QADDARARREN AURE

EP____________1️⃣3️⃣

by @swrites22

🕊️ DESTINED MARRIAGE 🕊️



*HAUSA EDITION*



🕊️ QADDARARREN AURE🕊️



          SWRITES 
              A-K-A 
     YOUNG WRITER✍🏻





EP____________1️⃣3️⃣





Haka rayuwa ta cigaba da gungurawa. Sosai Faryal tayi ƙoƙarin ganin bata bar abin da ya faru ya rusa rayuwarta ba ko ya hana ta gudanar da harkokinta na yau da kullum ba, saboda ta yarda ita baiwa ce, dan haka wacece ita da za ta ja da ƙaddararta? Bayan ta san cewa yarda da ƙaddara wajibi ne a matsayinta na Musulma, dan haka ta karɓi tata a yadda ta zo mata, ta ci gaba da rayuwarta tana addu'a.

Appa ne da Maama zaune suna tattaunawa, saidai daga yadda suke tattaunawar tasu zai shaida maka cewa abin da suke tattaunawa a kai me muhimmanci ne.

Appa ne ya gyara zama yana faɗin, "Kuma bayan haka Sharmila, kin san irin kusancin da ke tsakanina da Alhaji Sarakee, babban aminina ne, kuma ke ma kin shaida irin alherinsa a gare ni tun muna da jajayen sawunanmu. Kuma tun bayan faruwa wannan al'amarin, ya yi min magana a kan Faryal, amma na faɗa masa mu dan bata lokaci saboda ta samu sauki daga raɗadin da zuciyarta ke mata. Dukda a baɗini ba wai saboda hakan bane, na faɗa masa hakan ne kawai saboda in samu lokacin da zan gyara kuskuren da na yi a baya. Na binciki dabi'u da halayen ɗansa, kuma daga dukkan bayanan da na samu, babu wata matsala a tattare da yaron. Mutumin kirki ne. Shiyasa naga babu buƙatar mu ƙara jan lokacin. Yanzu kimanin watanni uku kenan, kuma kin san har yanzu muna fama da matsalar su Yaya Turai saboda har yanzu tana kan bakarta na cewa dole sai na aurawa dan wurin kamal Faryal ɗin, wanda kuma tun farko shi ne burinsu, amma naki aminta da hakan".

Maama ta sauke numfashi kafin ta ce, "Ko ni ma Hafiz, zan yi farin ciki idan wannan al'amari ya tabbata, domin iyalan Alhaji Sarakee mutanen kirki ne. Ba su da wata ɗabi'a marar kyau, sannan kuma Alhaji Sarakee ya nuna maka tsantsar ƙauna. Dan mutumin da zai nuna sha'awar haɗa jini da kai ta hanyar auratayya, ai kuwa me kaunar ka ne. Ni ma ina goyon bayanka a wannan lamarin".

"Na gode Sharmila, kullum kina ƙarfafa min gwiwa a duk abin da nazo dashi. Allah ya miki albarka".

"Ameen ya Allah. Ai matukar abu ne mai kyau Hafiz, hakkina ne in ƙarfafa maka gwiwa kuma in tallafa maka wurin yin sa a matsayina na matarka. Amma a cikin ya'yan nasa, wanne ne yake so ya aura wa Faryal ɗin?"

"Aryan!".

"Aryan?". Maama ta maimaita.

"Eh, autansa. Kin san ai yayan nasa maza biyu ne sai mace ɗaya. Wadda ta kasance babbar yarsa, sai kuma Ammar, wanda shi ma yana da aure, har matarsa ta haihu ma kwanaki, ko kin manta ne?".

"Oh yes, na tuna. To Allah Ya ba ku ikon ƙulla alheri, ya nuna mana lokacin".

"Amin ya Allah". Ya amsa cikin jin dadi, kafin ya kara da, "Amma ya kamata s sanar da ita ko, sai mu ji ra'ayinta ko".

"Hafiz, babu buƙatar jin ra'ayinta. Kai mahaifinta ne, kuma tunda ba aure ta taɓa yi ba, kai ke da hakkin zaɓa mata mijin da kaga ya dace da ita. Amma haka muka runtse ido a baya muka ba ta zaɓi, ta kawo wadda take so ɗin, kuma ga yadda abin ya kasance".

"Ban musa miki ba, amma dai yanzu kira ta ɗin". Maama ba ta ƙara cewa komai ba, ta miƙe tsaye ta je ta ɗauko wayarta dake kan gado, sannan ta kira Faryal ɗin.

Faryal tana zaune sanye da kayan bacci, tana tsokanar Manira wadda take waya da Amin, yayin da Hadiyyah take gefensu tana musu dariya. Wayar Faryal ɗin ta fara ringing, Hadiyyah ta ɗauka ta miƙa mata tana faɗin ungo Maama ce.

Karba tayi ta ɗaga tana faɗin, "Barka da dare Maama".

"Ab apane Appa ke paas men aayen". (Ki zo bangaren Appanki yanzu) Maama ta faɗa.

"To". Faryal ta amsa, sannan ta kashe wayar. Ta miƙe, ta ɗauki mayafinta ta fice daga ɗakin, tana tunanin dalilin da ya sa Maama ta kira ta a wannan lokacin.

Da sallama ta shiga falon, in da ta tarar da su zaune. Ƙarasa shigowa tayi sannan ta zauna a kan rug ɗin, daga gefen ƙafar mahaifiyarta ta tana faɗin, "Main yahan hun Ma". (Gani maama).

Appa ne ya yi gyaran murya tare da faɗin, "Na ɗauka kun kwanta ai kiranta ne ya tashe ki, ban ma duba lokaci ba sai bayan da nasa ta kira ki".

Faryal ta ɗaga idanunta zuwa ga agogon da ke manne a bangon falon. Ƙarfe 12:08 na dare. "Muna shirin kwanciyar ne dai na ji kiran".

"Ka manta Manira na nan? Ai in akace sunyi bacci yanzu ma, sai inyi mamaki". Maama ta faɗa.

"Amma ya kamata ku dinga ƙoƙarin samun isasshen bacci, at least 7 hours, saboda ƙwaƙwalwa ma tana buƙatar hutu ai".

"In sha Allah Appa". Faryal ta amsa.

"Faryal!". Appa ya kira sunanta a nutse.

"Naam Appa". Ta amsa tana bashi dukkan hankalin ta.

"Shin mun ba ki damar zaɓar wanda kike so ki aura?".

Faryal ta yi shiru na ɗan lokaci kafin ta ce, "Eh, Appa".

"To, me ya faru?". Appa ya sake tambaya.

"Nothing good Appa". Faryal ɗin ta sake bashi amsa.

"Shin akwai wanda kike so a yanzu?". 

"A'a Appa!". Faryal ɗin ta amsa ba tare da wani tunani ba.

Appa ya kalli Maama kafin ya ce, "Shikenan to, za ki iya tafiya".

Sai da safe Faryal ta yi musu, sannan ta tashi ta fita, zuciyarta cike da saƙe saƙe iri iri kan dalilin waɗannan tambayoyin na Appa.

Ko da ta koma ɗakinsu, ta tarar da Manira wadda ta gama wayar, tana kwance ita da Hadiyyah suna hira. Neman wuri Faryal ɗin tayi ta kwanta, tana sauraron hirar tasu ba tare da ta tsoma musu baki ba.

A wannan daren kowa ya yi barci, amma banda Faryal. Haƙura tayi ta tashi ta je ta ɗauro alwala, tazo ta fara nafilfili. A haka har ta fara jin barci, ta zame ta kwanta nan kan prayer mat din baccin ya ɗauke ta.

Washe gari sai da yamma suka fito su ukun cikin shirin fita. Inda suka tarar da Daadee zaune a falo, ita ma cikin shiri tana jiransu. Tana ganin su ta shiga faɗin, "Haba! Wannan wani irin abu ne, kusan awa biyu ina zaune anan wurin ina jiranku, me kuke yi a cikin ɗakin haka? Kwaliya, kwaliya! Shin za ku canza yadda Allah ya halicce ku ne?".

"To daadee, as the saying goes dai, idan kana da kyau, to ka ƙara da wanka". Manira ta faɗa.

"Ki zama tarwatsa ma idan kin so". Daadee ta faɗa, tana miƙewa tsaye ta shiga kwalawa Maama kira, "Sharmila! Sharmila. To ita kuma waccan bera ina tayi? Mu kenan in zamu fita duk sai an haɗa gari kamar yaqi".

Beta ce ta shigo falon, ita ma tayi adonta cikin doguwar riga yar kanti, ga jelar two babies din ta ya sauka har kan kafaɗunta, Maama na biye da ita suka shigo falon.

Daadee ta ce, "To, Sharmila, mu za wuce. Sai mun dawo ko". Daadee ta faɗa tana gyara mayafinta.

"To Daadee Allah ya tsare. Ku kuma ku kula sosai". Maama ta faɗa tana kallon Faryal, Hadiyyah da Manira kafin ta ƙara da cewa, "Waye zai tuƙa motar a cikin ku?".

"Ni ce". Faryal ta amsa.

"To banda gudu da mota, kin san Daadee dai ba ta son gudu". Maama ta faɗa cikin sigar gargadi.

"Gwara dai ki faɗa musu, dan kan su na rawa". Daadee ta faɗa tana nufar ƙofa, jikokinta nata suka rufa mata baya bayan sun yi wa Maama sallama.

Faryal ce ta shiga mazaunin driver, Manira ta shiga bangaren me zaman banza, yayin da Hadiyyah, Beta da Daadee suka shige back seat, da haka taja suka fice daga gidan.

Sai da suka ɗauki hanya, sannan Daadee ta ce, "Za mu fara zuwa mu ga jaririn Jamila, kafin mu wuce wurin bikin".

"Shikenan kuma Daadee ba za ki fara cewa za mu je nan da can ba sai bayan mun bar gida? Bikin da aka sa ƙarfe uku na rana, akace banda African time, amma ki duba yanzu kusan ƙarfe biyar har yanzu bamu je ba". Hadiyyah ta faɗa tana ɗan turo baki.

"Ba na son raba fitar ne. Kin san ba yawan fita nake ba, shiyasa idan na fita, nake son in je duk wuraren da nake da buƙatar zuwa". Daadee ta faɗa.

"Ku sauke ni a wajen biki ni, sai ku wuce". Hadiyyah ta sake faɗa.

"Saboda kyankyashe mu kika yi?". Faryal ta faɗa, sannan ta ƙara da faɗin, "Daadee a ina suke? gida ko hospital?".

"Har yanzu suna asibiti, ba'a sallamo su ba ai". Daadee ta amsa.

"Okay". Faryal ɗin ta amsa tana shiga kwana.

Suna isa asibitin, Faryal tayi parking, sannan suka firfito. Idanun ta ne suka sauka a kansu. Magana suke, amma kamar kullum, yana maganar ne cikin bacin rai. A haka suka zo suka wuce su suka shige cikin asibitin.

Faryal ta kalli su Daadee kafin ta ce, "Daadee, ku ƙarasa. Ina zuwa, barin dan duba wani abu a mota".

Manira ta harareta kafin ta ce, "Ke fa kin fiya tsugudidi! Miye baki duba ba tun daga gida sai yanzu?".

Ita dai Faryal ba ta kula ta ba, ta juya ta koma cikin motar ta zauna, domin gabaɗaya ba ta son ma ta shaƙi iska ɗaya da mutumin nan. Ba ta san meysa ba, amma duk lokacin da suka haɗu, sai wani mummunan abu ya faru a tsakaninsu. Shi ya sa ta yanke shawarar zama a cikin motar har lokacin da zasu fito su tafi.

Sai dai an shafe kusan mintuna ashirin da shigarsu amma shiru, a lokacin kuma wayarta ta fara ringing. Ganin manira ya sata ɗagawa da faɗin, "Ya akayi?".

"Daadee ce ta ce ki shigo ki ga jariri wai". Manira ta faɗa.

"Dan Allah Manira, idan kun gama kawai ku fito...". Ta faɗa, dan bata jin zata iya shiga bayan su Aryan ɗin na ciki.

Daadee ce ta karɓi wayar tare da faɗin, "Faryal ki shigo mana. Ki gaishe da Hajiya Yakana, gata nan tana ta tambayar ki".

Kamar zatayi kuka ta ce, "Wayyoooo Allah Daadee, plea...". Kashe wayar Daadee tayi ba tare data saurare ta ba.

Faryal ta bi wayar da kallo, kamar zatayi kuka. Ta ɗaga kai ta kalli ginin asibitin kafin ta buɗe ƙofar motar ta fito cikin sanyin jiki.

Tana shirin shiga asibitin, su kuma suna shirin fitowa. Aryan ne a gaba, hakan yasa suka yi karo. Kanta ya bugu da ƙirjinsa, har glasses ɗin ta ya faɗi. Da sauri ta sunkuya domin ɗaukar medicated glasses din nata. Zuciyarta na dukan tara tara dan ta san da wanda ta yi karo, duk da kuwa ba ta ga fuskarsa ba, amma familiar scent ɗin sa ya sanar da ita ko waye.

Miqewa tayi bayan ta ɗauki glasses ɗin, ta buɗi baki da niyyar ba shi haƙuri, sai dai kafin ta kai ga furta komai, taji ya kaiwa wuyanta wani irin damqa yana faɗin, "Wallahi, wallahi, idan kika ci gaba da bibiyata sai na halaka ki".

"Me kake ƙoƙarin yi ne Aryan? Are you out of your senses?". Mansur ya faɗa yana ƙoƙarin cire hannun Aryan daga wuyan Faryal, amma ya kasa.

"Ni dai na faɗa miki, idan kika sake na sake ganin fuskarki, whl sai kin yi nadamar zuwan ki duniya, wawiya kawai". Ya ƙarashe yana ture ta gefe, ya nufi motarsu.

Mansur ya bi bayansa yana faɗin, "Wallahi ban taɓa sanin kana da damuwa a cikin kanka ba sai yau. You need to see a psychiatrist gsky".

A zafafe ya ce, "Idan ka sake yi min magana Mansur, wallahi sai na ci ubanka".

"In ka fasa kai ba Aryan ba ne, ka ji". Mansur ɗin ya faɗa shi ma cikin ɓacin rai.

"Okay". Aryan ɗin ya amsa yana buɗe motar ya shige, Mansur ma ya bude bangaren me zaman banza ya shiga ya zauna.

Faryal dake tari, tana riƙe da wuyanta, ta fashe da kuka a daidai lokacin da su Daadee suka fito. Hadiyyah ce ta yi saurin isa wajenta tana tambayarta abin da ya faru. Saidai bata iya cewa komai ba sai kukan da take yi me cin rai.

"Fada min mana Faryal, me ya faru da ke ne?". Daadee ta sake tambaya cikin tashin hankali.

Juyawa kawai Faryal tayi ta bar su a wurin ta ruga mota da gudu ta shige ta zauna tana cigaba da kukan nata.

Bikin da basu je ba kenan. Saboda yadda Faryal din ke kuka, gashi tambayar duniya sunyi, ta ƙi magana.

Ƙarashen wannan ranar kuwa, Faryal ta yi shi ne cikin baƙin ciki. Dan da suka dameta da tambaya ma ce musu tayi kawai kan ta ne ke ciwo, ba dan sun yadda ba suka haƙura suka kyale ta dan dole.

Haka washegari, suka tashi da rigimar yaya Turai. Faryal ce kawai a gidan dan duk sauran yan uwanta sun wuce makaranta, itama yau makara tayi saboda baccin da bata samu da wuri ba jiya, dan yanzu har an doshi wuraren goma na safe.

A gurguje ta leqa ta yi wa Maama sallama wadda take ɗakinta tana rearranging kayan wardrobe din ta. Tana fitowa falon ta ji ana knocking. Bata yi Magana ba tunda har fita zatayi itama, tana zuwa ta buɗe ƙofar sai kuwa tayi baya da sauri ganin yaya Turai da Uncle Kamal, tare da ɗansa Jabeer.

Cikin falon suka ƙarasa shigowa, Faryal ta rufo ƙofar falon sannan ta biyo bayan su tana faɗin, "Sannu da zuwa Hajiya, ina kwana. Uncle Kamal, ina kwana". Ta faɗa tana kallon Jabeer, wanda tun lokacin da suka shigo idanunsa suke kanta. Yana sanye da ash coloured crazy jeans da white armless t shirt, gashin kan nan nasa kuwa ya sha Dada kamar wani ɗan daba.

Kafin Faryal ta sake cewa wani abu, Jabeer ɗin ya riga ta da faɗin, "How are you Babe?".

 "Lafiya". Faryal ta amsa a taƙaice, sannan ta kalli Hajiya Turai wadda ke faɗin, "Za'a tafi gantalin da aka saba ne?".

 Sunkuyar da kai tayi tare da faɗin, "Zan tafi wurin aiki ne, har ma na yi late".

"To shiga ki sallamo min sallamammiyar uwar taku".

Faryal ta kalle ta da kallon da ke nuna tana son yin tsokaci a kan sunan da tayi addressing ɗin mahaifiyar su dashi, amma dai ta ɗaure ta yi shiru, ta juya ta wuce ciki.

Tana fita, Jabeer ya juya ya kalli Auntyn tasa ya ce, "Gaskiya Hajiya, ya kamata ki yi wani abu a kan wannan maganar. In ba haka ba, whl Uncle ba zai yarda ya aura min wannan precious daughter ɗin tasa ba".

 "Ka kwantar da hankalinka Jabeer. Idan ka ga ba ka auri Faryal ba, to ka sani Hafiz ya sauya iyali ne".

Dakin Maama Faryal ɗin ta koma, ranta a bace. Maama na ganin shigowarta ta ce, "Ah Faryal, ba ki tafi ba daman?". 

"Mun yi baƙi, suna nemanki". Faryal ɗin ta faɗa kamar an mata dole.

"Su waye?"

"Yaya Turai ce...".

Katse ta Maama tayi ta hanyar jan tsaki ta ce, "Mtwee! Ke wuce ki tafi wurin aikinki. Ba Yaya Turai ba ko boarder ce ita daidai nake da zamaninta. Ta zauna ta jira, sai na gama abin da nake. Me ma ya kawo ta da sassafe haka? Matar da tun ranar aurenki da ta gama iban albarkarta, ba ta sake sa ƙafarta a wannan gidan nan ba".

"Tare take da Uncle Kamal da Jabeer ai".

"Jabeer kuma?".

"Eh Maama. Ni whl tun da na gan su, na rasa sukuni".

Maama ta yi ɗan murmushi kafin ta ce, "Kar ki damu, na san abin da ya kawo su, kuma ba za su taɓa samu ba". Tana faɗin haka, ta jefa mayafin da take ƙoƙarin linkewa a kan gado, sannan ta nufi kofa ta fice daga ɗakin.

Faryal ta biyo bayanta, amma ba ta shiga falon ba. Ta laɓe tana sauraron abinda zai faru.

Bayan sun gaisa, Yaya Turai ta ce, "To, ba dogon zance ya kawo mu ba. Na zo ganin Hafiz ne, amma tunda ba ya nan, babu matsala, zan iya miƙa miki saƙon in yazo ki faɗa masa. Maganar yaran nan ce. Ina ta yi masa magana a kan batun Faryal da Jabeer, amma har yanzu bai ce da ni komai ba. Ina ganin ya kamata su fara fahimtar juna, duk da cewa ba na son a sa auren da nisa, tunda dai duk yan uwa ne kuma a cikin Family guda ne".

Maama ta yi murmushi kafin ta ce, "Faryal tana dab da yin Engagement ne da wani a halin yanzu, dan haka maganar Faryal da Jabeer babu ita".

"What?". Kamal ya faɗa, kafin ya ƙara da faɗin, "Ni ban taɓa ganin matar da take qin dangin mijinta har take son farraqa shi da ahalin sa ba sai ke Sharmila. To saurare ni kiji, Yaya Hafiz ɗan uwan mu ne, kuma ke baki isa ki datse zumuncin dake tsakanin mu ba".

"Calm down Kamal". Yaya turai ta faɗa kafin ta juya ga Maama ta ce, "Bari in faɗa miki Sharmila, ba ke kaɗai kike da iko a kan waɗannan yaran ba. Mu ma muna da iko a kansu a matsayin dangin mahaifinsu. In fact, mun fi ku iko ma dasu".

"Ai ku kuka haife su ma". Maama ta faɗa da sigar shaguɓe tana murmushin cusa haushi.

"Ke Sharmila, ki kalli cikin idona. Kar ki kuskura kice za ki yi min rashin kunya. Kuma ina so ki rubuta ki ajje, Faryal ba ta da wani miji face Jabeer".

Tana fadin haka ta miƙe tsaye ta nufi hanyar fita daga falon tana faɗin, "In kin ga dama, in ya dawo, kar ki faɗa masa ina jiransa a gidana".

Tashi Kamal ya bi bayanta, kafin Jabeer ma ya miƙe. Ya kalli Maama ya ce, "Zan iya ganin Faryal ɗin kafin mu wuce?"

Maama ta watsa masa kallon banza kafin ta ce, "Zo ka fito da ita daga cikina mana marar kunya".

Ɗage kafaɗunsa yayi irin like I don't care ɗin nan kafin ya bi bayan mahaifinsa.

A sanyaye Faryal ta shigo ta zauna kusa da mahaifiyarta bayan sun fice, fuskarta dauke da damuwa, ta ce, "Maama, dan Allah kar ki bari su tilasta wa Appa ya aurar da ni ga Jabeer. Wallahi dan iska ne. Ki kalli gashin kansa fa, kamar kashin jinjirin jaki".

Dafa kafaɗarta Maama tayi kafin ta ce, "Kar ki damu Faryal, mahaifinki ba zai amince da hakan ba. Domin tun bayan fasa aurenki da akayi, Yaya Turai take matsa masa a kan ya aurar da ke ga Jabeer ɗin, amma ya ƙi. Kuma nan ba da daɗewa ba za ki auri mutumin kirki wanda zai kula da ke, in sha Allah".

Kafin Faryal ta samu damar sake Magana, Daadee ta shigo, da alama bata jima da tashi daga barci ba.

"Me ke faruwa ne? Ina barci, na jiyo hayaniyarki Sharmila, ke da waye da sassafen nan?".

"Yaya Turai ce da Kamal, Wai sun zo ne a kan maganar auren ɗansu Jabeer da Faryal. Wannan ɗan daban, yaron Kamal".

"Whatt? Jabeer dai?". Daadee ta faɗa cikin mamaki. "Wai me waɗannan mutanen suke nema damu ne? Ba fa fin mu ƙarfi sukayi ba. Mun yi shiru ne kawai saboda mun ga mahaifin yaran nan yana nan kuma ba ya goyon bayan abin da suke yi. Da ba haka ba ko hmmm!". Ta ja kwafa.

"Kar ki damu Daadee, shi ya sa ni ma ban damu ba, tunda Hafiz ɗin ba ya tare da su, kuma ba ya goyon bayan abin da suke ƙoƙarin yi". Maama ta faɗa, sannan ta juya ga Faryal ta ƙara da faɗin, "Idan ba za ki je wurin aikin ba, ki koma ciki ki kwanta".

Miqewa tayi tana faɗin, "A'a, zan tafi yanzu".

"To Allah Ya tsare. Ki kula da kanki". Daadee ta faɗa kafin ta juya su cigaba da tattaunawa da Maama.