kasan me kake fada kuwa?". Ko kallon ta baiyi ba ya wuce gaban gado inda kayansa suke, ya shiga sawa. "Ahhhhh lalle Babe, ba shakka, ni nasan waccen tsohuwar mayyar ba haka ta barka ba, tabbas wani surkullen aka maka dan lokaci kadan baza kabi ka birkice haka ba, to bari kaji ni gidan ubana ma daya kamata nayi na samu lada ma banyi ba dan haka gidan ka ba bauta nazo yi ba, aure mukayi dan muji daɗin rayuwar mu, mu mori soyayyar mu. Yoo da can ban cika macen ba ma ka auroni? kaji mutum fa wai na zama mace to kai ka fara zama namijin mana. Bangaren Ka kuma gashi nan yai ta hada dattin sa in ka kaji Ka gyara da kanka".

 Tana gama faɗin haka tayi waje a fusace. Tsayawa yayi daga balle maballan rigar tasa ya shiga tunani kwarai ada ya yadda shi ba namiji bane tunda duk zaman sa da jumayma tsawon shekaru 3 bai san miye dadin aure ba, bai kuma gane hakan ba saida ya amshi Asum matsayin mata, dan daga lokacin zuwa yanzu ya fuskanci zaman da yayi da jumayma wani irin zamane da bai san me zai kirashi ba dan auren ta kawai yake amma kamar kowa zaman kansa yake, Jumayma duk abinda taga dama shi takeyi kwata² bata san banbancin lokacin da take budurwa da yanzu da take matar aure ba, amma koma miye shi ma yanzu ya farka daga baccin asarar da ya dauke shi kuma itama dole ya taso ta ko taqi ko taso, da wadannan tunane tunanen ya karasa shiryawa ya fice.

 A dining ya sameta zaune tana chatting sai dariya take kamar wata kwarkwar, tsaki yayi kasa² ya ja kujera ya zauna ba tare da yace komai ba. "Freddie!!!". Jumayma ta kwala masa kira. Da gudu wani bature ya fito daga kitchen din, cikin girmamawa ya gaishe da Nabeel din sannan ya fara kokarin serving ɗin su, dakatar dashi Nabil yayi ta hanyar yi masa alama da ya tafi da hannu, cikin girmama ya amsa da Okay Sir sannan ya juya ya bar dinning ɗin.

 Yana wucewa ta kallesa tare da fadin, "Baza kayi breakfast ɗin bane?".

"Ke aikin me kike yi da baza ki yi serving ɗina da kanki ba ko hoto ce ke?".

"Ban gane hoto ba ce ni, wai meke damunka ne? Da ba Freddie din bane ke serving din mu tsawon shekaru nawa yanzu kuma Ka fito da wani sabon tsarin, tho Ka sani ni ba zan iya ba tun wuri ma gwara Ka koma yadda kake, naji da kai da jarabarka ko naji da wata dawainiyar gida, gsky ba zai yiwu ba".

Zuba mata Ido yayi yana kallo kamar ya samu wata sabuwar halitta, da wata irin murya kamar me mura tsabar bacin rai yace, "Tashi ki bar wurin nan Jumayma". Buɗe baki tayi zatayi magana Assum ta shigo, tayi kwalliyar ta cikin Egyptian abaya black mai adon golden stones tayi rolling din gyalen, takalmin ta da jaka kuwa duk golden yellow ne sai handout din dake riqe a hannunta, idanunta manne da yellow generic heart shaped sunglasses wanda ya Kara fito da ainihin kyawun fuskar ta.

 Sallama ta musu, dakyar Nabeel ya iya amsa mata tare da kakalo Murmushin dole yana kallon ta, tasowa Jumayma tayi ta shige jikin sa cikin shagwaba ta shiga faɗin, "Babe plz Ka tsaya kaci wani abun mana, duk da dai jiya da daddare da shauqi ya ɗaibe ka cewa kayi in ina kusa da kai yunwa ma bata gigin zuwa in da kake, amma dai yanzu fita zakayi bana son yunwar nan ta samu sararin zuwa inda kake". Shi kam ji yake kamar yayi cilli da ita amma ganin idon asum yasa shi dannewa.

 Duk da maganar ta daki Assum amma bata bari hakan ya bayyana akan fuskar ta ba, tace, "Beul habiby ina kwana". Ta fada da wata irin murya me tsayawa a rai. Wani sanyi yaji yana ratsa shi ya ce, "Kin tashi lpy surbajo am (an mata na)?".  Murmushi tayi tana mai jin dadin sunan da ya kira ta dashi ta amsa da, "Lpy kalau alhamdulillah, zan shiga scul ne saboda an fara shirye shiryen exams".

"Ohk to muje sai mu sauke ki ni ma fitar zanyi". Da sauri tace, "Ah ah ka bari kawai nasan su Charlie ma na waje su na jirana barin wuce kar na makara".

 "Thom naji amma zauna kiyi breakfast dan nasan baki ci komai ba". Cikin qaguwa da tsayuwa a wurin dan ba karamin kokari tayi ba wurin riqe kanta tana kallon Jumayma a jikin sa, tace, "Eyyerh Habiby ai kasan bana yin breakfast da wuri, in naje scul zanyi I promise".

"To shikenan, a dawo lpy Allah ya bada sa'a, take care of yourself for me okay?". Murmushi ta masa tana amsa da Ameen ta juya ta bar dinning ɗin.

Tana karasa ficewa Jumayma ta tashi daga jikinsa, a fusace tace, "Nifa banasan irin wanna cin fuskar Nabeel haba, a gabana Ka tsaya Kana wani janta da zance". Tashi yayi kawai dan dama yasan wannan lakwas din da tayi duk salon makirci ne saboda kawai taga Assum, shi addu'a ma yake Allah yasa ran Assum din bai sosu ba dukda bai gani a fuskar ta ba amma yasan dole sai taji wani iri tunda ya san yanayin zafin kishinta. A fili yaja tsaki tare da faɗin, "Kin dai ji kunya whl".

 "Ehh lalle kwarai ba laifin Ka bane tho whl koma wani irin asiri ne sai na balla shege ba wani bokan da ya isa ya tsafe min miji. Rufanan ma naci uwassu naci ubansu duk ifritun daya fasa yin gaba da gaba dani bai cika sunan sa ifritu ba, ni za'a kawo ma dan salo a cikin gida na, toh whl duk wanda yaci tuwo dani miya ya sha". Shi dai wucewar sa yayi ba tare daya Kula ta ba wanda hakan ya sake tunzirata ta cigaba da sakin maganganu ita kaɗai.

Asum kuwa tana shiga scul ta hadu da kawarta Naela take ta manta da bacin ran data fito dashi suka shiga hira.