Chapter 14
╔══════════════════════╗
🌹 *WASAN ƘADDARA* 🌹
╚══════════════════════╝
_A Story of Love, Pain and Destiny. That Even Fate Cannot Escape_
> ✍️ BY ASMEETAH WRITER
━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━
🏆 JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION
🌟 Under:
THE SHIDORIA WRITERS TEAM
━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━
📞 ***
📚 BOOK 1
📖 CHAPTER ___27 and 28
━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━
Wasu soyayyar ƙaddara ce ke haɗata...
Wasu kuma ƙaddara ce ke raba su...
Amma me zai faru idan zuciya ta ƙi amincewa da hukuncin ƙaddara?
━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━
Bayan sati ɗaya da faruwar hatsarin, jikin Zaitun ya yi sauƙi sosai, sai dai zuciyarta ba ta samu natsuwa ba har yanzu. Tana zaune a kan gadon asibitin, ta zuba wa guri guda ido kamar mai nazarin wani abu mai zurfi, can cikin ranta tana jiran abin da zai fito daga bakin mijin nata.
Tana cikin wannan yanayin, aka tura ƙofar ɗakin. Doctor Arman ne ya shigo da sallama, ɗauke da wata leda mai nauyi cike da ire-iren kayan itatuwa da ya siyo mata. Da sauri ta ɗago kai ta kalle shi, gaba ɗaya jikinta ya samu kwarin gwiwa, domin tun bayan da ta farfaɗo bai sake bari sun haɗa ido haka ba...
A zabure ta yi yunkurin sauƙowa daga kan gadon don ta tarɓe shi, amma da sauri ya ɗaga mata hannunsa guda, fuskarsa ɗaure ya ce,
"Relax please..."
Ganin yanayinsa ya sanya ta koma ta zauna a hanzarce, ta turo baki gaba kamar za ta fashe da kuka.
Arman ya taka a hankali ya ajiye ledar fruits ɗin a kan teburin dake gefen gadon, sannan ya dawo ya zauna a bakin gadon nata. Ya zura mata idanuwansa na wasu daƙiƙai kafin ya sauƙe muryarsa ya ce, "Ya jikin naki?"
Ta kalle shi cikin rawar murya ta ce, "Da sauƙi Ya Arman... Amma idan har za ka ci gaba da nisantar da kanka daga gare ni, ba zan taɓa samun sauƙi ba har abada."
Ba tare da ya ce uffan ba, illa ma shiru da ya yi yana kallonta, yana jiran ya ji sauran bayanin da ke tafe a ranta.
Ganin bai katse ta ba ya sanya ta ci gaba da zubar da hawaye tana faɗin,
"You know ina masifar sonka... Ba zan iya ci gaba da rayuwa ba tare da kai ba... You are the partner of my life. Dan Allah my husband ka yi haƙuri ka mayar da ni ɗakina... Kar ka rabu da ni mana..."
Arman ya sauƙe wani nauyayen numfashi, ya gyara zamansa sannan ya dubi tsakiyar idanunta ya ce,
"Meye damuwarki da yarinyar nan ne? Ita kaɗai ce macen da kika taɓa gani na da ita ne a rayuwata? And duk ba ki yi wannan haukar ba sai a kanta. Akan yarinya ƙarama kina neman ki kashe kanki? Shin kishi hauka ne? Idan za ki yi kishi ni ban hanaki ba, amma kiyi shi a kan hujja... A kan abin da kika sani mana"
Cikin kuka mai cin rai ta girgiza kai ta ce, "Sun ƙira ni da mahaukaciya..."
"Ke kika kai kanki ai, so ban ga laifinsu ba," ya ba ta amsa kai-tsaye ba tare da wata fargaba ba.
Ta share hawayen fuskarta da sauri, ta ɗora da cewa, "Sannan kuma... Sun nuna min letter da ka aika mata ta soyayya. Na ji ƙamshin turarenka a jiki dole na tabbatar da abin da nake zargi, Kuma... Kuma..."
A hankali Arman ya juyo gaba ɗaya jikinsa yana kallonta, idanunsa suka kaɗa lokaci guda saboda jin abin da bai taɓa zato ba. Wasiƙar da ya aika, ai an sanar masa cewa ta faɗi ne amma yanzu kuma gashi Zaitun tana yi masa maganarta, har da zancen ƙamshin turarensa...
Babu abin da ya ce, domin ya san tabbas ya rubuta wasiƙar kuma ya aika, sai dai sam bai yi tsammanin cewa ya je gare ta ba...
Kafin ya fito daga cikin wannan tunanin, Zaitun ta miƙa hannunta ta rungume shi ta bayansa, ta kwantar da kanta a bayansa tana kuka mai sauti..
"I love you... Basu isa su raba ni da kai ba. Kuma yarinyar kyakkyawa ce wadda babu namijin da zai kalle ta ya ƙi ta, dole na yi kishi, sannan na yi katangar ƙarfe a tsakaninku, please my love, leave that girl..."
Arman ya tsaya cak, jikinsa ya yi sanyi. Hannayen Zaitun da suka rungume shi suka yi masa nauyi fiye da yadda ya taɓa zato. Bai mayar da rungumar ba, haka kuma bai ture ta ba. Idanunsa suka lumshe na ɗan lokaci, yana ƙoƙarin haɗiye mamakin da ke neman bayyana a fuskarsa...
A hankali ya cire hannayenta daga jikinsa, ba tare da ya yi amfani da ƙarfi ba. Ya miƙe tsaye yana kallonta cikin nutsuwa.
"Wa ya nuna miki wasiƙar?" ya tambaya da murya ƙasa-ƙasa.
Zaitun ta share hawayenta cikin sauri.
"A gidan su... Sun ce kai ne ka rubuta mata."
Ya sauƙe numfashi mai nauyi. A zuciyarsa ya furta, "To kenan... wasiƙar ta isa gare ta?."
Ya ɗan yi shiru na wasu daƙiƙu kafin ya ce,
"Zaitun... akwai abubuwa da ba ki sani ba. Kuma idan lokaci ya yi zan gaya miki komai. Amma ki yi min alƙawari... kada ki sake cutar da kanki ko wani saboda zato."
Ya juya ya ɗauki ledar fruits ɗin ya buɗe, ya ciro apple ya ajiye a gabanta. "Ki gama samun lafiya tukuna."
Ya zauna yana yanyanka Apple tare da bata a baki cikin kulawa, ya ɗauko lemuka yana bata. Ita kuwa idonta na a kansa, ko ƙibtawa babu. Bayan ya gama ciyar da ita, ya ja tishu ya goge mata gefen bakinta da hawayen da suka ɓata fuskar, sannan ya tashi tsaye ya gyara tsayuwarsa.
ya juya ya ɗauko allura a cikin tiren magunguna domin ya yi mata.
Tana ganin allurar, ta shiga yi masa magiya cikin rawar murya,
"Dan Allah Ya Arman, yaushe zaka mayar da ni gidanka? Wallahi ba zan ƙara ɓata maka rai ba... Ka yafe min."
Arman wanda fuskar sa take sanye da facemask tun shigowarsa asibitin, ya zaro allurar yana dubawa, sannan ya ce a hankali, "Zan mayar da ke ɗakinki, amma kin san ba na son shirme..."
A can gefe guda kuwa, a daidai wannan lokacin, wata keke-napep ce ta tsaya a babban harabar asibitin Aurelion Hospital. Amira da ƙawarta Maryam ne suka sauƙa a ciki.
Yadda aka yi suka zo gurin kuwa, tsantsar wayo ne da tsari na Maryam. Sanin cewa Uma ba ta cika barin Amira tana dogon yawo ba, ya sa suka haɗa wani plan. Maryam ce ta fara zuwa gidan su Amira. Dake Uma tana son Maryam kuma ta amince da ita sosai, Maryam ta fake da cewa, "Uma, don Allah ki bar Amira ta raka ni mu duba ƙanwar Babana da ta yi karaya a sawu sakamakon faɗuwa da ta yi..."
Uma ta girgiza kai cikin tausayawa, ta jajanta musu sosai, har ta ba su saƙon gaisuwa zuwa ga mai jikin. Suka amsa cikin godiya. Haka Maryam ta biya kuɗin napep suka nufi cikin garin Kaduna zuwa wannan katafaren asibiti. Sun tsaya a hanya sun yi siyayyar kayan marmari masu kyau na marar lafiya, domin Amira tana da burin duba jikin Zaitun...
Kamar yadda Amira ta sani, kai tsaye sashin da aka kwantar da Zaitun suka nufa.
Suna isa ƙofar ɗakin, daidai lokacin da Arman ke gama faɗin "..ki daina sa damuwa a ranki," sai aka turo ƙofa da sallama...
Amira da Maryam cikin zaƙin murya da girmamawa suka ce a tare, "Assalamu alaikum..."
Zaitun ta kalli ƙofar tana shirin amsa sallamar, sai idonta ya sauƙa a kan fuskar Amira. Nan take ta haɗiye kalmar, fuskarta ta sauya ta yi wani irin murtuk.
Arman bai juyo ba, kuma bai maida hankali a kansu ba domin ya saba da shigowar ma'aikata ko mutane, ƙari da cewa hankalinsa yana kan duba na'urar da ke auna motsin zuciyar ta. Hakan ya sa sam bai san ko su wanene ba.
Maryam ta matsa gaba cikin ladabi, "Ina wuni? Ya jikin naki?.."
Zaitun ba ta amsa ba, ta zuba musu idanu tana yi musu wani irin kallo na up and down, cike da tsana.
Amira ita ma ta matso da sanyin jiki, "Ina wuni Aunty, ya jikin naki?..."
"Aunty ɗin ubanki?..." Zaitun ta furta cikin ɗaga murya da zafin rai.
A slow Arman ya sauƙar da idonsa akan Zaitun saboda jin wannan kalaman da suka fito daga bakinta.
Zaitun ta ci gaba da masifa, "Inaga na auri ubanki ne shi yasa kike ƙirani da Aunty...Wai ma me ya kawo ki inda nake? Kin wani kwaso dattin ƙafarki kin zo za ki ƙarasa kashe ni ko?..."
Arman ya juyo da sauri, ya sauƙe idonsa a kan su Amira. Cike da mamaki da tsananin firgici yake bin su da kallo ta cikin mask ɗinsa, ya rasa abin da zai ce na ɗan lokaci.
Maryam ta ce, "Baiwar Allah meye abin zafi anan? Zuwa mukayi mu gaishe ki da jiki ne..."
"Dallah rufe min dattin mouth ɗinki" Zaitun ta katse ta da tsawa. "Ke ɗin har wacece, ƙazaman banza! Ina da wata alaƙa ne da ku da za ku zo duba ni? Ko neman shishshige wa mijina kuke ne..."
Ta watsa wa Amira wani mugun kallo, "Munafukai masu bibiyar mazajen mutane. Ku je ku nemo kowane namiji amma ban da mijina, domin ya fi ƙarfinku..."
Ganin abin zai zama abin kunya, Maryam ta karɓi ledar fruits ɗin dake hannun Amira, ta ƙarasa da sauri ta ajiye a kan gadon da Zaitun take, tana faɗin, "Sorry ga wannan, mu zamu tafi. Ko ba komai mun samu lada..."
A haukace Zaitun ta ɗauki ledar ta watsa musu ita da ƙarfi. Duk lemukan da sauran fruits ɗin suka watsu a jikinsu da ƙasa. Ba ta tsaya a nan ba, ta miƙe a zabure tare da ɗaukan flower vase dake gefen tebur, ta ɗaga sama za ta wurga musu.
Arman ya yi hanzarin riƙe ta da ƙarfi ta baya.
"Wallahi ka sake ni! Kafin su kashe ni, zan fara hallaka su munafukai..." Zaitun ta shiga fizge-fizge tana ihu.
Arman yana rungume da ita da ƙarfi don kada ta jikkata kanta, ya juya idanunsa da suka kaɗa suka yi ja saboda ɓacin rai, ya ce
"Get out!..."
Amira wacce jikinta ya ɗauki ɓari, hawaye na wanke mata fuska, ta tsorata sosai tana ƙoƙarin bayani, "Daman... daman ba da wata manufa mu..."
Arman ya sake dakar musu wata zafafan tsawa da ta girgiza ɗakin, "I said GOOO!..."
Maryam ta ja hannun Amira da sauri, "A'a Doctor ka yi haƙuri, za mu fita..."
Nan take Maryam ta ja hannun Amira da gudu suka tura ƙofa suka fita. Har suka fice, idanun Arman suna kan bakin ƙofar, cike da wani irin lissafi da ɓacin rai da ya kasa misaltuwa.
Daga bisani, ya dawo da hankalinsa kan Zaitun, wadda a halin yanzu ta kifa kanta a kan ƙirjinsa tana wani irin kuka mai ban tausayi da ban haushi.
Ya ja numfashi, ya zaunar da ita a kan gadon a hankali, "It's okay..."
Yana duban na'urar kwamfuta dake nuna bugun zuciyarta, ya ga yadda lambobin ke tashi da sauri saboda zafin rai. Ya kwantar da ita ya ce, "Relax... wait for me."
Zai juyo ya fita sai Zaitun ta yi hanzarin riƙe rigarsa da kyau, tana kuka da magiya,
"Ina za ka je? Za ka bi bayansu ne? Babu inda za ka je dan Allah ka zauna da ni... Ba su fi ni da komai ba!..."
Ta jawo shi da ƙarfi ta zaunar da shi a kan gadon, ta rungume shi sosai kamar wacce ake ƙoƙarin ƙwace mata shi. Arman ya runtse idonsa, ya zauna nan, ya zaɓi ya yi mata abin da take so a halin yanzu domin ya kwantar mata da hankali, amma a can cikin ransa, wani sabon lissafin yake yi...
Bayan Amira da Maryam sun fito farfajiyar asibitin, zukatansu cike da ɓacin rai da takaicin wulaƙancin da Zaitun ta yi musu, kwatsam sai ga wata tsararriyar mota ta alfarma ta zo ta faka a gabansu.
Ƙofofin motar aka buɗe, Hajiya Mairo ce ta fito, tare da yaranta Ahan, Elham, Nana, da kuma Auta. Wannan shi ne karo na uku da suke zuwa duba jikin Zaitun.
Ahan yana gyara tsayuwarsa, ya furta wa Elham magana a hankali, "Ke kiga wasu ƴan mata, bari naga ko akwai wacce ta burge ni..."
Elham ta taɓe baki ta ce, "Ka shige su Yaya Ahan... Waɗannan yaran talakawan ma sai ka nema?"
Suna cikin radin maganar ƙasa-ƙasa, Hajiya Mairo ta yi gaba ta shice cikin asibitin. Nana wacce take ƙanwar Elham ce ta girgiza kai saboda ta ji abinda Ahan ya faɗa. Ta kama hannun Auta suka bi bayan mahaifiyarsu..
Sauran da suka rage a gurin su ne Ahan da Elham. Elham ta tsaya ta jingina da jikin motar tasu tana kallon gefe, shi kuma Ahan yana sanye da farin glass na alfarma, ya tako har gaban su Amira.
Ya ɗan tura glass ɗin saman hancinsa gami da washe baki,
"Ya ƴan mata adon gari..."
Daidai lokacin, idanunsa suka sauƙa a kan fuskar Amira. Ita ma Amira ɗaga kan da za ta yi, sai suka haɗa ido. Gaban Ahan ya buga wajen nuna mamaki,
"Buro uba. Daman kece? Na sake haɗuwa da marar kunya again..."
Amira ta cika ta yi fam, ta watsa masa harara, "Sannu ɗan masu kuɗi mai aron biro... Ka zo ka tare mu ka yi mana meye?"
Maryam dake tsaye cike da mamaki ta ɗan taɓo Amira, "Ke... Kin san shi ne?"
Amira ta ce, "Shi ne yaron da na ba ki labarinsa rannan, wanda muka haɗu a centre na JAMB registration."
Maryam ta zaro ido, "Ohhhh... Daman shi ne?"
Ahan ya haɗe fuska cikin jin zafin kalmar Amira, "Amma kin raina min wayo ƴar nan. Ni za ki duba ki ƙira da yaro?"
Elham dake tsaye tana jiyo koke-koken da ake yi, ta nufi gurin da sauri tana cewa, "Ni fa Yaya Ahan zan shige ciki fa. Ina ta jiranka ka tsaya biye da waɗannan..."
Maryam ta juyo kan Elham ta ce, "Taya zai tsaya biye mu alhalin shi ya zo ya same mu?"
Elham ta sha ginin gabanta tare da faɗin,
"A'a dakata Madam... Kada ki min rashin kunya."
Maryam ta saki lallausan murmushin rainin wayo, "Too pahh! Shin da kunyar ta mutu, sadakar nawa kika bayar? Ke har kin kai na yi miki rashin kunya, wacce ba ki wuce sa'ata ba?"
Elham ta buɗe baki za ta yi masifa, Ahan ya yi hanzarin tare ta ta hanyar ɗaga mata hannu, "Ke... ke please kar ki ce komai. Ita ɗin budurwata ce"
Maryam ta juyo kansa da sauri, "A ina na zamo budurwarka? Haɗuwar yanzu, rabuwar wulaƙanci..."
Ahan ya shafa kansa yana wani murmushi,
"Ai kina da kyau dole kowane namiji ya so ki... Duk da cewa wannan ta fiki fari da kyau." Ya nuna Amira da yatsa, sannan ya ɗora, "Amma ita matsalar ta rashin kunya... Don wata rana zan daka ta ne."
Amira ta turo baki ta harare shi, "Iyeee! Saboda ka samu sakwara ai dole ka daka."
Elham ta tsayar da idanunta a kan fuskar Amira, ta shiga ƙare mata kallo na sani. Can ta zaro ido ta nuna Amira da yatsa,
"Kai... Wannan fuskar yarinyar kamar na taɓa gani..."
Ahan ya juyo ya kalli ƙanwar tasa, "Kin san ta ne?"
Maryam ta shiga tsakani, "Wallahi matsalata da ƴaƴan masu kuɗi raini... Yanzu fa idan aka bibiya ba ta girme ki ba, amma wai yarinya take ƙiranki."
Ahan yana kallon Maryam ya ce, "Wallahi kuwa masoyiya, Shekararta 18 amma sai son girma."
Elham ta watsa masa harara mai zafi...
Maryam ta taɓe baki, "Assha! Mun girme ta ma ashe."
Elham ta ɗaga wa Ahan hannu da sauri, "Tsaya Yaya... Shin wannan ba ita ce wacce Aunty Zaitun ta same ta a makarantarsu ta ZABGA mata mari akan Babban Yayanmu ba?"
Gaban Amira ya buga da ƙarfi, ta zaro idanu tana kallon su cikin tsananin firgici.
Maryam ta juya da sauri ta kalli Amira, sannan ta dawo kan su Ahan,
"Kaiii... Kada dai ƙannensa ne ku?!"
Ahan ya matso kusa, ya shiga duba fuskar Amira da kyau, "Eh to... Bari na duba ta da kyau. Kuma fa wallahi... Kamar ita ce"
Elham ta ce, "Haba Yaya ita ce fa. Wai shin ka makance ne?"
Ahan ya jinjina kai, "Eh yanzu na gane ta. Amma a video abar tausayi, amma a zahiri ta fi kunama iya harbi, yasinnn..."
Maryam ta tare su, "Eh ita ce sai meye? Daman ana nemanta ne?"
Ahan ya ce, "A'a masoyiya, wai daman za mu ba ta haƙuri ne a kan abin da ya faru, amma tunda wannan ce... Mun fasa" Ya faɗa yana hararar Amira.
Elham ta shaƙi irin yadda Maryam take magana da gadara, ta ce, "Akan me za mu neme ta? Ko a matsayin ƴar aikin gidanmu ba za mu ɗauke ku ba balle..."
Maryam ta katse ta da cewa, "Dube ki! Kina nan kamar an rina kare amma kina kushe wasu. Kuɗin ne kawai amma babu tsari mai kyau."
"Keeee!..." Elham ta fusata, ta ɗaga hannu za ta mari Maryam.
Da sauri Ahan ya riƙe hannun ƙanwar tasa, "A'a... a'a! Masoyiya ce, kar ki taɓa min fuskarta."
Maryam ba tare da ta tsorata ba ta ce, "Ai wallahi da kin taɓa ni, da na nuna miki cewa Maryam nake ba Fa'iza ba"
Ahan ya saki baki yana kallon Maryam cikin sha'awa, "Wow! Na yi dacen samun masoyiya mai sunan uwata. Shikenan... Uwa Mairo, mata Maryam, ƴar da za mu haifa Marry"
Suna cikin wannan cacar bakin, sai ga wata baƙar tsararriyar mota guda ɗaya tamkar dubu, wato Escalade, ta fito daga harabar asibitin...
Gilasan motar duka tinted ne, ba ka ganin komai na ciki.
Elham tana ganin motar, idanunta suka zaro waje, ta yi hanzarin riƙe hannun Ahan cikin firgici,
"Yaya Ahan... Motar Big Bros! Mun shige su..."
Nan take Ahan ya rikice, ya tsure sosai. Ba shiri ya nufi gurin Maryam, ya ɗaga katoton hijab ɗinta yana ƙoƙarin sulalewa ya shiga ciki domin ya ɓuya...
Maryam ta ja baya da sauri tana hankaɗa shi, "Wannan ya haukace... Kana hauka za ka shiga cikin hijabi na?!"
Elham ita ma da sauri ta juya baya ta fake a jikin bangon motarsu ta yadda babban yayan nasu ba zai ga fuskarta ba.
Amira kuwa ta zuba wa baƙar motar idanu. Can cikin zuciyarta, tana matsanancin son ganin fuskar mutumin ko sau ɗaya ne, amma kash, motar ba ta da maraba da bango, ba a ganin komai sai baƙi.
Ganin Maryam ta ƙi ba shi haɗin kan ɓuyewa a hijab, kuma motar tana ƙarasowa, Ahan ya ranta ana kare. Ya ruga da gudu ya nufi cikin asibitin, Elham na biye da shi a baya suka shiga cikin corridor...
Motar Escalade ɗin ta wuce ta gabansu Amira... Haka suka tsaya bin bayan motar da kallo har ta ɓace musu, kafin daga baya su ma suka juyo suka tari napep suka shiga...
Suna cikin napep a kan hanyar komawa gida, Maryam ta shiga sabon korafi cike da takaici,
"Gaskiya matar nan tana da masifa, daga zuwa shikenan... Ai wallahi ba don a gadon asibiti muka same ta ba, da babu abin da zai hana na rufe ta da duka! Ƴar rainin hankali kawai. Gashi mun yi asarar kuɗinmu wurin siyan kayan fruits ta wulaƙanta mana shi, mu ba mu ci a cikinmu ba... Ga wasu gala-galan ƙannen mutumin marasa ji."
Amira ta sauƙe ajiyar zuciya, ta jingina kanta da jikin napep ɗin, "Ni wallahi so nake ma na ga mijin nata ko sau ɗaya... Ban san shi ba, ban taɓa ganinsa ba."
Maryam ta taɓe baki, "Gashi kusan duk social media na duba a wayata ban ga hotonsa ko sau ɗaya ba. Sai dai kamfanoninsa da ayyukan alheri da yake yi masu kyau. Domin ba za ki taɓa jin inda aka kushe shi ba."
"Dan Allah a ina za mu same shi?" Amira ta tambaya cikin zumuɗi..
"Ki masa me? Ina Maryama za ta san inda mutumin yake? Mutum mai mugun kwarjini... To na kusa da shi ma akwai waɗanda ba su taɓa ganin fuskarsa ba."
Amira ta yi shiru na ɗan lokaci, sannan ta ce, "Shikenan ma, na ma bar zancensa. Ganinsa ma ba shi da wani fa'ida... Kawai abu ɗaya na riƙe nashi, shine ƙamshin turarensa."
Maryam ta kalle Amira ta furta "Ke... Wataƙila ma ba shi ne ya aiko miki da wasiƙar nan ba, domin da wuya mutumin nan ya aiko miki da letter."
"Matarsa ma fa ta tabbatar mana da ƙamshin turaren mijinta ne da ta zo gidanmu."
Amira ta ba da amsa cikin tabbatarwa..
Maryam ta dafe kafaɗarta, "Dan Allah Meerah, ki cire wannan a ranki. Kada ki wahalar da zuciyarki a kan abin da ba zai taɓa amfanar da ke da komai ba."
Haka suka bar maganar gaba ɗaya, suka tsiri hirar wani abin daban har mai napep ya shiga da su cikin unguwarsu.
★★★
Suna shiga tsakar gidan, suka tarar da Uma tana aiki. Ta ɗago kai ta kalle su, "Har kun dawo? Gaskiya kun yi sauri. Ya jikin baabar takin?"
Maryam ta cire fargaba ta yi saurin ƙirƙiro murmushin yaƙe, "Wallahi ai kawai gano ta ne ba zama za mu yi ba, ƙafar da sauƙi. Wai ma tace tana gaishe ki."
Uma ta yi murmushin jin daɗi, "Allah sarki! Ni ma idan na samu lokaci zan je da kaina na gano ta."
Gaban Amira da Maryam ya faɗi, suka kalli juna da sauri saboda sun san ƙaryar da suka shirya za ta iya tonuwa idan Uma ta matsa...
Maryam ta sake yin caraf ta tare zancen, "Wallahi ai a yau ma za su bar garin saboda ɗaurin bai yi kyau ba. Za su je can wani ƙauye za a sake ɗaure ƙafar, kuma kamar za su ɗan yi kwanaki a can."
Uma ta jinjina kai cikin gamsuwa da tausayawa, "Allah sarki... Allah ya ba ta lafiya."
Suka amsa cikin sauƙe ajiyar zuciya, "Amin..."
★
Da daddare bayan Maryam ta koma gidansu, cikin ɗakin ya rage daga Amira sai Uma. Amira tana taya Uma naɗe busassun kayayyakinsu da suka kwaso daga shanya, suna sanya su a tsofaffin akwatunansu dake ajiye a kusurwar ɗakin...
Cikin kwanaki bakwai da suka gabata, tun bayan kai ta asibiti, maganar mahaifin Zaitun take ta faman juyawa a ƙwaƙwalwar ta. Ta kasa manta ranar da dattijon yake shaida mata cewa Zaitun ba ta da kowa a duniyar nan sai shi kaɗai...
Wannan furucin ya daki ainihin jigon zuciyarta, ya janyo mata wani irin tunani mai zurfi game da tata rayuwar. Ta kalli mahaifiyarta da ta duƙufa gurin raba kayan kashi-kashi, sannan ta ƙira sunanta.
"Uma..."
Uma ta amsa cikin sakin fuska ba tare da ta ɗago ba, tana ci gaba da gyara tsofaffin zannuwanta na atamfa, "Na'am Ambaby ta?"
Amira ta ɗan yi shiru, ta tuƙe numfashi kafin ta daure ta ce, "Mama... Wai ni babu wasu ƴan uwanmu ne?"
Katsam, hannun Uma ya tsaya cak daga naɗe zanen da take yi. Ta ɗago kai a hankali, idanunsu suka haɗe da na ɗiyarta, "Meye yasa kika yi wannan tambayar?"
Amira ta sunkuyar da kanta ƙasa, tana jujjuya gefen rigarta, "A asibiti na tambayi mahaifin wannan matar da ta zo... Na tambaye shi dalilin da yasa babu mahaifiyarta ko wani ɗan uwanta da ya zo duba ta. Sai ya ce min ba ta da kowa sai shi kaɗai a rayuwa."
Ta ɗago da kyawawan idanunta da suka soma canza launi ta kalli Uma, "Nan take na tuna da kaina, Mama...Ni ma tun ina ƙarama ban taɓa ganin ko ƙanin Baba ba, ko yayansa, ko ƙannenki, ko wani ɗan uwa na jini ba. Sai Baffa kaɗai da kika ce a wurinsa muka rayu, kuma shi ba ɗan uwanmu na jini ba ne..."
Uma ta yi shiru, gaba ɗaya jikinta ya yi sanyi, ta kasa magana.
Amira ta ci gaba da maganar cikin karaya,
"An ce min Babana ya rasu tun ina jaririya. Amma ai ko ya rasu, ya kamata ya bar ƴan uwa. Ke ma haka, ya kamata ki sami ko da yaya ko ƙanne. Amma ni a duniyar nan ban san kowa namu ba sai ke kaɗai."
Wannan maganar ta sauka a zuciyar Uma kamar ƙaton dutse mai nauyin gaske. Ta kalli yarinyar tata, ta ji wani irin tausayinta ya cika mata ƙirji. Ta ajiye zanen hannunta, ta matsa kusa da Amira sannan ta sa hannu ta shafa kanta cikin rarrashi.
"Meerah... Wasu ƙaddaroribidan mutum ya tuna su, zuciyarsa tana yin ciwo sosai. Ki bar wannan tunanin, kin ji?"
Amira ta girgiza kai, hawaye na zuba daga idonta, "Amma Mama, ni ina son sanin asalina. Ba na son na girma a matsayin wacce ba ta da kowa."
Uma ta kau da fuskarta da sauri gefe guda, domin kuwa tana jin yadda tambayar ta Amira ta motsa mata wani tsohon abu a can ƙasan ranta, wani tulin duhu da ba ta da ikon fassara shi ko fito da shi fili..
Kwatsam, wani irin mugun ciwon kai, mai rarrafe da tsananin radadi ya soma dabaibaye ainihin ƙwaƙwalwarta. Cikin zuciyarta da kanta, ta ji tamkar akwai wasu dishi-dishin hotuna na mutane da wurare masu nisa suna ƙoƙarin bayyana gare ta cikin sauri, amma da ta matsa ta yi yunkurin tace su domin ta gane ko su wanene... Sai duk hotunan suka ruguje, suka juye suka ɓace tamkar hayaƙin da iska ta kwashe...
Zafin ciwon kan ya tsananta har ya sa ta dafe goshinta da ƙarfi, tana rintse idanuwanta cikin wani irin nishi na azaba..
"Uma lafiya?" Amira ta tambaya cikin tsananin fargaba da kiɗima, ta saki kayan hannunta ta dawo kusa da mahaifiyarta.
Uma ta daure, ta sauƙe numfashi da kyar sannan ta tilasta kanta yin wani murmushin dole, ta janye hannunta daga goshin, "Ba komai Meerah... Wata ƙaramar ciwon kai ce kawai ta tashi."
Amira ta zubawa mahaifiyarta ido, cike da shakku amma ta daure ta yi shiru don kada ta ƙara ɗaga mata hankali....