Chapter 17
╔══════════════════════╗
🌹 *WASAN ƘADDARA* 🌹
╚══════════════════════╝
_A Story of Love, Pain and Destiny. That Even Fate Cannot Escape_
> ✍️ BY ASMEETAH WRITER
━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━
🏆 JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION
🌟 Under:
THE SHIDORIA WRITERS TEAM
━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━
📞 ***
📚 BOOK 1
📖 CHAPTER ___33 and 34
━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━
Wasu soyayyar ƙaddara ce ke haɗata...
Wasu kuma ƙaddara ce ke raba su...
Amma me zai faru idan zuciya ta ƙi amincewa da hukuncin ƙaddara?
━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━
Da ƙyar Chief Supervisor ya samu nasarar lallashin Amira ta daina kukan da take yi, kodayake idanunta sun riga da sun yi jawur sun kumbura tsabar tashin hankali. Ahan dake tsaye jikinsa duk a sanyaye, ya kama hannunta suka fito daga cikin ofishin.
Suna takawa a harabar gurin, Ahan ya juyo ya kalleta cikin fargaba da tausayawa, ya ce,
"Amira, don Allah ki kwantar da hankalinki, kada ki damu. In sha Allahu babu abin da zai faru... Zan yi magana da Yayana, kuma na tabbata komai zai wuce lafiya."
Amira ta jinjina kanta kawai, amma zuciyarta ba ta gamsu ba, domin ta shaida tsaurin hukunci.
Suna cikin tafiya, sai ga ƙawayenta su huɗu waɗanda suka fito daga makarantarsu don rubuta jarrabawar sun yo kanta da gudu. Dama can sun jima da fitowa suna jiran ta.
Suna zuwa suka karkame ta da tambayoyi cike da damuwa, "Amira me ya faru ne? Me ya tsayar da ke a ciki tun ɗazu kowa ya fito?"
Ahan ya yi saurin karɓar zancen domin kada asirin abin da ya faru ya tonu ya ce, "Kanta ne yake ciwo... Shi yasa aka ɗan tsayar da ita a ciki ta huta..."
Ƙawayen suka tausaya mata, ɗaya daga cikinsu ta kama hannunta tare da faɗin,
"Subhanallah! To mu je wani ɗan guri can mu zauna ta huta kaɗan kafin mu nemi motar tafiya gida ko?"
Suka nufi wani guri mai kyau da sanyin iska wanda ke ɗan nesa da ainihin ginin Centre. Gurin ya kasance kamar lambu na alfarma, domin akwai babban tafkin swimming pool dake haskawa a gurin. Su kuma suka sami guri suka zauna a kan wasu kujeru da ɗan nesa da ruwan...
Suna zama, ɗaya daga cikin ƙawayen ta miƙe tana fari da idanu ta ce,
"Bari na je na samo mana abin da zamu ci da abin sha, naga akwai wani babban kantin sayar da kayan marmari a can gaba."
Nan take kowace ta shiga lalubar jaka ta haɗa mata kuɗi. Amira ce kawai ta zauna ba ta miƙa ko kwabo ba.. Ba don ba ta da kuɗi ba sai don tsananin nauyin da zuciyarta ke mata. Zancen soke jarrabawarta da za a yi da kuma sanya sunanta a blacklist ya cika mata lissafi...
"Amira, miƙa kuɗinki mana a siyo miki wani abin da zai miki daɗi a baki," inji wacce ke karɓar kuɗin...
Amira ta girgiza kai a hankali ba tare da ta kalli kowa ba, "A'a... Ban buƙatar cin komai yanzu."
Wata ƙawarta ta ce, "Haba dai, ai ba za mu zauna muna cin abinci ke kuma kina kallonmu da yunwa ba. A cikin kuɗina a sayo mata abin da za ta ci dole, ba ta da lafiya ya kamata ta ɗan taɓa wani abu..."
Wacce aka tarawa kuɗin ta juya ta tafi da sauri. Sauran ƙawayen kuwa suka ci gaba da jefa hirarsu ta yadda jarrabawar kowa ta kasance, suna dariya. Amira kuwa ta daskare a gurin, sam hankalinta ba ya tare da su...
Tana cikin wannan matsanancin tunanin, sai idanunta suka sauƙa a kan wani tsararren bawan Allah dake tsaye can ɗan nesa da su, daidai saitin bakin ruwan swimming pool ɗin..
Mutumin ya juya musu baya, ya ƙafe ruwan da idanu ba tare da ya yi motsi ko kaɗan ba. Yanayin tsayuwarsa ya yi kama da wanda rayuwa ta yi mawa zafi, kamar wanda ke shirin jefa kansa cikin ruwan..
A lokacin, idanun Amira sun riga sun yi dishi-dishi, ga su sun yi jawur tsabar kukan da ta sha a ofis da kuma fargaba. A cikin rashin hasken idonta da kuma ruɗewar zuciya, ta fara gani kamar mutumin yana shirin yin tsalle ne don ya kashe kansa...
Mutumin ya sake matsawa daf da gaban pool ɗin, gaba ɗaya jikinsa ba motsi.
Amira ta ji gabanta ya faɗi. Ta kasa jure ganin wani zai halaka kansa a gabanta. Ta zabura ta miƙe tsaye, ta fara takawa zuwa gare shi tana ɗan tangal-tangal saboda jirin dake shirin kwashe ta...
Ƙawayen dake zaune suka bita da kallo da mamaki, "Ina zaki je ne haka Amira?"
Ba ta ko juyo ta kalle su ba, balle ta ba su amsa.
Ɗaya daga cikinsu ta ce, "Kyale ta kawai, wataƙila ba ta son hayaniyar da muke yi ne da surutu tunda kanta yana ciwo, shi yasa ta tashi."
Ita kuma Amira ta ci gaba da tafiya, duk da cewa kanta yana juyawa kamar za ta faɗi, burinta kawai ta isa gurin wannan bawan Allah kafin ya tafka babban kuskure...
A.Y.Z ne tsaye a bakin ruwan, ya sanya baƙin facemask, idanunsa suna kan ruwan amma hankalinsa yana kan wani aiki na sirri dake gabansa...
Kwatsam sai kawai ya ji an damƙe damtsen hannunsa na hagu da ƙarfi, an ɗan jawo shi baya da nufin raba shi da bakin ruwan. Amma duba da yadda ƙirarsa da ƙarfinsa suka ninka na Amira ninki dubu, ba ta iya matsar da shi ko da da rabi ba...
Arman ya canza fuska cikin tsaro, ya juyo da idanunsa a hankali cikin mamaki da ɓacin rai don gani ko wane ne wannan mara kunyar. Idonsa ya sauƙa a kan Amira.
Itama jajayen idanuwanta dake zubar da zafafan hawaye tana kallonsa, cikin muryarta mai ban tausayi ta fara magana tana rawar murya,
"Dan Allah kayi haƙuri kada ka kashe kanka! Meye ma amfanin wannan duniyar da har zai sa ka yanke ƙauna? Me yayi zafi haka da zaka halakar da kanka a cikin ruwan nan? Shin idan ka mutu a yanzu, me zaka ce wa Ubangijinka ranar gobe ƙiyama? Allah ya halicce mu ne domin mu bauta masa, Shi da ya ba mu wannan ran, ka jira mana har lokacin da zai karɓi aron ransa da ya ba mu... Me yasa kake hanzari haka?"
Arman ya daskare yana kallonta ta cikin baƙar gilashinsa da facemask. Gaba ɗaya ya kasa gane me wannan yarinyar take nufi, kuma ko a mafarki bai taɓa tunanin wani zai zo ya ƙira shi da mai shirin kashe kansa ba... Amma abin mamaki, hannunta yana nan dafe da damtsen hannunsa ba ta saki ba...
Amira ta ci gaba da kuka tana ƙara matse hannunsa,
"Shin idan ka mutu a wannan halin, ka san wane irin ƙuncin rayuwa iyayenka zasu tsinci kansu a ciki? Idan baka son kanka, to iyayenka da ƴan uwanka da abokan arzikinka... Har da mu duka muna son rayuwarka... Don Allah ko don halin da mahaifiyarka za ta shiga kada ka aikata haka... Allah yana jarabtar mu ne domin ya gwada imaninmu, kuma yarda da ƙaddara mummuna ko mai kyau shi ne cikar imanin mu"
Maganar Amira ta shiga ratsa jijiyoyin jikin Arman. Ya tsaya yana binta da kallo, domin duk da cewa ta yi kuskuren gano manufarsa, kalaman nata suna cike da ma'ana da ratsa zuciya...
Amira ta share hawaye da ɗayan hannun ta ci gaba...
"Ni a halin da nake ciki a yanzu, na tabbata na fika shiga cikin matsananciyar damuwa! Damuwarka bai kai nawa ba, duk da cewa ban san wane irin iftila'i kake fuskanta ba a rayuwarka... Ni fa, daga taimako a ɗakin CBT Hall, sai ga mummunan ƙaddara ta afku da ni... Wai an soke jarrabawar da na yi, kuma wai za a hana ni sake rubutawa gaba ɗaya... Ban san me yasa kowa ya tsane ni a rayuwar nan ba ban da mahaifiyata... Babu mai ƙaunata, gaba ɗaya mafarkina na rayuwa ya rushe... Amma kaga, duk da haka ban tafi da tunanin zan kashe kaina ba"
Yana cikin sauraron zafafan surutanta da kuka, kwatsam sai idonsa ya hango wani matashi sanye da baƙar riga yana tafiya da sauri-sauri ta gefen ginin. Wannan matashin shi ne ainihin mutumin da Arman ya zo gurin domin ya kamo shi, shi yasa ma ya tsaya a bakin pool ɗin yana fakonsa.
Take hankalinsa ya rabu da kalaman Amira, ya daina ma jin abin da take faɗi. Idanunsa suka koma kan mutumin dake shirin guduwa.
Amira kuwa tana nan tana faman sambatu tana kuka, "Dan Allah kada ka yi haka... Rayuwa ba tamu ba ce. Allah ne ya ba mu ita, Shi ne kuma zai karɓa idan lokacin ya yi. Ko wane irin damuwa kake ciki, kada ka kashe kanka. Ka tuna da iyayenka... Ka tuna da Ubangijinka..."
Ba zato ba tsammani, Arman ya sa hannunsa na dama cikin aljihun wandonsa, cikin ƙwarewa ya zaro wani ƙaramin pistol wato bindiga, ya kunna kunamar bindigar ta ɗan yi sauti..
Idon Amira ya sauƙa a kan bindigar dake haskawa a hannunsa. Jikinta ya ɗauki rawa, a zabure ta saki damtsen hannunsa ta ja da baya fuskarta cike da tsananin firgici da tsoro, tana kallon bindigar...
A daidai lokacin, wata na'urar sadarwa ta sirri dake makale a kunnensa ta ba shi saƙon cewa mutumin yana shirin tsallake katanga...
Arman ya ɗaga idonsa ya sake tabbatar da gurin da mutumin yake. Nan take ya mance da wata halitta mai suna Amira a gurin, ya cika da yanayinsa na zaki mai farauta. Cikin hanzari da takun sauri na musamman, ya juya da bindigar a hannunsa ya bar gurin da gudu, ya bi bayan mutumin...
Ya bar Amira a tsaye a gurin tana karkarwa, baki buɗe, tana bin bayansa da kallo cikin tsananin dimauta...
Cikin hanzari ya zagaya ta wata hanyar asirce ya sha gaban mutumin ya tsaya cak. Mutumin ya tsorata kaɗan, ya shiga kallon Arman daga sama har ƙasa cikin fargaba, ganin yadda Arman ya sanya facemask da gilashi ya sa bai gane ko wane ne ba.
Mutumin ya ɗaure fuska ya ce,
"Kai kuma fa? Wane ne kai da zaka tare ni?"
Arman ya matsa kusa da shi, ya ce cikin sanyin murya mai cike da kwarjini, "Magana ce ta sirri..."
Mutumin ya yi dariya ta rainin wayo, ya dube shi, "Amma ba a wannan yanayin ba domin za a iya kama mu a nan gurin. Kaga kai ka rufe fuskarka yadda babu wanda zai gane ka, amma ni fa da nake a buɗe?"
Arman ya kalli gefe da gefe, ya ce, "A yanzu haka babu wani mutum da yake kallonmu a gurin nan."
Mutumin ya sake waige-waige cikin tsoron kar a farmake shi, ya ce ƙasa-ƙasa, "Kana neman kayan nan ne?".
Arman ya ce, "Eh... Amma ba shi kaɗai nake nema ba."
Mutumin ya tsaya ya nutsu, "Ina jinka, faɗi abun ka."
Arman ya daidaita tsayuwarsa, ya ce, "Na gaji da aikin halal... Ina son kuɗi na hauka. Na ji ana cewa akwai mutanen da suke samun miliyoyi cikin dare ɗaya a gurin ku."
Mutumin ya yi dariya ƙasa-ƙasa mai cike da shakku, ya ɗan ƙara matsowa kusa da Arman...
"Kai... Ka san mutane nawa ne suka taɓa faɗin irin wannan maganar a gare mu?"
Arman ya amsa cikin natsuwa ba tare da fargaba ba, "Ban sani ba."
Mutumin ya girgiza kansa, "Suna da yawa sosai. Wasu 'yan sanda ne na fararen kaya, wasu jami'an DSS ne, wasu kuma tarkon gwamnati ne da aka ɗana mana... Don haka, duk wanda ya zo gurinmu yana cewa 'ina son kudi', ba lallai ne ya zama mai gaskiya ba."
Arman ya ɗaga giran idonsa ta karkashin gilashi, "To idan har haka ne, me ya sa ka tsaya kana saurarona a yanzu maimakon ka gudu?"
Mutumin ya ɗan yi murmushin mugunta, "Saboda ba ka yi kama da talakan da yake bara ba...Idanunka sun nuna min kana da wani dalili na daban da ya fi kuɗin girma. Amma ni hakan bai dame ni ba... Abin da ya dame ni kawai shi ne, ko zaka iya rufe bakinka muddin aka amince da kai?"
Arman ya ce, "Idan na ce zan rufe baki, to zan rufe shi har abada."
Mutumin ya dake, ya yi shiru na wasu daƙiƙa yana auna kalaman Arman, sannan ya ce cikin ƙatuwar murya,
"Akwai mutane da dama da suka taɓa shiga wannan hanyar tamu saboda kwaɗayin kuɗi... Wasu sun zama attajirai na gaban goshi... Wasu kuma ɓatan-damo suka yi kamar basu taɓa rayuwa a duniya ba... Wannan hanyar tamu ba kasuwanci ba ce ta wasa... Hanya ce da muddin ka sanya ƙafarka guda, to ba ta da sauƙin komawa baya."
Arman ya kalle shi kai tsaye ta cikin gilashinsa, "Na shirya wa kowane hali."
Mutumin ya sake yin wata dariya mara sauti, "Kowa haka yake faɗa da bakinsa kafin ya ga ainihin ƙofar shiga...Mutane da yawa sun taɓa ƙoƙarin gano mu a ƙasar nan amma babu wanda ya taɓa yin nasara... Wanda duk ya kuskura ya bi sawunmu, baya daɗewa a duniya. Kuma muna da tsatstsauran dokoki... Kafin ka shiga tsakiyarmu, sai ka tsallake matakai da dama na jarrabawar jini."
Arman bai nuna tsoro ba, ya ce, "Yanzu ta yaya zan iya shiga gurin?"
Mutumin ya haɗe fuska sosai, ya ce, "Ka sani... Idan ka shiga, babu batun fita. Kuma dokokin farko su ne, Ba a tambayar sunan Oga tashin farko. Ba a tambayar inda kuɗi suke fitowa... Ba a tambayar irin aikin da za a baka. Abin da aka ce ka yi kawai, shi zaka yi ba tare da musu ba."
Arman ya jinjina kai cikin sanyin murya ya amsa masa, "Babu damuwa, na amince da dokokin."
A ƙarshe, kafin mutumin ya juya ya tafi, ya kalli Arman da idanuwan gargadi na karshe, ya ce,
"Ka zo kai kaɗai a matsayinka na mutum guda. Idan muka hango ko da 'yan sanda guda ɗaya ne ko jami'i yana binka a baya... Ba kai kaɗai zaka mutu ba. Duk wani mutum da ya shafe ka a rayuwa, ko danginka, sai sun mutu baki ɗaya..."
Sannan ya sanar masa da ainihin inda zasu haɗu domin fara tafiyar..
"Yau da daddare ka same mu a Old Riverside Warehouse. Akwai wata baƙar mota dake fakin a gurin, kana zuwa ka shiga cikinta kai tsaye."
Sannan mutumin ya sanya hannu a aljihunsa, ya ciro wani baƙin kati na musamman wanda bashi da kowane suna ko rubutu a jiki, ya miƙa masa.
"Idan ka isa gurin, ka nuna wannan katin. Idan har ba ka da shi a hannunka... To ba zaka taɓa wuce Kofar farko ta ginin ba, kuma za a iya harbe ka a take."
Yana gama faɗin haka, mutumin ya juya da sauri ya ɓace ta cikin duhun lungun ginin, ya bar Arman tsaye riƙe da katin yana sake kulla yadda zai karkatar da wannan kungiyar baki daya...
Arman ya koma ta inda ya fito cikin hanzari, sashen wurin wanka na swimming pool zai wuce kai tsaye domin ya fice daga harabar makarantar...
Kwatsam yana daf da isa gurin, sai ya jiyo sautin kururuwa da muryoyi cikin firgici na dalibai mazauna wurin... Waɗannan kuwa ba kowa ba ne face kawayen Amira su huɗu. A wannan lokacin iya su kaɗai ne suka rage a sashen ruwan, babu kowa kusa da zai kawo musu ɗauki. Suna ihu da ƙarfi suna neman agaji cikin tashin hankali...
Abin da ya faru kuwa shi ne, bayan ganin Arman da bindiga ya tafi, firgici da tsoro sun sa kan Amira ya juye, nan da nan ta fara jin wata irin matsananciyar hajijiya. Ta juya da kyar da nufin ta koma gun kawayenta dake can kuryar daban sun baje suna hira. Tana tafiya tana dafe da kanta, yayin da idanunta suka disashe, komai bibbiyu take gani a gabanta. A lokacin da ta nufi saitin inda ruwan pool ɗin yake, ta ɗauka hanya ce sakamakon rabuwa biyu da idanunta suka yi mata. Kafin ta ankara, sai kawai ta tsinci kanta ta faɗa cikin babban ruwan tare da nitsewa kai tsaye..
Ta shiga harbe-harbe da shure-shure na fitar rai a cikin ruwan, ga shi kuma ba ta iya iyo ba, ba ta taɓa shiga irin wannan ruwan ba. Su kuwa kawayen nata suna can kuryar da aka ware domin zama, hankalinsu bai kai kanta ba sam...Amira ta yi ta ihu a cikin ruwan amma ruwa ya sha karfinta, murya ta kasa fita har ta kai ga daina motsi saboda karfinta ya ƙare, ta zame zuwa ƙasan pool ɗin...
Sai daga baya kawayen nata suka shiga tambayar juna, "Wai ina Amira ta yi ne? Ga shi har an kawo abincin da muka yi oda." Suka tashi tsaye suna dube-dube a zaton cewa tana nan kusa ta zo su ci abincin tare. Suka shiga ƙiran sunanta,
"Amira! Amira!!", amma shiru ba amsa. Suka lellaqa kowane lungu da saƙo na sashen amma basu ganta ba. Wata a cikinsu ta ce, "Ko dai ta wuce gida ne ba tare da ta faɗa mana ba?"
Sai ɗayar ta ce, "Tafiya kuma ba ko sallama? To ko da yake, zai yuyu tunda ɗazu ba ta da lafiya sosai... Muje kawai mu cika cikinmu kafin mu tafi."
Ɗayar kuwa ta tsaya a daidai bakin ruwan tana ƙare wa tsarin pool ɗin kallo, ta ce,
"Wow! Gaskiya ruwan nan akwai kyau... Ko dai mu shiga mu ɗana wankan ne kamin mu tafi?"
Ɗayar ta yi saurin tsawa gare ta, "Cabb! Baki taɓa shiga irin wannan ruwan ba, shi ne zaki ce zaki shiga kije ki mutu ko? To wallahi kin ga babu wani namiji a kusa da zai iya cetonki idan kika nutse."
Wacce ta yi maganar ɗazu ta turo baki, "Wasa ma nake yi, ina ni ina shiga wannan uban ruwan"
Suna cikin wannan maganar ne, sai idon ɗaya daga cikinsu ya sauƙa a kan wani abu mai launin riga a can tsakiyar kasan ruwan. Cikin nuna yatsa ta ce,
"Ku dubi can tsakiyar ruwan kuga, kayan waye a ciki rai?"
Dukansu suka zuba ido a gurin cikin nutsuwa, "Ehh, wallahi kayan mutum ne."
Ɗaya ta dafe ƙirji, "Wait... Kamar mutum ne a kwance" Dukansu suka zaro idanu cikin firgici. "Kuma kamar rigar Amira ce fa"
Tattalin tsoro ya ziyarce su, nan take suka yo da gudu zuwa bakin saitin inda abun yake, suka zuba idanu suna ƙare wa abin kallo da kyau. Ai kuwa nan da nan gabansu ya yanke, suka zabura suna faɗin,
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Amira ce"
Nan da nan suka shiga ƙiran sunanta da ƙarfi suna ihu amma ko gezau ba ta yi. Wasu a cikinsu suka ruga da gudu suna duba ko akwai wani ma'aikaci ko mutum a kusa, amma wayam babu kowa, duk daliban da suka gama jarabawar a ranar duk sun riga sun tafi gida...
A daidai wannan mawuyacin lokacin ne Arman ya hango su daga nesa yana kokarin wucewa. Suna ganinsa kamar an aiko musu da mala'ika, suka ruga da gudu zuwa gurinsa suna kuka da nuna damuwa,
"Dan Allah bawan Allah ka taimaka mana... Yar uwar mu ce ta faɗa cikin ruwan nan, yanzu haka ko motsi ba ta yi, dan Allah ka cece ta"
Jin haka ya sa Arman ya juya idanunsa zuwa saitin pool ɗin cikin sauri.
Idonsa ya sauƙa daidai kan jikin Amira dake nitse a hankali cikin ƙasan ruwan..
Ba tare da ya ɓata lokacin cire takalmansa ko tsayawa cire agogon hannunsa, ko rigarsa ba, ya yi wani irin zaburaren tsalle mai ƙarfi ya afka cikin ruwan.
Ruwan pool ɗin ya watse sama da ƙarfi.
A cikin daƙiƙa ƙalilan, ya shiga yin iyo cikin tsananin kwarewa kamar wani wanda ya shafe tsawon rayuwarsa yana yin atisayen ruwa. Cikin zafin nama ya isa gare ta a ƙasan ruwan, ya juyo da ita sannan ya kama kunkuminta, ya ɗago da kanta sama da sauri domin kada ta ƙara shakar wani ruwan...Ya janyo ta da karfi zuwa bakin pool ɗin. Kawayenta da suka ga haka, nan take suka haɗa ƙarfi da ƙarfe, suka kama hannunta suka taimaka masa wajen fito da ita zuwa waje...
Bayan an kwantar da ita a ƙasa, Arman ya durƙusa a gabanta da sauri. Ya sanya hannu ya cire mata hijabin dake wuyanta a hankali domin ya samu space ɗin mata aikin. Ya matsa yatsunsa biyu a saitin jijiya ta gefen wuyanta domin ya ji alamun rai, amma shiru kake ji...
Numfashinta ya riga ya tsaya cak. Bugun zuciyarta kuma ya yi ƙasa sosai ta yadda ba kowa ne zai iya ji ba.
Nan take, ba tare da jinkiri ba, ya shiga yi mata CPR cikin tsantsar kwarewa irin ta kwararren likita. Ya haɗa hannunsa guda biyu, ya shiga matsa kirjinta sau talatin a jere da juna cikin daidaitaccen ƙarfi da sauri...
Sannan ya karkatar da kanta kaɗan domin buɗe hanyar numfashi, ya toshe hancinta da yatsunsa, ya kai ƙaramin bakinsa ya haɗa da nata ya hura mata iska mai ƙarfi sau biyu jere. Ya sake komawa da sauri yana matsa kirjinta da hannayensa..
Kawayenta suna tsaye a kanta suna kuka.
"Dan Allah ka ce zata rayu..."
"Wayyo Amira, dan Allah ki buɗe idonki mana! Kar ki mutu ki bar mu"
Bayan wani ɗan takaitaccen lokaci yana kan matsa kirjin...
Amira ta yi wani irin zafafan tari mai ƙarfi. Ruwa mai yawa da ta shaƙa ya shiga fitowa da gudu daga bakinta. Bayan fitar ruwan, sai ta sake yin shiru ta lula cikin suma...
Arman ya sake miƙa hannu da sauri ya duba bugun wuyanta da na kirjinta. Ya ɗan sauƙe wani nannauyan numfashi na samun nasara...
"Alive..." ya faɗa a takaice cikin natsuwa..
Sai ya ɗago kai ya kalli kawayenta ya ce,
"Cikin motata zamu tafi da ita asibiti yanzu... Ba zamu tsaya ɓata lokaci wajen jiran motar daukar marasa lafiya ba."
Dukkansu suka jinjina kai cikin gaggawa da firgici, "Muje dan Allah bawan Allah"
Arman ya miƙe da sauri, da jiƙaƙƙun kayansa ya nufi wajen filin ajiye motoci na CBT Centre inda ya bar motarsa. Saboda ɗan nisan dake tsakanin gurin swimming pool ɗin da inda motocin suke, sai da ya ɗan ɗauki lokaci kamin ya isa gurin... Amma da zarar ya shiga motar, bai ɓata ko da sakan guda ba. Ya tada katuwar injin motarsa ta alfarma wato Mercedes-AMG, yana tuƙawa cikin gudun da ya dace da cikin harabar...
Da ya iso daidai pool ɗin, ya fito cikin sauri. Ba tare da ya bari kawayenta ko wani ya sanya hannu ba, ya sunkuya ya ɗauke ta cak a hannunsa, Jikinta babu wani gwari ko motsi, yayin da dogon gashinta da kayan jikinta suka jiƙe sharkaf da ruwa suna ɗiga..
Ya buɗe kofar bayan motar da hannunsa guda, ya zaunar da ita a hankali tare da kwantar da ita. Sai ya juya ga kawayen nata ya ce, "Ku shiga ciki yanzu."
Kawayenta uku suka rurrufa suka shiga bayan motar tare da ita cikin hanzari. Daya daga cikinsu ta zauna ta ɗora kan Amira a kan cinyoyinta, yayin da sauran biyun suka kewaye ta suna amfani da hannayensu wajen goge mata sauran ruwan dake fuskarta. Ɗaya kuma daga cikinsu ta zagaya ta shiga kujerar gaba ta kusa da direba.
Arman ya shiga mazaunin direba da sauri. Bai ƙara cewa uffan ba, ya canza giyar motar, ta fice daga harabar wajen cikin matsanancin gudu, ta ɗauki babban titin da zai kaisu kai tsaye zuwa babban asibitin zamani na kansa da yake mallaka kuma yake jagorantar manyan likitocinsa.
A cikin motar kuwa, babu abun da kake ji sai karar ajiyar zuciya da kukan kawayen nata dake cike da fargaba. Yayin da shi kuma Arman, idanuwansa duka biyu suna kan titi yana tuƙi, amma lokaci bayan lokaci zuciyarsa tana kallon madubin tsakiya na cikin motar domin bibiyar yadda yanayin numfashin yarinyar yake tafiya...
Suna isa harabar asibitin, ya danna wa motar fakin da sauri kusa da ƙofar shiga ta gaggawa. Bai ɓata lokaci ba ya fito, ya buɗe ƙofar baya tare da sake mata ɗaukan jaririya. Ya nufi dogon corridor ɗin asibitin da sauri, takunsa cike da natsuwa..
Ganin uban gidan nasu ya shigo ɗauke da marar lafiya a hannunsa kuma jikinsa duk ruwa, ya sa wasu ma'aikatan jinya dake tsaye suka firgice, suka shiga yi masa sannu cikin girmamawa, "Sannu da zuwa, Sir! Sannu da ƙoƙari..."
Arman ba shi da lokacin amsa su. Ya wuce kai tsaye zuwa ICU/VIP Emergency Room wanda aka ware don manyan matsaloli.
Ya shiga ciki tare da kwantar da ita a kan gado. Wasu ƙwararrun nurses guda uku da likita ɗaya suka rufa masa baya suka shiga ɗakin da sauri domin fara ba ta taimakon gaggawa na na'urori...
Ƙawayen Amira su huɗu dake biye da shi a baya duk sun ruɗe, sai kuka suke yi a wajen koridor ɗin, an hana su shiga ciki domin kar su takura wa ma'aikatan.
Bayan wasu 'yan daƙiƙu, Arman ya fito daga ɗakin da sauri, ya nufi wani ɓangare na Doctors' Changing Room..
Can sai gashi ya fito, ya sauya duka kayan jikinsa. Yanzu sanye yake da farar riga ta likitoci, sannan ya toshe fuskarsa da farin facemask na likita, sanye da gilashinsa na aiki. Yazo ya wuce ta gabansu cikin sauri ya sake komawa cikin ɗakin da Amira take.
Ƙawayen Amira duk suna zaune babu ko ɗaya a cikinsu da ta gane cewa wannan babban likitan da ya wuce yanzu shi ne ainihin kyakkyawan mutumin da ya tsamo ta a ruwa kuma ya kawo su a motarsa ba. Kwarjinin asibitin da canzawar kayansa sun sa sun ɗauka wani likitan ne daban aka ƙira domin ya ceci rayuwar ƙawar tasu.
A cikin ɗakin kuwa, Arman ya tsaya a gaban gadon Amira, ya karɓi sakamakon auna numfashinta da na'urar bugun zuciya daga hannun nurse, ya zuba mata idanu sosai...
Ya tabbatar da drip ɗin na tafiya yadda ya kamata, ya sake duba bugun zuciyarta da numfashinta. Bayan ya gamsu cewa haɗarin ya kau, ya gyara safar hannunsa ya kalli nurses ɗin...
"Ku ci gaba da sa ido a kanta. Idan ta farka kuma ta fara tari ko kuma ta sake samun wahalar numfashi, ku ƙira ni nan take."
"Yes, Doctor." Suka amsa a tare.
Ya juya ya fice daga ɗakin cikin natsuwa.
A bakin ƙofar ɗakin kuwa, ƙawayen suna zaune cike da tashin hankali.
Ɗaya ta dafe cikinta ta ce,
"Gaskiya yunwa tana damuna sosai... Abincinmu kam mun barshi, ko ɗan lasa ba mu yi ba."
Wata ta harare ta.
"Ke dallah! Wannan lokacin ne za ki tuna da abinci? Yarinya tana can tsakanin rai da mutuwa."
Ta sunkuyar da kai.
"To ai nima damuwa nake yi... amma yunwa ma daban take."
Suka yi shiru na ɗan lokaci.
Sai ɗaya ta ce,
"Wallahi mutumin nan da ya taimaka mana kam Allah ya saka masa da alkhairi. Da ba don shi ba... ban san me zai faru da Amira ba."
"Wai ma ina ya shiga ne?" wata ta tambaya tana waige-waige.
"Tun da ya shigo da ita nan bai ƙara dawowa ba."
"Wataƙila tafiya ya yi. Ai ya gama abin da zai yi."
Sai wata ta ce cikin damuwa,
"Amma kuɗin asibitin fa? Wannan ai private hospital ne. Wallahi ina jin zai ci kuɗi sosai."
"Wai ma ta yaya za mu sanar da Umanta? Duk babu waya a hannunu"
Suna cikin wannan magana, sai wata Nurse ta fito daga ɗakin.
Nan take suka miƙe suka taru a kanta..
"Sister... ya jikin ƙawarmu?"
Nurse ta yi murmushi.
"Alhamdulillah, tana cikin sauƙi yanzu. Ruwan da ya shiga cikinta an fitar da yawansa, kuma yanzu tana barci ne saboda magungunan da aka yi mata."
Duk suka sauƙe numfashin da ba su san suna riƙe da shi ba.
Sai ɗaya ta tambaya da sanyin murya,
"To... kuɗin asibitin fa?"
Nurse ta ɗan yi murmushi.
"Kuɗin komai wanda ya kawo ku ya riga ya biya tun kafin a fara treatment."
Suka zaro idanu gaba ɗaya.
"Ya biya duka?"
"Eh."
"Wai shi waye ne?"
Nurse ta ɗaga kafaɗa.
"Ban sani ba. Amma ya ce a tabbatar an kula da ita sosai."
Sai ta ƙara da cewa,
"Abin da ya rage yanzu shi ne idan kuna so ku sanar da iyayenta. Amma idan kuna ganin hakan zai firgita su kafin ta farka, za ku iya jira. Da zarar ta tashi, idan komai ya yi kyau, ana iya sallamarku."
"Nagode Sister."
Nurse ta juya ta koma aikinta.
A can wani sashe na asibitin kuwa...
Arman ya shiga office ɗinsa bayan ya cire safar hannunsa.
Ya zauna a exacutive chair ɗinsa sannan ya sauƙe wani nannauyan numfashi mai cike da gajiya da sarkakiya. Na wasu daƙiƙa idanunsa suka tsaya cak suna kallon tafukan hannayensa..
Kwatsam... Sai hoton yarinyar nan ta bakin swimming pool dake rike da hannunsa ya dawo masa cikin kwakwalwa..
"Dan Allah kada ka kashe kanka..."
Muryarta ta daki kunnensa.
Ba tare da ya shirya ba, fuskarsa ta ɗan sakko daga ɗaurewar da take, ya ɗan yi wani tattausan murmushin gefen baki wanda ke bayyana a fuskarsa lokaci-lokaci...
"Yarinya mai ban mamaki..." Ya furta ƙasa-ƙasa a ransa.
Ya shiga tuno yadda ta riƙe masa damtsen hannu cike da ƙarfin gwiwa ba tare da fargabar kwarjininsa ba, tana ta zabga masa zafafan nasihohi da rayuwa, alhali ita kanta tana cikin wata irin matsananciyar damuwa wadda ke neman raba ta da numfashinta..
Nan take kuma, wani hoton ya sake giftawa ta cikin tunaninsa... Ita ce dai wannan yarinyar da ta sume a cikin ofishin CBT Hall lokacin da aka sanar da su cewa an rubuta rahoton malpractice an tura wa JAMB... Shi kuma a lokacin yana zaune a kan kwamfuta ya juya musu baya, bai nuna ya damu da ita ba..
Arman ya sake ɗaure fuskarsa sosai, kwayar idonsa ta kaɗu.
"Ashe wannan shi ne ainihin dalilin da ya sa take cikin wannan irin tsananin damuwar..."
Ya ayyana a ransa, yayin da ya sake tuno kalamanta tana kuka "Ni ma mafarkina ya rushe... Wai an soke JAMB ɗina, kuma wai ba zan sake rubutawa ba..."
Ya runtse idanunsa na wasu gajeren lokaci, yana mai jin yadda sautin kukan yarinyar yake sake dakar masa kai... Ba zato ba tsammani, sai wani tunani na daban ya daki zuciyarsa.
A gabanta fa ya zaro ƙaramar bindigarsa, kuma ya shigo da yanayin yaƙi lokacin da ya hango mutumin da yake nema..
Nan take ya buɗe idanunsa...
"Ko dai tsoron bindigar da na ciro ne ya ƙara firgita ta?" Ya tambayi kansa. Ya tuna yadda ta zaro idanu ta saki hannunsa tana ja da baya cikin matsanancin tsoro lokacin da ta ji karar kunamar bindigar...
"Ita da take ƙoƙarin hanani meyasa ita tayi haka?.."
Ya yi shiru na wasu mintuna, A karo na farko tun bayan faruwar lamarin a ɗakin jarrabawa, Arman ya ji wani ɓoyayyen nauyi na daban ya daki ƙasan zuciyarsa game da yarinyar. Ya san cewa da ace bai ciro bindigar nan a gabanta ba, ƙila da ba ta firgita har ta rasa hayyacinta ta afka cikin tafkin ruwan ba...
Sai dai halinsa na sadauki bai bar shi ya daɗe a cikin wannan tunanin ba. Ya miƙa hannunsa mai tsawo ya ɗauki wayar ofishinsa dake kan tebur, ya danna lambar sadarwa ta cikin asibitin.
Bayan an ɗaga daga ɗayan bangaren...
"Hello." Arman ya faɗa a takaice cikin muryarsa ta bada umarni...
"Sir!" Inji muryar ma'aikacin dake kula da sassan asibitin..
"Waɗannan 'yan matan da suka zo tare da patient ɗin nan... tabbatar an kai musu abinci da ruwa yanzu."
"Yes, Sir. Za a aiwatar nan take."
"Sannan idan suka kammala a sallame su, a ƙira musu Napep ko taxi. A tabbatar sun isa gida lafiya."
"An gama, Sir. Komai zai je yadda kace...har patient ɗin?.."
Arman ya ce, "No! Iya su domin ɗalibai ne, ya kamata su je gida kar iyayensu su damu..."
"An gama Sir.".
Arman ya ɗan yi shiru kafin ya ƙara da cewa,
"Da buƙatar su je gidan iyayen yarinyar domin sanar da su abin da ya faru..."
"Okay Sir."
Daga nan ya kashe wayar a hankali ba tare da ya ƙara cewa uffan ba. Ya jingina kansa a jikin kujera yana kallon rufin ofishin...
Bayan kusan mintuna goma, wata Nurse ta fito tare da wani ma'aikacin asibitin, hannunsu ɗauke da ledojin abinci da ruwan sha da lemuka...
Ta miƙa musu tana murmushi.
"Ga wannan... an ce ku ci kafin komai."
Dukansu huɗu suka kalli juna cikin tsananin mamaki da fargaba, basu taɓa ganin asibiti mai karramawa da kula da baƙi irin wannan ba.
Daya daga cikinsu ta tambaya, "Don Allah Nurse, waye ya aiko mana da wannan abincin?"
Nurse ɗin ta sake yin murmushi ta ce, "Wanda ya ceto ƙawarku daga ruwa kuma ya kawo ku asibitin nan a motarsa ne ya bada umarnin a kula da ku."
Dukansu suka yi shiru na ɗan lokaci, suna jin wani irin sanyi a zukatansu..
Daya ta share hawayen fuskarta ta ce cikin muryar tausayi, "Wallahi mutumin nan Allah Ya saka masa da gidan aljanna... Mutumin kirki ne na gaban goshi."
Wata kuma ta ɗora da cewa, "Gaskiya kam, a wannan zamanin da muke ciki, ban taɓa ganin mutum mai yawan taimako da karamci irinsa ba. Bai san mu ba, bai san ta ba, amma duba irin hidimar da yake tayi mana."
Nurse ɗin ta gyada kai, sannan ta ƙara da cewa, "Kuma kada ku damu da batun tafiya gida, an riga an kammala shirin Napep ta musamman wadda zata kai ku har kofar gida..."
Jin haka ya sa ɗaya daga cikin kawayen ta kalli sauran, ta ce
"Muna godiya sosai. Amma mu dai ba za mu tafi gidanmu kai tsaye ba muddin aka sallame mu a nan. Dole ne mu fara zuwa gidansu Amira domin mu sanar da Umanta ainihin abin da ya faru. Ba za mu iya ɓoye mata wannan babban al'amari na fitar rai ba."
Sauran ukun duka suka jinjina kawunansu cikin gamsuwa da goyon baya..
"Haka ne, maganarki gaskiya ce. Uma ita ce mahaifiyarta, kuma ita ce ta fi kowa cancanta da ta san ainihin halin da kaddarar 'yarta take ciki a yanzu domin ta taya ta da addu'a."
Nurse ta ce "hakan ma na da kyau.." daga nan ta wuce..