UQUBA

Chapter 17

by @115427907984105099906

‎BY
‎
‎FATIMA USMAN 
‎SHA LELEN TERAWA.......
‎
‎
‎
‎A gigice Momi ta shiga ja da baya tana salati ,
‎Domin bata iya gane kokami kafin kace me Momi ta fita daga hayyacinta "
‎Take ta sulale a gurin a sume.
‎
‎Faiz ya shigo gidan amma beji motsin Hisham da Naznin ba '
‎Ganin umma bata parlor ne yasa ya shiga d'akin Rafi 'a amma be ganta ba Babu irin kalar neman da beyimata ba amma babu alamar tana cikin gidan ..
‎
‎Hakan ne ya tilastashi nufo d'akin umma a hanzarce .
‎Faiz ka dawo ?
‎Umma ina shahinas ? Tambayar da Faiz ya jefawa umma kenan "
‎
‎Sheqe qe take kallonsa kafin tace ,
‎Ta koma inda ta fito mana.....
‎Wani irin duka qirjinsa yayi saboda yadda yaji maganar umma kamar sauqar aradu a kunnensa "
‎
‎Besan sanda yayi baya da sauri yayi saurin durqushewaba domin qafafunsa qoqari suke su kasa d'aukar sa .
‎Ta koma inda ta fito ? Ta koma inda ta fito fa kikace umma......
‎
‎Yanzu ashe seda kika kori yarinyar nan daga cikin gidan nan?
‎Haba umma ban ta'ba sanin rashin tausayinki yakai haka ba.
‎
‎A qalla de ko baki tausayamata a matsayinta na qaramar yarinya kuma mace me rauni ba ,
‎Ya kamata ki tausaya mata a matsayinta na uwa domin kema uwa ce kin haifa kuma kinsan zafin abun .
‎
‎Haba Faiz......
‎Yanzu saboda na kori wannar yarinyar daga gidan nan ne kake fad'amin haka?Bawai na kore ta ne domin bana qaunar ta ba kawai na koreta ne saboda banaso ta lalata maka rayuwa .
‎
‎Seda Faiz ya had'iye wani abu me d'aci sannan yace '
‎Wow gaskiya kinyi abun a yaba miki kuma kin cancanci azo a kalleki Domin kin aikata abunda iya mutane masu matiqar son kansune kawai zasuce kinada gaskiya akai '
‎
‎Saboda gudun kada rayuwar d'anki guda d'aya ta lalace kin lalata rayuwar mutum uku wad'an da basujiba basu gani ba basusan komai ba ,,
‎
‎Mu d'auka ma a matsayin tayimiki lefi '
‎To sukuma qananan yaran me sukayimiki ?
‎
‎Da kika koreta ina zata shiga da jarirai ?
‎Waye ze kar'beta da hannu bibbiyu?Hannu na gari zata fad'a ko mugun hannu?
‎Ya rayuwar wad'an nan yaran zata kasance babu muhalli ?
‎
‎Tabbas kin aikata abunda kikejin shine dede umma amma inaso ki tina wani abu ,
‎Kawai dan ta rasa danginta da tunaninta hakan baya nufin ita ba mutum bace "
‎Itama mutum ce kamar kowa wacce jini yake gudana a jikinta Sannan Kuma itama tanada zuciya zata iya jin ciwo idan aka cutar da ita Tunaninta kawai ta rasa amma bata rasa hankalinta ba Kuma bata rasa darajar da Allah yayimata na d'an adam ba .
‎
‎Yana kaiwa nan ya juya da sauri ze fice sekuma ya dakata saboda jin umma ta kira sunan sa ,,
‎Faiz tabbas nayi kus kure kaje ka nemota ta dawo taci gaba da zama da mu Koda aurenta kakesonyi a yanzu na amince maka wallahi dan Allah ka nemota kasa ta dawo .
‎
‎Seda Faiz ya d'anyi mur mushin jin dad'i sannan ya fita ,
‎Yaje duk inda yake sakaran ze sameta amma be sameta ba Babu inda be je ba yana neman ta haka ya ini yana bulayi amma ko qurar ta be gani ba ,
‎
‎Har kusan sha d'aya da rabi na dare yana yawon nemanta amma ko me kama da ita babu '
‎
‎Seda ya zauna a cikin motarsa yayi kuka me isar sa sannan ya kad'a kan motar ya nufi gida.
‎
‎Rafi 'a kuwa tana fitowa daga gidan su Faiz tafiya kawai takeyi ba tare da sanin inda zataje ba ,,
‎Tana tafiya tana sharar kwalla Tun tana tafiyar da qarfin ta har ta fara tafiya dak'yar '
‎
‎Ga yunwa ga ishi ga gajiya ga Hisham a bayan ta ga Naznin riqe a kafad'ar ta ,,
‎Ga yaran se kuka suke saboda ishi idan ta sakamusu nono a baki daga sun fara sha se su sake domin ko ruwan nonon ya qafe babu shi .
‎
‎Duk inda taje tana neman a temaketa da abunda zataci ko da ruwan da zata bawa yaran ta se a koreta kowa seyace duniya babu yadda yanzu zaka temaki mutum shikuma ya cutar da kai "
‎
‎Gefen wani bola ta samu ta zauna ta qurawa Naznin Ido Wacce tuni ta riga ta fice a hayyacin ta saboda yunwa da qishirwa  Ganin yarinyar tana neman mutuwa ne yasa ta sake sa'ba ta a kafad'a taci gaba da tafiya ,,
‎
‎Tafiya kawai takeyi amma ko inda take takawa bata gani.....
‎Bata saniba ta hau tsakiyar titi mutane sunayimata magana amma ina Ko kad'an bata jinsu har seda wata baqar mota da ta taho tayi nasarar kwasheta ,
‎
‎Wata kyakkyawar mata ce da wani kyakkyawan mutumi suka fito daga cikin motar,,
‎A rikice suka d'auki Rafi 'a da yaran suka sakasu a mota suka nufi asibiti  .
‎
‎Jiki babu kwari Faiz ya shiga gida.....
‎A parlor ya tarar da umma tana zaune "
‎Tana ganinsa ta miqe da sauri tana fad'in ,
‎
‎Ina shahinas d'in ?
‎Ina fatan de kasamota hankalina ya tashi sosai tun d'azu na kasa nitsuwa '
‎Wallahi idan rayuwar yarinyar nan da yaranta ya salwanta bazan ta'ba yafewa kaina ba ,,
‎
‎Tabbas inada son kaina da yawa .
‎A'a umma ......
‎Ki dena d'aurawa kanki lefin insha Allah za a sameta Babu abunda ze same ta .
‎
‎To Allah yasa "
‎Amin umma se da safe umma,To mu kwana lafiya .
‎
‎Kai tsaye asibiti mafi kusa suka wuce donin Rafi 'a tasamu mugun rauni sosai har seda jini ya bunne mata fuska '
‎
‎Suna zuwa aka shiga emergency room da Rafi 'a ,,
‎Suka bawa wani nurse yaran domin suma a bincika lafiyar su Yaran basu farka ba se kusan qarfe takwas da wani abu na dare  yaran sun farka sede da alamu sunajin yunwa sosai "
‎
‎Wata nurse tazo ta sanarwa matar yaran sun farka amma da alamu sunajin yunwa sosai gashi mahaifiyar su bata farka ba .
‎
‎Rafan dubu dubu matar ta ciro ta miqawa nurse d'in tace a sayi madara a basu susha se ayimusu wanka ,
‎Haka kuwa akayi nurse d'in ta basu madara sukasha se da cikinsu ya d'auka sannan suka fara wasa .
‎
‎Yaran sunada shiga rai sosai cikin d'an qan qanin lokaci sun saba da nurse d'in "
‎
‎Matar tana zaune mijin nata ya shigo yana magana a waya '
‎An samu matsala bazamu samu dawowa Gombe a yau ba Saboda haka bazan iya halartar meeting d'in da zamu gabatar qarfe bakwai ba ,,
‎
‎Ya kamata a d'aga meeting d'in zuwa yamma kokuma safiyar jibi idan Allah ya nuna mana se muga abunda Allah zeyi .
‎
‎Be jima da shigowa ba ya yanke wayar ya dubi matar "
‎Ya kamata mu tafi hotel mu kwana idan yaso da safe se mu dawo mu duba yanayin jikin nata koh?
‎
‎Eh Alhj ,
‎Amma yaran nata kuma ya zamuyi da su?Idan babu matsala se mu tafi dasu gaba d'aya tunda babu wani Wanda yasanta anan koh '
‎
‎Babu matsala to mu tafi da su d'in kawai ,,
‎Suna tsaka da maganar se ga nurse d'in ta shigo d'auke da yaran Seda suka gaisa ta miqawa matar Naznin ta kar'beta tana yimata wasa "
‎
‎Wani irin sauti qirjin ta ya bada da qarfin gaske ta shiga kallon Naznin tana kallon mijin nata ,
‎Wani gumi ya shiga karyo mata tana jujjuya yarinyar .
‎
‎Shima mutumin kallon yarinyar yakeyi cike da mamakin irin mugun kamar da yaga sunayi kamar yayi kaki ya tofa,,
‎
‎Matar bata sake razana ba seda yarinyar tayi mur mushi se taga kamar photon mijinta aka d'auka '
‎Dak'yar ta iya saurin riqe yarinyar da take shirin fad'uwa daga hannun ta saboda mamaki da al ajabin kamar ta da mijin ta,
‎
‎har nurse d'in ta juya zata fita matar tayi saurin cewa "
‎Dan Allah yarinya d'an zo mana ......
‎Nurse d'in ta dawo ta tsaya matar tace ,
‎
‎Idan babu damuwa dan Allah munaso muga marar lafiyar tamu kafin mu wuce. 
‎A'a hajiya gaskiya bazeyiwu ba yanzu tana d'akin hutu ne kuma kunga har yanzu bata far fad'o ba Ba a buqatar hayaniya a cikin d'akin domin marasa lafiyan su samu hutu sosai .
‎
‎Dan Allah yarinya ki temaka mana muganta ko na minti biyu ne Bazamuyi hayaniyaba kawai munada buqatar ganinta ne,
‎
‎Photon ta mukeson d'auka zamu turawa wani marar lafiya ya gani dan ya samu nitsuwa '
‎Tunda akace tayi hatsari yaketa damuwa sun shaqu ne sosai Idan bega photon ta ba baze iya samun nitsuwa ba kuma baze yadda tana raye ba .
‎
‎Seda nurse d'in ta d'an yi shiru kamar me tina wani abu sannan tace  '
‎To ba damuwa dan kunce akwai larura ne amma gaskiya kada ku jima idan kuka shiga Hakan ze iya zamamin matsala.
‎
‎To yarinya mun gode sosai Allah yayi albarka ya jiqan mahai fa,
‎Ameen Ameen babu komai .
‎
‎Suna shiga d'akin gabansu yayi wani irin fad'uwa a tare '
‎Seda matar taji kamar zata fasa qarasawa sede ta kwad'aitu da son ganin mahaifiyar yaran .
‎
‎Cak numfashin matar ya tsaya da tayi Ido hud'u da Rafi 'a dake baccin wahala '
‎Kamar mijintane yake bacci domin hatta yatsun qafar Rafi 'a da na hannunta irin nasa ne Hatta yadda take fitar da numfashi kamar mijine yake numfashi'
‎
‎Shi kansa abun yayi matiqar basa mamaki domin inda Rafi 'a namiji ne babu makawa duk wanda ya ganta zece shine .
‎
‎Faiz na kwance a kan gadon sa ya kasa bacci se juyi yake '
‎Yanajin wata azababbiyar soyayyar Rafi 'a a cikin ransa ,,
‎
‎Ko yanzu shahinas tana ina?
‎A ina zata kwana tare da Hisham da Naznin? Ta fad'a hannu na gari ne kokuma akasin haka ta fad'a ?
‎
‎Bayan hannunsa ya saka ya share wasu hawaye masu zafi tare da had'iye wani busasshen yawu me kauri .
‎Ya Allah ka temaki shahinas kasa ta fad'a hannu na gari Kasa duk inda take tana cikin salama babu qunci .
‎
‎Ba iya umai ma da Momi kawai ba har Dadi seda ya rasa hayyacinsa da yaga gawar yazid ,
‎
‎Madadin suyiwa kansu fad'a su gane gaskiya Se suka qara d'aukar karar tsana suka d'aura wa Muazzam domin suna ganin a dalilin sa yazid ya mutu.
‎
‎Shima kansa Muazzam ya gigice sosai da mutuwar yazid yayi kuka kamar ba gobe ,,
‎
‎umai ma da Momi da daddy sun lashi takobin ganin bayan Muazzam ko ta wace hanya. 
‎
‎Da sauri matar ta kai hannu tana shafa jikin Rafi 'a ,
‎Alhj Kaga wannar yarinyar yadda take kama da kai ? Kominku iri d'aya fah babu abunda ba irin nakaba a tare da ita Hatta numfashinku da bugun zuciyarku iri d'aya ne ,
‎
‎Wacece ita kuma daga ina take ?
‎Ko made wacece tabbas kamanninku sunyi yawa .
‎
‎Haba Maryam ki nitsu mana nan fa d'akin marasa lafiya ne ,,
‎Ko kin manta ne an fad'a miki cewar ba ason surutu a cikin nan '
‎
‎Shiru hajiya Maryam tayi sannan a hankali ta saka hannunta a cikin hannun Rafi 'a ,,
‎Da qarfi zuciyar Rafi 'a ta harba har seda ta bud'e idanunta tare da qan qame hannun hajiya Maryam a cikin hannunta .
‎
‎Wayyo Allah kaina........
‎A ina nake ne? Ina yara na? Kubani su zan basu ruwa sunajin qishirwa sosai Dan Allah ku bani yara na suna ina ?
‎
‎Nurse d'in tace ,
‎Ki kwantar da hankalinki yaranki suna lafiya babu abunda ya samesu "
‎
‎A'a 
‎Nide kawai abani yara na kubani su na shayar da su sunajin yunwa ban basu komai ba .
‎
‎Nurse d'in zata qara magana mutumin yayi saurin miqawa Rafi 'a Hisham '
‎Da sauri ta kar'beshi ta shiga basa nono tana hawaye duk da babu wani wadataccen ruwa a cikin nonon ,,
‎Allah sarki Hisham d'ina sannu kaji Kayi haquri na barka da yunwa sosai koh ?
‎
‎Gaba d'aya seda jikinsu yayi sanyi da ganin irin qaunar da Rafi 'a takeyiwa yaran ta ,
‎Ta manta duk halin da take ciki damuwar ta kawai ta shayar da y'a y'an ta domin tabasu kariya daga yunwa .
‎
‎Wasu hawaye ne suka kwaranyo daga idanun hajiya Maryam Domin ta tina ciwon da take ta d'awainiyar sa a zuciyar ta Tsawon shekaru sha takwas kenan har yanzu ta kasa samun maganin wannan ciwon '
‎
‎Hannu ta kai ta shafa kan Rafi 'a tana mur mushi tare da share hawayen dake gudu akan fuskar ta ,,
‎A tare zuciyoyinsu suka bada wani irin sauti lokaci guda '
‎
‎Da sauri Rafi 'a ta d'aga Ido ta kalli hajiya Maryam tare da sanya hannu ta riqe hannun ta "
‎Tanajin wani abu nayimata yawo a zuciya .
‎Batasan dalili ba se taji har cikin ranta ta aminta da matar sosai takejin qaunar matar tana ratsa ta. '
‎
‎Daga 'bangaren hajiya Maryam ma haka abun yake ,,
‎Jitake qaunar Rafi 'a tana tsirga mata tun daga tsakiyar kanta .
‎Wani irin ajiyar zuciya suka sauqe a tare hajiya Maryam tayi mur mushi ,
‎
‎Yarinya ya qarfin jiki?
‎Alhamdulillah.......
‎Rafi 'a ta fad'a da sassanyar muryar ta wacce batada bam banci da na matar Sede har lokacin Rafi 'a bata d'ago ta kalli mutumin da yake tsaye a gefen ta ba kuma bataji zata iya d'agowa ta kalleshi ba ,
‎
‎Domin haka kawai taji yayimata matiqar kwar jini,,
‎Se takejin bazata iya had'a ido da shi ba.
‎Hajiya dan Allah idan babu damuwa zaku iya tafiya An riga an hana shigowa nan saboda d'akin marasa lafiya ne ,
‎
‎Kuma ai dama kafin ku shigo seda kukayi alqawari bazaku jima ba "
‎Domin wallahi hajiya idan akasan na bari kun shigo zan iya rasa aiki na .
‎
‎Hajiya Maryam ji tayi kamar tace bazata tafi ba amma batada yadda zatayi ,,
‎Haka suka tafi hotel d'in da mijin ta ya kama musu .
‎Har suka isa hajiya Maryam bata dena zubar da hawaye ba '
‎
‎Me yake faruwa ne Maryam?
‎Na kula tun da muka shiga gurin marar lafiyar nan kike kuka har zuwa yaushe ne zakici gaba da wannan kukan?
‎
‎Har zuwa qarshen rayuwa ta.....
‎Ta fad'a tana sharar kwalla tare da qara qurawa Hisham da Naznin Ido tana kallonsu '
‎
‎Ajiyar zuciya ya sauqe ya zauna a bakin gado sannan yace ,,
‎Haba Maryam....
‎Meyasa kika kasa kar'bar qaddarar ki ne?Shekara sha takwas kenan fa amma har yanzu kin kasa manta wa '
‎
‎Ya kamata zuwa yanzu ace kin dangana kin barwa Allah komai ,,
‎Shine ya za'bi ya jarabcenu ta wannan hanyar Kuma bawai yayi hakan ne dan baya sonmu kokuma ya manta da mu ba '
‎
‎Yayi hakan ne domin ya gwada qarfin imanin mu ,
‎Ni kaina wannan abun yana matiqar damu na sosai To amma ya muka iya da hukuncin qaddara?
‎
‎Dole haka zamu zuba ido domin dukiya bazata ta'ba samar mana da abunda muke muradi ba ,,
‎Tabbas wannan jarrabawa ne daga uban giji Idan mukayi haquri zamuci jarrabawar .
‎
‎Bayan hannunta ta saka ta share hawayenta tana fad'in ,
‎Allah yasa......
‎
‎Rafi 'a kuwa tunda suka tafi take take tunanin "
‎Wace mata ce wannar?
‎
‎Da alama tanada kir ki sosai domin naga kamar bata kyama ta Kuma da alama ba qananan mutane bane amma a haka ta zauna kuma ta kula da ni .
‎
‎Se kuma ta sake fashewa da kuka da ta tina tana samun sauqi sallamar ta za ayi '
‎
‎Itade har ga Allah bataso a sallameta domin idan aka sallameta batasan ina zasu shiga ba ita da yaran ta .
‎
‎Safiyar talata Muazzam na kwance ya rasa me yake yimasa dad'i '
‎Kewar kallon yaran kawai yake domin ya jima yana zuwa baya samun damar ganin su ,,
‎
‎Kamar wanda aka tsikara da kifiya ya tashi ya d'au makullin motar sa ya nufi qofar fita ko wanka be tsaya yi ba '
‎
‎Ina zakaje da wannan safiyar haka?
‎Fad'in umai ma da tashin ta daga bacci Kenan ,,
‎
‎inda naga dama......
‎Muazzam ya bata amsa a taqaice yana murd'a hannun qofar ze fita '
‎
‎Da izinin wa?
‎Kamar daga sama yaji tambayar umai ma Seda ya juyo ya qare mata kallo sannan fuska babu wal Wala yace '
‎Da izini na ko kinada magana ne?
‎
‎A'a "
‎umai ma ta basa amsa a d'an tsorace domin ta kula kamar maganin ya fara sakeshi kwana biyun nan .
‎
‎Amma naga kamar baka karya bane shine nace "
‎Ba buqata zan karya a hanya  .....
‎Muazzam ya fad'a yana ficewa daga parlorn .
‎
‎Na shiga uku ni umai ma maganin bokan nan ya fara dena aiki "
‎Gashi kuma yanzu kullum naje se yace bashida abunda ze iya min Kode sena nemi wani boka ne?
‎
‎Ta fad'a tana zama akan kujerar kusa da ita tare da dafe kanta da qarfi ..
‎
‎Kusan qarfe sha d'aya na rana hajiya Maryam da mijin ta suka shigo cikin asibitin ,
‎Lokacin Rafi 'a tana zaune tana shan tea da wainar kwan da nurse d'in ta kawo mata Domin da dare kafin su tafi seda suka bawa nurse d'in kud'i sukace duk abunda Rafi 'a take buqata a tabbatar an bata shi kafin su zo .
‎
‎'Daga Idon Rafi 'a keda wuya tayi Ido hud'u da babban mutumin da ke shigowa cikin d'akin , 
‎Wani mummunan fad'uwa gaban ta yayi domin tunda take a rayuwa bata ta'ba ganin kama irin nata da na mutumin ba Har suka qaraso idon Rafi 'a na kansa .....
‎
‎sannu yarinya "
‎Yauwa sannu ina kwana
‎Lafiya qalau yaya qalfin jikin naki ?
‎Da sauqi Alhamdulillah....,
‎
‎Wata nurse ce ta shigo tace ,
‎Naga jikin nata da sauqi sosai anjima idan babban likita yazo ze rubuta muku sallama se ku biya kud'in gado ku tafi gida .
‎
‎Da qarfi zuciyar Rafi 'a ta buga itade bataso a sallameta to amma ya zatayi haka dole zata haqura "
‎Idan yaso idan aka sallameta ta d'au Hisham da Naznin ko cikin kango ne su koma su dinga kwana .
‎
‎Take idanunta suka cicciko da hawaye jikinta yayi mugun mutuwa '
‎Ya Allah ka dubeni nasan baka manta da ni ba amma ka yankemin wannan wahalar  ,
‎
‎A tunaninta a zuciyar ta take addu ar sede bata sani ba addu ar ta fito fili ,,
‎
‎Menene sunanki yarinya?
‎Shahinas.....
‎to inane gidan ku kuma ina haifin yaranki yake?
‎
‎Gidan mu ni?
‎Rafi 'a ta fad'a tana nuna kanta da hannu idanunta suka kawo ruwa ,,
‎
‎Eh gidanku yakamata mu kaiki da kanmu mubada haquri domin kada ayimiki fad'a kinga tun safiyar jiya kike nan baki koma gida ba .
‎
‎An koreni daga gidan bamuda gida yanzu Subhanallah......
‎Wani lefi kika aikata haka wanda har yasa aka koreki daga gidan ku?
‎
‎Babu abunda nayi wallahi ,
‎Banyi komai ba fah "
‎Uncle d'ina ne yace yanaso ya aureni shine se mamar uncle d'in nawa ta koreni tace wai nafita nabar musu gidan su Nayita bata haquri nace ta kyaleni bansan ko inaba amma tacemin sede na tafi nabar gidan na tafi duk inda zani .
‎
‎Ta qarasa maganar tana goge hawaye da bayan hannun ta "
‎To meyasa ta kore ki Ba ita ta haifeki bane?
‎
‎Ban saniba amma nide ita kad'ai na sani '
‎Menene sunan babanki?
‎
‎Sunan babana ?
‎Eh ki fad'amin ina sauraronki ,,
‎Uncle Faiz.......
‎Rafi 'a ta fad'a da iyakar gaskiyar ta domin shi take d'auka a matsayin mahaifin ta.
‎
‎Kenan sunan mahaifinki Faiz ?
‎Eh "
‎Masha Allah amma menene asalin sunan ki ?
‎Shahinas......
‎Asalin sunankine nake nufi ,Ban saniba banida shi ,,
‎
‎Toh shikenan ba matsala '
‎Kikace korarki akayi daga gidanku bakida inda zakije koh?
‎Eh........
‎To kada ki damu zaki koma gidanmu da zama ni zan zama mamanki Ina kinaso?Eh ,,,
‎
‎Da yamma aka basu sallama suka d'auko Rafi 'a da y'a y'an ta suka d'auki hanyar Gombe .
‎Tunda suka fara tafiya window kawai Rafi 'a ke kallo ,
‎
‎A dede mashigar garin kaduna suna qoqarin fita daga garin shikuma Muazzam yana sako kan motar sa yana qoqarin shiga "
‎
‎Kamar an cewa Rafi 'a d'aga Idon ki se kuwa ta sauqe su akan rabin fuskar Muazzam ,
‎Wani irin baya tayi da sauri qirjinta na harbawa da qarfi Qoqari take ta tina fuskar amma ta kasa Tana tunanin kamar taso ta ganeshi sede ta rasa waye shi '
‎
‎Da sauri ta kalli fuskar Hisham ta qara d'agowa da niyyar sake kallon Muazzam sede motarsa ta riga tayi nisa .
‎Bata dena leqa motar ba har seda ta 'bacema ganin ta,,,
‎
‎Quri tayiwa Hisham tanason tino wani abu akan mutumin da ta gani yanzu sede kwakwalwar ta taqi bata dama "
‎
‎Jin tana qoqrin fita daga hayyacinta ne yasa tayi saurin maye gurbin wannan tunanin da wani .
‎
‎Muazzam be jima da tsayawa a qofar gidan ba Faiz yazo da niyyar shiga gida '
‎Sallamar da Muazzam yayimasa ne ta dakatar da shi tare da juyowa "
‎
‎Muttsuka idanunsa yayi sannan ya sake waresu yana qarewa Muazzam kallo ,
‎Saboda wata muguwar kamanni da yaga sunayi da Hisham Faiz besan sanda ya saki baki yana kallon Muazzam cikin mamaki ba ,
‎
‎Shima Muazzam da mamaki yake kallonsa saboda irin kallon da yakeyimasa kamar ya sanshi.
‎Shiru ne ya ratsa tsakanin su na wani lokaci se kallon kallo kawai suke babu wanda ya cewa kowa komai a cikin su Domin kowa da abunda yake tunani a cikin ransa '
‎
‎Muazzam ne yayi qoqarin kawo qarshen shirun ta hanyar miqawa Faiz hannu da sallama ,,
‎Seda suka gaisa sannan Muazzam ya fara magana......
‎
‎Sunana Barrister Ibrahim Ibrahim Yuri  "
‎Ni haifaffen garin Gombe ne kuma mazaunin garin Gombe Watarana Shari a ta ta'ba kawoni garin nan se nabiya ta super market zanyi sayayya Na kammala sayayya ta kenan zan tafi senaga shigarka da wani yaro , Nayi mamakin ganin yadda yaron yake matiqar kama da ni kuma har cikin raina naji ina qaunar yaron Se nayita bin bayan ka har se da naga gazo ka shiga gida sannan na juya '
‎
‎Tun daga wannan ranar' se ya zamana kusan kullum ina hanyar zuwa kaduna duk da banida kowa a nan ,,
‎Kawai ina zuwa ne na tsaya a qofar gidan nan domin naga fitowarka da yaron na kalleshi Se daga baya na gano ashe ma yaran su biyu ne ,,
‎
‎Tun daga ranar da na kalli d'ayar se nakeji kamar inada wata dangantaka da su saboda qaunar da nakeyimusu '
‎Inajin inama ace zaka bani koda renon su ne Sede kuma kwatsam se na dena ganinka tare da yaran.
‎
‎Koda nazo haka zan gaji da tsayuwa banga yaran ba nakoma '
‎Wani lokacin kai kanka bana samun damar ganin ka balle su Shiyasa na yanke shawarar zuwa na fad'a maka gaskiya ,
‎
‎Idan ba damuwa mu zama abokai kodan saboda yaran .
‎Cike da mamaki Faiz yace "
‎Wai dama ba kaine mahaifin su ba ?
‎Da qarfi kalmar Faiz ta daki ran Muazzam Seda ya d'an ja wani goron numfashi sannan yace ,,
‎
‎Ban gane me kake nufi ba......
‎Kamar ya dama ba yara na bane ? Tare da su fa na ganka Kuma na fad'amaka ni banida kowa a kaduna me ze kawo yara na kuma nan?
‎Nida mata ta ma bata ta'ba aihuwa ba taya zaka yimin wannar maganar ?
‎
‎Seda Faiz ya d'an numfasa sannan yace '
‎To maganar gaskiya de mahaifiyar yaran nan muma bamu santa ba ,,
‎Ina tafiya ne na tsinceta a hanya cikin wani yanayi da tsohon ciki kuma bata cikin hayyacinta Shine na d'auko ta na kawota gidan mu domin na temaka mata "
‎
‎Take Faiz ya kwashe labarin komai tun daga lokacin da ya tsinci Rafi 'a har zuwa lokacin da umma ta kore ta da kuma irin nadamar da umma takeyi a halin yanzu '
‎Haka kawai Muazzam yakejin kamar yanada wata alaqa me qarfi da mahaifiyar yaran duk da shi be ta'ba ganin ta ba .
‎
‎Haka sukayi musayar number da Muazzam Faiz ya shiga gida cike da mamakin kamanni irin na Muazzam da da Hisham,
‎Abunda yafi basa mamaki kuma wai shine Muazzam baida wata alaqa da su Hisham .
‎
‎Muazzam kuwa haka ya nufi hanyar Gombe cike da kewa da takaicin rashin ganin yaran "
‎
‎Su Rafi 'a suna isa garin Gombe kai tsaye mutumin ya wuce da su anguwar investment '
‎Anguwa ce ta manyan masu kud'i masu ji da kansu ,,
‎Ba iya masu kud'i ba kawai hatta manyan y'an siyasa da manyan y'an kasuwa masu kud'in da ya amsa sunansa kud'i a anguwar suke zuwa suyi gini "
‎
‎Shiru anguwar babu hayaninya se wani lallausan sautin kukan tsun tsaye me dad'i da sautin wata iska me dad'in gaske Wacce take kad'awa ta ko ina a cikin anguwar .....
‎
‎Wani irin k'yalli anguwar takeyi duk da cikin dare ne amma koda allurar kace ta fad'i a gurin zaka sameta saboda hasken gurin .
‎Baki kawai Rafi 'a ta sake tana kallon yadda aka tsara gidajen kamar daga aljannah "
‎
‎Gidajen sunyi mugun tsaruwa kamar gasa akeyi wajen ginasu ,
‎Kai idan kaga wani gidan kamma zakace ba a Nigeria yake ba .
‎
‎A qofar wani qaton katafaren gida mutum yayi hon "
‎Memakon me gadi yazo ya bud'e se gate d'in ya bud'e kansa da kansa Idanun Rafi 'a na sauqa akan qofar gidan se taji ta rena gaba d'aya sauran gidajen da ta gani a anguwar'
‎
‎Tarazo ne shumfud'e a harabar gidan da wasu qananan qoyayen wuta masu haske idan dare tayi ,,
‎
‎Yana danna kan motar a cikin gidan wani irin qamshin furanni masu sanyi da dad'i ya daki hancin Rafi 'a.....
‎A hankali ta d'an lumshe Ido tana shaqar qamshin tanajin wani irin sauqi har cikin ranta ,,
‎
‎Wata lallausar ajiyar zuciya ta sauqe had'e da bud'e idanunta ta zubasu a kan harabar gidan wacce taji shuke shuken floor's da korayen ganyayyaki masu matiqar ban sha awa .
‎
‎Motar na shiga cikin gidan da ita se taji ta manta da duk wata damuwar ta "
‎Tamkar an yayemaka duk wata matsala a cikin ranta .
‎
‎Mur mushi ta saki lokacin da ta hango wani qaton Garden d'auke da wasu shukoki da bishiyu masu kyau ,
‎Se wasu y'an qananan kujeru na shan iska ga wani qaton swimming pool ruwan cikin yayi shud'i gwanin sha awa.....
‎
‎A wani parking Hall me d'auke da motiti sama da ashirin yayi parking '
‎Da kansa ya fito ya bud'e mata qofar motar dede lokacin da hajiya Maryam ta fito daga cikin motar riqe da Naznin a hannunta  ,,
‎
‎Alama yayimata da hannu na ta fito daga cikin motar '
‎Rafi 'a tana taka qafar ta a cikin gidan taji wani irin sanyi Sanyin ba na zazza'bi bane amma batasan dalilin jinsa ba ,,.
‎Take jikinta ya fara 'bari zuciyar ta tana harbawa da sauri "
‎
‎Da sauri ta saka hannu ta danne qirjinta da takejin kamar ze 'balle saboda yadda taji yana bugawa da qarfi ,
‎Take wani irin gumi ya wanketa daga sama har qasa duk kuwa da irin sanyin da takeji .
‎