Chapter 8
Da sauri ya qarasa inda take
Maza kizo mu tafi zan kaiki inda zaki zauna "
Seda tayi kamar bazata bishi ba sekuma wata zuciyar tace da ita,
To idan baki bishi ba ina zakije?
Bakida wanda ze iya temakonki a duniyar nan '
Gara ki bishi kawai idan mugu ne koda baki bishiba zeyimiki abunda yaga dama ba fashi.
Ganin kamar bata gama yarda da shi bane yasa yace ,,
Ki kwantar da hankalinki qanwa ta bazan cutar da ke ba,
Zan temakeki kasancewarki mace kuma qaramar yarinya be dace ki zauna anan gurin ba '
Kinga dare ta fara yi kuma akwai 'bata gari sosai a duniya"
Inajin tsoro kada wasu mugayen su cutar da ke.
Dak'yar ta miqe tana rawar sanyi ta shiga motar yaja da sauri '
Hanyar guest house d'insu ya nufa da ita,
ya shiga yayi parking ya fito ya bud'e mata qofa ta fito"
Amma seta kasa binsa su qarasa cikin gidan '
Saboda ta tina yadda taga mamansa tana yimasa fad'a d'azu.
Muje mana......
Muazzam ya fad'a yana rufe qofar motar,
Gir giza masa kai Rafi 'a tayi cikin hawaye tace,,
Bazan iya shiga ba yallaboi tsoro nakeji wallahi bazan iya shiga ciki ba.
Turus Muazzam ya d'anyi yana kallonta da mamaki '
Dodo ne nid'in?
Ko kin ganni da kai biyu ne kikejin tsoro na?
A'a "
Rafi 'a ta fad'a har yanzu bata dena kuka ba ,
To akwai qaho a kai na ne?
Nan ma a'a kawai tace masa"
Fuskar horror kika ganni da shi?
Kad'a masa kai tayi alamar,
A'a.....
Tsawa Muazzam ya daka mata.
Toh menene matsalar? Kina tunanin zan cutar da ke ne? Ko kina tunanin zanyimiki wani abun ne?
Inda ace cutar da ke nakeson yi da ba sena d'auko ki na kawoki nan ba ma "
Da kikasan bakya buqayar temakon meyasa kika nemi a temaka miki?
Kode kina tunanin ni irin y'an iskan garin nan ne da zan d'auke ki dan na buqaci wani abu daga gareki?
Da sauri ta gir giza masa kai,
A'a,,
Wallahi yallaboi ba haka nake nufi ba '
Inajin tsoro ne kar mahaifiyar ka ta koreni idan na shiga"
Naga tanayimaka fad'a akan cewa kada ka temakamin.
Muazzam ya furzar da wata iska daga cikin bakinsa sannan yace '
No"
Bazata gankiba balle ma har ta kore ki,,
Bayan ni babu wanda zesan kina nan ,
Wannan guest house d'in mu ne "
Babu kowa a ciki..
Zakici gaba da zama a nan babu wanda ze takuramiki kokuma ya koreki,
Tare suka shiga ciki,
Wani qaton parlor ne me kyau sosai,,
Wani stor ne kawai da kitchen a qasa se d'akuna a sama.
Cikin sassarfa Muazzam ya fara hawa a hankali '
Seda ya kusa qarasawa ya juyo yaga Rafi 'a tsaye a gurin da ya barta,,
Ki taho na kaiki d'akin da zaki zauna a ciki mana.
Ya fad'a yana cigaba da hawa"
Bazan iya ba ban ta'ba hawa irin wannan ba.
Rafi 'a tayi maganar da iyakar gaskiyarta,
Domin ita tunda take ko a mafarki bata ta'ba shiga gida me beni ba"
A hankali Muazzam yayi mur mushi Sannan ya sauqo ya riqe hannun ta,
A hankali ya fara janta zuwa sama '
Wayyo baffa na......
Na shiga uku baffa yaya Ajimal wayyo Allah .
Sosai Rafi 'a ta qanqame Muazzam tana ihu saboda yadda taji kanta na juyawa daga fara hawa '
Ke "
Kanki d'aya kuwa? Menene hakan?
Kidena wannan ihun babu abunda ze sameki .
A'a nikam ka sauqeni,
Dan Allah ka sauqeni wayyo baffa na na shiga uku"
Shhhht.....
Muazzam ya fad'a tare da d'aura yatsarsa akan lips d'insa.
Shiru Rafi 'a tayi amma har yanzu jikinta kyarma yake kuma bata sassauta riqon da tayiwa Muazzam ba '
Sakeni toh,,
A'a ' Wallahi fad'uwa zanyi Wayyo baffa Dan Allah ki sakeni bazaki fad'i ba ,,
Ki dena kallon qasa zan riqeki seki haura babu abunda ze sameki.
A'a,
Wallahi ina sakeka fad'uwa zanyi '
Dan Allah ka sauqeni qasa ,,
Ganin zata 'bata masa lokaci ne yasa ya d'aga ta cak ya nufi saman da ita.
Seda ya shiga cikin d'akin sannan ya sauqe ta"
Inane band'aki?
Kabani buta zanyi alwala Toilet d'in kawai ya nuna mata da hannu ta shiga '
Da sauri ta fito.....
Babu buta a cikin band'akin nan fah' dan Allah ka samamin buta.
Ke"
An fad'a miki ana amfani da buta a irin wannan band'akin ne?
Da sauri Rafi 'a ta zaro manyan idanunta , Ba a amfani da buta?
Idan mutum yanaso ya kama ruwa ko yayi alwala kuma fah?
Kode ba a alwala a gidan nan ne?
A'a ,
Anayi mana amma ba da buta akeyi ba. To da meye akeyi?
Kode kuma da gora kukeyi ne?
Nikam ko gorar nema kabani na samu nayi sallah ko sallar azahar banyi ba ,,
Ganin tana tayimasa tambayoyi ne yasa ya shige toilet d'in ya nunamata famfo,
Laaaaa.,......
Harda famfo '
Dama ana saka famfo a cikin band'aki ne?
Kiyi alwala kiyi sallar bari naje na dawo "
Muazzam ya fad'a sannan ya fice daga toilet d'in.
Tana idar da sallah ya shigo riqe da ledodi a hannunsa ,
Wata doguwar riga ruwan powder ya ciro ya miqamata "
Je kiyi wanka ki canza kaya.
Batayi musu ba ta amsa ta shige toilet d'in ,
Sede batasan taya zatayi wankan ba domin bataga bokiti a cikin band'akin ba '
Ganin ta fito batayi wankan bane yabawa Muazzam mamaki"
Se a lokacin ya tina ashe batasan yadda zatayiba.
Da kansa ya shiga ya kunna mata ruwan sannan tayi wankan '
Kayan sunyi mugun kar'bar ta ,,
Idan ka ganta seka rantse ba waccar Rafi 'atun bace.
A bakin gado ta tarar da Muazzam a zaune yana danna waya '
Duk da shi ba ma abocin kallon mata bane amma da ya kalleta se da yayi sha awar qara kallonta "
Saboda yadda yaga ta qara kyau kamar ba ita ba .
D'ayar ledar ya miqamata sannan yayimata sallama ya tafi yacemata ze dawo da safe a qasa ta zauna ta bud'e ledar kaza ce a ciki da yogurt seda ta cinye tass sannan ta kwanta domin tun safe bataci komai ba,
Haka kuwa akayi da safe ya dawo ya tambayeta ko tana buqatar wani abu '
Tacemasa... A'a ,,
To amma kin iya girki? Eh na iya sosai ma ,,
Okay , Bari naje nayiwomiki cefanen kayan abinci idan kina buqatar wani abu ki sanar da ni .
Toh yallaboi "
Kada ki sake kirana da yallaboi , Toh da wani suna zan dinga kiranka? Seda ya d'an nisa sannan yace ' Ki kirani da Barrier...
Toh Barrier.
Besan dalili ba amma se yaji kamar babu wanda ya iya furta sunan dede kamar yadda ta furta,
Seda ya d'an yi mur mushi Sannan ya fita "
Satin ta d'aya a gidan kullum Muazzam seyazo kafin ya wuce gurin aiki '
Kuma bayan ya dawo aiki kafin ya koma gida seya zo ,,
Haka da dare kafin yayi bacci se yazo ya dubata.
Sede duk lokacin da ya tambayeta wani abu game da rayuwar ta ,
Bata bashi amsa sede tayita kuka ' Haka ze gaji ya rabu da ita.
Qarfe bakwai da talatin na safe ,,
Kamar yadda aka saba Muazzam yazo dubata ya tarar da ita a lullu'be tana rawar sanyi ,
Subhanallah.....
Rafi 'a me yake damunki? Zazza'bi ne da ciwon kai da jiri " Sannu koh ....
Kinci abinci ne ?
A'a ,,
Babu abunda naci tun jiya ' Subhanallah "
Ki jirani ina zuwa kinji koh '
Ya fad'a sannan ya sauqo qasa ya shiga kitchen.
Tea ya had'a me kauri da wainar kwai "
Ya kawomata seda ya temaka mata sannan ta tashi ta zauna ta fara ci,
Ko kammala cinyewa batayiba ta kwaro amai ya wanke masa jiki da bed sheet d'in .
Sosai taji tsoro idanunta suka cicciko da hawaye"
Dan Allah kayi haquri Barrier Wallahi bana sane nayi ,
No '
Karki damu..,..
Ya fad'a sannan ya saka hannu ya d'ago ta ya shiga toilet da ita "
Se da ya wanke mata jikinta tass sannan ya d'auko kaya ya miqa mata ta saka ,
Seda shima ya wanke jikinsa sannan ya tattara bed sheet d'in ya wanke.
Rafi 'a kam ji take kamar mafarki take wai itace akeyiwa wannan kulawar kawai saboda batada lafiya ,
To wani irin kulawa ake bawa masu iyaye kenan?
Ta d'anyi mur mushi me d'aci tana kallon Muazzam cike da mamakin dama har yanzu akwai mutane irin su a duniya.
Muazzam nayi magana da dadyn ku akan maganar da mukayi dakai ranan "
Kuma yace tunda kace bakada budurwar da kakeso ,
Tunda ga umai ma qanwarka se a had'aku kawai ' Kaga anyi tuwo na mai na kenan.
Shiru Muazzam ya d'anyi yana tunani ,,
Kamar baze amince ba se kuma wata zuciyar sa tace da shi '
Kai da ba soyayya kake ba menene ma na rashin amincewa kawai ka kar'beta tunda dama ba sanin soyayyar kayi ba?
Inde ita yarinyar ta amince kawai ka cikawa Momi burinta na ganin ka mallaki iyali "
Shikenan Momi babu komai duk yadda kuka yanke ,
Idan ita umaian ta amince babu wani abu se ayi.
Wani irin dad'i ne ya lullu'be umai ma da tun shigowar Muazzam take maqale a bakin qofa '
Jin yana yiwa Momi bankwana ne yasata juyawa da sauri ta koma d'akinta ,,
Tsalle ta shiga yi tana rawa '
Se da ni wallahi amaryar Muazzam komi dozin .
Kusan kullum yazu se Rafi 'a tayiwa Muazzam amai "
Har yariga ya fara sabawa da hakan shiyasa yake d'auko wasu kayan idan ze zo .
Besan dalili ba amma duk abunda yarinyar tayi bata bashi haushi,
Haka kuma duk da kasancewarsa me tsafta da kyama "
Bayajin komai Idan Rafi 'a tayi masa amai ,
Wani lokacin shi da kansa yana tambayar kansa dalili "
Amma se zuciyarsa ta fad'a masa cewar wataqila saboda yanajin tausayin ta ne .
Ga wasu sabin abubuwa da take fama da su '
Kullum da yamma tayi se zazza'bi ya rufeta amma da zarar gari ya waye shikenan ,,
Gashi wani lokacin haka kawai se taji tana sha awar '
D'anyen mangoro agwaluma da de sauran wasu abubuwa ,
Yau ta tashi da kwad'ayin wainar fulawa.
Kamar kullum Muazzam yazo dubata "
Barka da safiya Rafi 'a ,
Barka da shigowa Barrister "
Ina kwana....
Lafiya qalau Rafi 'a kin tashi lafiya? Eh Lafiya qalau Alhamdulillah.
Ina fatan de kinci abinci?
A'a '
Banason cin komai ne ,
Kallon robar hannunta yayi da tunda ya shigo yaga tanata faman lasar abun ciki.
Menene wannan kuma?
Man quli ne da yaji zaka sha?
A'a ,
Na gode"
Akwai dad'i sosai fa ka ta'ba zakaji.
A'a gaskiya nide bazan sha ba ,
Man gyad'a da yajin borkono ni ba maye ba.
Dariya tayi tace ,,
Ai kuwade yanada dad'i kam dan baka ta'ba sha bane '
Meyasa bakici komai ba se wannan ?
Wainar fulawa kawai nake sha awa kuma banajin dad'i shiyasa banyi ba.
Wainar fulawa kuma Rafi 'a?
Ohhhh '
Ban iya wainar fulawa ba Rafi 'a kinada fitina wallahi ,,
Sekace wata me ciki '
Muazzam ya fad'a yana qaremata kallo.
Kai kawai ta sunkuyar ba tare da tacemasa komai ba,
gefen gadon ya samu ya zauna sassanyan qamshin turarensa na dukan hancin ta "
Wayar sa ya zaro ya lalubo number umai ma'
Hello Umai ma kina gida ne? Eh ina gida kana buqatar wani abun ne?
Eh dan Allah.....
wainar fuwala nakeso kiyimin ,,
winar fulawa kuma yaya Muazzam?
Na tafi office ne se naji sha awar ci shine nace bari na kiraki ,
Okay my future husband bari nayimaka kawai kad'an jira just 30 minutes.
Umhm "Okay "
Idan kin kammala se ki kirani nazo na kar'ba koh ,
Shikenan an gama kar ka damu.
Sauqe wayar yayi daga kunnensa ya kalli Rafi 'a yana mur mushi "
Shikenan zaki samu abunda kikeso ba sekin ini da yunwa ba koh.
Daga masa kai tayi tana mur mushi sosai takejin dad'in kulawar da yake bata'
Shikam kallon ta kawai yake yana mur mushi ,,
Besan meyasa yakeson kallon ta cikin farin ciki ko yaushe ba '
Haka yayita janta da hira har umai ma ta kira tace ta gama '
Toh sarkin rigima bari naje na kar'bo miki wainar fulawar da kika kasa cin komai saboda ita .
A dawo lafiya ,
Rafi 'a ta fad'a tana mur mushi '
Sosai takejin dad'in irin kulawar da yake bata duk da besan wacece ita ba.
Bewani jima ba ya dawo riqe da kula har da plate da ruwan sanyi,
Da kansa ya zuba ya miqa mata "
Barrister kaima kaci mana ,,
A'a '
Gaskiya ni irin abubuwan nan basu dameniba.
Befi loma uku tayi ba ta fara sheqa amai ''
Gaba d'aya ta 'batawa Muazzam jiki ,
Da dare bayan ya dawo gida dady ya sanar masa ya sanya ranar aurensa da umai ma nan da wata biyu .
Yadda beyi farin ciki da maganar ba haka ma beyi baqin ciki ba '
Domin baya qin umai ma haka kuma be ta'ba ji yana sonta ba ,,
umai ma kuwa murna da farin ciki ba a cewa komai "
Gaba d'aya ta gama sanar da qawayenta nan da wata biyu zata zama amaryar yaya Muazzam.
Saboda yadda jikin Rafi 'a yaqi dad'i Muazzam yace ta shirya zasuje asibiti tare ,
Batayimasa musu ba ta shirya tsaf cikin wata koriyar atamfa me kyau "
Ta d'auko farin hijabi ta saka '
Tayi wani bala in kyau kamar ka sace ta ka gudu .
Tare suka shiga office d'in likitan ya basu gwaje gwajen da zatayi ,
Bayan tayi yace su jira sakamakon gwajin ya fito '
Bayan kamar mintuna talatin likitan ya fito yace yanason ganinsu a office d'in sa.
Congratulations malam Muazzam ,
Ina tayaka murna matarka tana d'auke da ciki wata biyu "
Ciki..........
Muazzam ya furta da qarfi yana kallon Rafi 'a yana gir giza kai ,
Noooooo.......
Dr noooooo '
Kinajin abunda yake fad'a Rafi 'a?
Kicemin qarya ne ba gaskiya bane "
Rafi 'a dan Allah kicemin ba dede kunnuwa na suka ji ba .
Rafi 'a kam suman tsaye tayi dan kallon Muazzam kawai take yana magana amma batasan me yake cewa ba ,
Tana tsaye kamar an dasa ta "
Bayan hawaye da sukebin fuskar ta babu wani abu da yake motsi a jikin ta domin hatta zuciyar ta seda ta dena bugawa na wasu mintuna .
Muazzam kam mamaki ne had'e da tsoro bayyane akan fuskar sa ,,
Ganin yadda Rafi 'a ke tsaye ta kasa ta'buka komai ne yasa Muazzam kai hannu ya jijjigata da qarfi '
Se a lokacin taja wani dogon numfashi had'e da fashewa da wani irin kuka me ban tausayi.
Durqushewa tayi a gurin tana rera kuka zuciyar ta kamar zata fashe ,
Wani mugun damqa Muazzam ya kai mata ya ja hannunta suka fice "
Da qarfi ya hankad'a ta cikin motar ya shiga ya fizgi motar a guje ya nufi hanyar gida,
Rafi 'a kam tunda suka kama hanya banda kuka babu abunda takeyi ,,
Yana shigowa cikin guest house d'in be ko tsaya gyara parking ba ya fito ya fizgota da qarfi ya nufi ciki da ita.
Suna shiga ya cillata ta fad'a a kan gado da qarfi ,
Duk jikinta se rawa yake domin ko da wasa bata ta'ba ganin bacin ran Muazzam kamar na yau ba.
Kai komo ya shigayi a tsakiyar d'akin '
Idanunsa sun kad'a sunyi ja gaba d'aya jijiyoyin kansa sun mimmiqe ,,
Wani irin huci yake kamar wani mayunwacin zaki.
Da qarfi ya yake dukan bangon d'akin da hannunsa kafin ya juyo kamar ze yiwo kan Rafi 'a ,
Se kuma ya kaiwa Waldorf duka da qarfi da qafarsa.
Dammm... Dammm... Dammm....
Qirjinta ya bada da wani irin sauti me mugun qarfi lokacin da Muazzam ya zauna a kusa da ita "
Kansa ya dafe yana fitar da numfashi da qarfi '
Ya kai kusan mintuna biyar a haka kafin yace ,
Wacece ke Rafi 'a?
Jin tayimasa shiru ne yasashi mai maita tambayar cikin tsawar da ta saka Rafi 'a zabura da sauri ta fashe da wani irin kuka me qarfi.
" I said , who are you ? "
Wacece ke ?
Menene ya baro da ke daga gidan ku?Taya akayi kika samu ciki da wad'annan qananun shekarun naki?
Menene dalilinki na 'boyemin ke wace?Cikin jikin ki shege ne ko yanada uba?Idan yanada uba to menene dalilinki na baro gidan ubansa da shi?
Jin kukan da takeyi yaci qarfin ta har yana neman hanata magana ne yasa ya miqe ya nufi qofa da niyyar ficewa.
Hannunsa ta riqe da sauri cikin kuka tace '
Tafiya zakayi Barrister?
Dan Allah kayi haquri da 'boye maka asalina da nayi ,,
Ba nayi hakan ne kawai saboda banaso kasan wacece ni ba '
Nayine saboda inajin tsoron kada kaima ka kyamaceni kamar yadda sauran mutane suke kyama ta ,Cikin jikina kuma na rantse maka da wanda numfashina yake hannunsa "
Ba shege bane d'an halak ne da aure na sameshi.
Dafe kansa yayi da sauri cikin mamakin kalmarta ta qarshe '
Aure..... Aure....
Aure Rafi 'a? Ashe dama ke matar aure ce? Meyasa kika 'boyemin?
Why Rafi 'a?
Why?
Ya fad'a yana zubewa a bakin gadon tare da dafe kansa.
Dan Allah kayi haquri Barrister "
Zan fad'a maka komai game da ni yanzu babu abunda zan 'boye maka ,
Amma dan Allah idan na fad'amaka wacece ni kada kaima ka gujeni kamar yadda sauran mutane sukayi '
Duk dunuyar nan bayan kai banajin akwai wanda ze iya temako na saboda Allah "
Idan ka gujeni bansan ina zan shiga ba '
Koda bazaka ciyar da ni ba ,..
Dan Allah kabani iya gurin zama zan fita in nemi abinci ,, Idan na samu naci idan ban samuba dama na saba zama da yunwa.
Ta qarasa maganar hawaye nabin kuncin ta "
Se kuma Muazzam yaji tayi matiqar bashi tausayi sosai , Kalamanta sun tsaya masa a zuciya ,,
Cikin sanyin murya yace....
Ki fad'amin wacece ke Rafi 'a " Ina sauraron ki kuma a shirye nake da kar'ba ki koma wacece ke d'in.
Ni shegiya ce....
What?
subahanallahi " Menene haka Rafi 'a?Meyasa kike kiran kanki da sunan da yafi ko wani suna duhu da qunci?
Rafi 'a meyasa kike kiran kanki da sunan da duk duniya babu wanda yake sha awar a kwatan tasa da shi?
Duk da kowa bayason sunan amma masu sunan ya zama dole su amsa shi "
Koda kuwa hakan baya yimusu dad'i.
A nan Rafi 'a ta bashi labarin rayuwar ta tun daga farko har ranar da suka had'u ,
Sosai jikin Muazzam yayi sanyi se yaji wani tausayin yarinyar ya qara kamashi,,
Kiyi haquri Rafi 'a '
Kuma ki dena kiran kanki da wannan sunan ko da wasa kar na sake ji , Kawai dan an tsinceki baya nufin ked'in shegiya ce " Tabbas kin fiskanci qalubale sosai a cikin rayuwar ki ' Amma inaso kisani duk wata wahalar ki matakin kaiwa ga nasarar kice a cikin rayuwar ki.
Bazan ta'ba rabuwa da ke ba Rafi 'a kuma yanzu ne na d'aura d'amarar temakonki a koda yaushe ,
Kuma insha Allah zanyi iyakar qoqarina wajen ganin na sadaki da iyayenki.
Sosai kalaman Muazzam sukayiwa Rafi 'a dad'i ,, Se a lokacin ta d'an samu nitsuwa a cikin ranta '
Seda Muazzam ya kwantar mata da hankali sosai kafin ya tafi.
Ya jima yana jinjina irin zalunci da rashin imanin Amo a zuciyar sa '
Saura sati d'aya bikin Muazzam da umai ma,
Ko kad'an Muazzam baya farin ciki da auren "
Yanajin kamar yace a dakatar domin zuwa yanzu duk da besan meye so ba amma ya gama fahimtar ko kad'an bayason umai ma a zuciyar sa.
Ya qara yawaita zuwa wajen Rafi 'a ,
Domin haka kawai yake samun kansa cikin farin ciki a duk lokacin da yake tare da ita ,,
Wata nitsuwa ta musamman yake samu idan tana kusa da shi wanda shi kansa besan dalilin ta ba .
Ita kanta Rafi 'a ta saba da shi sosai duk lokacin da yazo jitake bataso ya tafi saboda kad'aici'
Haka kawai ta tsinci kanta da fad'uwar gaba lokacin da Muazzam yacemata zeyi aure ,
Batasan dalili ba amma tanajin inda za a fasa auren da se yafi.
Wani lokacin idan taji ta gaji da zama a gidan seta roqi Muazzam su tafi sayayya tare "
A garin haka ne aka samu wani munafuki yaje yacewa Momi , Muazzam ya d'auko karuwa ya ajiye a guest house d'insu har hotonsu seda aka nuna mata tare dan ta qara tabbatarwa.
Cikin Rafi 'a ya fara girma gashi yana bata wahala sosai '
Wani lokacin ko band'aki zata shiga se Muazzam ya temaka mata ,, Hakan ne yasa kusan fiye da rabin wuninsa yanayine tare da ita kuma be ta'bajin ya gaji ba.
Cikin yana yawan sakamata ciwon qirji wasu lokutan haka yake sakata aman daskararruen jini guda guda '
Rafi 'a ta fito daga toilet taji wani jiri na d'ibar ta har yana shirin jefar da ita ,
Dede lokacin da Muazzam ya shigo ya ganta dafe da qofar toilet d'in tana shirin fad'uwa.
Da sauri ya qarasa ya tallafo ta ya riqo hannun ta ' Sannu Rafi 'atu......
Ki dinga kulawa sosai kinga kefa yanzu ba ke d'aya bace saboda haka ki dinga.....
Idan ba ita d'aya bace to ita da ubanta ne?
Muryar Momi yaji kamar daga sama.
Suman tsaye yayi yana bin umai ma da Momi da suka shigo a tare da kallo " Wato Muazzam abunda aka fad'amin a gari gaskiya ne kenan?
Kaje ka d'auko karuwa ka ajiye a gida harda ciki ai dole kace baka damu da aure ba ,
Haba Muazzam wallahi ka bani kunya kuma kabanin mamaki '
Momi dan Allah ki tsaya ki saurareni wallahi ba ,,
Tass..... Momi ta d'aukesa da mari ta sake d'aukesa da mari ' Ta rufesa da duka ko ta ina tana fad'in "
Wallahi Muazzam kabani mamaki ka lalata rayuwar ka ka zubar da darajar gidanmu da na iyayenka .
Me kakeso ka kawo mana a cikin zuri ar mu Muazzamu?
Cikin shege? D'an shege a ahalin mu Muazzamu?
Momi ta qarasa maganar tana fashewa da kuka.
Muazzam baida qarfi ko kad'an da ze kare kansa ,
Saboda haka yanaji tana dukansa amma ya kasa koda motsa d'an yatsar sa "
Hajiya dan Allah kiyi haquri wallahi ba lefinsa bane d'anku bashida......
Bata qarasa ba Momi ta d'ageta da wani wawan mari seda ta kife a qasa ,,
Sosai Muazzam yaji marin da Momi tayiwa Rafi 'a har cikin ransa.
Yimin shiru baqar munafuka algunguma kawai "
Ke har kina da bakin da zaki yimin bayani?
Idan ba shi yayimiki cikin nan ba to ubankine yayimiki shikuma yazo yake Reno?
Daga Muazzam har Rafi 'a babu wanda ya sake cewa komai bayan kukan da sukeyi gaba d'ayan su.
Momi ki barni naci kutumar uban shegiyar yarinyar nan y'ar iska karuwa kawai me kwacen mazan mutane.
Cewar umai ma da take qoqrin damqo wuyan Rafi 'a a zuciye '
Rabu da ita umai ma ai idan akwai wanda ya kamata a hukunta baze wuce wannan baqin munafikin ba domin inda be d'auko ta ba da baze qunsa mata wannan abun kunyan da take d'auke da shi yanzu ba .