Chapter 11
BY
FATIMA USMAN
SHA LELEN TERAWA.......
Ke umai ma bakida hankali ne me ya kawoki nan da wannan lokacin ?
Cewar Muazzam da yake qoqarin kare Rafi 'a da taketa faman 'boyewa a bayansa .
Kasheta zanyi yaya Muazzam ,,,
Wallahi sena kasheta Na fad'a maka bazan iya shearing naka da wata ba saboda haka duk wacce ta aureka wallahi sena kasheta ta.
Ta qarasa maganar tana nufo inda Rafi 'a take gadan gadan "
Ta d'aga wuqar da niyyar cakawa Rafi 'a Muazzam yayi saurin saka hannunsa wuqar ta yankeshi ,
Umai ma ta sake yunqurawa zata kaiwa Rafi 'a farmaki da wuqar '
Wani mugun mari Muazzam ya d'auke ta da shi wanda yasa wuqar hannunta fad'uwa .
Ashe ke jahilace ban sani ba "
Ke mahaukaciyar ina ce ? Me tayimiki da kike neman kasheta?
Kawai saboda ta aureni shine lefinta?
To idan saboda wannan ne kikeson ganin bayanta kifara kasheni '
Domin ba ita tace tana sona ba nine da kaina naga tayimin kuma na nemi auren ta ,,
Saboda haka kada ki sake ki ta'ba y'ar muyane .
Ni ka mara akan wannar aljanar?
umai ma da ke dafe da kuncin ta tana ta faman kuka ta fad'a cikin suyar rai '
An mareki ko zaki rama ne?
Muazzam ya bata amsa yana takowa zuwa gaban ta ,
A'a "
Bazan rama ba amma wallahi sena kashe wannar tsinanniyar .
Ta fad'a tana qoqarin janyo mayafin Rafi 'a da keta faman 'buya "
Wani marin Muazzam ya sake d'auke ta da shi seda taga duhu ya wulga '
Kada ki sake ki ta'ba ta idan kika ta'ba ta wallahi sena sa'ba miki a gidan nan ,
Ba iya yanzu ba ko wataran duk randa kika sake kika kai hannunki jikinta da sunan cutarwa To wallahi a bakin auren ki kuma ki kama hanya ki ficemin daga nan yanzun nan .
Muazzam ya qarasa maganar yana nuna mata hanyar fita '
A bakin aure na?
Yaya Muazzam yau ni kake cewa zaka saka saboda ka kawo sabuwar mata gidan nan ?
Baka ta'ba mari na ba se yau a kanta kuma insha Allah daga yau bazaka sake koda dunguri na ba inde akanta ne ,,
Kekuma zan tafi amma inaso ki rubuta ki ajiye '
Wallahi... Wallahi.... Wallahi...
Sekinyi dana sanin sanin mijina a rayuwar ki Se nasa kin gwammaci mutuwa da rayuwarki "
Kuma abu na qarshe inaso ki rubuta ki ajiye ,
Wallahi kozan tafi tsirara se nasa kin d'an d'ana kud'ar ki Se nasa rayuwar ki ta shiga uku kuma wallahi sekin barmin miji na .
Fuuuuu......
Ta banka qofar ta fice cikin sauri kamar zata tashi sama ,,
Na shiga uku Barrister....
Na shiga uku....
Shikenan rayuwata ta shiga wahala wayyo ni Rafi 'a .
Rafi 'a ta kai qarshen maganar tana durqushewa had'e da fashewa da wani kuka me ciwo '
A gaban ta Muazzam ya durqusa ,,
Ki kwantar da hankalinki Rafi 'a kada ki bari abunda ta fad'a ya dameki '
Kawai kishi ne ya rufe mata ido har ta furta wad'annan kalaman amma babu abunda zata iya yimiki.
Haka Muazzam yayita faman kwantar mata da hankali har seda yaga ta d'an samu nitsuwa "
Washe gari da safe Muazzam ya nufo d'akin umai ma Domin a tunaninsa zuwa yanzu ta fara sauqo wa '
Mun tashi lafiya uwar gida na?
Wata uwar harara umai ma ta watsa masa ta kawar da kai ,,
Naga kamar bakiyi girki ba koh?
Eh banyiba se me?
Amma kinsan kece zaki ciyar da mu har na tsawon kwana uku kafin mu fara raba kwana Koh?
Dole na ciyar da ku na kwana uku tunda ga qanwar uwa ta ka kawo gidan '
To wallahi bari na fad'amaka k'wayar abinci bazan dafa na bawa wannan jakar ba a cikin gidan nan ,,
Inde har bazata dafa ba to wallahi sede yunwa ta kasheta '
Domin ko jinya takeyi inde bazata iya girki ba wallahi bazan dafa lomar abinci na sammata ba.
Mur mushi kawai Muazzam yayi ya fice daga d'akin '
Yana fita umai ma ta d'auko waya ta kira Momi ,,
Hello Momi na.....
umai ma ta fad'a tana rushewa da kuka '
Subhanallah umai ma menene ya sameki kike wannan kukan ?
Momi kece kike tambaya ta dalilin kuka na ? Alhali kuma kinfi kowa sanin dalili na.
Haba umai ma yanzu akan wannar qaramar alhakin kike asarar hawayen ki?
Ki dena damun kanki ki saka a ranki baqunta tazo gidanki na wani lokaci ,
Momi wallahi abun ya wuce yadda kike zato "
Jiya fa yaya Muazzam har Mari na yayi a cikin gidan nan yayimin dukan tsiya ya tattakani saboda ita,
A gaban ta yayita kwallo da ni dak'yar aka kwace ni '
Kuma yace wallahi duk randa na sake na ta'ba ta a bakin aure na .
Wai Muazzam d'in ne yayi haka ?
Ki kwantar da hankalinki umai ma wallahi Muazzam se yayi nadamar abunda yayimiki ,,
Kuma yarinyar nan se tabar gidan wallahi dole ki rayu ke kad'ai a gidanki ki juya ta inda ranki yaso '
Maza yanzu ki taho mu koma gurin boka wallahi setayi dana sanin had'a miji da ke Seta gwammaci ta qare rayuwar ta babu aure .
Kamar de ranan boka ya tabbatar musu babu nasara amma su d'an qara jira zasu samo wata hanya ,
A ranar da Muazzam ya cika kwana uku a d'akin Rafi 'a suka fara raba kwana kamar yadda musulici ya tanadar "
Dariya kawai umai ma take bashi yadda taketa wani sha ssha masa qamshi tanata abubuwa wai ita a dole kishi ,
Rafi 'a na zaune tana kallo a parlor umai ma ta fito '
Rimot d'in ta d'auka ta canza tasha tana wani taunar cingam qasss qasss......
Ina kwana aunty Rafi 'a ta fad'a cikin ladabi ,
Ke......
Wacece auntyn taki? Ni sa ar wasan ki ce da kika wani d'ebo gaisuwar ki ta kini bibi da muna furci ke ga me hankali koh?
To wallahi ki kama kanki ki shiga tai tayin ki ,,
Kiyi rayuwar ki nayi tawa kada ki sake ki shiga harka ta Munafuka kawai wani wai ina kwana aunty salon ace tanada hankali .
Ta qarasa maganar had'e da jan wani dogon tsaki ta wuce fuuuuu tabar Rafi 'a zaune a gurin ,
Ohh ni Rafi 'atu na shiga uku "
Wace iriyar uquba ce tattare da qaddara ta? Da farko Amo se Gaddafi ,
Na rabu da su yanzu na fad'a hannun kishiya ,,
Allah kana ganina nasan baka manta da ni ba kana sane da ni Ka gaggauta kawomin agajin ka .
Rafi 'a na kitchen tana had'a musu break fast ta kammala jera sauran a dining ,,
umai ma ta shigo da sauri ta bud'e plass d'in ta d'auko gishiri ya kusa gwan gwami biyu ta juye a ciki ta fice da sauri '
Bayan Rafi 'a ta kammala soyamusu wainar k'wai da bread ta jera ,
Muazzam da kansa yaje kiran umai ma domin su karya ya tarar da ita tana baccin qarya "
Har ya juya kamar ze fita se kuma ya dawo ya tasheta suka fito tare .
Sosai yayi mamakin ganin yadda ta sake kamar ba ita ba '
Se da Rafi 'a ta zubawa kowa sannan ta zuba nata ta zauna suka fara ci ,,
umai ma se Allah Allah take Muazzam ya fara shan tea d'in domin taga wani irin mataki ze d'auka a kan Rafi 'a .
Wani mur mushi ta saki a 'boye ganin Muazzam ya d'auko tea d'in ze fara sha ,
Amma murnar ta ta koma ciki ganin Muazzam yayi kur'ba na farko ya qara na biyu ba tare da yace komai ba '
Ganin yadda Muazzam yake shan tea d'in kamar babu komai ne yasa umai ma fad'in ,
To kode ta canza ne? A cikin ranta "
Se ta kai hannu ta d'auko tea d'in dan taji kode Rafi 'a ta canza ne yasa Muazzam be jiba .
Kur'bar fari umai ma ta fesar saboda wani gishiri da taji kamar ze yankemata harshe ,
Oh my God......
Wannan wani irin tea ne?
umai ma ta fad'a tana faman zubar da yawu a tunaninta Muazzam ze goyamata baya suyiwa Rafi 'a fad'a '
Ga mamakinta se ji tayi Muazzam yace mata ,,
Menene ya sameshi?
Gishiri a cikin tea wannan wani irin hauka ne? Gishiri kuma?
Gaskiya nide ban ji ba sede ko bakin ki ne .
Wallahi ba baki na bane gishiri ne a cikin wannan tea d'in "
To kode acikin naki abun yake ne?Muazzam ya fad'a yana miqa hannunsa ya d'auko tea d'in gabanta ya kur'bar ,
Banji komai ba fah na fad'a miki bakin ki ne kawai amma babu wani gishiri a cikin tea d'in nan koh Rafi 'a ta ?
Yayi maganar yana qiftawa Rafi 'a ido domin bayaso ta fad'i gaskiya ,,
Se a lokacin Rafi 'a ta d'anyi ajiyar zuciya na jin dad'i tace '
Eh ,,
Gaskiya nima banji komai a ciki ba Ta qarasa maganar tana qara kaiwa bakin ta Babu yadda umai ma batayiba amma Rafi 'a da Muazzam sukace basuji komai ba .
Sosai jikinta yayi sanyi da ganin yadda Muazzam ya shanye tea d'in tass ya ajiye kofin ,
Itade tunda take bata ta'ba gani Muazzam ya shanye tea a gurin karyawa ba se yau "
Da sauri ta juya ta shige d'akinta ta fad'a a kan gado ta fashe da kuka .
Muazzam da Rafi 'a har suna rige rigen shigewa toilet '
Gaba d'aya suka amar da abunda sukaci suka fito ,
Muazzam ya janyo Rafi 'a da keta faman nishi Sosai ya had'a ta da jikinsa yana mur mushi '
Sannu Rafi 'a ta yau kinsha wahala sosai saboda kishi koh?
Seda ta qara narkewa sosai a jikinsa sannan tace ,,
Barrister dan Allah kayi haquri wallahi ban sani ba .
Kumatun ta ya d'an ja a hankali yana mur mushi ,
Ke kallleni......
Kai ta d'ago ta kalleshi tana mur mushi "Kinaso nayi haquri ?
Eh dan Allah '
Rafi 'a ta fad'a cikin shagwa'ba .
Bakinsa ya turo mata yana mur mushi "
Kiss me.......
Bakinta ta kai ta kama lips d'insa da haqoranta ta ciza ,
Aushhhh......
Muazzam ya fad'a yana janye jikinsa da sauri .
Ya saka hannu yana mul mula lips d'insa domin da gaske yaji zafin cizon '
Da gudu ta miqe tayi parlor tana dariya Muazzam ya biyo ta yana dariya ,,
Zo nan Rafi 'a yau sekin gane idan na kamaki bazanyi haquri ba sena rama,
Jin hayaniya a parlor ne yasa umai ma tasowa ta leqo ta window "
Wani abu me d'aci ya taso ya tokare mata qirji .
Tanajin sauqar dariyan su kamar narkakken ruwan dalma a zuciyar ta ,
Wasu hawaye suka fara sulalowa daga idanunta Jitakeyi kamar an huramata wuta a ciki qirjinta .
De'bes ta fad'i ta baya dede lokacin da taga Muazzam ya d'aga Rafi 'a ya shige bed room d'in sa da ita,,
A gurin ta kwanta tanajin numfashin ta yana sama sama saboda 'bacin rai .
Muazzam kuwa a kan gado ya ajiye Rafi 'a yana dariya yace Yanzukam kin shigo hannu na se nayi maganin wannan d'an bakin "
Yayi maganar yana jan lips d'in ta .
Barrister ......
Ummm ,
Meyasa ka sha wannan tea d'in kuma kacewa aunty bakaji gishiri a ciki ba?
Saboda nasan Rafi 'a ta tana da hankali bazata aikata haka ba.
Ai naga umai ma tana mur mushi lokacin da na d'auko zan fara sha saboda haka na gane dole akwai sa hannunta a ciki "
Domin babu yadda za ayi da hankalinki ki zuba gishiri a cikin tea .
Rungumeshi Rafi 'a tayi tana mur mushi ,
Na gode da kake fahimta ta a ko wani hali miji na .
Yau umai ma ce tayi girki yau da kanta ta zubawa kowa kamar yadda taga Rafi 'a tanayi kullum "
Rafi 'a tana kai lomar farko ta ajiye cokalin da sauri ,
Ji tayi kamar da zallan yaji akayi abincin ,,
Kofin lemo ta d'auko ta kur'ba tana faman goge bakinta da hannun ta '
Me ya faru Rafi 'a?
Muazzam ya tambayeta domin a iya rabon Rafi 'a juriyya ta zuba yajin "
Shiru kawai Rafi 'a tayi ta riqe kanta tana hawaye ,
Hannu Muazzam ya saka ya d'auki cokalin ya kai lomar abincin Rafi 'a baki'
Da sauri ya furzar Sannan ya d'ebi na juriyya ya kai bakinsa amma beji wannan azababben yajin a ciki ba .
Da sauri ya miqe ya riqo Rafi 'a ,
Sannu kinji Rafi 'a ta Muga bakin "
Harshen ta ta zaro masa tanajin kamar ana hura mata wuta a kai ,
A hankali ya fara hura mata iska a cikin bakin se kuma ya saka bakinsa ya fara tsotsar harshen nata a hankali .
Se da ya d'an jima a haka kafin ya sake mata bakin yace "
Kin d'an ji sauqi?
Kai ta d'aga masa alamar eh tana share hawaye da bayan hannun ta.
Sosai ya rungumeta a jikinsa yana sauqe numfashi ,
Sannu kinji Rafi 'a ta kiyi haquri dan Allah taho muje restaurant muci wani abincin "
Yayi maganar yana jan hannunta suka fice daga parlorn.
umai ma kam daskarewa tayi a gurin ta kasa koda jan numfashi me kyau ,
Hawaye ne suka fara ambaliya akan fuskar ta "
Da gudu ta shiga d'aki ta d'auko makullin motar ta ta fizgi motar a guje ta nufi gidan Momi ,
Tana isa ta fad'a a jikin Momi tana kuka ta bata labarin qarya da gaskiya '
Basu bata lokaci ba suka wuce gurin boka obina ,,
Cikin sa a boka yace musu bata jima da samun tsarki ba saboda haka yanzu magani ze iya tasiri a kanta ,
Yanzu me kikeso ayi mata?
So nakeyi a hanasa mu amalar aure da ita kullum jini ya dinga binta a qarshe har ya gaji ya kore ta.
Wani ruwa ya bata a kwalba yace ta tabbatar ta sakawa Rafi 'a a abinci ko a abun sha "
Inde tasha komin qan qantarsa to buqata ta biya .
Haka kuwa akayi tana dawowa gida ta bud'e preach d'in Rafi 'a ta d'auko wani lemo da ta tabbatar Muazzam baya sha kwata kwata ,
Ta ja ruwan maganin a Sirinji ta d'ura a ciki ta meyar ta ajiye .
Su Muazzam basu dawoba seda aka idar da sallar' magrib ,,
Domin seda suka d'an yi yawo sosai kafin su dawo '
Rafi 'a ta gaji sosai gashi ta dawo tanajin qishirwa saboda haka ta bud'e preach d'in ta d'auko lemon ta bud'e Tanajin ishi sosai saboda haka ta kafa kai seda ta shanye tass ta yasar da robar.