7
**********Da bala'in gudu ta shigo gidan tana ture Ibrahim da yau da wuri ya dawo saboda zai je Abuja Interview ya dawo domin ya shirya ya kuma siyo kayan da baya da shi.
"Ke me yasa baki da hankali ne wai dan Allah?
Washe masa baki ta yi ta ce, "Ka tayani murna. Na samu admission, zan zama likita ne fa".
Tsaki ya ja kawai yana cigaba da karkaɗe takalminsa.
Ya ce, "Bana jin zaki zama ko likitan Mahaukata ne bare na mutane, marar hankali kawai....
Daada tana daga parlour ta ce, "Kawai ka ce mata mahaukaciya bata da hankali, shine abinda ya kamata ka ce mata, tunda kai a duniya bazaka taɓa yin farin ciki da abinda ƙanwarka ta zo maka da shi ba".
"Yoo ta zama likitan mahaukata ai ta zama babbar likitar da za'a yi alfahari da shi da fariya da kuma tutiya. Tunda ba kowa ne yake yin aikin ba. Kai ɗin da baka san komai ba, shashahan banza kawai".
"To Dadda kinga a yarda ta shigo ne? Kalleta ki ga dan Allah. Yarda kika san doya haka take, take yawo sandar sandar da ita, sai anyi magana ku ce ta girma ta balaga ta fara period. Amma ba hankali a tattare da ita. Wawiya kawai".
Ganin ba zai yi shiru ba yasa Daada fitowa daga parlourn, Salma ta yi wurinta tana kwanciya a jikinta ta rungumeta tana turo baki.
"Rabu da shi kinji? Allah yana tare da mai gaskiya, kuma duk ɗan baƙin ciki a haka zai ƙare".
Taɓe baki shima ya yi kawai yana maka mata harara.
"Shi kayan na ta wanke ne ba zaka yi ba? Ka wanke iya nawa ko me?
Yana ɓata rai sosai ya ce, "Ni bance ba".
Ya faɗa yana maka mata harara. Gwalo ta yi masa tana rugawa da gudu ta shige cikin ɗaki tana sake kwaso wasu kayan.
"Ka ga wasu kayan Yaya Ibrahim....
"Dan ƙaniyarki ba zan wanke ba, wannan kayan ba ranar nan na wanke ba? Zaki mayar ko sai na ballaki shegiya kalar aljanu".
Tana wani irin kalar tura baki ta ce, "Ai de uwarmu ɗaya ubanmu ɗaya,idan ni shegiya ce kai ma...
Taku ɗaya ya yi ya cimmata ya riƙe hannun da kyau, daman tun safe yake jin haushinta.
"Dawa kike?
Ya faɗa yana murɗe mata hannu da kyau yana kallonta.
"A'a Ibrahima, saketa, kada mu yi haka da kai, zan bugawa Malam waya ya dawo ya cimmaka fa".
Sai da ya bubbuge mata bakin sannan ya saketa.
"Kuma wallahi na sake ganin kin fita waje a haka. Banza marar kamun kai".
Tana share hawaye ta yi wajen Dadda tana turo baki.
"Ka cigaba da abinda ka ke yi".
"Gaba ɗaya kun bi kun ɓata yarinya, kun sangarta ta".
Dadda ta ce, "Dan ka ga zaka tafi Abuja? Shine ka ke yi min a abinda ka ga acikin gidan nan ko?
Kamar ita ce ke kuka ba ta wani kalar irin washe baki ta ce.
"Daada Abuja zai je? Me zai je ya yi? Interview ɗin aka kira shi?
Taɓe baki ta yi ta shige parlour tana cewa, "Tambaye shi ni bansan masa ba".
Matsowa zata yi kusa da shi ya maka mata harara, ba shiri ta darwaje baki ta ja baya, tana ƙarasa share hawayenta.
Sai ga ƙawarta Maryam ta shigo da gudu ta yi tsokana. Ta shige parlourn Dadda. Daga waje suka ji an acewa ai ba dawwama zaki yi a gidan ba zaki fito.
"Babban bala'i, Maryam ke da waye haka, yake mako wannan zagin? Baki tsaya kin fasa masa baki ba, kike gudu?
"Bari ki ga na je".
Ta faɗa tana saɓar taɓarya ta fice da gudu ko kallon Ibrahim bata yi ba balle ya yi gigin hanata.
Kawai da kallo ya bita yana sauke ajiyar zuciya tare da girgiza kan sa.
"Sai de fatan shiriya".
Ya faɗa yana kallon Maryam da take leƙowa ta bayan labule. Hayaniyar da ya ji a waje ce yasa shi dole fita, yana zuwa yaga abinda Salma ta yi, ta fasawa yaro kai da taɓarya kuma ta haƙiƙance tana masa masifa.
"Ba uban da ya isa ya taɓa ni a cikin garin nan ban ƙaddar masa ba. Uban waye yace ya zageni? Ai ba dani yake faɗan sa ba. Uwar kuturu ta yi kaɗan balle ta makaho. Kuma daman na ce masa kada ya kuskura ya sake ya cikawa kwaɓarsa ruwa. Ehen".
Ibrahim rasa abinda zai ce ya yi, mutane suka zagaye su ana bawa yaron haƙurin ga jini sai malala yake. Sai kuma ta koma gida da gudu ta ɗauko First aid ɗin su, ta zo ta shiga gyara masa wurin.
"Na ce maka ka dena shiga harkata da ta ƴar uwata baka jin magana, yau na fasa maka kai, gobe Bansan ina ne zan fasa maka ba kuma. Amma ka kiyaye gaba, ka gane ai?
"Yanzu de sannu ka ji?
Ibrahim takaici da haushi ba wanda be ji ba, kawai ya juya ya koma yana yiwa Dadda faɗa. Daada ne ya shigo shima da nasa faɗan akan mutane sun tare shi a waje akan batun Ummu.
"Idan bata kwatarwa kan ta ƴan ci ba. Wa suke so ta ƙwatarwa? Sun fi so yarinya ta zama raguwa ko kuwa me?
Ibrahim ya ce, "Amma de abinda take yi bata kyautawa".
"Tunda ta kama uwarka ko?
Shiru ya yi be sake cewa komai ba. Ta shigo ta samu waje ta zauna a parlourn su, suka fara hira da Maryam kafin kuma can aka aiko ana kiran Maryam ɗin, sannan ta tashi ta shiga ɗaki. Jikinta zafi yake yi mata sosai, tun jiya da aka buge ta. Amma ƙarfi hali irin na ta bata nuna ba. Kwanciya ta yi dan ta gaji da gudun da ta shawa a titi. Ibrahim ne ya shigo ya sameta a kwancen bacci ya ɗauketa.
Jikinsa ne ya bashi dan daman ɗazu ya bugeta ya ji jikinta da zafi. Yana taɓa ta kuwa ya ji zafi, zazzaɓi ya rufe ta.
"Daada Ummu fa bata da lafiya".
"Subhanallahi, bacci ka ga tana yi? Wallahi mugun da wancan ubannaku ya yi mata yasa ta wannan halin ya jefa wannan halin".
"Ka yi haƙuri".
Tsaki ya yi kawai yana jin ɓacin rai.
"Ba zaka je ka ɗauko mota mu je asibiti ba?
Ba musu ya tafi ya ɗauko motar, suka tafi asibitin da Kawu Mudan yake aiki. Dan shi likita ne babba.
Ita da kɗai ta shiga , Daada ya je duba marasa lafiya a cikin asibitin, da hijabi a jikinta Dan karami da ya tsaya mata a gwiwar hannunta. Fuskarta ta yi fayau da ita, amma san shegen zance.
"Laaaaaa Malam Mufeed? Waye ka kawo asibiti? Waye ba shi da Lafiya? Kai ne?
Ta faɗa tana taɓa goshinsa, ta ji ba zafi, amma shi kuma ya ji zafi a hannunta. Ga idon ta da ya yi wani iri.
"Sannu, to mene yake damunka?
Kawu ya ce, "To Shalele ko zaki duba shi?
Murmushi ta yi mai kyau tana komawa kujerar Kawun ta ce.
"Ehh kasan ai zan iya ko?
Jinjina kai ya yi ya ce, "Sosai zaki iya ai nasan halin ki".
Dariya ta yi sosai tana jin daɗi. Sai kuma ta shiga yi masa tambayoyi akan abinda ta ga yana yi. Ya gwada masa bp ga kuma sauran allurai nan da za'a yi masa.
"Ka tabbatar kana shan maganin ka akan lokaci. Kada ka yi sake da su ka ji? Allah ya kara sauƙi, yanzu komai naka ya dawo normal. Ka ke samun hutu a dena tunani".
"Me yake damun sa shi din?
Yana rubuce-rubuce ya ce, "Abubuwa da dama".
"Kamar me da me?
Ta faɗa tana dawowa kusa da Mufeed ɗin ta tsaya.
"Wacce damuwar ce ka sawa kan ka? Ka ga wannan rayuwar kowa da ka ke ganinsa yana da damuwa ko Kawunmu?
Jinjina mata kai Kawun ya yi. Sai kuma aka sake turowa Kofar aka shigo, wasu couples ne suka dawo amsar test ɗin su. Da murmushi a fuskar Kawu ya ce.
"Congratulations".
Ya faɗa yana miƙa musu takardar.
"Fatan in the next 7 months ku dawo mana".
Juyawa ta kalle su sannan ta kalli yarda suke murna.
"To cikine da ke ke ɗin?
Ta faɗa tana kallon matar. Murmushi tsananin jin dsdi suka yi.
"Allah ya raya".
Ta faɗa tana kallon cikin.
"To Kawu ya cikin nata be girma ba?
Su de fita suka yi suna rabu da ita, tana yi masa tambayoyi. Shi kuma yana amsa mata daki-daki. Sai jin dadi take yi. Yayin da Mufeed ke zaune kawai yana jin ta.
"Ka jirani, ka kaini gida ka ji?
"Dan Allah, sai mu je ka sha coffee kyauta ne a cafe ɗina".
Ganin idon likitan dake tare da ita wanda ga dukkan ƴan uwana jin tana ce masa Kawu sannan da zuwan da Daada ya yi yasa shi yin shiru be tafin ba.
"Daada ka tafi kawai, idan ya kammala zai tafi da ni...
Wani irin mugun kallo Ibrahim yake aikata mata.
"Daada akan me za'a ɗaura masa nauyi, shikenan kawai....
Ɓare baki ta yi ta shiga rera kuka, harda majina sosai kai ka ce an daketa ne.
"Zan kauɗa maki mari idan baki yi min shiru ba, shashaha kawai".
"To sai ka mareni ai...
"Ibrahim fice tunda ba kai ka kawo ta ba, marar kunyar banza marar kunyar wofi".
Cewar Daada yana tsawar masa. Kafin ya ce.
"A dubaki mu tafi gida ko? Kinga ba'a san inda zai je ba Uhm?
Ya faɗa mata cike da lallashi. Mufeed ya ce..
"A'a can zan je daman, sai na tafi da ita ba damuwa Kaka"..
"Ba Kaka ake cewa ba, Daada zaka ce ka ji ko?.
Ta gyara masa kamar ba ita ta sa kuka ba.
Shi de Kawu na zaune yana kallon ikon Allah, dan yanzu yana tofa a abin zai zama cibi, shi yasa Kawu a yanzu yake mugun yinsa, idan suka ce abu fari ne, to binsu yake a farinne ba ruwan sa be ɗaurawa kan sa ba. Kuma daman shi ba mutum ne me faɗa ba, Baba ya fishi tsauri kowa a wurin sa yake samun sassauci.
Allurai aka yi mata da magani sannan suka tafi. Shine ya bude mata motar ta shiga sannan shima ya shiga yana kallan yarda take darwaje baki. Koda suka shiga surutu kawai take zabga masa kafin ya ji ta fara shirme sai kuma ta yi bacci, kawai kallonta ya yi ganin yarda take bacci. Kawai girgiza kan sa ya yi yana gangarawa bakin titi ya gyara mata kujerar sannan ya gyara mata kan ta dan kar ya ƙage. Sai da ya gama ƙare mata kallo sannan ya ja suka tafi.
Hannunsa ya sa a saman goshinta ya ji zafi har yanzu hakan yasa shi ƙin tashinta, yana ɗauke hannunsa ta buɗe ido a hankali a kan sa.
"Mun zo? Wai bacci ne na yi?
Be yi mata magana, kawai ya bude motar ya fito, itama ta buɗe, tana fitowa direct kitchen ta nufa ta haɗo masa coffee da emoji na smile a kai da kuma ɗayan kuma small cup cake ne a tray an rubuta zanen heart alamar I love you.
"Lemme propose you".
Ta faɗa tana durkusawa da tray ɗin a hannunta.
"I love you".
Ta faɗa tana kallon cikin idanun sa, da ya kafe mata da ido yana kallon abubuwan mamaki.
"Yes I meant it".
Ta tabbatar masa tana tashi tsaye kafin ta yanka cake ɗin ta ta sa baki. Sai kuma ta tura masa coffee ɗin nasa.
"Ya ka gani?
"Please smile".
Ta faɗa tana masa alamar smile da hannunta tare da sakar masa narkakken murmushinta mai kyau......