Chapter 12
BY
FATIMA USMAN
SHA LELEN TERAWA.......
Seda tayi sallar' magrib da insha sannan tayi wanka tayi shirin kwanciya ,
Kusan qarfe sha biyu da wani abu Rafi 'a taji kamar tanajin fitsari ta tashi ta shiga toilet ,
Amma abunda ta gani ya bata mamaki '
Jini kuma?
Tayiwa kanta tambayar da mamaki domin tasan kwananta uku kenan da samun tsarki ,
Seda ta qara shiryawa tsaf sannan ta kwanta Fata d'aya takeyi shine jinin ya tsaya nan da kwana biyu Domin bataso Muazzam ya dawo d'akin ta ba tare da ya tsaya ba "
Abun kamar wasa jini yaqi tsaya wa har yau Muazzam ze dawo d'akin ta.
Babban abunda yake qara bawa Rafi 'a tsoro shine Memakon jinin ya ragu kullum qara yawa yake ga qarni ga yauqi ga baqi Gashi yana zuwa da guda guda kamar wacce ta aihu ko tayi 'bari .
Rafi 'a na tsaye a gaban madubi sanye da riga da wando ,
Rigar bata qarasa cibiyar ta ba wandon ma be ko qarasa guiwar ta ba Kanta babu d'an kwali Tasha manyan ibira a wannan lallausan gashin nata Tayi wani bala in kyau se wani siririn qamshi take .
Muazzam ya shigo se da yayi wata lallausar ajiyar zuciya sannan ya qaraso ya rungumeta ta baya ,,,
I Miss you so much Rafi 'a ta.....
Wani duka qirjin Rafi 'a yayi da qarfi itakam batasan me ma zatayi ba ,
Umhm Kawai tace ta d'an tureshi ta hau gado ta kwanta.
Dan Allah Barrister ka kyale ni yau banajin dad'i '
Kin ma isa ? Seda kika gama tsokanoni Sannan ki cemin bakya jin dad'i .
Muazzam ya fad'a yana qoqarin had'a ta da jikinsa ,,
Ganin iya gaskiyar sa yake magana ne yasa Rafi 'a fashewa da kuka tace Dan Allah ka kyale ni Barrister wallahi bana sallah yau ..
What?
Ban gane bakya sallah ba "
Ba kwananki uku da samun tsarki ba ?
Eh amma se naga ya dawo wallahi nima bansan dalili ba Ta qarasa maganar tana qara fashewa da kuka .
Shikenan.......
Calm down Rafi 'a ta Ya isa ki dena kukan haka kinji dama ya saba yiwa mata haka kada ki damu kin ji .
Toh ,,
Ha'bar ta ya d'ago yana kallon cikin idanunta cike da qauna Ya sakar mata mur mushi yana fad'in ,,
Toh ki saki fuskar mana tunda ba ni nayimiki lefin ba ai seki dena fushin koh .
Batasan sanda tayi dariya ba '
Yauwa Rafi 'a ta na fiso kullum na ganki a haka banason ganin damuwar ki Ki dena saka damuwa a ranki sosai saboda banaso damuwa ta cutarmin da ke .
Toh zan dena '
Yauwa Rafi 'a ta kinyi alqawari? D'aga masa kai tayi alamar eh ,
To kiss me"
seda ta d'an rufe fuskarta sannan tayimasa wani passionate kiss me zafi .
mur mushi yayi ya shafa kanta '
Toh kwata na lullu'be ki koh .....
Toh ,,,
Kwanciya tayi ya janyota ya rungumeta sosai yana shafa bayanta a hankali har tayi bacci .
Yanajin yarinyar sosai a cikin ransa ,
A yanzu ji yake duk duniya bashida wani abu me muhimmanci sama da ita "
Wasa gaske an shafe wata guda babu alamar tsayawar jinin '
Qarya kam har Rafi 'a ta rasa wace iri zatayiwa Muazzam ,,
Har bata sha awan kwanan ta ya zagayo domin kullum da zarar ya dawo d'akin ta ya zame mata dole tayimasa qaryar rashin lafiya .
Gaba d'aya Muazzam ya kasa ganewa matan sa "
Kullum Rafi 'a a cikin cemasa batada lafiya take ,
umai ma kuwa dama tunda ya qara aure bata shiga harkar sa ,
Duk ya rasa abunda yake masa dad'i.....
Rafi 'a na kwance a kan gadon ta tana kuka,,
Saurin share hawayen ta tayi saboda jin motsin Muazzam yana shigowa .
Bakin gadon ya samu ya zauna '
Rafi 'a ina buqatar ki bani hakki na yanzun nan "
Dammm........ Dammm..,.....
Qirjin Rafi 'a ya bada wani sauti da qarfi .
Barrister dan Allah kayi haquri kasan ina fama da zazza'bin dare kullum ka bari sena qara samun sauqi .
Ba zazza'bi ba koma menene wallahi yaukam sekin bani hakki na kokuma ki fad'amin dalilin da yasa kike gudu na '
Haba Rafi 'a kada ki mayar da ni mahaukaci mana ,,
Ko saboda kinga ina biye miki kin d'auka bansan me nakeyi bane ? Kullum idan ina d'akin ki bakida lafiya amma idan bana d'akin ki lafiya qalau kike kwana "
To wallahi yau Rafi 'a ko mutuwa zakiyi sena kar'bi hakki na ko da qarfi ne .
Muazzam yayi maganar yana fizgota da qarfi ya had'ata da jikinsa ,
Qoqarin kwacewa ta shiga yi amma ta kasa saboda haka ta gasa masa lafiyayyen cizo me rai a hannu '
Saurin saketa yayi yana duba gurin "
Rafi 'a tayi wani irin mirginowa ta fad'o qasa Ko zafin fad'uwar batajiba ta kwasa a guje ta fad'a toilet ta rufo qofar da key .
Sosai ran Muazzam ya 'baci ......
Wato yarinyar nan annoba ta mayar da ni kenan ,,
Yaushe har na zama abun tsoro haka har ake gudu na kamar wani annoba ?
Sosai idanunsa sukayi ja jijiyoyin kansa suka mimmiqe saboda 'bacin rai .
Dak'yar ya miqe ya nufi d'akin sa yana tallafe qasan cikin sa "
Yayiwa kansa alqawarin baze sake neman Rafi 'a ba inde ba itace ta nemeshi da kanta ba.
Rafi 'a kuwa tana shiga toilet d'in ta sulale qasa tana kuka tana fad'in'
Dan Allah ka yafemin Barrister nasan ina cutar da kai saboda 'boyemaka gaskiya da nayi Amma nasan sanin gaskiyar se yafi cutar da kai fiye da rashin sanin ta,
Kamar yadda kake gudun 'bacin rai na haka nima banason ganin 'bacin ranka "
Inama ace inada damar samar maka da farin ciki a wannan yanayi Da tabbas bazan kasa biya maka buqatar ka ba koda a gadon asibiti nake .
Shikuwa Muazzam yana shiga d'akin sa kai tsaye ya shige toilet ya sakarma kansa ruwa ,,
Ya fito ya kwanta amma ya kasa bacci se juyi yake .
Tun biyar da Rafi 'a ta tashi tayi sallah bata koma bacci ba Domin a yanzu kullum wankan ta take tana sallah tunda ta fahimci jinin ba na al ada bane ,,
Tana idar da sallah ta shiga kitchen ta fara qoqarin had'awa Muazzam abun karyawa '
Tana kammalawa ta shiga tayi wanka tayi kwalliya ta had'e cikin wani leshi fari Anyimasa ado da zare me ruwan gold da qananan stone masu kyalli "
Kayan sunyi mugun yimata Kyau sosai ,
Ta d'auko wani turare me sanyi ta fesa sannan ta nufi d'akin shi Sede cikin rashin sa a ta samu ya jima da fita tun kan bakwai tayi yariga ya fita amma be sanar musu ba .
Sosai Rafi 'a taji babu dad'i domin tunda suke be ta'ba fita ba tare da ya sanar da su ba "
Wayar ta ta ciro seda tayimasa wajen qira goma kafin ya d'aga ,
Seda ta d'anyi ajiyar zuciya sannan tayimasa sallama cikin sassanyar murya '
Lafiya kike kirana da wannan lokacin ?
Ko akwai wani abu da kike buqata ne?
A'a ,,
Dama na kammala break fast ne nazo na tarar bakanan shine nace ko .
Bana buqata ne.......
Muazzam ya fad'a ba tare da yajira ya kammalajin me zata ceba sannan ya kashe wayar sa ,
Seda Rafi 'a ta kusan mintuna biyar tana tsaye a tsakiyar d'akin Muazzam kafin ta fice da gudu .
D'akin ta ta shige ta rufo qofar da qarfi ta fad'a kan gado ta fashe da wani marayan kuka na tausayin kanta "
Batasan kowa ba se Muazzam Shi kad'ai ne take zuwa gurinsa taji dad'i shi ya fara sanar da ita yadda zatayi farin ciki a gidan aure Bayan shi batada wani wanda yake sonta balle ya zauna yayi hira da ita yaji damuwar ta ,,
Muazzam ne kad'ai kwarin guiwar ta idan yayi fushi da ita ya dena shiga harkar ta ina zata saka kanta.
Tabbas na sani kana iya qoqarin ka dan ganin ka farantamin rai Sede gashi ni na gaza baka farin ciki ,
Tabbas kanada hujjar yin fushi da ni sede bani na za'bar wa kaina hakan ba qaddara tace takeda zafi .
Da dare kuwa Rafi 'a tun tana jiran Muazzam ya dawo har bacci ya kamata babu alamar Muazzam ze dawo '
Da sassafe Rafi 'a ta shiga d'aki Muazzam cikin sa a ta tarar da shi ya fito daga wanka ze fara shiryawa ,,
Ina kwana Barrister....
Fitamin a d'aki Rafi 'a Ya fad'a ba tare da ya kalli koda inda take ba .
Barrister dan Allah ka tsaya ka saurareni wallahi ni ,
Rafi 'a nace ki ficemin daga d'aki.....
Ya fad'a cikin tsawa Da gudu Rafi 'a ta fice daga d'akin tana sakin wani kuka me ta'ba zuciya .
Gaba d'aya rayuwa ta yiwa Rafi 'a zafi "
Muazzam baya kulata baya shiga harkar ta baya cin abincin ta baya wal Wala Baya shiga d'akin ta Idan ita taje d'akin sa se ya kore ta ko ya fice yabar mata gidan gaba d'aya .
Gashi ita batasan kowa ba '
Daga d'ayan 'bangaren kuma ga matsin lambar umai ma,,
Abun yayiwa Rafi 'a yawa ta rasa ina zatasa ranta Sati biyu kenan Muazzam be bari koda gaisu ya shiga tsakaninsu ba '
Gashi kuma larurar ta ta jini kullum gaba take qarawa ,,,
Har qarfin ta ya qare domin jininta ya kusa qarewa ,Tana cikin damuwa sosai kullum a kwance take wuni tana kuka"
Tayi fari tass ta kumbura sosai saboda rashin jini .
Daga ta miqe tsaye se hajijiya ta dinga d'ibar ta tana ganin duhu a idonta .
Qarfe goma da wani abu na dare ,,
Muazzam ya dawo gida yana zaune a bakin gadon sa Yanajin kewar Rafi 'a sosai se yanzu yakejin be kyauta mata ba ko kad'an Ya kamata yayimata uzuri koda neman dalilin gujemsa takeyi ai ita qaramar yarinya ce ,,
Hannu yasa ya riqe kansa a fili yake magana '
Tabbas na cutar da Rafi 'a ban kyauta mata ba ko kad'an Yarinyar abun tausayi ce sosai amma na kasa yimata uzuri Na d'auko ta da niyyar temakon rayuwar ta se gashi na zama d'aya daga cikin masu zaluntar ta ,
A baya banason ganin hawayenta koda ta silar wasu ne "
Se gashi a yau ni da kaina nayi sanadin kukan ta Zan iyayin fushi da umai ma na dena kulata domin ita tanada Momi da Daddy ,,
Amma idan na share Rafi gurin waye zataje?
Da sauri ya miqe yana fad'in Sorry Rafi 'a ta ganinan zanzo gareki nariga na saba da ke banason fushinki .
Da sauri ya nufi d'akin Rafi 'a be tarar da ita a ciki ba saboda haka ya zauna a bakin gado yana jiranta "
Ganin jiran yayi yawa ne babu ita babu motsin ta yasa Muazzam miqewa ya tura qofar toilet d'in ta ya shiga'
Rafi 'a ya Gani durqushe harta fara fita daga cikin hayyacinta ,
Ga wani jini guda guda baqi qirin me yauqi yana fita daga jikin ta '
Da sauri yayi kanta ya riqota ,,
Rafi 'a ta........
Ganinan nazo gareki dan Allah ki yafemin na kasa yimiki uzuri ,
Cikin wata wahalalliyar murya Rafi 'a tace Barrister dan Allah ka yafemin ba lefi na bane ka dena fushi dani dan Allah wallahi bansan komai ba .
Bana fushi da ke ko kad'an Rafi 'a meyasa kika 'boyemin baki fad'amin gaskiya ba?
Inda kin fad'amin da bazanyi fushi ba ,
A hankali jinki Rafi 'a ya sake yayi sanyi qalau "
Hannu Muazzam ya kai kusa da hancin ta amma babu alamar numfashi ,
Rafi 'a ta.......
Dan Allah ki tashi Rafi 'a ta kada ki barni wallahi bazan iya rayuwa babu ke ba '
Ki tashi dan Allah bazan sakeyin fushi da ke ba ,,
Wayyo Rafi 'a ta......
Kuka Muazzam yakeyi sosai da hawayensa yana gir giza Rafi 'a amma babu alamar zata tashi '
Da sauri ya d'auketa ya nufi hanyar fita yana kiran sunanta yana kuka hawaye wasu na bin wasu ,,
A parlor suka ci karo da umai ma'
Cikin kissa ta matso ta kai kannu da niyyar ta'ba Rafi 'a tana fad'in ,
Toh fah"
Yaya Muazzam menene kuma naga......
Da qarfi Muazzam ya tureta seda ta fad'i qasa,
Kada ki sake ki ta'ba ta "
Kada kiyi kus kuren ta'bamin mata Ki kyalemin ita kada ki ta'ba ta ,,
a haukace ya nufi qofar ficewa da Rafi 'a da take sandare babu motsi a hannunsa.