Chapter 16
BY
FATIMA USMAN
SHA LELEN TERAWA.......
umai ma da Momi sun koma gurin boka amma bokan yace babu abunda ze iya musu yanzu ,
Kawai tasan yadda zatayi da kirsa da dabara ta hanashi tino Rafi 'a "
Umma na zaune a d'akin ta Faiz yayi sallama ,
Barka da dare umma mun yini lafiya '
Lafiya qalau Faiz zauna mana.
Tayi maganar tana nunamasa gefen gado ,,
Memakon Faiz ya zauna a kan gadon se ya samu guri a qasa ya zauna '
Umma dama nazo ne inaso muyi wata magana......
Toh Faiz , Ina sauraron ka .
Dama akan yarinyar nan shahinas ne nace tunda kinga mun jima tare da ita bamusamu kowa nata ba Ina tunanin batada kowa ne.....
Kuma har ga Allah umma nafarajin ina qaunar ta ,,
Toh shine nace memakon zaman da takeyi haka ba wani nata kuma babu aure Me ze hana idan kun amincemin ke da Granny na nemi auren ta.
Kul kada ka soma wannan maganar Faiz baze yiwuba ko da wasa ,
Yarinyar da bamusan wacece ita ba bamusan asalin ta ba bamusan daga ina ta fito ba Ita kakeson aura?
To wallahi tunda wuri gara ka dena wannan tunanin Kuma koda sunan wasa kada na sake jin furuci irin wannan a bakinka .
Haba umma dan Allah.....
Menene a ciki dan na auri shahinas ?Yarinyar tanada nitsuwa batada wata matsala ,
Wallahi a iya zamanta da mu ya kamata ace inda tanada wani hali na daban musani '
Kai dalla gafara can kayimin shiru.....
Sha Sha Shan yaro kawai wanda besan ciwon kansa ba ,,
Idan na kula alfarmar da mukayimata na riqeta da mukayi ne yasa har ta d'anamaka tarkon soyayya kuma ka afka ,..
Kuma bari na fad'a maka Faiz wallahi inde ina raye wannar yarinyar bazaka ta'ba auren ta ba har abada '
Kuma wallahi daga yau ta gama zama a cikin gidan nan sede ta tattara taje duk inda zataje .
Umma tana gama fad'ar haka ta miqe ta fice ,,
Da sauri Faiz yabi bayanta yana yimata magiya '
Dan girman Allah umma kiyi haquri kada ki kori shahinas a gidan nan ,, Umma idan kikace ta tafi a daren nan ina zata shiga ?Wallahi umma shahinas batada lefi ko kad'an domin bata ta'ba sanin ina qaunar ta ba Dan Allah ki tausaya mata kada ki kore ta kinga tana da qananan yara ina zata shiga da su ?
Ko ta kansa umma bata bi ba ta shige d'akin Rafi 'a wacce ta fara bacci .
Ke munafuka baqar algun guma annamimiya y'ar tallen sharri "
A razane Rafi 'a ta farka saboda yadda umma tayimata magana cikin tsawa ,
Magana umma taci gaba da yi dede lokacin da Faiz ya shigo d'akin "
Baqar macijiya wato saboda mun temake ki mun d'auke ki mun rufa miki asiri bamu bari rayuwar ki ta walaqanta ba ,
Shine kika rasa abunda zaki sakamana da shi se jefa d'an mu a tarkon ki koh?
To wallahi baki isa ba sekin bar gidan nan a yau ba se gobe ba .
Wani irin dirowa Rafi 'a tayi daga kan gadon ta riqe qafafun umma "
Dan girman zatin Allah umma kiyi haquri kada ki koreni daga cikin gidan nan ,
Dan darajar Allah kiji tausayi na.....
Umma duk dunuyar nan bayan ku bansan kowa ba Banda gidan nan babu wani guri da na sani a yanzu Umma idan kika koreni ya zanyi? Ina zan saka Hisham da Naznin da ni kaina ma? Wallahi umma bansan komai ba .
Duk yadda Rafi 'a taso fahimtar da umma taqi fahimta tace sede ta bar gidan '
Ganin umma taqi sauraransu ne yasa Faiz fita da sauri ya nufi d'akin Granny ,,
Granny dan Allah kizo kisaka baki kiyiwa umma magana kada ta kori shahinas a cikin gidan nan '
Wallahi idan ta kore ta batada inda zata shiga a duniyar nan Amma umma tace wai sede ta bar gidan nan akan lefin da ba nata ba.
Lefi Kuma?
Akan me kake magana ne Faizu ?
Meye abunda shahinas d'in tayi da Zainab takeso ta koreta ?
Batayi komai ba Granny zan fad'a miki komai daga baya Amma dan girman Allah mu fara zuwa kiyiwa umma magana ta kyale shahinas '
Tare Granny da Faiz suka shigo d'akin dede lokacin da Rafi 'a ke shirin ficewa tana kuka ,,
Ah ah......
Meyake faruwa ne Zainab? Me tayimiki da kikeson korar ta da wannan lokacin ?Bakya ganin tanada jego ne ' Ina kikeso ta shiga ita da yaran idan tabar gidan nan a cikin daren nan ?
Da sauri umma ta juyo ta kalli Granny "
Kibari kawai mama Wallahi yau se yarinyar nan tabar gidan nan ,
Daga temako yarinya ta maqalewa Faiz wai har yana cewa ze aure' ta '
Wallahi wannan daga gani bata barshi haka ba domin ko kad'an Faiz baya soyayya "
Y'an mata nawa ya sani be sosu ba se wannar y'ar tsintuwar kuma me y'a y'a ,
Ni wallahi abunda yafi damuna ma yaran nan na Sunnah ne kode kawai ta samesu ne ta wata hanya .
To ban amince ki koreta ba Zainab "
Menene a ciki dan Faizu yace yana sonta?Ai naga ba lefinta bane tunda ba ita tace tana sonshi ba sannan kuma ba tursasa shi tayi yasota ba .
Amma Mama.....
Ya isa haka Zainab .....
Nace babu inda zataje Kuma na gama magana Zataci gaba da zama tare da mu har se Allah yasa ta samu danginta Idan Kuma gadararki itace mijinkine ya mutu yabar gidan To yakamata ki tina cewar d'a na ne ya mutu yabar gidan' saboda haka ina tunanin ko babu komai inada hakki a cikin gidan ,
Saboda haka inada damar yanke ko wani irin hukunci .
Wani harara umma ta zabgawa Faiz wanda a fakaice da Granny take ta fice daga d'akin da sauri ,,
Wallahi Faiz zezo ya sameni sena sa'ba masa sosai Wai har ni zekai qara gurin mama saboda wannar yarinyar ?
Bari yazo ya sameni wallahi yau se yaga fushi na Kuma ko mata sun qare a duniya wallahi baze aure ta ba.
Bazeyiwu ba Momi wallahi a yau zan nemawa kaina mafita base gobe ba "
Dole ne Muazzam ya mutu a yau Bazan iya ci gaba da jira ba har zuwa yaushe kukeso na jira ne?
Babu amfanin barinsa a raye tunda an tabbatar cewa umai ma bazata ta'ba aihuwa ba "
Saboda haka ni bazan iya jiran jira har se wacce zata haifamasa magaji tazo ba Dole nasan abunyi a yau base gobe ba .
Cewar yazid wanda yaketa fad'a kamar ze ari baki ,,
Se wani huci yake kamar kumrci .......
Yazid kai yaro ne bazaka gane ba Kabari ni da Dadyn ku zamusan yadda zamuyi da shi da kanmu Kasan gaggawa aikin shed'an ne a garin gaggawa se a 'bata goma d'aya bata gyaru ba Saboda haka kabari mubi komai a hankali .
Gaskiya na gaji Momi bazan iya ci gaba da jira ba ,,
Kullum cewa kikeyi za abi komai a hankali' kuma babu abunda kukeyi a kai ,
Tunda kun kasa yimasa komai to wallahi zan kawo qarshen labarinsa a yau d'innan babu wanda ya isa ya dakatar da ni .
Yana gama fad'ar haka ya juya ya fice da sauri Momi tana kiransa amma ko waigowa beyi ba '
Rayuwa tayiwa Rafi 'a zafi a gidan su Faiz ,,
Kullum umma tana cikin zagi dayimata habaici ,
Bata amsa gaisuwar ta bata shiga harkar yaranta ga zagi da cin mutuncinci na safe daban na rana daban "
Ko parlor bata iya fitowa saboda umma haka take ini a d'aki tana kuka ,
Tana fatan ta dawo cikin hayyacinta wataqila tasamu inda za a kula da ita "
Koda ta fito bata wuce d'akin Granny domin ita kad'ai ce take kwantar mata da hankali ,
Faiz yanason zuwa gurinta kodan ya d'ebemata kewa amma umma ta hanashi Duk ranar da taga yayi koda gaisuwa ne da Rafi 'a to a ranar ko gaisuwarsa bata amsawa ,
Dede da abinci umma ta dena bata a gidan sede idan aka kaiwa Granny nata ta d'auka ta bata Wani lokacin idan Faiz ya sayomata abu sede ya 'buya ya jefamata ta window domin kar umma tagansa Yasha rufe kansa a d'aki yayi kuka saboda tausayin Rafi 'a da yaran ta '
Musamman yaran sun riga sun shaqu da shi sosai ,
Da zarar ya shigo gidan zakaga sunata fara a sunayimasa wasa Idan umma tana gurin baya iya kulasu domin hatta su ta hanasa shiga harkar su .
Wataran idan yaran sukayimasa wasa be kulasuba se su fashe da kuka ,
Wataran yana kula hatta Rafi 'a tana kuka idan ya share yaran to amma babu yadda zeyi Umma tariga ta kafamasa doka akan ita da yaran kuma tace idan ya karya dokar seta tsine masa .
Idan ya zauna yana tunanin rayuwar Rafi 'a baya sanin sanda hawaye masu ciwo suke gangaromasa ,,
Wace irin qaddara ce haka?
Kenan idan bata samu dangin ta ba a haka zataci gaba da rayuwa '
Ko a mafarki be ta'ba tunanin umma zata iya aikata abunda take aikatawa ba ,,
Yanada tabbacin inda y'ar ta akeyiwa da tabbas bazataso hakan ba .
Muazzam yana cikin damuwa sosai domin a yanzu bayaganin yaran koda yazo ,
Duk sanda yaga fitowar Faiz daga gidan seyaji dad'i domin yana tunanin ze ga yaran Sede yana matiqar jin babu dad'i idan yaga ba yaran .
Kullum tambayar kansa yake ,
Shin meye dalilin da yasa Faiz ya dena fitowa da yaran ? Kode ya gane inazuwa ne kawai domin na gansu ?
Sede abunda Muazzam be saniba shine ,
Ko sau d'aya Faiz be ta'ba kula da tsayuwar sa a gurin ba .
Ranar jumma a da misalin qarfe 2 na dare jikin Granny yayi tsanani "
A cikin daren faiz da umma suka kaita asibiti ,
Likitoti sunyi iyakar qoqarinsu dan ganin sun ceto rayuwar granny amma abun yaci tura domin zuciyar ta ta kumbura sosai saboda wani tsiro da yake cikin ta "
Tun cikin daren aketa faman abu d'aya amma ina ....
Jikin Granny babu sauqi ,
Da asuba likita ya fito ya tarar da umma da Faiz tsaye a bakin I . C . U .
Da sauri Faiz ya taso.....
Dr. Ya jikin kaka ta?
Ta samu sauqi kuwa kode ta samu tayi bacci ne ?
Dan Allah zamu iya shiga mu dubata ?Bazamuyi hayaniyaba ganinta kawai zamuyi bazamu hanata bacci ba .
A rikice Faiz yake sosai domin duk duniya baida abokiya kamar Granny '
Yayi mugun shaquwa da ita domin a hannunta ya tashi yana mugun qaunarata fiye da komai a cikin rayuwar sa .
Calm down aboki na ka nitsu dan Allah ,
Haba kakoyi jarumta mana kai fa namiji ne yakamata qarfin halinka ya zarce haka Hannu Faiz yasa ya share hawayen sa sannan yace ,
Toh likita na nitsu dan Allah ka fad'amin ya jikin kaka ta ?
Seda likitan ya d'an ja numfashi sannan ya d'an bubbugi kafad'ar Faiz ,,,
Sorry aboki na sede Allah ya baku haquri domin wanda ya fiku buqatar ta ya kar'bi abunsa '
Munyi iya qoqarin mu wajen ganin mun ceto rayuwar ta amma.......
Be qarasa ba Faiz ya d'auke sa da wani wawan mari ya sake d'aukesa da mari a d'ayan gefen ,
Ya cakwameshi ya had'asa da jikin gini "
Are you mad ?
Kai wani irin daqiqin likita ne bakada hankali ne?
Qarya kikeyi Granny bazata mutu yanzu ba domin ban shirya kar'bar rashinta nan kusa ba ,
Dama kasan baka kware akan aikinka ba meyasa kasaka wannan uniform d'in ?
Wannar farar rigar bata dace da kai
ba batada amfani a gurinka kawai ka cireta ka yar ka koma gida ka d'aura d'an kwali kafara girki ,
Dak'yar aka kwace likitan daga hannunsa idanunsa sun fiffito saboda cakwamar da Faiz yayimasa "
Da gudu ya shige d'akin ya yaye zanin da aka rufe Granny da shi ,
A kwance ya ganta kamar ka kira sunanta ta amsa sede babu motsi Harta fara sandarewa.....
Wasu zafafan hawaye suka gangaro daga idanun Faiz ,,
Granny dan girman Allah ki tashi kada ki barni ban shirya rasaki ba wallahi Ba haka mukayi da ke ba kince bazaki tafi kibarni ba har sekinga mata ta To menene kuma na canza shawara cikin sauri haka ?
Bazan iya jure rasakiba kin sani amma me yasa kika tafi yanzu ?
Dan Allah ki tashi mu tafi gida Shahinas Hisham Naznin duk suna jiran komawarki gida Dan Allah ki tashi ko dan su kinsan basuda gata sama da ke a halin yanzu ,,
Ya kikeso nayi ne da rayuwa ta Granny ?
Kinga na manta ban fad'a miki ba yanzu nasamu wacce zuciya ta takeso,
Zanyi aure kin fad'amin cewar kece zaki fara bud'ewa matata fuska Dan Allah ki tashi ki cika wannan alqawarin wallahi zanyi auren nan kusa idan kika tashi .
Umma da ke tsaye a jikin qofa tana rusar kuka ta qaraso cikin d'akin dak'yar ta dafa Faiz ,,
Haba Faiz......
Kayi haquri mana kaifa musulmi ne kada ka manta tauhidinka mana Tabbas kanason Granny kowa ya sani sede amma sonda kakeyimata baze hanata tafiya ba idan lokacinta yayi domin mutuwa bata barin wani dan wani .
Dak'yar Faiz ya d'ago rinannun idanunsa ya kalli umma ,
Ta rasu umma ta mutu Shikenan yanzu Granny ta tafi ta barni na har abada kenan?
Inason ta fa umma tafi kowani abu muhimmanci a cikin rayuwa ta amma lokaci d'aya ta tafi ta barni ,
Taya zan iya jure hakan cikin sauqi umma ta yaya ?
Faiz ya fad'a yana rungume umma da qarfi had'e da fashewa da wani irin kuka me qarfi ,,,
Haka umma tayita faman rarrashin Faiz tana tinatar dashi kada ya rasa imanin sa .
Rafi 'a tayi Kuka kamar ranta ze fita domin itama ta saba da Granny sosai'
Ko da akakai Granny makwancin ta haka Faiz ya kwanta akan kabarin ta yana kuka dak'yar aka janyoshi aka sakashi a mota suka dawo gida .
Bayan rasuwar Granny da sati biyu umma ta shigo ta samu Rafi 'a a zaune tana shayar da Naznin '
Sannu da shigowa umma ....
Umma bata amsa ba ta fara magana "
To shahinas ina tunanin daga yau zamanki a gidan nan ya qare Dama kinsan albarkacin mama kikeci to yanzu wa adi ya cika babu mama saboda haka lokaci yayi da ya kamata kema ki kama gabanki bazaki ci gaba da zama a cikin gidan nan ba .
Dan girman Allah kiyi haquri ki rufamin asiri umma "
Idan kika koreni a gidan nan ina zan shiga ?
Ki shiga duk inda kikeso a duniya amma wallahi banda gidan nan .
Babu yadda Rafi 'a batayiba amma ko kad'an umma taqi saurarar ta ,
Haka ta d'au Hisham ta goyashi '
Ta saka hijabi ta sa'ba Naznin a kafad'ar ta ta fice daga gidan tana zubar da hawaye ,,
Momi na zaune a parlor wayar ta ta fara amsa kuwa '
Takai hannu ta d'auko wayar Private number ta gani ta kara wayar a kunnen ta tare da yin sallama .
Kece mahaifiyar yazid ?
Eh nice me yake faruwa ?
Dama an kawo yazid asibitinmu ne yayi hatsari kuma rai yayi halinsa shiyasa muke neman dangin sa '
Innalillahi wa inna ilaihir raji 'un .........
A wani asibiti ne?
Asibitin sunshine hospital ,,
Da gudu Momi ta fito ta nufi asibitin aka shigar da ita inda gawar yazid take ,
Dak'yar Momi ta iya ganesa saboda yadda yayi kaca kaca Babu inda yake tare da wani a jikinsa .....
Ga hanjinsa a gefe hannunsa a gefe qafafunsa a gefe,
Ya rabe biyu daga cikin sa kamar wanda aka rabashi da adda Ga cinyar sa tayi wani irin dandaqewa kamar an markad 'a ta dak'yar aka saka cebur aka kankaro wasu sassan jikin nasa akan titi domin a garin yana sauri zeje kashe Muazzam ne ya shiga qar qashin babbar mota ta takeshi '
Wani irin jiri ne ya fara d'ibar Momi ta fara ganin duhu baqi qirin a idanun ta ,
Innalillahi wa inna ilaihir raji 'un .