28
by @rukyelmuaz
Tunda ta fito wanka ta rasa kayan da zata saka sai kaiwa da komowa take tsakanin clothset ɗinta zuwa bakin gado ta rasa wani kaya zata zaɓa Daddy ya ce ta yi kyau sosai, a yi mata photo a tura masa, ganin ta rasa kayan zaɓa yasa ta fito tana kiran Kaka.
"Kaka ki zo ki bani kaya in saka, Daddyna ya ce in yi gayu in yi kyau, za'a min photo a tura masa."
"Zo ki fara ɗaukar abincinki in kika gama karyawa, sai kisa kayan"
Babu gaddama ta ɗauko potato chips & chicken ne, tana ɗauka ta dawo parlour ta zaune tana cin chips ɗin da fork.
Shiru cikin su babu wanda yama ɗan uwansa magana, kamar ma basu lura da juna ba.
Sai da ta gama cinyewa tas sai ƙasu,suwa ta bari a plate ɗin, ɗaukar kashin ta yi zata fara tauwana.
"Sannu zakanya a she haƙoranki sun iya tauna ƙashi kura kyaci da gashi"
Tura baki tayi gaba tana kallonsa babu shiri ta ɗauki plate ɗin ta fidda waje, bata dawo ɗakin ba tana waje tana jiran Kaka ta gama aiki ta zo ta ɗauko mata kayan da zata saka.
Saida Kaka ta gama komi sannan ta fito kitchen ɗin, ta biyo bayanta suka shiga parlour, Kaka taga babu kowa sai tray ɗin abinci da plates ɗin dake ciki da alama bai wani ci abincin da yawa ba, duk da dama tasan ba da yawa zai ci ba tunda baya son cin abinci sosai.
Suna shiga ciki, bedroom suka wuce kaya Kaka ta ɗauko mata wata black Atamfa ce da suka yi anko da Jannat.
Kaka na bata kayan ta amsa ta saka ko kallabi bata ɗaura ba hijabi kawai ta saka,
"Na tafi gidansu Mairo tamin kwalliyar ƴan gayu Daddyna ya ce, in yi kyau sosai"
Bata jira amsar Kaka ba ta fita ɗakin ta wuce tana addu'ar Allah ya sa karta haɗu da wannan mugun, sauri kawai take ta samu ta fita a gidan.
***
Zaune take tana mitar an korota kuɗin sati a islamiyya don haka ba zata koma ba, Inno ta yi banza da ita, ta shige kewaye don ta lura rigimar Mairo ba mai ƙarewa bace.
tun daga soro ta ke jin ana kiran sunanta murya da a ko yaushe take kwana da ita a zuciya take tashi da tunaninta da muradin ganin mai muryar.
"Mairo, Mairo, wai kina ina ne ina ta faman kiranki ba zaki amsa ba"
"Ke dallah Malama gani nan kike kirana ko kin makance ne, kina neman ɗan jagora"
Mairo tayi maganar tana kallon wurin da tasan tanan Haisu zata shigo, tana ware ido alamar ta ƙosa taga mai kiran nata.
Tana shigowa idonsu suka haɗu duka murmushi suka sakarma juna, da gudu Haisu ta ƙarasa wurin da Mairo take zaune, wata ƙaramar kujerar ƙatako ce ta samu ta zauna a kai, tana kallon Mairo dake zaune a saman wani benci.
Da fara'a cike da murmushi me nuna tsantsar yanda take son sanar da ita abinda ke cikin zuciyarta.
"Ke Daddyna yace in yi kyau sosai, kimin irin kwalliyar da kike in zaki je dandali, irin wacce Rashidu ya saya mana rogo da ƙuli kin tuna ta?."
"Lahhhh yarinya zan yi miki irin wacce ko ni kaina ban taɓa yin irinta ba, wannan wacce Rashidu ya gani ai bata yi kyau ba"
"Don Allah da gaske? zaki min wacce ta wuce taki kyau, to yi sauri ki ɗauko kayan kiyimin, kin san basamude yana nan bana son yamin duka."
"Ke yarinya ina da wata addu'a zan faɗa miki daga yanzu in kika yi ma wannan mugun yayan naki laifi irinta zaki ringa yi."
"To shikenan faɗa min in ji ai kuwa kullum sai na yi masa ita"
"Bari zan faɗa miki in muka haɗu anjima."
Mairo na faɗin haka ta miƙe ta shiga cikin ɗaki. Dauko kayan kwalliyar da zata ma Haisu make-up da su ta yi, kwalli da gazar ne sai red din janbaki, ta fito dasu a cikin wani kwandon kayan kwalliya.
Tana fitowa ta samu wuri ta zauna saman bencin da ta tashi, Haisu ta miƙe ta ɗauki kujerar da take zaune ta matso da ita kusa da Mairo sosai yanda zata ji daɗin kwalliyar.
Tunda suka zauna Mairo ta fara kwalliyar kamar tana shirya boƙanya zata yi baƙin aljanu, tana ƙara gyara Haisu duk in da bai ji baƙin kwalli ba Mairo na ƙara gyara shi janbaki ta shafa mata a kumatu a matsayin barbaɗa kumatu.
Sun ɗauki lokaci suna wannan kwalliya, sannan suka gama.
Haisu sai ƙara kallon kanta a madubi take yi, tana jin daɗin irin kwalliyar da Mairo ke yi ne, in zata taho dandali, a yi ta kallonta har Rashidu yana saya musu kifi.
Girarta da a ka cika da baƙin kwalli ta kalla ta yi dariya, mai cike da farin ciki da ganin tsantsar kyaun da tayi.
"Mairo ke ma zan baki tsaraba in muka dawo, Basamude bai bani abinda a ka aiko min da shi ba, amma in muka fita Daddyna duk na faɗa masa abinda nike so da mun dawo zan taho in kawo miki.
"Da gaske don Allah in ya je dake wannan wurin ki yo min tsarabar ice cream ɗin nan, na ƴan gayu irin wanda Daddy ya kawo miki daya taɓa zuwa."
"Hahahaha, kyal kyal kyal" Jamilu ke wata dariya, wanda tun da ya shigo idonsa ya sauka a kan fuskar Haisu da ta zama kamar an yi ma biranya kwalliya, dariya ya ke sosai yana kallon fuskar Haisu wanda yana da tabbacin in suka fita tashe ba ƙaramin kudi zasu samu ba domin fuskarta kawai abin dariya ce a yanda take.
Tun Jamilu na dariya sunƙi kula shi har ran Mairo ya fara ɓaci, ta gama zuwa wuya kamar wata kubu,buwa.
"Inno kin ga Yaya Jamilu na min dariya koh?
"Wai Mairo ba zaki bar bakina ya huta ba?"
Turo baki ta yi ta janyo hannun Haisu suka shige ɗaki suka bar Jamilu a tsakiyar gida har yau bai daina dariyar ba.
Suna shiga ɗaki Mairo ta kwance kan Haisu da yake a cunkushe ta tsaga mata biyu ta ɗaure mata gefe da gefe, Haisu dake kallon komi ta cikin mirror sai ƙara murmushi take yi tana jin daɗi gani take yi babu kamarta.
Inno ce ta shigo ɗakin, Haisu ta gaidata amma Inno madadin ta amsa gaisuwar suna haɗa ido ta kalli fuskar Haisu sai dariya ta subuce mata, cikin dariyar ta amsa gaisuwar, ran Haisu da Mairo ya gama ɓaci sun rasa me a ke ma dariya haka, cikin ɓacin rai Haisu ta miƙe tama Mairo sallama ta fito gidan.
Tana fitowa taga an fara kallonta ana waige sai ta ji duk damuwarta ta tafi domin ta gama kyau maƙura.
Tafiya take ranta babu damuwar komi ji take kamar tafi kowa kyau a cikin ƙauye, sai wani annuri take shiga da zarar ta ɗan yi tsalle taji gashin kanta ya yi tsalle saita saki wata dariya mara sauti.
Tunda ta taho hanya mutane ke kallonta suna ƙunshe dariya don sun san halinta in dariyarsu ta fito fili ta gani, ba ƙaramin tashin hankali zasu sayama kansu ba, babu wani wanda ya yi ƙoƙarin yi mata magana.
Tana isa gida ɗaki ta wuce ganin babu kowa a tsakar gidan da alama Kaka tana ɗaki, tana shiga parlour ta iske babu kowa nan ma, cikin bedroom ta shiga ganin Kaka kwance a saman gado yasa ta ƙarasawa.
"Kaka na dawo, ki tashi ki kira basamude ya ɗaukeni photon ya tura ma Daddyna."
Tana maganar tana ɗan bugun jikin Kaka alamar ta tashi, magana take amma Kaka taƙi tashi, sai da ta kira sunanta da wani irin ƙarfi.
Cikin firgici Kaka ta buɗe ido suka sauka a kan fuskar Haisu.
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un gamo na yi ko tabbas muryan Haisu ce ba taba yaran Aljanu ba"
"Kaka nice fa"
"Ke Hafsatu dambe kika yi da kura ne?"
Turo baki tayi gaba tana kallon Kaka cikin shagwabar da ta zame mata jiki a ko da yaushe.
"Ni ki tashi ki kira wannan Basamude ɗin ya zo ya ɗauke ni photon a turama Daddyna"
Shiru Kaka ta yi kamar ba zata motsaba amma ganin mitar Haisu bazata ƙareba yasa ta miƙe ta fito ɗakin.
Tana fitowa ɗakin Julaibib ta wuce, daga bakin ƙofar ɗakin ta tsaya bata ƙarasa ciki ba, tana magana daga bakin ƙofar ɗakin.
"Kai Zuraibib zo ka raba ni da wannan fitinar ta Haisu, zo ka mata shi wannan ƙyasta ƙyastar, ka turama ubanta da shi ko ta barni in samu in yi bacci.
Shirun da taji an yi ne yasa ta shiga ciki don ganin ko yana cikin ɗakin ne yana ji ya yi banza da ita.
"Zuraibib baka ji na ne?"
Ganin babu kowa a ɗakin yasa ta fito ta janyo ɗakin, har ta kai ƙofar ɗakinta ta ji sallamar shi ya shigo gidan riƙe da wasu manyan ledojin kaya, wuri ɗaya ta samu ta tsaya ya ƙaraso.
"Alhamdulillah faɗuwa ta zo dai'dai da zama"
"Shiga ka a ji ye kayan don Allah ka yi ma yarinyar nan kyasta ƙyasta, don Allah ko zan samu salama."
Cikin parlour ɗinta ya shiga da kayan hannunsa don ba zai iya wannan tsayuwar ba bayansa ta biyo, sai da ya a jiye kayan hannunsa sannan ya kalleta a wahale kamar ya yi aikin wahala ya ce.
"Meye ƙyasta ƙyasta kuma?"
"Photon ku na zamani mana"
"Sai na dawo masallaci yanzu gab a ke da kiran sallah sai an yi sallah, na yi bacci na huta sannan zan yi mata"
"A'a kana dawowa masallaci ka yi mata"
"To" Shine abinda kawai ya ce mata ya tashi ta fita ko ledar bai buɗe ba, ita ma bata tsaya ganin me ye a ciki ba ta wuce ta koma ciki.
Lokacin da ta shiga Haisu na zaune baki gado tana jiranta,
Julaibib yana shiga ɗakinsa, toilet ya wuce ya yi alwala kasancewar lokacin sallar Azahar ya yi.
Yana fitowa bai jima ba a ɗaki ya ɗauki casbaha, ya fita ya wuce masallaci.
Haisu na zaune Kaka ta ce, "Ya ce sai ya yi sallah sannan kema ki wanke wannan kwalliyar ta yaran Aljanu kiyi sallah, lokacin ya dawo."
"Sai ya dawo ya yi min sannan zan wanke fuskata"
Shiru Kaka ta yi mata don tasan tun da ta ce sai an yi zata yi, ba zata canja maganar ba, kuma yanzu a ke sallar, duka ƙarfe ɗaya da wasu minutes.
Tashi ta yi ta wuce ta ɗauro alwala, ta dawo ɗakin ta gabatar da sallah, duk Haisu na zaune tana kallonta, har ta gama tana addu'a.
"Kaka kima Mamana addu'a, sannan kiyi ma Babana, addu'a shima."
Sai bayan Kaka ta gama sannan ta kalli Haisu da ke zaune a saman gado ta ce.
"Kullum cikin yi musu addu'a nike babu dare babu rana."
"Kina jin yunwa ne?"
"A'a kada ki yi girki ni bana so yau ki bari sai dare sannan ki yi abinci mai daɗi."
"Ummm shi Zuraibib ɗin waye zai bashi abinci yaci?"
"Shi ya cika cin abincin tsiya"
"To ko a daina basa abincin ne"
"Ehhhhh"
Dariya kawai Kaka tayi ganin tsantsar yarintar Haisu da shiri'rita.
Kaka tashi tayi ta fita tabar Haisu a ɗakin, tana fitowa ta ci karo da Julaibib ya shigo, zai shige ɗaki.
"Harka dawo"
"Ehhhh, barka da gida"
"Yauwa"
Ɗaki ya shiga, ya yi wanka yana fitowa ya ɗauko wasu kayan a cikin wardrobe ɗinsa , bai jimaba ya gama shiryawa cikin.White T-shirt, dark burgundy button-up shirt, dark burgundy trousers, burgundy suede loafers with silver buckle, burgundy leather wristwatch.
Kayan sun zauna a jikinsa sosai ya yi matukar kyau, jikinsa ya shiga fesama turare kala kala ƙamsun su ya gama rikita zuciya da ɓargon jikinsa duk ɗakin ya gama cika da ƙamshin, key ɗin mota ya ɗauka ya fito ɗakin.
Yana fitowa ɗakin Kaka ya wuce.
"Ke kina ina fito in miki photon in wuce in tafi in da zan tafi."
Tana jin muryarsa ta miƙe ta fito, hankalinsa na kan wayarsa da yake duba yana yin report ɗin kayan da aka turo masa daga Company.
Tsaye take tana kallonsa bata ce komi ba ganin alamar mutum tsaye a kusa dashi kuma yana jin sauƙar nunfashinta ƙaɗan kaɗan, yasa ya ɗago kai ya kalleta.
Tun daga ƙafarta yake kallo har zuwa kan fuskarta da a ka gama cikawa da wata kwalliya wacce ba zai bada discription exactly yanda a kayi ta ba.
"Ke gasar fidda shugan ƴan bori zaki je?, ko bokanya kika zama bani da labari, ko shugabsncin bokaye zaki amsa."
Baki ta turo tana kallonsa taƙi magana sai ma wani juya ido take alamar wacce take wurin tantance sarauniyar kyau.
"Ba magana nake miki ba?" Taji maganarsa a tsakiyar kanta don ya yi maganar ne cikin ɗaga murya, wanda har saida ta tsaida idanunta wuri ɗaya.
"Ni haka nike son gayuna irin na Mairo ne kuma kowa yasan nayi kyau, har kallo na ake yi"
"Ba dole a kalleki ba tun da kin koma kamar wata bokanya, wuce ki wanke wannan fuskar bana son kallonta"
Buga ƙafa ta fara tana kuka, wanda kukan yake hawa kansa sosai baya son kuka kwata kwata a rayuwarsa, cikin wata kasalalliyar murya ya ce.
"Please ki koma bedroom ki gama kukan sai ki wanke fuskar, ki fito in miki abinda zan yi in wuce ina da abinda zan yi."
Jin yace haka yasa ta wuce ta koma cikin bedroom ɗin, komawa tayi ta zauna a ƙasa tana kuka ganin kukan a ƙasa ba zai mata ba, saita miƙe ta haye saman gado tana wurgi da Pillow.
"Ni wallahi ina son kwalliya ta, kuma wallahi baƙin ciki a keyi mi ni, wallahi ba zan wanke ba, sai dai a kashe ni."
Duk maganar da take Julaibib na jinta, bai ce mata komi ba kuma bai fita ɗakin ba.
"Don kawai mutum na baƙin ciki a binni babu masu irin kwalliyata shine za'a ce in wanke, yasin sai dai matsatstsaku ta kewaye gidan nan amma ba zan wanke ba."
Jin kalmar matsatstsaku yasa Julaibib sakin dariya mara sauti, a zuciyarsa yana jinjina girman mugunta ta wannan yarinyar.
Jin ya yi shiru bai ce mata komi ba, kuma Kaka bata shigo ta ce mata komi ba, yasa ta koma tsalle a saman gadon tana tuma tana tashi.
Ganin haukar tayi yawa ne yasa ya tashi ya shigo ɗakin, tana ganinsa ta ruga da gudu ta shige cikin toilet bata wani daɗeba ta fito ta wanke kwalliyar duka.
"Kuma wallahi ba zan kwance gyaran gashi na ba"
"Ki fito in kin gama haukar, mahaukaciyar banza me kama da ƴan bori"
"Kai kuma boka ɗan dugaji" a hankali ta yi maganar amma saida yaji abinda ta ce girgiza kai kawai ya yi bai ce komi ba ya wuce parlour.
Ledar da ya a jiya ɗazu ya ɗauka ya fara fito da wasu kaya.
Burgundy and ivory satin princess dress, high neckline, short puff sleeves with sheer ivory fabric, fitted burgundy bodice, full flowing skirt with ivory center panel, burgundy side panels, intricate gold and burgundy floral embroidery with pearl and bead embellishments, matching burgundy-and-ivory hair bow.
Tana tsaye tana kallonsa kayan sun yi mata kyau sosai tun da yana fiddosu take kallo tana jin daɗi.
Ɗago kai ya yi, ya kalleta, "Zo ki ɗauka ki saka."
"Ni ban iya saka kaya ba, Kaka ce ke saka min"
"To ni kike so in taɓa wannan jikin naki da baya samun wankan kirki"
"Nima ai bance ka taɓa ni ba, Allah ya kyauta namiji ya taɓani in yi ciki."
Zaro ido Julaibib ya yi don bai yi tsammanin jin wannan maganar a bakinta ba, Kaka ce ta shigo parlourn tana shigowa idonta suka sauka akan kayan da Julaibib ya fiddo ma Haisu.
"Kai wannan kaya da kyau suke"
"Kaka zo ki saka min kayan"
"Ke bana son iya shege yanzun nan da kanki kika saka kaya kika fita ko?"
"Ni wallahi ke zaki saka min"
Ganin rigimar zata yi yawa yasa Kaka ta ɗauki rigar ta ce "Cire kayan jikinki in saka maki"
"A gaban namiji Allah ya kyauta"
"To don iyayenki ba ɗan uwanki bane"
"Ni wallahi ba zan cire kaya a gaban ƙato ba"
Ta ƙare maganar tana murguɗa baki cikin zafin nama Julaibib ya ɗago tako ɗaya ya kai wurin da take.
Bakinta ya murɗe wanda sai da ta saki wata ƙara mai ƙarfi, sannan ya saki ya koma ya zauna yana mata gargadi da hannu ba tare da ya ce komi ba zuciyarsa sai wani haushi yake ji wato shine katon don ubanta.
Uban me zai gani a shegen ƙirjinta mai kama da ƙirjin kaza.
"Mtswwww" yaja wani tsaki mai sauti duk yaji wani haushinta yake ji wanda in ya biyema zuciya zai iya mata dukan da zai iya mata illa.
"Na shiga uku zan zama leɓatu Kaka dubamin leɓena ya ƙara girma"
"Ni wallahi tallahi bana son in zama leɓatu mai katon baki"
"Ke don iyayenki ki fita ido na in rufe muje kisa kayan ki wuce ya miki abinda zai yi tunda baya jin tsoron Allah yana zaluntar marainiya"
Kaka ta kama Hannun Haisu ta ɗauki ledar kayan suka shiga bedroom ɗin.
Suna shiga basu jima ba Haisu ta fito sanye da doguwar rigar tayi mata matuƙar kyau ta haske farar fatarta, kasancewar rigar Marron da Milk sai kayan suka ƙara hawa jikin nata sosai.
"Gani"
Ko kallonta bai yi ba ya miƙe ya fita tabi bayansa, a tsakiyar gida ya tsaya, ganin hakan yasa ta je wurin da yake.
"Dawo nan wurin rana." Babu gardama ta wuce wurin da ya nuna mata, tana tsayawa ya ɗago yana kallonta gaskiya rigar tayi mata kyau sai yanzu yaga tsananin kanninsu da ita, bai bari tunanin ya yi tasiri ba, ya fara ɗauƙar photon, photo biyu ya ɗauka, ya ce ta wuce ta basa wuri.
Babu gardama ta wuce, ko ɗaki bai shiga ba ya shiga WhatsApp ya turama uncle photon, kamar jira yake, ana turawa ya buɗe ya gansu, ba'a ɗauki lokaci ba ya masa reply.
"Son please why not ka kaita photographer ya mata wannan photon basu min kyau ba, Jannat ta fika iya ɗaukar photo"
Reply ɗin ya gama karantawa, jin jikinsa ya yi, ya masa wani nauyi, yanzu duk wannan ƙoƙarin da ya yi sai kuma Uncle ya haɗa sa da wani sabon aikin na zuwa wajen wani photographer.
"Please Son ka je ka kaita tasa duka kayan a ɗauketa photo da su in da dama, Please ka mata video da an fara photon har a gama."