Chapter 20
BY
FATIMA USMAN
SHA LELEN TERAWA.......
Alhj Hafiz yana dawowa hajiya Maryam ta sameshi ta bashi labarin Rafi 'a ,
Sannan tace idan babu damuwa yayimata izini gobe suje gurin baffa ya basu abunda yace ze bawa Rafi 'a Idan aka dace Rafi 'a zata iya kasancewa y'ar su .
Alhj Hafiz beyi musu ba ya amince gaba d'ayan su zasuje gurin baffa gobe '
Haka kuwa akayi........
Da misalin qarfe takwas na safe suka shirya suka nufi anguwar abganistan ,,
Kai tsaye Rafi 'a ta nufi gidan Amo da su '
Sukayi sallama suka shiga.....
Baffa kad'ai suka tarar kwance a tsakiyar gidan be fita kasuwa ba saboda bayajin dad'i .
Baffa yana ganin Rafi 'a ya washe baki yana fara a ,
Rafi 'atu.......
Ashe zan qara sakaki a idona kafin na mutu ?
Alhamdulillah Allah na gode maka da ka bani damar da zan roqi yafiyar wannar mareninyar taka da na kasa tsaremata maraicinta saboda matata tafi qarfi na .
Ki yafemin dan Allah Rafi 'a "
Jikinsa Rafi 'a ta fad'a ta fashe da kuka tana fad'in'
Babu komai baffa ba lefinka bane kuma nasan ba yin kanka bane kawai anfi qarfin ka ne Dan Allah ka dena neman yafiya ta domin kai mahaifi ne a gare ni .
Naji dad'in ganinki Rafi 'atu.....
Allah ya miki albarka '
Amin amin baffa ina Naja 'atu da Amo ?Jim baffa ya d'anyi sannan yace ,,
Rafi 'atu gara da Allah ya kawo ki kinzo a dede lokacin da ya dace '
Lokacin da Aminatu take kar'bar hukuncin irin abunda ta aikatamiki na zalunci ,,
Nasan duk abunda yake samunta a yanzu duk alhakin kine yake bibiyar ta .
A hanyar ta na biye binyen gidajen bokaye da malamai tayi hatsari Qashin bayan ta ya karye qafarta ta dama ta ru'be aka yanke ta Amma duk da an yanke ciwon yaqi warkewa se wari yake ,,
Naja 'atu da take fifitawa a kanki gudunta tayi tace bazata iya jinyar ta ba '
Daga qarshe ma ta tattara ta bar gidan wai kyama ciwon yake bata .
Tana cikin ciwo akazo akace mata an samu gawar Naja 'atu a hotel An yayyakata anyimata kisan walaqanci '
Sannan an cire wasu sassa na jikinta sannan aka samu gawar lokacin har ta ru'be ta fara wari ,,
Tashin hankalin mutuwar Naja 'atu ne yasa hawan jini ya kamata Ta kamu da shanyewa r 'barin jiki .
Daga baya Cancer mama ya kamata aka yanke mata nono d'aya "
A yanzu haka maganar da nakeyimiki ko magana bata iyawa domin bakinta ya kar kace ,
Ga Ajimal ya zama mugun d'an daba a halin da ake ciki yanzu haka nan da sati biyu zasu shiga kotu saboda ya yankewa d'an wata mata hannu"
Matar tace bazata yadda ba d'an ta shine kad'ai gatanta shi yakeyimata komai saboda haka tayi qarar sa dan a bimata hakkinta.
Da Aminatu taji wannan labarin seda zuciyar ta ta kamu da ciwo '
Yanzu haka tana jibge a d'aki ba abunda takeyiwa kanta ,,
Hatta juyawa ma bata iyawa idan zata wuni a kwance in ba a juya ta ba bazata iya juyawa ba ,
Gashi babu wanda yake iya shiga d'akin da take saboda wari da d'oyin da takeyi "
Ga wasu manyan tsutsotsi da suke fita daga jikinta harda masu firewa ,
Duk da irin azabar da Amo ta ganawa Rafi 'a seda taji tana tausayin ta "
To baffa tana ina ne ?
Inaso na ganta.......
Hajiya Maryam tayi saurin cewa ,
Ba ganin ta ne ya kawomu ba saboda haka mu fara yin abunda ya kawomu idan yaso koma menene ya biyo daga baya .
Jikin Rafi 'a a sanyaye tace '
Dama baffa ka ta'ba cewa akwai abunda zaka bani wanda ze iya temakamin na gano iyaye na amma baka bani ba Shine yanzu mukazo mu kar'ba '
Eh gaskiya ne dama banyi tunanin aurenki da Gaddafi zeyi nisan kwana bane shiyasa ban baki ba ,
Domin abubuwa ne masu muhimmanci idan na baki kika tafi da su za a iya samun matsala Domin kinsan Gaddafi ba mutum ne me gaskiya ba kuma kowa yasan ya na d'auke d'auke '
Saboda haka ne naci gaba da adanasu domin idan kin dawo na d'auki kayanki na damqa miki "
Amma se labarin 'batar ki naji ,
Nayita nemanki dan nasamu na baki kayanki amma ban samekiba har na haqura na de na nemanki "
Amma kullum cikin jiran dawowarki nake dan na samu na sauqe nauyin da ya rataya a wuya na ,
Na godewa Allah da yau lokaci yayi da zan baki kayanki na rabu da wannan nauyin .
Baffa ya tashi ya shiga d'aki '
Ba a jima ba se gashi ya fito da wata tsohuwar baqar leda me layi layi Ya miqawa Rafi 'a.....
Da sauri Rafi 'a ta kar'bi ledar ta fara bud'ewa "
A tare hajiya Maryam da Alhj Hafiz suka miqe tsaye suna furta kalmar ,
Alhamdulillah.....
Domin abunda suka gani a cikin ledar '
Bargo ne me laushi na jarirai tare da kayan sanyi masu tsada Se d'an kunne da zobe wanda Alhj Hafiz ya saka akayiwa jaririyar sa da kansa .
Hakan yana nufin Rafi 'a y'ar muce Kenan ?
Hajiya Maryam ta furta wasu hawayen farin ciki suna gan garawa daga idanunta ,,
Alhamdulillah Allah na gode maka da ka sake sada ni da y'a ta wacce akayi nasarar rabani da ita tun bata kwana a duniya ba .
Hajiya Maryam da Alhj Hafiz gaba d'aya suka rungume Rafi 'a sunata kuka dagasu har Rafi 'a '
Sosai baffa yaji dad'in ganin yaran Rafi 'a domin yanajin kamar shi ya haifeta .
Ko da suka shiga d'akin da Amo take gaba d'aya kasa zama sukayi saboda wani wari da takeyi da d'oyi .
ga wani yawu me yauqi yana fita daga bakinta '
Rafi 'a ta nemi a kaita asibiti amma hajiya Maryam da Alhj Hafiz basu yadda ba ,,
Se cewa sukayi a barta taci gaba da girbar abunda ta shuka '
Ita kuwa Amo tunda taga Rafi 'a banda kuka ba abunda takeyi ,,
Gafarar ta takeso ta nema amma ta kasa saboda bata iya magana .
Alhj Hafiz yace alfarma d'aya ze iya yiwa Amo ,
Shine ze sa a kaita gidan gajiyayu a jibgeta a can.......
Sannan ze sayawa baffa gida da mota ze had'a masa da jarin million goma kuma ya sakemasa sabon aure "
Suna fitowa daga cikin gidan suka hangi wani d'an shaye shaye yana fad'a da wani me shago Akan yaqi basa kayan maye saboda be biyasa bashin da yake binsa ba.
Rafi 'a tana kallonsa idanunta suka cicciko da hawaye ,,
Innalillahi wa inna ilaihir raji 'un......
Yaya Ajimal kaine ka dawo haka ?
Ta fad'a a cikin ranta saboda ganin yadda gaba d'aya damatsunsa suka mummurd'e Yayi baqi qirin idanunsa sun koma jajaye ,,
Ga wani tarin suma da qasumba da ya bari baya gyarawa kamar wani mahaukaci ,
A taqaice de kamar ba wannan Ajimal d'an gayen da ta sani a baya ba .
Da sauri ta nufi inda yake tana addu ar Allah yasa ya iya gane ta "
Itade tasan ko a wani yanayi tagansa babu makawa zata ganesa ,
Wasu come boys d'in Alhj Hafiz ne suka rufa mata baya .
Malam nawane kud'in kayan mayen naka gaba d'aya ?
Nera dubu biyar da d'ari hud'u ce.......
Jakarta ta bud'e tazaro dubu ashirin ta miqa masa "
Gashi ka d'au dubu biyar d'in ka ka basa iya na shan yazu ka riqe canjin ,
Kuma daga yau ko da kud'in sa yazo kada ka sake bashi kayan maye .
Se a lokacin Ajimal ya juyo da niyyar yin magana "
Se kuma yayi saurin tsayawa yana murtsuka idanunsa domin idan ba gizo sukeyimasa ba kamar Rafi 'a yake gani ,
Ganin ya rufe idonsa ya sake bud'ewa kuma ya sake ganinta tsaye ne ya tabbatar masa da cewar itace ,,
Da sauri ya qaraso ya rungumeta yana hawaye .
Wad'an nan come boys d'in suka shiga dukansa kamar an aikosu '
Rafi 'a tanayimusu magana amma ko sauraran ta basuyi ba ,,
Hakan ne yasa ta koma gurin Alhj Hafiz ......
Abba dan girman Allah kacemusu suyi haquri su kyaleshi su dena dukansa ,
Kyalesu su koyar da shi darasi dan ya gane a ina ze je yayi iskancin sa "
A matsayinsa na bugagge dan shaye shaye harshi waye da ze kai hannu ya ta'ba ki kuma a gaba na ,
Shi d'an iskan gari ne ke kuma kinada daraja saboda haka idan ya ta'ba ki dole ze fiskanci hukunci .
D'an iskan gari kuma d'an shaye shaye bugagge "
Rafi 'a ta mai maita maganar cikin jin d'aci sosai ,
Yaya Ajimal wai yau kai ake jifa da irin wad'annan kalaman kuma saboda ni .
Ta fad'a a cikin ranta tanajin wani irin quna a zuciyar ta ,,
Tana tina yadda Ajimal ya kasance kamilin mutum me nitsuwa a baya '
Ji tayi zuciyar ta na neman tarwatsewa da ta tina saboda ita ya fad'a wannan halin "
Amma ga mahaifinta yana kyamatar sa Kuma yana jifansa da maganganu marasa dad'i .
Hawaye ta share sannan tace a cikin ranta.......
Babu komai yaya Ajimal nasan rayuwa ce ta mayar da kai haka Kuma na d'aukar ma kaina alqawarin sena dawo da kai Ajimal d'in baya "
Me nitsuwa da sanin ya kamata kuma me haquri da adalchi akan mutum koda besanshi ba .
Sannan a Fili tace......
D'an shaye shaye bugagge d'an iskan gari Abba kasan wanene shi kuwa kake kiransa da wad'annan mugayen sunayen?
Tabbas inda kasan waye yaya Ajimal bazaka fad'i haka a kansa ba domin shi mutum ne me hankali da nitsuwa ,,
Ka kirasa da d'an shaye shaye kuma d'an iska amma kasan dalilin waye ya zama haka ?
Ta fad'a tana kallon Alhj Hafiz da jikinsa ya riga ya gama mutuwa domin be ta'ba ganin Rafi 'a a irin yanayin da ta shiga ba .
Seda ta kalli Ajimal tayi wani mur mushi me d'aci sannan tace "
To rayuwarsa ta koma haka ne kawai saboda ni......
Duk da yasan babu alaqar jini a tsakanin mu amma ya riqeni a matsayin qanwar sa ,
Ya bani duk wata kulawa da ya kamata ace yaya ya bawa qanwar sa Kasancewar sa a matsayin d'an shaye shaye a yau ba za'bin sa bane ,
Sadaukarwa yayi irin wanda babu yayan da ze iya Kuma duk dan saboda ni.........
Ya za'bi ya bar mahaifiyar sa da gidansu kawai domin kada yaga kuka na akwai d'an uwan da ze iya wannan kawai saboda d'an uwan sa ne ?
Tun a baya ya bar gidansu saboda ni gashi a yau yana fad'a da rayuwarsa saboda ni amma duniya ta kasa yimasa adalchi ,
Yasha ciyar da ni da hannayensa a lokacin da nake cikin matiqar yunwa "
Wasu lokutan yana iya zama da yunwa domin ni kada na kwana da yunwa '
Iya wannan abunda da yayi a rayuwata beci a kirashi da nagartaccen mutum ba ?
Wallahi Abba a yanzu samun mutum me kyakkyawar zuciya irin ta yaya Ajimal se an tona .
Rafi 'a ta qarasa maganar tana rushewa da kukan takaici ,,
Cikin sanyin jiki Alhj Hafiz ya qarasa ya d'ago Ajimal yana bashi haquri '
Ajimal kam ko ta kansa be biba ya juya ya nufi inda Rafi 'a take da sauri ,
Hannunta ya riqe yana fad'in "
Rafi 'a kin girma kin qara kyau sosai Ina kika shiga kika 'buya ne ?
Babu inda ban zagaya ba ina nemanki meyasa kikayi haka ?
Hannu Rafi 'a ta kai ta shafa fuskar sa tana hawaye '
Yaya Ajimal Kaine ka zama haka ?
Me yasa yaya Ajimal meyasa ka za'bi ka illata rayuwar ka kowa ya kyamace ka ?
Shin yanzu kanajin dad'in kasancewa a haka kowa na gudun ka ?
Yaya Ajimal d'in da na sani a baya kullum shine yake fad'a min nayi haquri kada na ta'ba bari zuciya tafi qarfi na ,
Amma se gashi a yau zuciyar wannan Ajimal d'in tafi qarfin sa .
Wasu hawaye masu yaji suka zubo daga idanun Ajimal domin yasan duk maganar da Rafi 'a ta fad'a gaskiya ne "
Ba zuciya ce tafi qarfi na ba Rafi 'a........
Uban giji ne ya za'bi ya mayar da ni haka domin ya saka miki irin cutarwar da mahaifiyar mu tayimiki a rayuwar ki '
Kibari na rayu a haka domin ina kar'bar hukunci ne bisa lefukan da mahaifiya ta ta aikata ,,
Hakan qaddara ta ce babu yadda na iya da ita .
A'a yaya Ajimal.......
Ka dena fad'ar haka domin Allah baya hukunta wani bisa lefin wani '
Kuma har yanzu baka makara ba kanada damar da zaka gyara rayuwar ka ta nan gaba ,,
Mur mushin takaici kawai Ajimal yayi sannan yace '
Rafi 'a kinga hukuncin Allah koh?
Kinga yadda Amo ta zama kamar ba itace waccar muguwar macen ba "
Ke da take jifa da kalaman 'batanci gashi baki lalace ba se gashi mu yaranta Allah ya jarabcemu .
Duk da kullum tana jifanki da kalaman fasiqanci sede baki ta'ba d'auko abun kunya kamar yadda take fata ba '
Amma kafin Naja 'atu ta mutu har d'an shege seda ta haifa a cikin gidan mu kuma Amo tana kallo ba yadda ta iya da ita .
Bana baqin ciki da lalacewa ta.......
Domin kalaman mahaifiyar mu a kanki ne suka dawo sukayi tasiri a kanmu Ko babu komai zata gane kus kuren ta ta gyara tun kafin ta bar duniya '
A'a yaya Ajimal.....
Ka dena fad'ar haka domin ni ko kad'an ban ta'ba riqe Amo a cikin raina ba koda na minti d'aya ,,
Kuma nima a matsayin mahaifiya na d'auke ta bazanji dad'i ba idan har wani abu ya same ta .
Shiru kawai Ajimal yayi yana kallon Naznin wacce yaga kamanninta da Rafi 'a tayi yawa "
Rafi 'a ta miqamasa Hisham tace ,
y'a y'an ka ne yaya Ajimal Yara nane da nayi aure na haifesu Twins ne sunada irin qaddara ta domin har yau basu san mahaifinsu ba Kuma shima be san suba '
Ajimal ya kar'bi Hisham yana fad'in ,,
Masha Allah yau Rafi 'a ce da twins 'Allahumma bariki Allah uban giji ya rayasu cikin aminci da albarka .
Rafi 'a tace Amin ,
Ya miqa mata Hisham ya shafa kan Naznin sannan yace "
Bari na wuce koh kada na 'bata muku lokaci naga kamar rana ta fara yi sosai .
Ina zaka tafi ?
Wad'an nan sune iyaye na kamar de yadda ka fad'a ni ba shegiya bace kuma wad'an nan sune asali na '
Baka kyamaceni lokacin da banida kowa ba saboda haka nima bazan kyamaceka saboda rayuwar ka ta kasance a haka ba .
Dan Allah kazo mu tafi tare.......
Inaso ka koma mutum kamar da "
Wannan hanyar da ka d'auka ba me 'bullewa bace ,
Rayuwar da ka za'bawa kanka ba rayuwa bace '
Dan Allah ka taho tare da mu zaka sake gina rayuwar ka tayi kyau kamar baya koma tafi baya kyau .
Dak'yar Ajimal ya yadda ze bisu ,
Nan ma seda hajiya Maryam da Alhj Hafiz suka saka baki sannan ya yarda suka tafi ,,
Inin ranar tare da shi Rafi 'a ta wuni sunata hirar yaushe gamo '
Domin Ajimal yana qaunar Rafi 'a har cikin ransa kamar qanwa ya d'auke ta .
Rafi 'a ta kallesa tace , nikam yaya ya labarin Gaddafi ne ?
mur mushin takaici yayi yace , Gaddafi ya haukace sanadiyyar shaye shaye haka ya koma tsince tsince a bola yanzu haka ma ba asan inda yake ba '
ita kuma mahaifiyar sa ta zama gur guwa batada wani gata hatta gurin da zata zauna ma ya gagareta domin Gaddafi ya sayar da gidan da take ciki ya kashewa mata kud'in "
haka ta koma rayuwa a qar qashin gada tana bara har Allah ya kar'bi rayuwar ta .
Washe gari Alhj Hafiz ya qira hajiya Habiba ya tarasu a parlor domin yayimata bayanin kasancewar Rafi 'a y'ar sa ce ,,
Wani dirarren mutum sanye da baqaqen kaya ya shigo ya sanar da Alhj Hafiz wani mutum me qafa d'aya yazo qofar gidan '
Anyi anyi ya tafi yace shi babu inda zeje se an barsa ya shigo ya had'u da shi da hajiya Maryam ,,
Alhj Hafiz yace babu damuwa a qaraso da shi ciki '
Ganin dottijon me qafa d'aya da ya shigo yayi matiqar gir giza hajiya Habiba ,,.
Wani mugun zabura tayi ta miqe tsaye wata zufa tana karyo mata "
Rafi 'a kuwa murna ta shigayi da ganin mutumin domin kallo d'aya tayimasa ta ganesa ,
Wannan mutumin me bara da ya ta'ba temaka mata har ya fara bata labarin Alhj Hafiz ne '
Innalillahi wa inna ilaihir raji 'un.......
Na shiga' uku '
Hajiya Habiba ta fad'a tana d'aura hannunta a kayi .