SALMA ELM

10

by @hijjartabdoul06

*********Kamar da wasa Mufeed ya fara kula Salma suna soyayyar wucin gadi kamar yarda ta buƙata. Amma a yarda suka shaƙu abin sai ya maka mamaki. Kullum sai sun haɗu a cafe ɗin ta. Haka zata zauna ta yi ta bashi labari yana saurarenta tana dariya, shi de sai kawai ya yi murmushi yake jinta. Idan ta tambaye shi zai amsa. Zai kuma bata amsa cikin kulawa. Hakan daɗi yake yi mata,amma zancene yake kulata suna yi a'a sai de ya ji ta kawai. Kuma be taɓa ji ya gaji da ita ba. Domin tun yana yi mata alfarmar a maimakon Alhaji har ya dena. A yanzu sosai yake jinta a cikin zuciyarsa da kwakwalwarsa, gami da jijiyoyin jikinsa. Ta gama narkar da komai dake cikin ran sa. Ba wanda zai zauna da ita ya ji be son ta, sai de idan mugun hali ne da kai. Amma ta iya mu'amala sosai da mutum. Duk wani hali da dabi'a ta sa, gaba ɗaya ta sauya shi batare da shi kan sa ya sani ba, kama daga bada haƙuri zuwa neman permission ko idan zai fita har ƙarin bayani idan ya yi abu. Gaba ɗaya Mama da su Abbah da sauran ƴan uwan sa kallon mamakin sauyawarsa suke yi. Har kallo yake zama ya yi a cikin su, idan ya gama zai je ya bawa Salma labari idan ta tambaye shi me ya yi da ya dawo gida zai ce mata ya yi kallo, zata ce wannan Film ya kalla. Zai ce ga shi an yi abu kaza da kaza, musamman series film din ya san tana kallo, duk idan ta zauna yin hadda bata samu ta kalla ba.....

Yau tana zaune tana waya da shi.

"Ka kalla Zoya da Aditya yau?

"Eh".

Dariya ta yi sosai ta ce, "Baka cin abinci ko? Idan ka tashi yau zan ce ka shiga kitchen ka daga tea ka ci abinci. Idan baka da shi ka zo ka amsa yanzu ko na kawo maka?

"Ki kawo min kuma?

Ya faɗa tana kallon time.

"Baka so? Gobe sai na baka a islamiyya tunda gobe Asabar zaka je?

Shiru ya yi alamar tunani sai kuma ya ce.

"Ehh zan je".

"Amma ajinmu zaka shigo ko?

Murmushi ya yi a hankali ya ce, "A'a sai kin yi min alkawarin zama a gaba".

Dariya ta yi ta ce, "Na yi, dan Allah ka zo".

Jinjina mata kai ya yi a hankali sannan ya ce, "Ki kula".

"Ba zaka ce ya sunan yayar tawa ba ya kasance? Na yi ɗa, na haihu kuma na faɗa maka? Kai me yasa ka ke da mantuwa? Sannan yaushe zaka je ka gano shi".

Dariya ya yi ya ce, "Ai nasan yarda zai kasance, faɗa da dukan yaran unguwa da neman tsokana zaku yi ta yi ke da Maryam, akwai wani abu sabo ne?

Dariya yi a yi sosai ta ce, "Wallahi kamar ka sani, dan sai da na yiwa wasu yara dukan tsiya wai ni za su rena, kasan karfi gareni kamar dokiya".

Dariya ce ƙwace masa sosai ya ce, "Allah dokiya".

Kawai ya sake sakin murmushi sosai har sautin sa na fitowa.

"Me ka ke yiwa dariya?

"A'a ji na yi kin ce ai dokiya".

Sai ya sake fashewa da dariya kawai yana jin dariyar tana ƙwace masa.

"Allah zaka sani".

"A'a yi hakuri dokiya, ni banda ƙarfi".

Ƙwafa ta yi masa.

"Ina zuwa Mama tana kirana. Allah yasa ba laifi na yi ba".

Dariya ta yi ta ce, "Daman ta ɗan buge ka".

Shima dariyar ya yi yana fitowa daga daki.

Ya ce, "Da sai na kawo ƙararta wurin Daada".

Dariya sosai ta sa cike da jin daɗin yarda ya ɗauka Daada da muhimmanci sosai, har cikin parlourn su yake zuwa su zauna su yi ta hira da shi yana jan sa da magana musamman da ya ji yana cewa ya yi zaman England tuni zance ya barke dan shima Daada ya yi zaman nan din. Haka ma Dadda ba ruwan su.

"Mama gashi za'a gaida ke".

Ba Mama kawai ba har Abbah sai da ya juyo ya kalle shi jin abinda ya ce, ga murmushi akan fuskarsa. Wayar ya ɗaura a kunnen Mama yayinda ita kuma tace.

"Innalillah haka muka yi da kai?

"Assalamu alaikum Warahamatullah".

Ta ji muryar Mama. A hankali ta amsa tana gaida ita kamar tana gabanta. Duk ta san ta.

"Ya kike?

"Alhamdulillah Mama".

Ta faɗa a hankali. Kai ka ce ba ta surutu. Mufeed banda dariya ba abinda yake jin muryarta so innocent ba zaka taɓa cewa tana da magana ba.

"Ga Abbah".

Ya faɗa yana miƙawa Abbah duk zuwa suka yi suna kallon rubutun da ya yi saving numbern na tada shi Miss Chaos. Duk gaisawa suka yi da kowa bata nuna ta gane Fahad ba jin ya fi kowa surutu harda cewa wani Anty...

Tana kashewa ta ji sallamar Ibrahim, da bala'in gudu ta fito daga cikin parlourn tana zuwa ta dane shi ko ƙarasa shigowa be yi ba.

"Yayana sannu da dawowa, wallah kasan wani abu? Allah na yi kewarka sosai. Sai yanzu ka dawo? Da ka ce ba zaka zo ba. Gaskiya ka jima. Ya aikin? Daga zuwa interviewe fa shikenan. Yaya Allah na ji daɗi sosai. Allah ya ƙara arziki ya ƙara budi".

"Na ji sake ni".

Ya faɗa yana raba jikinsa da na ta. Ya na shigewa tare da dacewa.

"Har yanzu baki sauya ba naga ranar da za'a ce yau kin zama wata mutuniyar kirki....

Daada ya ce, "To ita ta banza ce? Kawai ka ce mata bata da hankali bata da kirki, kuma bamu iya reno ba".

Dadda ta ce, "Tunda na ji sallamar ka gabana ya faɗi, kwana biyu bakina shiru bana bari bari. Mu uku a cikin gidan nan, ba wanda yake takurawa Shalele sai da ka dawo".

"Sannun ku da gida".

Ba su kula shi ba, sai de Daada ya tashi suke yana kallon sa.

"Ina tsarabata?

Sai da ya harareta sannan ya buɗe jakarsa ya miko mata leda.

"Bari na je na kaiwa Maryam na ce Yayana ya dawo mai so na".

"A'a ni da nake maƙiyi a wurin ki?

Ya mayar mata da amsa yana kallonta. Darwaje baki ta yi tana janyo mayafin Dadda ta rufa ta fita sai da ta ke waje sannan ta ga kayan, a wajen ta ajje nata sannan ta wuce ta tafi. Gidan su Fahad ta fara zuwa ta bawa mai gadin na su, tace a bashi.....

"Amma yarinya ce ko Ya Mufeed?

Fahad ya faɗa yana wani yatsine fuskarsa.

"Gaskiya bata da ce da kai ba".

Idris ya ce, "Tunda Kai ne zaka zauna masa da ita dole ka ce haka ai".

"A'a wallahi yarinya ce, daga jin muryar ta har na ce mata Anty".

Ta ƙarasa da turo baki gaba, Mufeed be kula shi ba ya kalla Mama ya ce.

"Kika ce kina son magana da ni?

"Eh, akan batun wajen Barrister ne, shi Abbanka ya zuba maka ido, kana zaune kawai a gida. Ba zaka koma ba ka cigaba da aiki? Ba abinda ka ke, sai zaman gida kawai? Ga dukkan alamu kuma gashi nan ka kammala warkewa ba wata sauran abinda yake damunta har ka fi da sakewa da magana kamar ba kai ba".

"Soyayyar da ya fara ne Mama...

Fahad ya faɗa, kallon da Maman ta yi masa ne yasa shi turo bakin sa.

"Tashi ka bani wajen, kafin ranka ya yi mummunan ɓaci a wurin nan".

Idris ya ce, "Allah ya shirye ka Fahad".

Mai gadi ya yi knocking masu ƙofa, Safira ta je ta buɗe.

"Yaya Mufeed kai ake nema".

Shiru ya yi yana tunanin waye kuma? Sai kuma ya tashi ya fita yana zuwa yaga Mai gadi ne ya miƙa masa sakon sa a leda. Cookies biscuits ne guda biyu manya da chocolate guda biyu suma manya masu ɗan tsada da su. Murmushi ya yi a hankali kafin ya ce.

"Ta yi nisa ne?

"Yanzun de ta kawo...

Be ma rufe bakin sa ba ya wuce yana buɗe gate ɗin su. Dake haske sai ya hangota tana tafiya da wata ledar a hannunta. Tana tafiya ta ji an hura mata iska a kunne, da sauri ta firgita tana sakin ihu tare da kiran sunan Daada da Dadda. Ganin shine yasa ta sauke ajiyar zuciya. Daman kana ganinta kasan a bala'in firgice take kamar ma wanda ta yi gudu.

"Kasan ba kyau? Yanzu da na mutu fa?

"Ba zaki mutu ba, sai kin ajje wanda za su maki addu'a in sha Allah".

Jinjina masa kai ta yi.

Ta ce, "Yaya Ibrahim ya dawo, tsarabarsa ce".

"Nagode".

"Ka koma".

Girgiza kan sa ya yi ya ce, "A'a mu je na rakaki".

"Gidan su Maryam zan je".

"Ehj mu je".

"Bana son zuwa gidan su, dan matar Babansu bata da mutunci. Kuma ni ba tsoron kowa nake ji ba, tsaf zan ci ubanta idan ta kama harda uwar".

"Ke baki da hakuri Sam".

"Ai babu haƙuri a wurin mutumin da ya da mutunci, mu ba sahabbai ba, ba kuma tabi'ai ba".

Murmushi ya yi a hankali suna tafiyar suna zancen su. Har suka kara so kofar gidan su Maryam. Ta shiga ta kai mata sannan ta fito. Ta fara bashi labarin Fahad da yace yana son ta.

"Baka ga tijarar da naje na yiwa Fahad ba, na je na faɗawa Abbah na ce ya jawa ɗan sa kunne, haka itama Mama. Kuma kasan me?;

"Mama sai da ta yi burabusko da miyar kabewa, tace min ga abinci, na zauna na ci na koshi na sha zobo mai sanyi, na ce mata na koshi amma bari na zuba. Na zuba min a flask na tafi da shi, sannan na faɗa musu abinda na zo da shi".

"Kuma flask ɗin ko? Fahad na bawa ya dawo da shi".

Tana bashi labarin tana dariya. Shi kan sa dariya yake yi sosai.

"Shiyasa bana son su san waye ce, ni ɗin , Allah yasa ma kar su hanani alaƙa da kai".

Murmushi kawai yake yi yana kallonta, amma wannan bata san su waye Abbah da Mama ba ko? Ba ruwansu Mama ta fi Abbah ɗan zafi. Kowa ya san wannan yarinta ce. Banda yarinta kai da ka je kashe har ka zauna cin abinci? Bayan ka ci sannan ka ce zaka tafi da sauran wanda ka ci, har a zuba maka a flask?

Har ƙofar gidan su ya kawo ta.

"Na gode. Kuma zaka iya zuwa? Kada ka ɓata".

"Zan kira ki, ki mayar ni idan na bata ɗin".

Dariya ta yi kawai tana shigewa gidan, shi kuma ya juya yana murmushi tare da shafa kan sa ya shiga gidansu.

"Sai yanzu? Daga cewa ana nemanka? Kuma aka leƙa baka ƙofar gida?!

Bala ya faɗa yana kallonsa. Shiru ya yi kawai be ce masa komai ba, ganin kowa ya zuba masa ido shida ledar hannunsa. Kawai ya na kallon Mama.

"Kin gama maganar?

Dariya ta yi ya ce, "Ai naga kamar baka son zancenne, kuma Abbanka be goya maka baya ba. Bansan me zance maka ba".

"Ki yi min addu'a".

"Yaya Mufeed abin hannun naka fa?

Fahad ya faɗa yana tasowa.

"Ko zaka mutu Fahad ba zaka ci ba".

Ya ce da ita yana wucewa. Da kallo kawai ta bishi tana girgiza kan ta. Ohh idan aka ce Mufeed zai zama haka zata ce a'a karya ne ake yi masa. Sanda ta kira shi da dadaddare idan sa biyu har ya saba kiran ta......

Ina kwana".

Ta faɗa a hankali tana dafe mararta da take yi mata ciwo. Shiru ya yi yana sake nutsuwa jin muryarta haka, ga numfashinta da yake sauka a hankali.

"Baki da lafiya? Me yake damunki?

"Ciwon mara".

"Ciwon mara? Me kenan?

Dan da gaske ne gane ba ɗin.

"Period cramp".

Ta faɗa masa a hankali tana jin yarda cikinta yake ɗaurewa. Duka duka yaushe ta gama wancan? Sannan ya lura tana jimawa kafin ta yi wanka, sanann kuma ya sake dawowa? To kwana nawa take yi sannan a yaushe yake dawowa?

"Is okay, sannu".

Ya faɗa a hankali jin shima gaba ɗaya jikin sa na so ya bashi rashin lafiyar. Dan tunda ya ji muryarta haka baƙaramin jin jiki take yi ba.

"Sannu".

Ya sake faɗa a hankali yana tashi.

"Ba cin biscuits da tea kenan irin na Zoya?

Ya faɗa mata a hankali muryarsa acan ƙasa. Ɗan murmushi ya ji ta yi mai sauti kafin ya ce.

"Ai idan da rai da lafiya akwai gobe....

Ƙarar da ta saki ne yasa shi saurin miƙewa daga zaunen da yake yana zabura, dan zuciyarsa sai da ta motsa. Last cramp da ta yi be wani nuna ya damu ba, amma yanzu yarda yake jinta ya wuce misali.

"Sannu, ga ruwan zafin ki samu ki sha, kafin gari ya waye mu tafi asibiti aje a sa miki ruwan sannu".

Ya ji muryar Daada yana faɗa, ita kuma Dadda na ɓalla mata maganu tana cewa ta tashi ta je ta sha.

"Sannu ki bari asuba ta yi, bana so na tashi Baba, kinji? Yi haƙuri".

Shima Ya Ibrahim ɗin ya faɗa ga dukkan alamu yanzu suka shigo.

"Ni wannan karon mutuwa ce kawai zan yi. Ahhhh".

Ta faɗa tana riƙe hannun Ibrahim ɗin sosai, janyota ya yi yana jin tausayinta a ran sa. Indai zata yi kamar wacce zata haihu kuma abin gaba yake yi ba baya ba. Anyi magani duk a banza ba wanda yake mata aiki.

"Yi hakuri".

Kawai kashe wayar ya yi ya zari makullin mota ya fita. Ganin gate ɗin a kulle yasa shi duba motar dake hannunsa ko akwai makullin gate ɗin, gwadawa ya ringa yi har ya samu na gate ɗin sannan ya ja motar ya fita, yana fita mai gadi ya fito daga ɗakin sa yana mamaki waye ya fita haka? Rufe gate ɗin kawai ya yi yana zama a kan barandar sa yana jiran tsammanin wanda ya fita.

Mama ce ta leƙa ta window kafin ta kalla Abbah dake zaune akan sallaya.

"Ko waye ya fita a cikin su yanzu?

"Da wacce kalar mota aka fita?

"Fara wacce ake kai su Khadijah makaranta".

"Mufeed ne hala?

Ya faɗa yana tashi ya naɗe sallaya.

"Amma me ya fita yi da wannan tsakar daren? Ina jin tsoro".

"Relax in sha Allah ba abinda ya faru. Dawo zo ki kwanta".

Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta dawo ta zauna badan ta gamsu ba sai dan musu ita da shi basu saba yin sa ba, amma hankalinta be kwanta ba sam. Kallon sa ta yi ya girgiza mata kai, hakan yasa ta yin shiru tana kwanciya kawai.....