SALMA ELM

5

by @hijjartabdoul06

***********Daada na zaune ya ga lokacin tashi ya yi, Ya kira Ibrahim yace masa ba zai samu damar zuwa ba.

"Amma shine be sanar da ni ba tsabar iskanci sai da na ɗauki waya na kira shi. Anya wannan yaron zan riƙe ita kuwa da amana ko bayan rammu?

Dadda ta taɓe baki ta ce, "Ina zancen amana anan Malam? Ai babu ita, kaf cikin Yayunta bana jin wanda zai iya riƙeta, ba kamar ma ace Manniru da Ibrahima".

"Tana ƴar uwarsu idan basu riƙeta ba uwarsu za su riƙe? Kina gani itama uwar ta bata son ta take ba, har dukan take yi, na rasa gane wannan ƙiyayya daga ina ta fito ta so".

"Uhm Malam kenan, ai lamarin nan sai addu'a kawai amma babu zancen so acikin lamarin yaran nan. Kamar wanda suka tsaneta".

Tashi ya yi yana cewa, "Bari ni naje na dubata da kai na, na ganta".

Sai ga Maryam nan ta shigo da sallama ta gaida su sannan ta bada jakar Salma.

Daada ya ce, "A'a yau ba'a tashi ba ta taho ne?

Ta ce, "Ehh daga break bata dawo ba".

Dadda ta ce, "Ikon Allah to ina wannan yarinyar ta tsaya haka?

Maryam ta ce, "Furaira tace min ta tare mata faɗa yanzu da zan shigo, kuma sai Baban wai ya kama hannunta suka tafi, wataƙila suna can gidan".

Dadda ta ce, "Shikenan, ya kashe ta".

Ta faɗa tana tana taɓa hannu da sallallami.

Daada ya jinjina kai ya ce, "Je ki Maryam".

Sai kuma ya ƙarasa takalminsa ya fice.

"Yooo Malam, nima ai zama be kama ni ba".

Cewar Dadda tana miƙewa ta saɓi mayafinta itama ta fito ko rufe gidan bata yi ba ta suka fice abinsu. Yana gaba tana bayansa har suka ƙarasa gidan Baba dake babu nisa.

"Tsabar iskanci da rashin mutunci ne wannan, ina take Ummun tawa?

Daada ya faɗa a cikin parlourn Umma anan ya san zai same su gaba ɗayansu, da gudu ta fito daga cikin ɗaki, tashinta daga bacci kenan zata yi fitsari ta wuce gida ko toilet ɗin bata shiga ba ta fito ta ɗale jikin Daada. Da wuya ka ga Salma ta yi baccin rana sai idan bata da lafiya.

"Innalillah wa'inna ilaihirraji'un, innalillah wa'inna ilaihirraji'un".

Suka haɗa baki shida Dadda suka faɗa.

"Me nake gani haka? Kuna cikin gidan nan? Lalle Mariya da Sakinah baku da imani wallahi. Saboda ina son ƴar? Shine zaku haɗa baki da mijin ku ki kashe mana ita? Wato mijina ya faɗi ya mutu ko?

Cewar Dadda tana riƙe haba, ita kuma Salma ta sake fashewa da kuka tana ƙanƙame Daada. Daada tsabar haushi be iya furta magana ko daya ba kawai ya kama hannunta ya fice daga gidan. Tatas Dadda ta yi musu sannan itama ta fito.

"Innalillah mukam munga bala'i a cikin gidan nan".

Sadiq ya faɗa.

Bala ya ce, "Muna kan gani zaka ce. Ai bamu gani ba".

Mama tace, "Ohh ni Wann lamarin har tsoro yake bani yarda suke son wannan yarinyar da yawa, tunda suke da mu fa, ba su taɓa shigowa inda muke ba. Har gwara Daada yakan zo ya yi sallama yace a miko masa yaro a kofar gida. Amma Dadda haka tacewa be zata je ta dauko a gidan surukai".

"Amma ku duba, tun tana jarira suke shigowa har su zauna saboda ita kawai".

Umma tace, "tsufa ne, suna girma suna rage faɗa, sai kuma suke son yara"..

Sadiq ya ce, "Umma wanne irin suna rage faɗa kuma?.

Ta ce, "Sadiq wannan ai ba faɗa ba ne. Rikici ne".

**********Tana kwance ta yi lumus da ita tun dukan da Baba ya yi mata, yau ba inda ta fita. A ɗaki ta wuni ko cafe ɗin na ta bata je ba. Sai sha ɗaya Ibrahim ya shigo gida yau ya yi aiki sosai ya gaji tun safe da ya fita be dawo ba, tunda ya shigo be jita ba har ya yi wanka. Be ci abinci abinci ba dan ya dare ya yi.

"Ina Ummu? Na jita shiru yau ko ba lafiya?

Dadda ta ce, "Uhmm ubanku ne ya zaneta, tana can a ɗaki gobe asibiti zamu je. Yoo jikinta zafi ƙau da shi bata da lafiya ba dole mu je asibiti ba".

Shiru Ibrahim ya yi karya ce ace ya ce.

"Ayyahhh. Allah ya sauwake".

"Allah yasa har zuci. Dan a ranka kana nan na cewa calama haka".

Daada ya faɗa masa yana sake ƙure volume ɗin radio. Be ce komai ba ya ce.

"Sai da safenku".

"Allah ya bamu alheri".

Suka bashi amsa a takaice. Salma na ɗaki ta ji wayar Dadda na kara a ƙasan pillow. Ita yau duka bata yi waya da ko ɗaya daga cikin samarinta ba, numbern Mufeed kawai ta sa Fahad ya turo mata, kuma ta yi ta kira ne be ɗaga ba. Ganin number ba numbern Mufeed ba, har zata ƙi ɗagawa sai kuma kawai ta ɗaga ta yi shiru.

Ita bata yi magana ba, haka wanda ya kira shima be yi magana ba, har tsayin minti goma, kuma batare da kowa yace da kowa komai ba. Ba kuma numfashin juna suke ji ba. Ganin lokaci ya na tafiya kuma dare ne ba rana ba hakan yasa shi cewa.

"Bakya magana a waya kika jera min kira?

Dan ya ga sunanta a truecaller.

Da sauri ta tashi zaune zumbur tare da ƙwalalo ido.

"Malam Mufeed kai ne?

"Ai ba wannan layin na kira ka ba".

"Ina yini? Assalamu alaikha, ya yau? Ka yini Lafiya? Ya ka yi? Dan Allah ka yi hakuri. Ban taɓa tunanin zaka kira ba. Kuma a yau din ma. Kasan me? Gaskiya ka bani mamaki. Kasan wani abu?

"Allah ka burgeni, to wanne daga ciki? Abota? Ko soyayya? Uhm?

Yana daga kwance ya tashi a hannun ya jinjina da jikin gado yana shafa kan sa. Baya jin ya taɓa haɗuwa da yarinya mai tarin abubuwan mamaki kamar wannan yarinyar haka..

"Ka yi shiru ka bani amsa mana".

"Wacce amsar zan baki daga ciki?

Ya faɗa a hankali yana sake lumshe idan sa.

"Amsar dukkan tambayata kama daga sallamar da na yi maka zuwa abubuwan da na tambaye ka. Ko na sake jero maka su?

"Uhm?

Ta faɗa a hankali tana sakin murmushi. Kana jin muryarta zaka gane ta ji daɗin kiran da ya yi mata ne ba komai ba.

"Nikam xan iya cewa wani abu? Ina son ka".

Dum kunnensa ya ji ya yi masa wani iri. Dan wallahi be yi expecting wannan abin ma zai ji.

"Ka yi shiru. Ka yi haƙuri. Ban sakewa idan baka ji daɗi ba. Amma fa soyayya ta wucin gadi ba ta gaske ba uhm?

"Ka yi magana mana wai".

Ta sake faɗa a hankali. Sai kuma ta lanƙwashe ƙafarta daga zaunen da take akan gado.

"Ka yi shiru fa, ina ta magana".

Hannunsa a hankali a cikin sumar kan sa.

Ya ce, "Kin bani damar yin hakanne?

"Tohm ka yi bacci. Zan barka ka yi tunanin. Amma ka sani soyayya kaɗan na nema a domin na ga na cika ka da farin cikin. Sannan akwai sharaɗi da dokoki da za'a bi. Ka yarda? If baka yarda ba, mu tsaya a iya abota kawai. Ka ji Malam Mufeed?

"Yanzu sai da safe ka yi bacci".

Ta faɗa tana kashe wayar, kawai ya bi wayar da kallo cike da tarin ɗimbin mamakin yarinyar nan. Gaba ɗaya ya tafi wani tunanin na daban a cikin kan sa, wato kam ita ce zata barshi ya yi tunanin ma kenan ko?..m

Cikin dare yana bacci kawai ya ji wayar sa na vibrating, a hankali ya buɗe idan sa tare da janyo wayar dake kan drawern sa ya ƙurawa numbern ido. Aka sake kira, kafin ya ɗaga.

"Bacci ka ke?

Sai ta saki murmushi mai sauti.

"Dan Allah da kuma girman sa, da cewar shi ɗin shine, na sake haɗa ka da shi da kuma girman sa, ka tashi ayi sallah ka ji? kar a koma wannan baccin dan Allah. Zaka yiwa su Alhaji addu'a ko? Sallahr dare tana sanyawa mutum duk wani hali ya dena. Zan ke roƙar Allah yasa nake ta ganinka kana murmushi. Yanzu de ka tashi lokacin faɗawa Allah buƙata ne".

Ta faɗa a hankali cikin wata irin murya mai daɗi ta alamar daga baccin itama ta tashi. Sai kuma ya ji ana a wayar ana cewa.

"Ke da wa kike waya da wannan tsakar daren?

"Malam Mufeed ne, wanda na ce masa ina so mu yi abota da ko soyayyar wucin gadi na sa shi farin ciki? Kin tuna shi?

Be gama jin ƙarashen zancen ba ta kashe. Amma kam ya gama cika da tarin ɗimbin mamakinta. Is she that serious da zata tashe shi tsakiyar daren nan tace masa ya yi abu? Sai kuma ya yi juyi, kafin a hankali ya rufe idon sa dan komawa bacci.

Kasa komawa baccin ya yi hakan yasa shi tashi ya shiga toilet ya yi alwala, yana fitowa ya ga kiran ta, ta katse amma sai ya ga an sake kira.

"Baccin ka koma? Ko ka tashi? Ka yi haƙuri na dame ka ko?

"Kar ka ji haushina fa, ka tashi ka yi Sallah. Idan kai ba zaka yi addu'a ba. Ni ka yi min addu'a"

Ta faɗa tana kashe wayar. Be sanda ya yi wani irin murmushi shi ba yana shafa kan sa. Wato shine zai mata addu'a? Idan ba zan yi ba shi kenan to meye amfani ta shin nasa?

Murmushi sosai ya ji yana ƙwacewa a fuskarsa.

'ikon Allah'

Ya faɗa a ran sa yana jinjina kan sa. Sak kuma ya girgiza kan sa kawai yana kallon gabas ya tada sallahr.

Ƙarfe biyar na asuba ta sake kiran sa, ya kalli wayar, dan har lokacin be koma bacci ba. Ƙin ɗagawa ya yi ya wuce ya tafi masallaci da ya dawo ya ga tarin missed calls ɗin sa sai kuma ya ga message ɗin sa.

"Na kira ka na tashe ka sallah. Allah yasa ka tashi. Ka yi haƙuri da ni ka ji?

Girgiza kan sa ya sake yi kawai yana ajje wayar be kulata ba, shikam ya gamu da hau kala-kala.

Ƙarfe bakwai dai-dai wayarsa ta sake yin vibrating. Cike da gajiyawa ya buɗe idan sa ya zubawa wayar ido, yana jin ƙinwar miƙa hannu ya ɗaga dan besan waye yake kiran sa ba da wann safiyar ba. Hakan yasa shi jan ƙaramar tsuka yana juyawa. Batare da yaga waye ba ko ya ɗaga ba har ta katse. Aka sake kira, hakan yasa shi sake jan wata doguwar tsuka yana jin ɓacin ran da be san daga ina ba yana bacci an katse masa shi. Sai kuma ya sake juyawa ya miƙa hannu ya ga numbern Salma ce. Kafin ya ɗaga yana yin shiru.

"Assalamu alaikha. Ina kwana. Kana magana da Ummusalma El-Mustapha ne. Ya ka ke? Ka tashi lafiya? Idan bacci ka ke,ka tashi bakyau baccin asara da safe haka kawai. Yauwa na gode".

Sai kuma ta kashe. Kawai ya bi wayar da kallo cike da mamakin ta, wai wannan yarinyar anya kan ta ƙalau kuwa?......

Sai kuma ya rufe idan sa yana so ya koma bacci, amma jin baccin ya tafi yasa shi tashi kawai yana mai jan tsaki sosai. Wanka ya yi yasa kayan sa kamar ko yaushe ƙanana kaya. Kafin ya fito daga ɗaki. Yaran gidan su duk sun tashi za su je makaranta sun shirya tsaf abinsu. Yayinda kowa na gidan ya tashi ma su tafiya makaranta da aiki. Dukan su shida ne a gidan su. Yana da Yayu biyu sannan shi sai kuma Fahad, sai kuma Khadijah da Safira.

"Ina kwana?

Suka gaida shi. Jinjina masa kai kawai ya yi yana kallon Fahad dake shan shayi yana kuma duba handout.

Mudan ya ce, "Kai Fahad, wai sai yanzu ka ke duba abinda zaka yi test din akai?

"Babban Yaya kawai sarawa fa ake. Da asuba fa naga wai za'a yi test din".

Idris ya ce, "Daman Fahad baka karatu kwata-kwata".

Tsuke baki ya yi, Khadijah ta ce, "Wai Yaya Idi kasan me nawa yake ci a test ɗin sa? Wallahi 2 naga ya ci over 30".

Kwabe mata baki ya yi ya ce, "Ke ki ci 2 ɗin mana, banza magulmaciya".

Abbansu ke saukowa shi da Mamansu yana jin sa yana cewa, "A'a me ya faru ake dukanta? Fahad ban hanaka saurin hannu ba?

Shiru duk suka yi suna maida hankalin su wurin abincin na su. Kafin suka gaida iyayen na su.

Mufeed ya kalle su kafin ya ce, "School ɗin na ku haka ake zuwa ba hijabi?

Ganinsu dukan su daga su sai hula kuma rigar bata ƙarasa musu har ƙasa ba.

Mudan ya ce, "Haka suke zuwa mana, kamar wasu kiristoci gasu nan".

Be ce komai ba.

Maman su ta ce, "Zaka fita ne? Naga ka tashi da wuri".

A hankali ya girgiza kan sa kawai yana zuba shayin shima. Ya sauka daga dining din yana komawa ƙasa ya zauna. Da kallo kawai ta bishi tana girgiza kan ta. Taga ranar da zai zauna su ci abinci.....