8
*********Ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke a hankali yana cigaba da kallonta. Sai kuma ya kalla abinda aka ajje masa kafin ya kalleta. Sannan ya sakin cute smile yana ganin tarin snacks ɗin da ake ajjewa. Idan sa cike da ƙwalla.
"Remember something?
Ta faɗa masa tana kallonsa. Kallonta ya yi yana mamakin yarda akayi ta gane da sauri haka. Sai kuma ya sake kallon abubuwan yana shareta. Murmushi ta yi masa mai sauti ta ce.
"A'a, kada ka ɓoye shi, ka sanar da shi. Hakan zai sa ka ji daɗi. Ko ba wani ba uhm?
Sake kallon ta ya yi sannan ya kalla coffee din sai kuma ya ɗauka da tea spoon zai yaɗe kumfar. Da sauri ta riƙe hannunsa.
"Heyy stop, ba cirewa ake yi ba. Da shi ake sha, idan baka sha da shi ba taya ne zaka yi dariyar?
Be san sanda ya dariyart ta zo masa. Sai ta gyaɗa masa kai tana sake sakar masa wani irin narkakken murmushinta mai kyan gaske tare da gyaɗa masa kai.
"Ehh man".
Wata ajiyar zuciya ya sauke a hankali yana lumshe idan sa. Sannan ya bude akan hannunta dake kan nasa har yanzun, hakan yasa ta ajjewa tana furta sorry a hankali.
"Inna tana son cake, Shi kuma Alhaji, ya yi ta yi mata faɗa. Sai ta ɓoye ta ci abinta".
Ya faɗa tana tuno Kakanninsa.
"Ban taɓa ganin wanda suke so junansu da kulawa da juna kamar su ba".
"Allah ya baka matar da zata so ka ta kula da kai fiye da yarda Inna da Alhaji suka kula da junansu".
Ta bashi amsa tana kallonsa tare da haɗe tafin hannunta ta ɗaura fuskarta a ciki bayan ta daurasu akan table. Wani abu ya haɗiye mai ɗaci be ce da ita komai ba de.
"Ya Subhanallah".
Ta faɗa da sauri tana nufar wani matashi da ta hango shi ya ji ciwo. Juyawa yayi yana kallon yarda take gudun da ƙarfinta ta ƙarasa inda yake.
"Kar ka jira sai ka je asibiti, ka fara yiwa kan ka taimakon gaggawa bana son musu ƙara so nan".
Ta faɗa tana riƙe hannunsa ta ƙara so da shi barandar da zata sa ka shiga cikin cafe ɗin. Ita kuma ta bada umarnin aka kawo mata first aid. Ta shiga treating din sa. Duk motsawa kadan ya yi zata ce masa sannu kuma cike da kulawa kai ka ce wata likita ce.
"Allah ya sauwake, ka tabbatar ka je asibiti za'a baka magani. Kuma ka kiyaye gaba. Banda faɗa, sannan idan ka ji rauni ka dena ɗaurewa da tsumma na faɗa maka".
Sai kuma ta tashi ta dawo tana zare hand gloves aka kawo mata ruwa ta wanke hannunta ta sa sanitizer ta zauna tana kallonsa. Tunda ya haɗu wannan yarinyar take sa shi a cikin mamaki, har yau kuma be gama fita daga wannan mamakin na ta ba. Ba abinda bata hada ba ita kam.
"Kasan wani abu?
"Kana da ɗan kyau kaɗan, gwara da baka yi fari ba dan da ace kai fari ne ba abinda zan yi da kai. Lemme tell you something,I hate white men".
Ta faɗa tana yatsine fuskarta tare da ɗan gyara zama sai kuma ta ɗauka hoto chocolate ɗin da aka ajje mata.
"Kawai bana son su, kaf samarina babu fari dan basa burgeni. Amma kai kam ka ga nan kamar wani baƙin America da kai".
"Kuma wannan sumar ta yi maka kyau, duk da baka gyarata. Kasan fa ko? Yaya Balan gidan mu yarda yake gyara kan sa ko? Har ya fi wata macen.......
Sai ta yi shiru kafin ta tuntsire da dariya.
"Irina, a duniya na tsani ace za'a min kitso".
"Faɗa min ke ka ke so? Da wanda baka so? Ya ka ke so matar da zaka aura ta kasance? In fact komai na rayuwarka".
Wani gajeren murmushi ya sake yi a hankali yana juya cup ɗin dake hannunsa. Sai kuma ya kalleta.
"Kana kyau da murmushi, ina ma ace fuskarka zata kasance ma'abociya wannan kyakkyawan murmushin?
Murmushi gefen baki ya sake yi yana kallon wani waje.
"Ban yi tunanin aure ba. Dan haka ban san wacce kalar mace zan aura ba".
"Sanda ka yi tunanin aure sannan zaka yi?
Sai ya jinjina mata kai. Sai ta sakar masa kyakkyawan murmushi tana ɗaga masa gira tare da haɗe yatsunta alamar great.
"Hakan ya yi".
Be sake cewa komai ba, ita ce ta cigaba da maganarta, har lokacin sallah ya yi sannan ya tashi yana duba agogon hannunsa.
"Ni bana sallah, kai ka je ka yi sai ka dawo mu tafi".
Har ga Allah sai da ya ji mamakinta, amma kuma sai ne nuna ba ya wuce, sallah ya je ya a wajen cafe ɗin na ta sannan ya dawo yana kallonta.
"Shall we?
Ta faɗa tana tashi, ya gyaɗa mata kai sannan suka wuce.
Ana Isha suka ƙara so gidan dan baya wani gudu sannan sun sami hold up a hanya. A Kofar gidansu ya ajjeta.
"Na gode Allah ya saka da mafificin Alkhairi. Allah ya jikan Alhaji da Inna. Bye bye take care of yourself for....
Sai ta yi dariya tana fita tare da leƙowa ta window.
"Only me before ka samu future wife".
"Byee".
Girgiza kan sa ya yi a hankali yana shafashi sai kuma ya kalleta ganin yarda ta talle ƙeyar wani yaro tana sa gudu ta shige cikin gidan na su.
"Miss Chaos".
Ya faɗa yana sakin numfashi, kafin ya ja motar sa ya yi gaba.....
**********Sai da ya tsaya ya yi sallah sannan ya wuce gidansu. Motar aminin mahaifinsa ya gani a gidan hakan yasa shi sauke ajiyar zuciya a hankali kafin ya shiga parlourn na su. Suna parlourn shi da Abbansu suna tattaunawa. Ya gaida su kawai zai wuce Abban ya kira shi.
"Ga Barrister fa, yace min yana ta so ku yi zance amma kana ƙin zuwa shine ya zo domin ka".
"Uhm".
Ya faɗa yana kallon Barristern sai kuma ya maida hankalinsa kan wayar sa da Salma ta kira. Hakan yasa shi ɗagawa.
"Hi Trial boyfriend".
Be san sanda ya saki murmushi ba jin sunan da ta kira shi wai Trial boyfriend wannan yarinyar bata ji sam.
"Ka je gida lafiya? Hope ban tauye maka hakki ba. Ka yi haƙuri dan Allah idan na ɓata maka rai".
"Ka yi magana mana".
"Uhm".
Ya faɗa a hankali be ce da ita komai ba.
"Na godewa Allah. Byeee".
Ta faɗa tana kashe wayar. Sai ya bi wayar da kallo sannan ya sa sunanta da Miss Chaos kafin ya ɗaga kai yana kallon su Abbah. Shi Abbah waya yake dannawa yayinda shi kuma Barrister ya zubawa Mufeed ido kawai.
"Muna magana da kai kana waya ko? Tsabar reni ne wannan ɗin Ko me?
Be yi magana ba, fuskarsa ta sauya ba kamar yarda yake ba. Sai kuma ya kalli Barrister da ya yi maganar.
Ya ce, "ina ji?
Abba ya ce, "Ka yi haƙuri".
Ya cewa Barrister yana kallansa. Mamaki ne ya ishi Barrister, ko da yake ba abin Mamaki ba ne ba, sam shi be fiye yiwa yaran sa faɗa ba. Kuma sai Allah ya bashi yara masu hankali nutsatsusu da ba ruwansu. Duk inda yaga ana yiwa wani yaron faɗa be so, shi kuma haka Allah ya halicce shi, amma ka ga Alhaji babansa da rasu? Bashi da dama, akwai shi da faɗa sosai....
Ajiyar zuciya ya sauke ya ce, "Game da Companyn Kakanku ne. Kai ne wanda ya ce a bawa. Domin Kai ne ka ke kula da shi, domin ya dawo hannunka sai mun je da kai, ka cike cike sannan mun je har banki da su court domin ayi abun cikin tsari, sannan kowa ya shaida ya kuma ga wasiyyar da ya bari akan a baka ɗin".
"Akwai buƙatar duk ayi wannan?
Ya faɗa yana kallon Barrister. Sai kuma ya shafi kan sa..
"Bana so yanzu. Ka cigaba da ajjewa kana kula da shi for now. Har zuwa sanda zan yi magana akai".
Sai kuma ya sake kallonsa.
"A cigaba da ginin wannan masana'antar da ake ginawa har a kammala abinda aka fara. Idan ta kama a buɗe yi a zuba ma'aikata a fara kasuwanci a wurin a cireta daga cikin gadon da za'a raba domin bana sa ba ne".
"What?
Barrister ya faɗa cike da mamakinsa yana kallan sa. Shima kallon na sa ya yi kafin ya yi magana Barrister ya ce.
"Amma bansan da wannan maganar ba, kuma dukkan dukiyar Alhaji nasan su, sannan Bansan da wannan maganar ba. Ganin ya rasu ya sa na ce a dakatar da ginata".
"Ni kuma nasani. Ba lalle sai ka sani ba".
Ya faɗa kan sa tsaye kawai yana kallon Abba.
"Abbah dan Allah kai na yana ciwo zan iya tafiya?.